lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

YARO MATASHI TARE DA TSOHO

An hakaito cewa wani mutum tsoho ya kasance yana zaune cikin jirgin kasa tare da `dansa da shekarunsa zasu kusan 25, dukkanin Alamomin nishadi da annashuwa sun bayyana a fuskar wannan matashi da yake zaune kusa da tagar jirgi, sai ya mika hannunsa cikin taga ya fitar da shi waje yana jin iska yana mai daga murya kwarmata ihu yana cewa (baba ka ga bishiyoyi suna tafiya suna komawa bayanmu!) sai wannan tsoho yayi murmushi yana mai biyewa annashuwa da nishadin `dansa, a daidadi kusa da su akwai wasu ma'aurata da suke sauraron tattaunawa tsakanin `da da Uba, hakan ya sanya suka dan takuru ta kaka za a ce katon yaro matashi `dan shekara kusan 25 ya dinga wannan tasarrufi na kananan yara, kwatsam sai wannan matashi ya kara kwarmata ihu yana cewa (babana kalli kwalabati da abinda yake cikinta kalli hadari da girgije suna tafiya tareda jirgin da muke ciki) sai wadannan ma'aurata suka cigaba da shan mamaki cikin tasarrufin wannan matashi, ruwan sama ya fara sauka digon yayyafi na ta sassauka kan hannun wannan matashi wanda ya kasance cikin nishadi, sai ya kara kwarmata ihu yana cewa (baba kalli sama na zubar da ruwan sama ga ruwan yana shafar hannuna! Baba kalli ) a wannan lokaci wadannan ma'aurata sai suka gaza cigaba da zuba ido sai suka tambayi wannan tsoho: (me yasa ba zaka je ganin likita ba domin magance cutar da take damun `danka?) sai wannan tsoho yace(daga asibiti muka dawo yanzun nan Allah ya azurta shi da fara gani tun zuwansa wannan duniya) Natija daga wannan hikaya: kada ka gaggauta yanke hukunci gabanin sanin hakikanin al'amaura

Tura tambaya