lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

BAHASUL KARIJUL FIKHU 6 RABIUS SANI 1441 H, WANDA BA ZAI IYA KARATTU BA TAREDA KUSKURE BA KO CANJA BA'ARIN WASU HARUFFA

 

Wuri: Qum mai tsarki cibiyar Muntda Jabalul Amil Islami tareda Samahatus Assayid Adil-Alawi.

 

Mas'ala 33: wand aba zai iya karatu ba tareda kuskure ko canja ba'arin wasu haruffa kuma ba zai iya koyan juzu'ansu ba wajibi kansa ya bi limami sallah, duk da cewa ihtiyadi shi ne ya bi limami sallah, haka zalika wanda yake Baibai shim aba wajibi bane sai ya  bi limami sallah.

 

Ina cewa: cigaba kan bahasin da yagabata da kara fadadawa cikin wanda bai iya kyawunta karatu kuma bai iya karatu  face karatun da yake cike da kuskure, misdaki na biyu ga wanda bai kyawunta karatu shi ne wanda yake canja ba'arin wasu haruffa da wasu, wadannan kamar yanda bayani ya gabata wajibi ne kansu suje su koya su gyara karatunsu tareda iko da dama idan bai samu damar koya ba ya kasance gazajje da gazawar kasawa kamar yanda ya gabata, lallai zai kawo abinda yake iyawa daga gareshi sannan sallarsa ta kasance tauyayya kamar yanda ya kasance a mukamin larura mai isarwa daga sallar cikin zabi kammalalliya, ko kuma dai ta zama itace sallarsa tabbatatta bisa gini kan cewa tabbata tana da misdaki biyu, tabbata ta zabi da ta larura sai kowanne daya ya kasance cikin bijarar dayan, sai dai cewa wadanda suka tafi kan isarwa da wadatarwa suna ganin na larura cikin mikar zabi, ka lura sosai wannan yana daga rigima ta magina mabnawi kamar yanda yake a Ilmul Usul.

Ajizi yana kawo abinda ya zai iya daga sallarsa da karatnsa, hakan ya wadatar da shi kamar yanda aka nakalto bayani karara kan haka daga manyan malamai, wasu sun tafi kan sabani cikin haka kan zahir babu kuma ishkali. 1

Ana kafa hujja kansa: da shuhura ko kuma Ijma'i bisa riko da wani ayari daga riwayoyi wadanda ba'arinsu raunana ne cikin isnadi sai dia cewa malamai sunyi aiki da su, daga cikinsu: Kabaru Mas'adatu Ibn Sadakatu

عبد الله بن جعفر في (قرب الإسناد) عن هارون بن مسلم عن مسعدة بن صدقة قال: سمعت جعفر بن محمد عليهما السلام يقول: إنّك قد ترى المحرم من العجم لا يراد منه ما يراد من العالم الفصيح، وكذلك الأخرس في القراءة في الصلاة والتشهد، وما أشبه ذلك فهذا بمنزلة العجم، والمحرم لا يراد منه ما يراد من العاقل المتكلم الفصيح([2]).

Daga Abdullah Ibn Jafar  cikin (Kurbul Isnad) daga Haruna Ibn Muslim daga Mas'adatu Ibn Sadakatu yace: na ji Jafar Ibn Muhammad amincin Allah ya kara tabbata a gareshi yana cewa: lallai zaka ga  abinda ake nema daga bakauyen daga Ajamawan mutanen da suke ba larabawa ba, ba a nemi hakan daga malami mai magana da fasaha, haka zalika Bebe wanda baya iya magana cikin karatun sallah da zaman tahiyya, da abinda yayi kama da haka, wannan yana matsayin  Ajamawa, bakauye daga gareshi ba a neman abinda ake nema daga wurin ma'abocin hankali mai magana mai fasaha.

Fuskar kafa hujja: bayan raunin da isnadin yake tattare da shi da Irsal da kuma gyaruwar da ya samu ta sakamakon malamai sunyi aiki da shi, sannan kuma abinda ake nufi daga (Almuhram) bakauyen da bai rayu a rayayyen waje ba daga Ajamawa wadanda ba larabawa ba shi kiamar misalin balaraben kauye ne daga larabawa wanda shi ne wanda bai rayu cikin maraya ba daga birni wanda bai kyawunta karatu da rubutu kuma bazai iya koyan karatu ba, lallai iya abinda zai iya ya wadatar daga gareshi ba a neman wazifar da ake bukata daga mai magana dan birni mai fasaha.

Amma lafazin Akilu da ya zo cikin hadisi mai daraja: ta yiwu ishara ce ya zuwa ga sirrin lugga cikin amfani da Kalmar Ajami kan wanda ba balarabe ba, lallai larabci ya zo ne da ma'anar fasaha da li'irabi ma'ana dai bayyanarwa kamar bayyana wasali kan haruffan domin sanin abinda suka kunsa daga sassabawa cikin ma'ana da af'al da sunaye, a cikin mukamin fahimtarwa da karkasawa tsakanin ma'abota hankali kadai yana kasance da kalmomi da lafuzza wadanda suke bayyana manufa da ma'anoni, babu wani rashin bayyanuwa, amma mubhamai daga sautuka lallai su suna daga dabbobi kuma ana kiransu da Ajamawat wadanda basa magana ma'ana sautinsu ba irin sautin mutane ba da ake iya fuskantar abinda yake nufi daga gareshi, bari dai mutum bai iya fahimtar abinda dabba ke so cikin sautinta, sautin dabbobi sai ya kasance mubhami gareshi ma'ana ya zama Ajami ba balarabe bayyananne mabayyani, anyi kinaya da lugga Arabiyya fasiha da Akili wanda shi ne mutum kishiyan dabba wacce ba a iya fahimta manufarta cikin sautinta, ka lura, wannan yana daga ta'asubbancin larabawa wanda ya zo cikin hadisi da cewa mutane shida zasu shiga cikinsu har da larabawa za su shiga wuta ne sakamakon ta'assubanci, ya zama wajibi mu tsarkake zukatanmu mu tarbiyantar da ita da ilimi, lallai babu banbanci tsakanin balarane da ba'ajame ma'ana wanda balarabe cikin ilhama face da tak'wa, basu girmama Allah hakikar girmama shi  har sau uku kamar yanda ya zo cikin Kur'ani, da ma'arifa da soyayya da biyayya da wilaya da cton Allah ta'ala.

ومنها: خبر السكوني عن الصادق عليه السلام عن النبي صلى الله عليه وآله وسلم: إنّ الرجل الأعجمي في أمتي ليقرء القرآن بعجميته فترفعه الملائكة على عربيته([3]).

Daga ciki akwai hadisin Assakuni daga Sadik amincin Allah ya tabbata a gareshi daga Annabi (s.a.w) : lallai mutum ba'ajame cikin al'ummata yana karanta Kur'ani da Ajamantarsa sai Mala'iku su daukaka wannan karatu kan larabcinsa.

Fuskar kafa hujja: a bayyane yake cewa lallai wannan hadisi yana shiryarwa kan tausasawar Allah matsarkaki kan bayinsa, ma'auni da sikeli shi ne tsoran Allah bawai yare da lugga da kabila, lallai dukkanin sabanin muslunci ne da Kur'ani da tsarkakakken tsatso amincin Allah ya kara tabata a garesu lallai (mafi darajarku a wurin Allah wanda yafi kowa tak'wa daga cikinku).

Daga cikin hadisin akwai hadisin Annabi (s.a.w) cikin kissar Bilal shi bilal uya kasance cikin kiran sallah yana fadin As'hadu maimakon Ash'hadu yayin na biyu yayi masa bore sai Annabi (s.a.w) y ace: hakika harafin Sinun da bilal yake fadi maimakon shinun a wurin Allah shinun ce.

Fuska kafa hujja: daga idlakin riwayoyin babin ya bayyana cewa gwargwadon abinda Ajizi zai iya karantawa yana wadatar masa, ko da kuwa zai iya bin limami, babu banbanci cikin kasantuwar mun tafi kan magina da mabna wanda ya tafi kan cewa karatun limami ta sauke masa nauyin karatu ko kuma kan mabnar wanda ya zabi bin limami daya daga cikin daidaikun misdakan wajibul takyiri ne.

Mawallafin ya tafi kan cewa mafi zama ihtiyadi cikin wannan fuska shi ne bin limami sallah, sai dai cewa wannan yana daga ihtiyadi istihbabi baya shiryarwa kan wajabcin bin limami kamar yanda yake a zahiri daga da'awar rashin sabani cikin  rashin wajabcin bin limami.

Haka Bebe ba wajibine kansa bay a bi limami sakamakon idlakin da ya zo cikin dalili isarwa da motsa harshensa da ishararsa da yatsunsa da kudurcewarsa.

Mas'ala 34: wanda yake da ikon kan koyo idan lokaci ya kurace masa ya karanta abinda ya iya karantawa daga Fatiha  sauran ayoyin nata sai canja su da karanta Kur'ani.

Ina cewa: cigaba kan abinda ya gabata cikin wanda baya iya kyawunta karatu lallai wajibi ne a kansa ya koya tareda iko kan koyowar, idan ya kasance cikin mukamin koyo baio je ya koyo dukkanin Fatihar ba lokaci ya kurace masa, sai ya karanta iya inda ya iya, daga Almuntaha na kore sabani cikin hakan bisa riko da ka'idar Almaisur.

Zamu cigaba da yardar Allah ta'ala.


([1]).المستمسك: 6: 222.

([2]).الوسائل: باب 59 من أبواب القراءة الحديث الثاني.

 


Tura tambaya