lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

(Zinare mai tsada cikin sanin sarkin muminai Ali (as


Akwai wata ma’arifa ta jamaliya ga Ahlil-baiti (as) : misalin Salmanu muhammadi (rd) yana tsinkayar ta, lallai shi ya san kyawuntar sarkin muminai daga abin da Abu Zar bai sani ba tare da cewa babu banbanci tsakaninsu cikin imani, lallai Salmanu yana da darajoji goma sai dai cewa tare da haka da Abu zar zai san abin da yake cikin zuciyar Salmanu da sai ya kafirta shi lallai da yace Allah ya jikan makashin Salmanu, daraje ce guda daya amma fadinta yakai nisan da ke tsakanin imani da kafirci, ya kai nisan sama da kasa.

Amma ma’arifa kamaliyya ga sarkin muminai Ali amincin Allah ya kara tabbata gare shi to abin da manzon Allah (s.a.w) ya fada yana shiryarwa zuwa gare shi kan Ali (as) :

يا عليّ لم يعرفک إلّا الله وأنا

ya Ali babu wanda ya sanka face Allah da ni.

 

Babu wanda ya san Allah sai manzonsa sirrin sirrin samuwa kudubin da’irar halittu, digon kan harafin ba’un din bismillah, cibiyar duniyoyi bayan manzon Allah (s.a.w) wanda aka tsago sunansa mai albarka daga Aliyul A’ala mafi tsarkakar haske daga hasken muhammadi, sai cimma daukakada kamalarsa ya yaye duhu da kyawunsa, dukkanin halayensa sun kyawunt, sai ya shiryar da mutane da girmamarsa, kuyi salati gareshi da dan baffansa da iyalansa, Ali amincin Allah yak ara tabbata gareshi mutum ne sai dai cewa ubangininsa ya yi tajalli cikinsa ya bayyana duk wanda yayi inkarin haka ya kafirta, lallai shi ne kammalallen mutum wanda cikinsa kyawawan sunaan Allah sukai tajalli da siffofinsa madaukak, sai ya kasanse mabayyanar tauhidi, kamar yanda ya kasance cikin gasarar annabta da tacewa da madarar wilaya, dukkanin abin da ake fadi cikin falalolinsa da kyawawan halayensa da daukakar mukaminsa lallai bai daya bisa dari ba daga gare su.

Ali waliyin Allah ne hujjarsa ne halifansa manzon Allah shugaban wasiyyai cikinsa sunayen ubangijinsa sun yi tajalli, yana dauke da dukkanin siffofin annabi (s.a.w) da ilimummukansa da sirrikansa da aka ajiye cikinsa in banda annabta da manzanci, shi mai kira ne mai shiryarwa zuwa ga tafarki madaidaici, shi tsani ne zababbe bayan manzon Allah cikin sadar da fairar Allah zuwa ga bayinsa, shi hanya ce mikakka madaidaiciya labari mai girma, gare shi ilimin littafi da faifaice bayani :

 

فاسألوا أهلَ الذكرِ إنْ كُنْتُمْ لا تَعْلَمون

Ku tambayi ma’abota Ambato idan kun kasance basu sani ba. 

Tura tambaya