lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

ADALCIN ALLAH MATSARKAKIN SARKI


Da sunan Allah mai Rahama mai jin kai
Dukkanin godiya da yabo sun tabbata ga Allah buwaya gagara misali
Tsira da amincin Allah su kara tabbata ga fiyayyen halittar wanda aka kira shi da Ahmad a sama a kasa kuma a ka kiraye shi da Muhammad da iyalansa tsarkaka jagorori.
Bayan haka hakika Adalci yana daga cikin Asalai filoli ginshikai da muslunci ya doru kansu kuma yana daga nag aba-gaba siffofin Allah na zati da bai taba rabuwa da su kamar yanda yake asali na biyu cikin Asalai guda biyar Tauhid, Adalci, Annabta Imamanci, Ma’ad
... cigaba

TAKAITACCE SAKO KAN ASALAN ADDINI DA RASSANSA


Da sunan ubangiji tushen Rahama da tautayi da jin kai, dukkanin godiya ta tabbata gareshi mabuwayi tsira da amincinsa su kara tabbata ga fiyayye halittu alal idlak Muhammad da iyalansa tsarkaka.
Bayan haka hakika imani da addini bai samun karfafuwa face sai an fara sanin tushen magangararsa wato Allah mabuwayi cikin zati da siffa, larurar hakata sanya mu rubuta wata yar takaitacciyar Risala da ta kunshi bayani kan Asalan addini da Rassansa ma'ana abubuwa da suke biyo bayan tabbatuwar Asalai.
... cigaba

WANENE YA FI HATSARI TSAKANIN NAFSUL AMMARA DA SHAIDAN?


Da sunan Allah mai rahama mai jin kai
Dukkanin godita tabbata ga Allah ubangijin talikai tsira da aminci su kara tabbata ga fiyayyen halittu Muhammad da iyalansa tsarkaka.
Bayan haka: ta yiwu wannan tambaya ya zamanto ya fada cikin tunanin wasu ba’ari daga matasa sakamakon tarin sanin da suke da shi ko kuma bisa amsa bukatar halittarsu ta son neman tsinkaya kan abin da ya faku daga garesu, ko kuma sakamakon shiga sharar da ba shanu, ko kuma ya kasance daga babin barkwanci wannan tambaya mai hatsari ta fado tunaninsu cewa babu shakka Shaidan jefaffe ya sabawa ubangijinsa ya kuma halaka ya bata, amma to shi wanene Shaidaninsa da ya zama dalilin halakarsa? ... cigaba

YAYA ZAN RUBUTAWA YARA KISSA

Hakika duk wani wayayyen Balarabe marubuci ya na fadake da cewa kissoshin da aka tarjama daga turawan yamma basu bada fa'ida mai kyawu da iayayen yara ke fata yaransu su yi tsinkayi kansu, yaro karami Balarabe yana bukatar kissoshi da suke magana kan duniyar da yake ciki da tafi kusanci da yanayin muhallin da yake rayuwa cik, wacce take magana da harshensa da al'ummarsa da addininsa , wacce take karfafar al'adun mutanensa, saboda haka bakin kissoshi da aka tarjama su basu amfanarwa a wadannan fagage ada muka ambata, duk da nasararsu cikin kwadaitar da yaro cikin yin lafiyayyen tasarrufi, godaddun halaye wasu alamu da akai tarayya cikinsu ga haduffan kissoshi ga kananan yara cikin kowanne yare. ... cigaba

YARO MATASHI TARE DA TSOHO

An hakaito cewa wani mutum tsoho ya kasance yana zaune cikin jirgin kasa tare da `dansa da shekarunsa zasu kusan 25, dukkanin Alamomin nishadi da annashuwa sun bayyana a fuskar wannan matashi ... cigaba

DAGA ZANTUKAN IMAM MUHAMMAM BAKIR A.S


Imami na biyar Muhammad ibn Aliyu Ibn Husaini ibn Aliyu Ibn Abu Dalib mai tsaga ilimin Annabi (s.a.w)
Daga cikin zantukansa (as)
... cigaba

BEGEN SHUGABAN SHAHIDAI YA ZAUTAR DA NIDa sunan Allah mai rahama mai jin kai

Dukkanin yabo da godiya sun tabbata ga Allah tsira da aminci su kara tabbata ga fiyayyen halitta Muhammad da iyalansa zababbu tsarkaka.
... cigaba

SIRRIN SALATI

An rawaito daga wani mutum cewa ya fada cikin matsancin talauci ta yanda ta kai bashin da yake wuyansa ya kai dinare dari biyar ya kuma gaza biya gashi kuma masu kudin sun matsa masa sai ya biya su. ... cigaba

WANI TSONI DAGA HASKE DAGA RAYUWAR AYATULLAHI MUKADDISUL ARDABILI (KS)

An nakalto wata kissa da take bayyana kyawuntar dabi’a da badinin babban Marja’in shi’a a zamaninsa a’amarin da yake sanya mutum ya tsaye ya mamaki; yayinda aka nakalto cewa wata rana yana yawo cikin filin ginin Kabarin Imam Sarkin muminai Ali (as) sai wani mai ziyara ya tambaye shi a ina ne zai wanke kayansa ? yayi masa wannan tambaya ba tareda ya san wanne mutum yake tambaya ba, sai Mukaddisul Ardabili yace masa bani ni in wanke maka da kaina! ... cigaba

HAJJAJU IBN YUSUF!

Wata rana Hajjaju Ibn Yusuf ya fito farauta sai yaci karo da wasu karnuka guda tara kusa da su kuma gani wani karamin yaro wanda shekarunsa basu wuce goma ba, Allah yayi masa baiwar gashin goshi. ... cigaba

Tura tambaya