lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

sababun makaloli

KARIJUL FIKHU 15 GA SAFAR SHEKARA 1441 CIGABAN BAHASIN BAYYANA KARATU DA BOYE SHI

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai

Dorawa kan bahasin da ya gabata a 14 ga watan Safar kan bayyana karatun sallah da boye shi tareda-Samahatus Assayid Adil-Alawi

Wuri: Muntada Jabalul Amil Islami

Lokaci: karfe takwas na Asubahi.

 

Cigaba kan bahasin da ya gabata cikin bayyana karatun sallolin wajibi na yau da gobe da boyewa, hakika Magana cikin kafa dalilin abinda Mashhur daga wajabcin bayyana karatu cikin sallolin da ake bayyana karatu da boyewa cikin sallolin da ake boyewa kamar yanda bayani ya gabata, jigon dalilam ingantattun riwayoyin Zurara sai dai cewa sun ci karo da ingantacciyar riwayar Aliyu Ibn Jafar daga dan’uwansa Kazim amincin Allah ya kara tabbata a gareshi, mawallafin Almadarik ya tafi kan tattaron riwayoyin da dora bangaren farko daga riwayoyin kan mustahabbanci, yace: hakika bangare na biyu tafi bayyana da fito fili daga ta farko saboda haka babu fuska da zai sa a dora kan takiyya da har za tafi kan wajabcin bayyanarwa da boyewa, malamai da suka zo daga bayan zamanin Allama Hilli (K) sun bada amasa da cewa malamai sun kauracewa wannan riwaya ta Aliyu Ibn Jafar saboda haka ba zata iya zama hujja ba a cikin kankin kanta da har za ta iya cin karo da karyata wata riwayar.

 

An yi Ishkali kan hujjantakar riwaya ta biyu cikin kankin kanta kuma lallai kaurace aiki da ita bai wajabta rauninta, lallai ba ta dora riwaya ta farko kan mustahabbanci sakamakon zahirin ingantattun riwayoyin Zurara guda biyu sun kunshi umarni da sake sallah kamar yanda ya kasance a riwayar farko kuma mafhumin riwayar ta biyu, lallai umarni cikinsu bai kasance umarni na sauke taklifi ba kadai dai ya kasance umarni na irshadi da hukuncin hankali kan gurbatar sallah da rashin faduwar umarnin farko sai ya zama maimaici ya wajabtu, mustahabbanci bai kunsar ma’anar bacin aiki wadannan riwayoyi guda bas a daukar mustahabbanci bari dai sun kasance suna kunshe da ma’anar wajabci a zahirinsu karara.

Daga cikin abubuwa da suke doruwa kan wannan ma’ana da farko akwai abinda mawallafin Almadarik ya fada da cewa ingantacciyar riwayar Aliyu Ibn Jafar tafi karfafa ma’anance ita ta zo da bayani karara kan halasci, wannan ai bayyanannen al’amari ne, duka su biyun ta fuskanin ma’anarsu ta zahiri kamar misalin tafukan Sikeli da suka kafada da kafada, kamar yanda ingantacciyar riwayar Aliyu ta kunshi halasci karara haka zalika riwayoyin Zurara suke kunshi zahirin ma’anar wajabci.

Amma na biyu: shine abinda Akaramakallahu ya fada da cewa riwayar Aliyu tafi karfi cikin isnadi wannan ba bayyanannen lamari ba ne dalili bai tabbata kan haka ba.

Shaik Yusuf Bahrani (ks) yayi nufin kare mawallafin Almadarik da bashi uzuri da cewa bai ci karo da hanyar Shaik Dusi (K) ba kamar yanda ya ambata, sai dia cewa yayi kacibus da hanyar Shaik Saduk (K) sakamakon ra’ayi da cewa shi yana cikin mafi daukakar martabobin inganci.1

Anyi ishkali kan wannan Magana: da cewa lallai hanyar Shaik Dusi ya zuwa Harizu itama ingantacciya ce kuma karfaffa kamar hanyar da Shaik Saduk ya bi, adalci a wannan mukami lallai ingantattun riwayoyin Zurara guda biyu da riwayar Aliyu Ibn Jafar sun yi kafada da kafada ta fuskanin isnadi da ma’ana, abinda mawallafin Almadarik ya fada daga rinjayarwa da hujja karfafanta cikin isnadi da ma’ana cikin riwayar Aliyu Ibn Jafar babu dalili kan wannan ra’ayi bai ma inganta ba kwatakwata, sannan abinda mawallafin Almadarik ya fada kan hado dukkanin riwayoyin da juna da dora su kan mustahabbanci wannan Magana ta fadi daga idon la’akari da hujjantaka.

Kan abinda ya fada dole a samu wata fuskar daban don rinjayarwa baya tabbatuwar cin karo da juna da tabbata tsakaninsu a matakin farko, a mataki na biyu kuma hado su ama’anace bai yiwuwa ba, sakamakon kasancewar riwayar Aliyu Ibn Jafar tana dacewa da ra’ayin wadanda suka saba da matafiyar Ahlil-baiti, saboda su mudlakan basa ganin wajabcin bayyanar da karatu, ka duba littafin Almajmu’u juz 3 sh 389 da Ma’anar Mujtaj juz 1 sh 162, saboda haka babu fuska ga wannan riwaya sai dora kan takiyya kamar yanda Shaik Dusi yayi kamar yanda ya zo cikin littafin Alwasa’il kamar yanda bayani ya gabata, a wannan lokaci sai ayi watsi da riwayar Aliyu Ibn Jafar rinjayarwa sai ya takaitu tsakanin riwayoyin Zurara da suka sabawa ra’ayin wadanda suka sabawa Ahlil-Baiti, ka yi riko da ra’ayin da ya sabawa wadanda suka saba mana lallai shiriya da gaskiya na cikin saba musu, sai ya zama aiki da riwayoyin Zurara ya ayyanu daga tafiyan kan ra’ayin wajabcin bayyanar da karatu da boye shi kamar yanda hakan shine ra’ayin Mashhur kuma nima wannan ra’ayi na zaba.

Sannan mawallafin Almadarik ya tafi kan rinjayar da riwayar Aiyu Ibn Jafar kan riwayoyin Zurara da cewa riwayar Aliyu da yi muwafa da Asalul Ilmi, hakamkuma tayi muwafaka da Kur’ani mai girma, ku riki ra’ayin da ya da ce da littafin Allah.

Sai dai cewa a wurin ba’arin wasu malaman wannan zamani: fuskar wannan rinjaya bata bayyanu ba.

Bayani kan haka: amma batun Asali ma’ana asalin halasci: lallai duk da kasancewarsa hakika, sai dai cewa kuma asali dalili ga anda babu dalili gareshi, sannan bayan tsayuwar dalili kan wajabci babu ma’ana cikin riko da Asali.

Na biyu: hakika muwafakar Asali bai kasance daga dalili kan rinjayarwa ba cikin hadisan Ilajiya haka ma cikin wasunsu, saboda asali a cikin kankin kansa da waki’i kadai dai shi daga makoma yake bai kasance daga marinjaya ba, sai ka lura.

Amma maganar littafin Allah mai girma: lallai cikin ayoyinsa masu daraja babu abinda ya ratayu da wannan mukami face fadinsa madaukaki:

 (ولا تجهر بصلاتك ولا تخافت بها وابتغ بين ذلك سبيلاً) ([2]).

Kada ka bayyanar da sallarka kada ka boye ka nemi tafarki tsakatsakinsu.

Amsa a matakin farko: larura ne cewa karatu bai wofinta daga hali biyu kodai bayyanawa ko boyewa.

Mataki na biyu: rashin tabbatuwar tsatsaki tsakaninsu da har za ai umarni da shi a hana bayyanarwa da boyewa, wannan ana kirga a matsayin karina shaida yankakkiya kan cewa abinda ake nufi shine rashin ketare iyaka cikin bayyanarwa kamar misalin mai kiran sallah, haka rashin takaitawa cikin boyewa da yanayin da zai kasance kawai yana motsa bakinsa hatta shi a kankin kansa baya jin sautin abinda yake karantawa.

Mataki na uku: jumlar riwayoyi sun zo cikin tafsirin wannan aya mai daraja daga abinda aka ambata daga rashin wuce gona da iri da rashin takaitawa cikin sautin karatu cikin sallah, kan haka: cikin wannan aya mai daraja babu shiryarwa bayyane kan hukuncin bayyana karatu da boye shi ta fuskanin wajabci kamar yanda hakan ya kasance ra’ayin Mashhur ko mustahabbanci kamar yanda mawallafin Almadarik da Assayid Murtada da Ibn Junaidu Al’iskafi suka tafi akai, hakan baya kore wajabcin bayyanarwa cikin ba’arin wasu wurare idan ya zama ta tabbatu da dalili daga waje kamar yanda ya kasance cikin riwayoyin Zurara, ka lura.

Duk dai yanda ta kasance zahirin hukuncin ka’idar rinjayarwa cikin wannan mukami babu wata fuska da ta rage face dora riwayar Aliyu Ibn Jafar kan takiyya kamar yanda bayani ya gabata, sannan akwai wanda yayi munakasha cikin abinda riwayoyin Zurara  ke shiryarwa kamar yanda ya kasance daga mawallafin littafin Azzakira daga fuskoki biyu.

Fuskar farko: kamar yanda ya gabata cikin ba’arin nuskoki maimakon (nakada) da harafin zadi sai ya zo (nakasa) da harafin sadi mara digo, wannan Kenan da farko, wanda yake shiryarwa zuwa ga tauyewar lada bawai gurbacewar sallah ba, nuksani yana lazimtar mustahabbanci ba wajabci ba.

Na biyu: Kalmar (yanbagi) kamar yanda ya gabata cikin riwayoyin, zahiri na tabbata kan mustahabbanci bai dacewa da ma’anar wajabci.

Anyi ishkali kan na farko da cewa abinda yake tabbace cikin dukkanin litattafan riwaya kamar yanda aka fada shine (nakada) da zadi mai digo ba a nakalto (nakasa) da sadi ba mara digo ba face daga ba’arin litattafan fikhu, ba a la’akari da riwaya idan na nakalto ta daga masdarin ta daga litattafan hadisi ba.

Sai dai cewa  yayi ishkali kan wannan ishkalin da cewa: da farko dai yana mai nuna kin gamsuwa daga abinda aka nakalto daga littafin Muntakaj Juman da `dan Shahid Sani juz 2 sh 12, da cewa ba a nakalto ta ba da zadi mai digo, na biyu cikin Hamish din littafin Al’istibsar  juz 1 sh 312 bugun Najaf cikin ba’arn nuskokin littafin ya zo da (nakasa) babu digo na uku cikin Biharul-Anwar juz 82 sh 77 bayan nakalto riwayar Zurara daga Shaik Saduk yace: cikin ba’arin nuskokin akwai (nakasa) cikin wasu ba’arin kuma ya zo da (nakada) zahirin maganarsa sabani ne ba nuskokin Alfakihu shi gogagge ne cikin fannin hadisi (k) wannan yana daga abinda yake shiryarwa kan an nakalto (nakasa) hatta cikin ba’arin wasu litattafan hadisi bai takaitu ba iya litattafan fikhu kamar yanda wasu suke rayawa daga manyan malamai.

Na biyu: idan mun kaddara ta zo da (nakasa) lallai hakan bai cutarwa cikin shirywarta kan gurbatar sallah bawai cewa tawayar lada bane kamar yanda wani ya raya hakan, da bisa riko da shaidar da ta zo cikin karshen riwayar lallai nasaka na da ma’anar kishiyanyar cikawa da yake da ma’anar gurbata, a wannan lokaci yana shiryarwa kan wajabci kamar yanda fadin Imam (a.s) sake sallah ta wajaba kansa ya shiryar kan wajabci

Amma jawabin kan ishkali na biyu: lallai Kalmar (yanbagi) cikin misalin mukami zahiri ce cikin rashin saukakawa kamar yanda ya ta dace da ma’anarta ta lugga da istimalin Kur’ani kamar yanda ya zo cikin fadinsa madaukaki:

 (لا الشَّمْسُ يَنْبَغِي لَهَا أَنْ تُدْرِكَ الْقَمَر([4]).

Ba zai taba yiwuwa rana ta riski wat aba.

Ma’ana bai saukaka gareta kuma bai dacewa da ita da har zai dace da abinda ya gabata daga mustahabbanci cikin fikhu ba.

Na biyu: wannan kalma ta afku cikin maganar mai tambaya bawai daga Imam (a.s) take baa bind aya fi dacewa shine kafa hujja da maganar Imam (a.s) shi kuma gashi ya bayyana cewa a sake sallah wanda zahirinsa ke nuni kan gurbatar da yake lazimtar wajabcin bayyana karatu da boye shi, abinda ake bukata sai ya tabbata daga abinda Mashhur suka tafi akai kuma hakan shine ra’ayinmu.


([1]).الحدائق: 8: 131.

([2]).الإسراء: 110.

([3]).هامش شرح العروة: 14: 375.

([4]).يس: 40.

Tura tambaya