lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

Imam Bakir (as) babban malamin daga gidan Annab (s.a.w)

  Da sunan Allah mai rahama mai jin kai

Dukkanin godiya tabbata ga Allah tsira mara iyaka ya kara tabbata ga manzon rahama da mutanen gidansa (as)

Shin ilimi na shi kadai yana wadatarwa ?

Tana iya yiwuwa samun ba’arin wasu ilimummuka da ma’arifofi ya kasance abu mai sauki ko kuma mai wahala, dukkanin wanda ya zage dantse ya nema zai samu nasibi mai yawa daga garesu, sai dai cewa abu mai wuya anan shine ya hada ilimi da takawa da kyawawan dabi’u, ya zamanto  ya bayyanar da ilimin a aikace ta yanda zai wayi gari ilimi mai amfani kuma tsani don gano tabbatattun abubuwa yana mai nesantar jayayya da riya da jidali mara amfani da karkataccen tunani,

Ita rai mai yawan umarni da munanan ayyuka ce tana kora karfin iko da baiwar da mutum yake da ita zuwa ga sha’awar da ta  karkacewa gaskiya da alheri da adalci a mafi yawan lokuta, da wannan ne ilimi ke wayar gari ilimi mai cutarwa mara alfanu.

Me yafi da cewa ga wannan rai ta yi zurfin tunani da duba cikin Kalmar Imam Ali (as) da yake cewa:

يا طالب العلم ذو فضائل كثيرة ، فراسه التواضع ، وعينه البراءة من الحسد ، واذنه الفهم ، ولسانه الصدق ، وحفظه الفحص ، وقلبه حسن النية ، وعقله معرفة الاشياء والامور ، ويده الرحمة ، ورجله زيارة العلماء ، وهمته السلامة وحكمته الورع ، ومستقرة النجاة ، وقائدة العافية ، ومركبة الوفاء ، وسلاحه لين الكلمة ، وسيفه الرضا ، وقوسه المداراة ، وجيشه محاورة العلماء ، وماؤه الموادعة ، ودليله الهدى .

Ya kai mai neman ilimi ma’abocin falaloli masu tarin yawa, kirdadonsa tawali’u, idonsa ya kubuta daga hassada, kunnensa ya kasance kunnen fahimta, harshensa harshen gaskiya, haddarsa bincike, zuciyarsa zuciya ta kyakkyawar niyya, hankalinsa na sanin abubuwa da lamurra, hannunsa hannun rahama, kafafunsa na ziyartar malamai, himmarsa kan zaman lafiya, hikimarsa tsantseni, tabbatuwa tsira, jagoransa lafiya,mahayinsa cika alkawari, tausasa harshe makaminsa, yarda ita ce takobinsa, bi a sannu shine bakansa, tattaunawa da malamai shine sojojinsa, bankwana shine masaukinsa, shiriya itace dalilinsa.

Saboda ilimi mai alfanu shine wanda yake cudanye da da siffofi madaukaka da kyawawan dabi’u kuma shine wanda ake ganin kufaifayinsa cikin ayyukan mutum, shine kuma mai dora mai nemansa kan hanyar neman ma’arifa, da daukakar suluki, daga cikin wadanda wadannan siffofi sukai tajalli cikinsa shine Imam Muhammad bn Ali bn Husaini bn Ali bn Abu Dalib wanda akewa lakabi da Bakir (as) wanda cikin sha’aninsa Muhammad bin Dalhatu shafi’i yake cewa: Muhammad bn Ali Bakir shine wanda ya keta ilimi ya kuma tattaro shi ya kuma shaharantar da shi ya daukaka shi, kuma shine mai ciyar da mai tatsarsa da mai tsotsa, zuciyarsa ta tsaftata, nafsunsa ta tsarkaka, dabi’unsa sun daukaka, ya raya lokutansa cikin da’a ga Allah, kafafunsa sun tsaya kyam cikin tsoran Allah, alamomin tsarkakuwa da zabuwa sun bayyana cikinsa.

Ilimummukan Imam Bakir (as) sun doru kan cikin fuskoki masu zuwa kamar haka:

1-yada ilimummukan addini, da haskaka kwakwae da zukata da ilimummukan ubangiji.

2- kure masu shakkar akidun muslunci da masu neman kawo rudu da kuma cutar da Ahlil-baiti (as) ta hanyar bijiro shubuhohi

Hakika Imam Bakir (as) ya wa’azantar da musulmai ya kuma bada amsa kan tambayoyin masu neman kawo shubuha, ya kuma bayyana iyakoin shari’a, ya fitar da alamomin addini da hujjojin yankan shakku, wat arana an tambaye shi: yaya ka wayi gari? Tare da kasantuwar rashin bayyanuwar ma’anar tambayar mai tambaya sai ya bashi amsa da cewa: mun wayi garin cikin nutsewa cikin ni’imomin ubangiji, cike da zunubai, ubangijinmu na ta kaunar mu da ni’imomi, amma kuma mu muna ta fusata shi da aikata sabo, mu ne mabukata gareshi shi kuma ya wadata daga garemu.

Mai yafi kama daga abinda babansa Ali bn Husaini Zainul Abidin (as) ya fadi cikin addu’ar sahar: zunubanmu suna gabanka, muna neman gafararka ya Allah kuma muna tuba gareka, kana ta kaunar mu da ni’imomi mu kuma muna kishiyantarka da da aikata zunubai, alherinka na sauka garemu mu kuma sharrinmu na ta hawa zuwa gareka.

Hakika wannan wasu yan gajerun jumloli ne sai dai cewa sun bada mafi cikar amsa cikin mafi bayyanar zance, sun kunshi nuna godiya da ikirari da gazawa.

Wani lokaci An tambayi Imam Bakir (as) wane ne yafi kowa girma cikin mutane? Sai yace wanda bai ganin kimar duniya.

  Haka wani lokaci yace: wanda bai kulawa bai kuma damnuwa da hannun wanda duniya ta kasance. Gajeriyar jumla da ta iyakance falaloli da asasin daukaka a lokacin da mutum yake kau da gani zuwa yunbu, ya kuma nesanta kansa daga hassada zaka same shi yana kyalkyala cikin samaniyar badini, yana mai kudurce tunani da suluki da cewa dukkanin tarkacen duniya basu iya baiwa mutum kima da daraja, ma’auni cikin falala: tsoran Allah shine hanyar daukaka da karama, Jabir bn Yazid Ju’ufi yana tambayar Imam (as) mene ne ma’anar

 (( لا حول ولا قوة الا بالله )) ؟

Sai Imam (as) ya bashi amsa cikin wasu kidaitattun kalmomi da suke kasancewa cikin mafi kammaluwar bayani

معناه لا حول لنا عن معصية الله عز وجل.

Ma’anarta shine babu tsimi garenmu daga sabon Allah Azza wa Jalla.

Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, jumloli ne biyu da suke sauka kullin mai girman gaske cikin tunanin mutum shine mas’alar jabaru da tafwidu wadanda karnoni suka tsawaita kan bahasi cikinsu da dimauta kan neman fahimtarsu.

Bada ban Allah ta’ala ya baiwa mutum zabi ba ya yalwata shi ya kuma bashi yanci da mutum bai samu damar sabonsa ba, bada ban ya shiryar da shi ba da bai sami damar yi masa biyayya ba, kowanne lamari yana karkashin mashi’ar Allah, babu jabaru babu tafwidu kadai dai wani lamari tsakanin al’amura biyu, ba a tilasta bawa kan sabo ba kadai shi yanada zabi cikin sabo kuma an jarraba shi cikin iradarsa wadda Allah yayi masa kyautar ta, ukuba bayan aikata sabo wani lamari da hankali ke karbarsa bari yana wajabta shi yana kuma maraba da shi.

Ba a tilasta bawa kan da’a ba, kadai dai shiriya ce da ta game komai

 (( ليهلك من هلك على بينة ويحيى من حي عن بينة ... )) الانفال / 2 ...

Domin wanda zai bata ya bata kan hujja wanda kuma zai rayu ya rayu kan hujja.

Saboda haka shi lada kan da’ar Allah wata falala ce daga Allah da hankali yake maraba da ita.

Zamani Imam Bakir (as):

Zamanin da Imam Bakir (as) ya rayu ya fifita da kasantuwarsa zamani da aka samu budewa kan sakafar yammaci da falsafar kasar girka (grece) sai ya zamanto yankakkun ilimummuka da munanan sakafofi masu rudarwa da suke dauke da shubuhohi masu tarin yawa da shakku masu ban mamaki masu karkarewa zuwa ga inkarin bayyanannun lamurra da mugalada cikin badihiyat da kullewa cikin mas’alolin akida da zamantakewa sun fara kawo duniyar muslunci matsala.

 Sakamakon kasantuwar musulmi cikin zamanin mulkin umayyawa da kuma basu tsotsi ilimummukan muslunci kamar yanda ya kamata ba sai ya zama an sami karkata cikin wasu jama’a masu tarin yawa daga cikinsu sun bayyana da taken makarantun falsafa da zaurukan tunani da akidu.

Wannan Kenan sannan an nemi Imam Bakir (as) baban masani cikin Ahlil-baiti da ya tashi tsaye kan mas’aloli masu hatsarin gaske ta yanda a zamaninsa tambayoyi daga shi’a da sunna suke nufo shi, a wasunsu zaka samu wani nema sanin fikihu da fahimta, wani yana yin tambayar ne domin jarraba Imam da tabbatar da ingancin imamancinsa, wasu kuma kanyi tambayar ne kawai don takura masa da zubar da kimarsa daga idanun mutane da rusa imamancinsa wacce hadisin Annabi (s.a.w) ya nassanta ta, kamar yanda malami daga mazhabar hannafiya shail Salmanu kanduzi cikin littafinsa (yanabi’ul muwadda) ya ambaci hakan, hakama shaik Hamawini ya kawo hakan cikin (Fara’idul Simdaini) haka mawallafin (Kifayatul dalib) yayi bayanin hakan cikin babi na 76 da cewa lallai Annabi (s.a.w) ya bada labarun sunayen wasiyyansa 12 tareda ambaton sunayensu da lakubbansu daga cikinsu akwai Imam Bakir (as) kamar yanda ya zo cikin riwayar ibn Abbas da Jabir ibn Abdullah Ansari wand aya kasance manzo Allah (s.a.w) ya gaya masa:    

(( يا جابر ، يوشك ان تبقى حتى تلقى ولدا لي من الحسين يقال له : محمد يبقر علم النبيين بقرا ، فاذا لقيته فاقراه مني السلام )) المناقب / لابن هر اشوب ج 2 ص 2

Ya Jabir ya kusa ka wanzu har sai ka hadu da dana daga Husaini da ake kiransa da Muhammad zai keta ilimin Annabawa ketawa, idan ka hadu da shi ka ce ina gaishe shi.

وفي رواية اخرى : (( ياجابر ، يوشك ان تلحق بولد من ولد الحسين اسمه كاسمي ، يبقر العلم بقرا ( اي يفجره تفجيرا ) فاذا رايته فاقراه مني السلام . قال جابر : فاخر الله مدتي حتى رايت الباقر ، فقراته السلام عن جده رسول الله ( صلى الله عليه واله ) سبا الذهب – ص 72

A wata riwayar kuma ya zo cewa: ya Jabir ya kusa ka riski wani yaro daga yayan Husaini sunansa irin suna na, zai tsaga ilimi tsagawa, idan ka hadu da shi ka gaishe mini da shi,sai Jabir yace: sai Allah ya tsawaita rayuwata har sai da na ga Bakir, sai gaya masa sakon gaisuwa daga kakansa manzon Allah (s.a.w)

Amma babban malamin tarihi Yakubi ya rawaito cikin tarihinsa j 3 sh 63 cewa jabir yace:

جابر قال : قال لي رسول الله صلى الله عليه واله : ( انك ستبقى حتى ترى رجلا من ولدي ، اشبه الناس بي اسمه على اسمي اذا رايته لم يخف عليك ، فاقره مني السلام ) .

Manzon Allah (s.a.w) ya gaya mini cewa: lallai kan zakai tsawon rai har sai ka ga wani mutum daga yayana wanda yafi kow akama da ni sunanmu iri daya idan ka hadu da shi ka gaida mini da shi.

A daidai lokacin da zaka samu Muhammad bn Dalhatu shafi’i cikin littafinsa (Madalibul Su’al) sh 81 ya rawaito wannan riwaya cewa:

ان الرسول الله ( صلى الله عليه واله ) قال لجابر : ( ياجابر يولد لابني الحسين ابن يقال له علي ويولد لعلي ابن يقال له محمد ، ياجابر اذا رايته فاقراه مني السلام ) .

Manzon Allah (s.a.w) ya cewa: Jabir: ya Jabir za a haifarwa dana Husaini wani da` da ake kirsansa da Ali sannan za a haifawa Ali da` da ake kiransa Muhammad, ya Jabir idan ka ga shi kace ina gaishe shi.

Hakika ya kasance mai tsaga ilimi da keta shi ta yanda ya amsa dukkanin tambayoyi tareda dukkanin banbancin manufofin yinsu, ya kuma kunyata dukkanin kalubalen makiya, sannan ya haskaka kwakwalen dalibai da masu neman gaskiya da ma’arifa, ya kuma ruguza dukkanin shubuhohi da shakku.

Hakika amsar Imam ga sakon gaisuwar manzon Allah (s.a.w) da fadin

 ( سلام ربي عليه )

Amincin ubangijina ya tabbata gareshi.

Ta fifita:

1-kasantuwarta gajeriyar amsa cike da bayyanu da fituwa.


Tura tambaya