lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

Wasiyyai da tsarkakakken tsatso

 

idan cikamakin annabawa shugaban manzanni Muhammad (s.a.w) rahama ne ga talikai, lallai kadai shi wani yanki ne daga rahamar Allah mudlaka ba tared karshe ba, lallai Allah yana kare mutumcin bawansa gaban halittu idan ya kasance daga ma'abota raya daren lailatul kadari, amma wanda ya aikata zakkewa zunubi da sabo, ya munana littafin rekodin din ayyukansa, lallai ya yi kokari ya tuba cikin wannan dare kamar yadda ya tuba a daren farkon lailatul kadari, sannan ya yi ado da da'ar ubangijinsa ya kuma nemi gafararsa, lallai Allah zai gafarta masa zai kuma karbi tubansa zai masa sassaukan hisabi, ba zai tona asirinsa ba gaban mutane bari dai zai suturta shi ya rufa msa asiri ya bayyana kyawawansa, lallai shi wannan dare dare ne na tsafatace kai da ado da kyawawan dabi'u, lallai Allah zai masa gafara zai sanya kasa ta manta daga zunubansa, kamar yadda yake mantar da gabbansa, bari dai rahama Allah mai yalwa zata mamaye shi har ta kai ga Allah ya mantar da shi zunuban da ya aikata sai ya zama bai jin kunyarsa kansa, lallai wanda ya tuba daga zunubi kamar misalin wanda bai taba aikata zunibi bane, sannan Allah zai sanya shi cikin aljanna zai shiga, ba zai dinga tunawa da zunubinsa ba domin shi tunawa da zuna na kona da sanya bakin ciki, ita kuma aljanna cikin ba babu kunan rai babu bakin ciki babu damuwa, zai kasance kamar ranar da mahaifiyarsa ta haife shi tsarkake tsarkakakke kiyayayye daga zunubi.

Kan kowanne mutum wajibi ya zama mabayyanar lailatul kadari lokacin da yake kasancewa cikin halarto da kur'ani mai girma da tsatso tsarkaka a sulukinsa da ayyukansa da tunaninsa da akida da jihadi.

Daga nan muke kara yakini da sabati cikin akidarmu, lallai dararen cikin su zalunci da akaiwa sarkin muminai shugaban masu tauhidi imamin masu tsoran Allah zakin Allah mai galaba Ali bn Abu dalib (as) ina son in dan yi ishara zuwa ga wani haske daga haskayensa (as) karkashin ma'arifa jamaliyya mai haskaka, domin mu kasance cikin fadar sahibuz-zaman imaminmu wanda muke sauraro hujjar Allah ta goma sha biyu amincin Allah ya kara tabbata shi ne Abadan abidin, Allah ya gaggauwata bayyanarsa, ya sanya mu daga zababbun shi'arsa da mataimakansa masu tallafa masa ya sanya mu masu shahada a gabansa, ubangijin talika ya amsa.

Ku taho muje mu sha bishiyar hashimawa karkashin inuwar sarkin muminai Ali (as) mu gurfanar da gwiwowinmu gaban girma da tsarkakarsa, mu nemi tallafi da taimako daga gare shi domin ya ceto wajen Allah matsarkaki (ya mai alfarma wajen Allah kasa ma mana ceto wajen Allah)

Bahasimu da maganarmu za ta kasance kan hakika siradi mikakke lallai yadda ala'amarin yake shi ne wilayar sarkin muminai Ali (as)Tura tambaya