lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

Adalci hadafin daukacin addinai


 

Hakika adalci shi ne himmar dukkanin mutumin kirki a tsawon tarihi, a kowanne zamani baka rasa masu ji da ganin larurar samar da adalci wanda shi ne burin dukkanin mutane tun farkon duniya har zuwa wannan zamani namu, kamar yanda masu zurfin tunani cikin mutane da masana falsafa da hikima sun yi bincikai cikin wannan batu da ya bayyana himmatuwarsu.

Saboda haka ne bahasi ya zurfafa kan maudu'in adalci da adalci cikin zamantakewa tun zamanunnukan masu nisa da suka gabata zuwa wannan zamani, an kuma gabatar da nazariyoyi cikin wannan fage, sai dai cewa gudummawar addinai ta kasance gudummawa ta musammam, ma'ana hakika abinda addinai suka Ambato dangane da adalci suka kuma nufe shi da himmatuwa kansa ya kasance wanda babu misalinsa, misalin wannan bada himma da addinai suka yi bama ma iya ganinsa cikin ra'ayoyin masana falsafa da hikima da malamai.

Domin mutane su tsayu da adalci

Da farko, da shaidawar kur'ani hakika hadafin addini shi ne tsayar da adalci.

لَقَدْ أَرْسَلْنَا رُسُلَنَا بِالْبَيِّنَاتِ وَأَنزَلْنَا مَعَهُمُ الْكِتَابَ وَالْمِيزَانَ لِيَقُومَ النَّاسُ بِالْقِسْطِ (الحديد: 25).

Hakika mun aiko manzanninmu da hujjoji kuma mun saukar da littafin tare da su da mizani domin mutane su tsayu da adalci.

Babu shakka cewa wannan aya tana bada labari kan hadafin aiko manzanni da saukar da litattafai da halarto da hujjoji, ma'ana dalilai masu gamsawa da shakka bata iya kalubalantarsu, daga cikin abinda annabawa suka bijiro da shi mutane su tsayu da adalci.

Tabbas babu shakku da cewa tsayuwa da adalci da dukkanin abinda rayuwar duniya ta doru kansa da jama'a da daidaikun mutane share fage ne zuwa ga wancan babban hadafi da ya ratayu da halittu:

وَمَا خَلَقْتُ الْجِنَّ وَالْإِنسَ إِلَّا لِيَعْبُدُونِ‏ (الذاريات: 56)

Ban halicci mutum da aljani sai don su bauta mini.

Ma'ana bauta itace asasi da tushen hadafin halitta da zaman mutum bawa a gurin Allah ta yanda ake kidayata mafi daukakar kamala, sai dai cewa kan hanya zuwa kaiwa ga hadafi, mamufar aiko da manzanni da annabawa wacce daga cikin ta shi ne wancan abun wanda da wannan aya ta bayyana shi a sarari, sannan akwai wasu wuraren daban cikin wasu ayoyin da suke ishara zuw aga sauran haduffan aiko manzanni ta yanda zamu iya tattara su tare, saboda haka mafi bayyanar hadafi shi ne adalci, hadafin gina hukumomi da wayewa da dukkanin motsin mutum cikin zamantakewa shi ne adalci.

Kowanne lokaci annabawa suna fagen daga

Wani fifiko da addinai suke da shi ne cewa hakika annabawa (as) tsawon tarihi sun kasance tare da wadanda ake zalunta, hakika sunyi jihadi domin tsayar da adalci, ku duba sosai zaku hakika kur'ani yayi bayani karara cewa annabawa (as) sun kasance suna kalubalantar dawagitai dan yan jari hujja, su biyun dukkanin suna daga ajin azzalumai, mawadata yan jari hujja sun kasance suna kishiyantar annabwa.

وَمَا أَرْسَلْنَا فِي قَرْيَةٍ مِّن نَّذِيرٍ إِلَّا قَالَ مُتْرَفُوهَا إِنَّا بِمَا أُرْسِلْتُم بِهِ كَافِرُونَ‏ (سبأ: 34).

Bamu aika wani mai gargadi cikin wata alkarya ba face mawadantata sun ce lallai mu mun kafircewa abinda aka aiko da shi.

Bamu taba samun wani annabi ba face mun samu mawadata na kiyayya da shi shima kuma annabin yana kishiyantarsu, haka halin mutane da rike da madafan iko yake kasancewa.

Sannan ita Kalmar dagutu ma'anarta ta tattaro dukkan wadannan, saboda haka dukkanin annabawa (as) zaka same su suna tare da raunana wanda ake zalunta cikin yaki tsakanin azzalumi da wanda yake zalunta, annabawa sun kasance suna shiga fagen daga domin tabbatar da adalci da yakar zalunci, wannan abu ne da babu misalinsa.

Hakika masana hikima da ma'abota zurfin tunani sun yi magana dangane da adalci sai dai cewa sun wadatuwa da magana kadai ba a ganinsu a fagen daga.

Annabawa (as) basu kasance misalin haka ba bari dai sun kasance suna bijirar da kawukansu ga hatsari har ta kai ga yan jarin hujja su kan tambaye su mene ne ya sanya kuke kasancewa cikin bangaren wadanda ake zalunta, sun kasance suna neman annabawa (as) da su yi watsi da taimakon wadannan miskinai raunana, sai ayar kur'ani mai girma ta sauka da bayani:

وَلَا أَقُولُ لِلَّذِينَ تَزْدَرِي أَعْيُنُكُمْ لَن يُؤْتِيَهُمُ اللّهُ خَيْرًا اللّهُ أَعْلَمُ بِمَا فِي أَنفُسِهِمْ إِنِّي إِذًا لَّمِنَ الظَّالِمِينَ‏ (هود: 31)

Kuma b azan cewa wadanda idanunku suke kallonsu a raine ba Allah ba zai basu alheri ba Allah shi ne mafi sani da abinda yake cikin rayukansu lallai idan nayi nima na kasance daga azzalumai.

Wannan aya tana bada labarin amsa da annabi Nuhu (as) ya bawa masu jayayya da shi cikin wannan fage, ga wadannan mutane miskinai ababen tausayi da suka haramtu daga samun adalci, kuma sun kasance na farko-farkon wandanda sukai imani da annabawa.

Karshen lamari yana cikin tabbatuwar adalci

Dukkanin addinai sunyi ittifaki kan cewa karshen lamari dai shi ne wannan motsi na tsawon tarihin mutum zai cika da fata da adalci, ma'ana karshe dai za a samu wani zamani da zai kasance na adalci da tabbatuwar addini kammalalle, ya zo cikin addu'ar da ake karantawa bayan ziyarar Alu Yasin

«يملأ الله به الأرض قسطاً وعدلًا» أو «عدلًا وقسطاً»،

Allah zai cika kasa da shi da Adalci da daidaito.

Kamar yanda ta cika da zalunci da danniya. Dukkanin annabawa (as) da baki dayan addinai sun yi ishara zuwa ga wannan karshe sun karfafa kai, saboda haka lallai shi yana cikin mafara yana kan hanya yana kuma karshe, baki dayan annabta ta jingina ne kan adalci, wannan wani abu ne da babu irinsa.

Akwai wata nukuda mai muhimmancin gaske da ya kamata mu yi ishara zuwa gareta shi ne cewa adalci yana da wani bigire na musammam cikin juyin-juya halin muslunci a Iran-wacce ta kasance karkashin hasken motsin addini.

Hakika an samu nasarar cimma abubuwa da daman gaske tun farkon nasarar wannan juyin-juya hali, sai dai cewa abinda muke bukatuwa gare shi kuma muke sa'ayi kansa da tabbatuwarsa shi ne adalci da dukkanin ma'anarsa, mu bamu son mu ga rashin adalci yana da wani bigiren zama cikin al'umma

 


Tura tambaya