lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

Yanzu ba zaku yi duba zuwa ga Rakumi ba yaya aka halicce shi_ ina fuskar kamanceceniya

 

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai

(أَفَلَا يَنظُرُونَ إِلَى الْإِبِلِ كَيْفَ خُلِقَتْ * وَإِلَى السَّمَاءِ كَيْفَ رُفِعَتْ * وَإِلَى الْجِبَالِ كَيْفَ نُصِبَتْ * وَإِلَى الْأَرْضِ كَيْفَ سُطِحَتْ)

Yanzu ba zaku yi duba ya zuwa rakumi ba yaya aka halicce shi* ya zuwa duwatsu yaya aka kafa su* ya zuwa kasa yaya aka shimfida ta.

Ina ne fuskara kamanceceniyar da rakumi?

Me ya sanya Allah yake son mu kalli rakumi ta fuskar iyakancewa a wannan aya mai albarka?

Ina fuskar zurfafa lura cikin yanda aka halicci rakumi tsakanin sauran dukkanin dabbobi?

Tareda duba da mulahaza ambatonsa tareda sama da kasa da duwatsu ba a ambaci abinda ya shafi sauran dabbobi ba?

Ina cewa Allah mafi sani:

Galibin malaman tafsiri cikin tafsiransu sun kawo fuskoki dangane da muhimmancin rakumi, kai hatta a cikin wannan zamani da muke ciki bayan shudewar fiye da shekaru dubu da saukar kur'ani, saboda haka ne ma Allah ta'ala ya ambaci rakumi cikin kur'ani a kebance domin ya kasance mu'ujiza ga dukkanin zamanunnuka hatta ranar kiyama kuma ya kasance kalubale ga dukkanin daidaiku, na nakashceku wasu ba'arin fuskoki tareda jumlar ta'aliki da Karin haske saran mu mu kai ga cimma samu gamsashshiyar amsa da yardarm Allah a cikin wannan babi:

1-rakumi dabbace dayar rak da take iya cin abinci kadan sannan tareda da haka tayi aiki mai tarain yawa, wannan yana daga abubuwan ban al'ajabi da suke tattare da rakumi hatta cikin wanna zamani namu saboda a wannan zamani ba zamu iya kera wata mota da zata aiki fiye da na man fetur din da ta sha ba.

2-rakumi shi kadai ne dabbar da za a iya hawansa kuma aci namansa a sha nononsa a kuma yi amfani da fatarsa da gashinsa da…. Wannan wasu abubuwa ne da suka kebantu da shi babu wata dabba da take da irinsahar zuwa wannan zamani da muke ciki.

3-rakumi shi kadai dabbar da yake iya hakuri da jurewa kishirwa dukkanin dabbobi suna mutuwa sakamakon kishirwa bayan yan kwanaki kadan amma rakumi yana gogayya kan kishi, a wannan zamani an gano cewa mutum bai iya wanzar da rayuwar dabba ko dan'uwansa mutum ba tareda ruwa ba.

4-rakumi shi kadai ne dabbar da yake iya tafiya cikin sahara da duwatsu da doran kasa da ….. a wannan zamani bayan dukkanin cigaban da aka samu ba iya kera motar da take iya tafiya kan kasa da yashi da dutse da ruwa duka ita kadai

5-rakumi shi kadai ne dabbar da yake cin mafi kaskantar abinci a lokaci guda yayi aiki mafi kyawun ayyuka, am'ana yana yin aikin da bai dacewa da abinda yaci, wannan yana daga mu'ujizozin Allah bayyanannu, hatta cikin wannan zamanin da muke ciki mutum ba zai iya kera abinda bai cin bitamin masu karfafa jiki ba tareda haka yayi aiki irin na rakumi, abu mafi bayyana shine cewa cikin halittar rakumi akwai abinda ya sabawa dokokin illa da ma'aluli!

6-Rakumi shi kadai ne dabbar da tareda girman jikinsa yaro karami na iyan jansa wannan baya dacewa da dokokin tsarin dabi'a kamar yanda yake a wannan zamanin namu, duk sa'ilin da abinda aka kera ya kasance mai karfin gaske da girman gaske hakan na lazimta cewa dole wanda zai amfane shi ma ya kasance mafi karfi da girmama, ba zia yiwu mu kera wani misalin rakumi wanda tareda dukkanin girmansa da karfinsa yana biyayya ga karamar halitta hatta misalin bera idan ta jan linzaminsa lallai wannan ma yana daga cikin abinda ya shallake d aketare al'adar tsarin halitta.

7- rakumi shi ne kadai dabbar da tareda girmansa yake sunkuyawa yayin hawan bayansa, mu a wannan zamanin namu bamu iya kera babbar mai tsayi motar da zata sunkuya lokacin hawa kanta ba!

Sauran siffofin rakumi suna da yawan gaske wacce zamu iya kawo su a wannan fage wannan kenan, kari kan cewa larabawa suna a wancan zamani basu da wani mafi girmami da muhimmancin abin hawa kamar sa ba da kur'ani mai girma ya fara da ambaton kallonsa kamar yanda ya faru a mutanen Annabi Salihu (as) da suka nemi Annabinsu da ya fito musu da taguwa daga cikin dutse, wannan himmatuwa ta bubbugo ne daga siffofinsa wacce ambatonsu ya gabata.

Wannan kenan tareda kau da gani daga sauran abubuwan ban mamaki da suke tattare da rakumi da cikin halittarsa cikin kunnensa da idanunsa da kansa da kafarsa da hanjinsa da ….tareda rashin kawo alfanu da da suke cikin namansa da nononsa da gashinsa da kashinsa da kitsensa kai hatta cikin fitsarinsa da kashinsa akwai fa'idoji dukkaninsu sun sanya rakumi yana da wata kebantacciyar hususiya da taskatu gareshi kadai koma bayan sauran dabbobi da suke a doran kasa.

Ba zamu kutsa cikin tsawaita bayani ba bisa takaitcewa da karkarewa bakin iaya haka.

Dukkanin godiya ta tabbata ga Allah mai rainon talikai.  


Tura tambaya