lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

DAGA CIKIN SIRRIKAN TARON MINA

DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI

Dukkanin godiya da yabo sun tabbata ga Allah ubangiji talikai tsira da aminci su kara tabbata ga Muhammad da iyalansa zababbu tsarkaka.

Bayan haka:

1-cikin rana ta goma ga watan zul hijja mahajjata za su shiga mina wanda wani kwazzzabo ne tsakanin kwazazzabon Muhassar abayan mash'arul haram tsakanin Makka na da nisan kilomita 6 tsakankanin manyan duwatsu biyu wadanda haddin tsayinsu ya kai mita dari biyar da fadi- domin jifan Jamarat Akaba (Shaidan mafi girma) sannan kuma a gabatar da abin hadaya a yanka sannan daga baya a yi aski sannan mahajjaci zai wanzu a Mina har zuwa rana ta 12 a wani fadin har zuwa rana ta 13, a mina zai dinga kwana a nan ne zai yi jifan Shaidanu karo uku ma'ana rana ta 11 zuwa ta 12 ta yiwu ya kai ta 13 ga wanda ya zauna har darensa. ... cigaba

MASH'ARUL HARAM

1-an kiraye shi da wannan suna na Mash'arul haram a Muzdalifa sakamakon an ciro shi daga Kalmar zulfa (kusanci) ko kuma ace (taro), bawa na kusanta bayan saninsa da Allah matsarkaki ya kara fadaka da nauyin da ke kansa, ya tsinkayi yardar Allah da zuciyarsa, kamar yadda a wannan bigire yana haduwa da`yan'uwansa talakawa cikin Mash'arul haram, lalle yana kusa kusa da makka mai karamci. ... cigaba

SIRRIKAN ARAFAT



DA SUNAN Allah MAI RAHAMA MAI JIN KAI

Dukkanin godiya da yabo sun tabbata ga Allah mai rainon talikai, tsira da aminci su kara tabbata ga fiyayyen halitta Muhammad da iyalansa tsarkaka.

Allah matsarkaki madaukaki yana cewa:

(لَيْسَ عَلَيْكُمْ جُنَاحٌ أَن تَبْتَغُوا فَضْلاً مِن رَبِّكُمْ فَإِذَا أَفَضْتُمْ مِنْ عَرَفَاتٍ فَاذْكُرُوا آللهَ عِنْدَ آلْمَشْعَرِ آلْحَرَامِ وَآذْكُرُوهُ كَمَا هَدَاكُمْ وَإِن كُنْتُمْ مِن قَبْلِهِ لَمِنَ آلضَّالِّينَ * ثُمَّ أَفِيضُوا مِنْ حَيْثُ أَفَاضَ آلنَّاسُ وَآسْتَغْفِرُوا آللهَ إِنَّ آللهَ غَفُورٌ رَحِيمٌ [1] .(

Allah matsarkaki da daukaka na cewa: babu laifi kanku ku nemi falala daga ubangijinku idan kuka kwararo daga Arafat ku ambaci Allah wajen masha'arul harami ku ambace shi kamar yadda ya shiryar daku duk da cewa gabaninsa kun kasance daga batattu* sannan ku kwararo ta inda mutane suka kwarara ku nemi gafarar Allah lalle Allah mai gafara ne mai jin kai.

1-daga cikin wararen ibada masu alfarma akwai Arafat wadda ita wani bigire ne mayalwaci da yake tsakanin makka da mina da nisan kilo mita 22 cikin kudu maso gabas daga makka nada nisan kilo mita 18 murabba'i kusa kusa, wuri ne da mahajjata ke tattaruwa a rana ta tara ga Zul hijja daga farawar zawalin rana ya zuwa faduwarta ana kiran wanna taro da sunan tsayuwar Arafat, lalle shi yana daga cikin rukunan hajji.

«الحجّ عرفة ليدلّ على عظمة يوم عرفة وكأنّه هو الحجّ بتمامه ، فمن تركه متعمّداً بطل حجّه .

2-ya zo cikin ingantaccen hadisi daga Annabi (s.aw) shi hajji Arafat ne domin ya yi nuni ya zuwa ga girman ranar Arafat, duk wanda ya barshi da gangan lalle hajjinsa ya gurbata.

3-an kiraye ta da Arafat sakamSkon kasarta tafi daukaka daga waninta daga wuraren ibada daga Mina da Muzdalifa da Harami mai daraja.

4- an kiraye ta da wannan suna sakamakon fadin Jibrilu ga Adamu (as) da Ibrahim (as) da Manzon Allah (s.a.w) : ka san ayyukan ibadarka cikin hajji.

5- cikin Arafat akwai wani dutse da aka fi saninsa da dutsen rahama da dutsen Rafat a can samansa akwai wani farin sawu wanda yake ishara gameda abin da ya zo cikin riwaya da ke hakaitar da haduwar Adamu da matarsa Hauwa'u bayan saukowar su wannan duniya da rabuwar su zamani mai tsayi suna ta kuka kan kuskuren da suka aikata sai Allah ya amsa musu ya gafarta musu to shi ne suka hadu a wannan bigire mai albarka, daga haka ne aka kiran wajen da sunan Arafat, Allah ne mafi sanin daidai.

6- saharar Arafat na ishara ranar Arafat kan hadin kai da soyayya karkashin haimar Allah da kuma saharar ranar kiyama da tashin mutane da fitowarsu daga kabari zuwa ga ubangijinsu suna ta gudu suna addu'a suna kuka da shashshaka da neman fakewa da ubangiji mai girma da daukaka.
... cigaba

SHAHARARRUN MALAMAN DUNIYAR MUSLUNCI

Wayewa da cigaban muslunci, hakika wayewar muslunc cike take da haifar da nasarori cikin tsahon zamani, itace wayewar da ta kasance wayewa ta mutum ta habbaka da cika da cigaba daidai lokacin da duniyar turawa ke cikin duhun kai da jahilci, duhu da jahilci da talauci sune mafi bayyanar alama a cikin kasashen turawa, har yanzu galibin cigaba kirkire da nasarorin ilimi sun bubbugo daga malaman muslunci, ana karantar da nazariyoyinsu cikin jami’o’in kasashen turawa da na larabawa, ana la’akari da su matsayin masdarori da tushen ilimi mai muhimmancin gaske, wayewar muslunci ta bada gudummawa cikin tarihin habbakar tunani da ilimi, tsahon tarihi wasu adadi daga malamai daga muslunci sun bayyana wadanda suka bada gudummawa cikin wayewar muslunci, sai ya zamanto iliminsu ya fantsama ya yadu cikin sassa daban-daban na duniya lamarin da ya kai ga yaduwar sunayensu da daukakarsu. ... cigaba

MUTUMIN DA YA NEMI TAIMAKO

Daidai lokacin da yake bude hutunan rayuwar da yayi a zamanin da shige ya shude yana kuma tuna kwanakin ya barzu a bayansa, kamar misalin kwanakin bai kasance yana iya samarwa da kansa da matarsa da yayansa abincin da zasu ci a yini ba, a cikin wannan hali sai ya fara jin karar murya daga wani mai kwankwasa kofa yayi ta jin wannan kara har sau uku lamarin da ya tasar da fata da sa rai da ya ceci rayuwarsa daga kangin talauci ... cigaba

DAN KASUWA DA MAI KETARA


Malikul Ashtar ya kasance dogon mutum mai tsayi yana sanya da doguwar riga da rawani, idan ka ganshi zaka alamomin gwagwarmaya da yaki duk sun bayyana a fuskarsa, sadaukantaka da jarumtaka duk san bayyana a fuskarasa.
... cigaba

MALAMAI KAN TAFARKIN HUSAINI

An haifi Ayatullahi Shaik Muhammad Husaini Sibawaihi Ha’iri a shekarar 1306 hijiriya a birnin Karbala mai tsarki ... cigaba

ALLAH YANA GANI NA A KOWANNE WAJE


An hakito cewa wata rana wani tsoho yayi niyyar gwada kaifin basirar dalibansa, sai ya tafi wajen samari hudu ya baiwa kowannensu tuffa ya nemi su ci wannan tuffa a wurin da babu wanda zai gansu, ... cigaba

MA’ANAR ABOTA



Munana zato tsakanin abokan juna, a wani lokaci mu kan canja yanayin mu’amalar mu da abokan mu ba tare da wani kwakkwaran dalili ba sananna sai daga bayan idan mun yi bincike kan sababi sai mu samu babu abinda ya jawo haka sai munana zato da rare-rayen da muka kirkira muka gasgata su su ka wayi gari hakika muka zama muna gasgata su muna biye musu, sakamakon haka muka zamanto muna bin wani ayyanannen suluki da uslubi cikin mu’amalar mu ba tareda Ankara ba, alakokin da suke tsakanin mu suka munana matuka, shi aboki mutum ne kamar kowa yana kuskure yana kuma yin daidai, yana iya zamantow aya keta wani yanayi da ba zai iya bayyana abinda abinda yake cikin zuciyarsa gareka ba ko ga waninka, ta yiwu nan gaba ya fada maka dalilin canjawarsa, saboda haka ka tausasa masa ka bashi uzuri sau saba’in duk sanda ka ga ya aikata kuskure ko duk sanda kaga wani abu da zai iya bata alakarku ya faru, cikin wannan fage wata kissa daga cikin kissoshi ta burgeni cikin mu’amala tareda aboki da bayanin ma’adanin mutum bayan sauyawar yanayi da halaye, san naji ina kaunar in nakalto muku wannan kissa. ... cigaba

SHIN MUTUM YANA DA ZABI KO KUMA AN MASA TILAS NE_TAREDA AYATULLAH ASSAYID ALI-ALAWI

Idan kuna nufin zabi cikin Kalmar (mukayyar), to sai muce muku: Allah ta’ala yayi umarni da ayi masa `da’a , kuma zai bada lada kan yi masa `da’ar, haka kuma yayi hani kan aikata sabo kuma zai yi ukuba kai, sannan ya baiwa bawansa zabi cikin abinda yake aikatawa, idan ya aikata alheri sai ya ga alheri, idan kuma ya aikata sharri to nan zai ga sharri.
Daga cikin abinda ya zo cikin littafin Usulul Kafi cikin (babin Alkairu wa Sharru):
... cigaba

Tura tambaya