lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

JIFAN JAMARAT

 1-lalle shi yana daga cikin sunnar annabi Adamu (as) lalle bayan ya yi dawafi yayi tsayuwar Arafat da Mash'arul haram da Mina, sai Allah ya umarce shi da ya kara yin dawafi karo na biyu dawafin ziyara da soyayya, sai Adamu ya fuskanci Ka'aba mai daraja, sai dai cewa iblis jefaffe la'ananne ya kira Adamu yana mai cewa: ya Adamu ina ka nufa? Sai Adamu ya waiwayo zuwa ga Iblis, sai Jibrilu ya sauko ya cewa masa: wannan shi ne Shaidan ka jefe shi, sai Adamu ya jefe shi har karo uku a mahallai uku wadda ake kira yau da jifan Jamarat uku.

 Masoyi bai waiwaya face ga masoyinsa, abin tsamammani ga Adamu a misalin irain wancan lokaci wanda ya nufi dakin Allah mai alfarma domin shauki da soyayya da kaunarshi ne Adamu ka da ya waiwayi wani abu koma bayan Allah, sai Shaidan ya nufi yakau da fuskar Adamu shi ya sama ya kira shi, sai Jibrilu ya umarci Adamu da ya jefe Shaidan sai ya jefe shi ya nesance shi.

2-lalle hakika yana daga sunnar Ibrahim (as) lalle yayin da ya dauki dansa Isma'il ya kai mayanka Iblis ya zo masa surar dan Adam yace masa: ta kaka uba zai yanka diyansa? Sai Jibrilu ya umarci Ibrahim da ya jefe shi kada ya raunana shi da jinkirta shi cikin abin da ya kuduri aikatawa.

3-lalle jifa guda uku da ake yinsa a muhallai uku kabarburane ga dagutai uku daga dagutan cikin tarihi.

4- lalle shi muhallai ga gumaka ukun kuraishawa da wasunsu.

5-jifa da tsakuwowi bakwai na nufin jefe shaidan da hana shi katsalandan da kutsawa daga tagoginnsa guda bakwai: gabban sadarwa biyar na zahiri wadanda sune: (ji, gani, tabawa, shaka, dandano) da kuma kari kai da gabban fusata da sha'awa.

6- jifa na nufin yakar Shaidanu daga mutane da aljannu da yakar dagutai da jabberai da gumaka da dukkanin shakalinsu da launukansu da kungiyoyinsu da tarkunansu.

7-jifa da tsakuwowi bakwai na nufin jifan Shaidan da yanayin mutum guda bakwai: dabi'a da hankali da zuciya da rai da sirri da boye da buya.

8- jifa na ishara da jefe Shaidanun mutane da aljannu, duk wanda Shaidani ya zamanto aboki cudanyarsa ko kuma ya kasance mai yi masa waswasi cikin kirji to ta kaka zai iya jifansa? Ya zama tilas ya kubuta daga siffofin shaidanci ya tunkudesu ya ciresu domin ya samu damar tanadi rungumar ruhin mala'ikantaka.

9- dukkanin abin da ke dauke da rayuwa tun daga dabbobi ya zuwa tsirrai da mutane lalle yana da gabar jazabi( jawowa) da gabar dafa'I ( tukudewa)  ya kanyi tajalli cikin dan adam da dabi'ar fushi da sha'awa, wani lokutun kumada soyayya da kiyayya, na uku kuma shi ne  irada da karhanci da wasunsu sannan abin da ya tattaro dukkanin wadannan halaye shi ne bara'a da wilaya, daga cikin mafi bayyanar abin da ke cikin hajji cikin ayyukansa da hukunce hukuncensa da iliman da ke cikinsa da duniyoyinsa shi ne tabbatar da tauhidi da kore shirka, sannan su wadannan abubuwa biyu wato tabbatar da tauhidi da kore shirka suna siffantuwa cikin wilaya da bara'a da imani da Allah da kafircewa dagutu.

Ishara ta farko dawafi daura da dakin ka'aba cikin farkon tafiya zuwa ga Allah, kamar yadda ishara ta biyu shi ne jifan shaidan da kubuta daga tarkonsa da barranta daga gareshi da mataimakansa mabayyanarsa daga dawagitai da gumaka.

10-mustahabbi ne ga mahajjaci ya tsarakaka da yin wanka ko daura alwala, kai kace yana ishara da cewa shi tsarkake yake a badininsa daga kazanta da najasa yana dacewa da jifan shaidan da iblisai daga mutane da aljannu. Ba boye yake ba cewa zahirin take duk wanda ya samu damar jifan shaidan cikin badininsa to za a karbi jifan shaidanin zahiri daga gareshi, kadai dai mutum na karae kansa daga sharrin shaidani ta hanya neman tsarin Allah:

 (وَإِمَّا يَنْزَغَنَّکَ مِنَ آلشَّيْطَانِ نَزْغٌ فَاسْتَعِذْ بِاللهِ.( [1]

Idan shaidani ya fisgeka fisga to kanemi tsari da Allah.

11- daga cikin al'adu larabawa a zamanin jahiliya shi ne cewa duk mutumin da ya kasance abin fushi da shi to za a jefe shi yana raye ne ko ya mace, daga wannan aka samu larabawa suna jefe kabarin abu zugalu jagoran rundunar Abarahatama'abocin kissar giwa da tsuntsayen Ababil, malam Jariru cikin zagin da yakewa Farazdak yana cewa:  idan Farazdak ya mutu ku jefe shi kamar yadda kuke jifan kabarin abu Zugalu.

12- jifan Shaidan na kawo haske a badini, wannan nufi cewa jihadi da dauki ba dadi madawwami mai bibiya da wani adadi zai janyo masa rayuwa mai cike da haske, mutum zai rayu kan haske ba zai rayu cikin duhu ba da zalunci da zai kashe da karkacewa daga siradi ya fada cikin hawiyar kurakurai da zunubai da mahalakar laifuka ya yi karo da munana halaye da miyagin dabi'u.

13- mustahabbi ne yin kabarbari yayin jifan ko bayan yinsa, hakan nuni kan girman Allah matsarkaki da daukakarsa da kaskantar Shaidani da raunanarsa, girmama da daukaka baki dayansu ga Allah. Lalle yakar Shaidan da rundunarsa da kungiyarsa kadai dai anayinsa don Allah madaukaki da sunansa da girmamamrsa.

14- zaka yi jifan shaidan guda uku cikin kwanaki uku domin yayi nuni kan cigaban buga in buga da dauki ba dadi da gwagwarmaya cikin kan hanyar gaskiya, lalle duk sanda mhajjaci ya yunkura ya kusanci dakin Allah domin yi dawafi daura da shi dawafin soyayya da ziyara lalle sahidan zai dinga bin bayansa ta hanya sanya duwatsu a kan hanyarsa, saboda haka ya zama tilas a jefe Shaidan domin tsallake tuba-tubai da shingensa duk yanda yin hakan ya kai da kallafawa, koda kuwa da tsakuwa bakwai ne cikin kwanaki masu biye ma juna.

15-me yiwuwa sirri cikin fuskantar shaidan lokacin jifan Jamarat Akaba da kasantuwar Ka'aba a bayan mai jifan na nuni kan cewa da jifansa zai hanama Shaidan shiga harami zai kuma gaba da gaba da shi don yakarsa, lalle shi atukar bai yaki babban shaidani ba bai kubuta daga tarkonsa ba ta kaka zai iya fuskantar dakin ubangijinsa da alkiblarsa cikin mi'irajinsa da sallolinsa.

16-ya zama tilas cikin jefe Shaidan a samun hadin kai da daidaita sahu kamar yadda hakan ya kasance cikin Arafat da Mash'arul haram, domin hakan ya yi nuni da hadin kan musulmai cikin fito na fitonsu da makiyan muslunci kamar misalin Yahudawan Sahoyuniya da girman kai da `yan mulkin mallaka da Masuniya da `yan gurguzu da da kafirci da shirka da karkata da ma'abotan munanan kalamai da batattu da masu batarwa, da dukkanin abin da ke dauke da sunan Shaidan da dukkanin alaminsa.

17- shi dawafi wajibi a hajji na da kewaye 21 sa'ayi kewaye 14 sai dai cewa shi jifa kuma ana yinsa da tsakuwa 49 wanda hakan na nuni da karin dauki ba dadi kan makiyi kan Shaidan matuka kaka mutum zai kai ga ubangijinsa da dawafin ka'abarsa?

18- adadin bakwai na ishara da sirrika, dawafi kewaye bakwai ne, sa'ayi kewaye bakwai jifa sau bakwai kowanne karo ana yinsa da tsakuwa bakwai, me yiwuwa hakan ya zamanto ishara ya zuwa jihadi da fafutika cikin marhalolin rayuwa guda bakwai tun daga kulluwar kwayar maniyyi

 (وشاركهم في الأموال والأولاد)

Kayi tarayya da su cikin dukiya da `ya`ya.

Har ya zuwa lokacin shashshakar fitar rai da mutuwa.

ـ قال رسول الله 7: «رمي الجمار ذخر يوم القيامة ، والحاج إذا رمى الجمار خرج من ذنوبه » وقال الصادق  7: «من رمى الجمار حُطّ عنه بكلّ حصاة كبيرة موبقة ، وإذا رماها المؤمن التقفها الملک ، وإذا رماها الكافر قال الشيطان بأُستک  ما رميت » . [2]

Manzon Allah (s.a.w) yana cewa: jifan Shaidani wani tanadi ne ranar kiyama, mahajjaci idan ya yi jifa zai fita daga zunubansa, Imam Sadik (as) ya ce: duk wanda ya yi jifan shaidan za a kankare masa babban zunubi bisa kowacce tsakuwa da ya yi jifan da ita, idan mumini ya yi jifa sai Mala'ika ya tsinci tsakuwa, idan kafiri ya yi jifa sai Shaidani ya ce masa duwawunka me ka jefa.

Bai buya cewa Kalmar kafiri ta hada da wanda ya kafircewa tauhidi da Annabta da Imamanci, duk wanda ya kafircewa Imamanci bai san Imamin zamaninsa ba lalle shi idan ya jefi Shaidani kadai dai Shaidanin zai ce masa duwawunka me ka jefa, domin ingancin jifansa ya dogara da ingancin akidarsa da karbuwar wilayar Imami ma'asumi da yi masa biyayya.

20-an karbo daga baban Abdullah cikin wani hadisi: yace: sannan Jibrilu ya rike hannun Adamu (as) sai ya tafi da shi zuwa daki mai alfarma sai Iblis ya bijirowa Adamu lokacin jifan Jamarat sai iblisi la'ananne ya ce masa:  ya damu ina ka nufi zuwa? Sai jibrilu ya cewa adamu jefe shi da tsakuwa bakwai kayi kabbara kan kowacce tsakuwa sai Adamu ya aikata haka, sai iblis ya gudu, ya kara dawo masa a jamarat ta biyu y ace ya adamu ina zaka je? Sai jibrilu y ace masa jefe shi da tsakuwa bakwai tare da yin kabbara kan kowacce tsakuwa, sai Adamu ya aikata haka sai hakan ya kara kasancewa cikin karo na uku, sai jibrilu ya cewa da adamu ba z aka kara ganinsa ba bayan wannan mukamin naka har abada, saboda haka ku shiriya da shiriyarsu

 [1] A'araf:200

[2] Alfakihu:juz 2 sh 214

Tura tambaya