lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

Karijul Fikhu bahasi cikin kira'a da bayyanar da haruffa.


Wuri: birnin Qum mai tsarki Almuntada Jabalul Amil Islami-tareda Samahatus Assayid Adil-Alawi (h). 
lokaci: karfe 8 na safiya.
Fikhu (85)
23-Jimada Thani shekara 1441 hijri

Na uku: Tartil ma'ana jinkirtawa cikin kira'a da bayyanar da haruffa ta fuskar da mai sauraro zai iya kidaitasu. 
Ina cewa:. mustahabbi na uku cikin kira'a shine ya karanta a jerance cikin kyawuntawa, magana tana kasancewa cikin mukami guda biyu: na farko: cikin hukuncin Tartil jeranta karatu, na biyu: cikin ma'anarsa a luggance, amma mukami na farko lallai yin hakan mustahabbi ne. 
yana nuni kan hakan: da farkk: Ijma'i  da dukkanin kasonsa biyu ya zo cikin littafin Almadarik cewa cikin mas'alar malamai sun yi Ijma'i wanda haka na nuni kan cewa Ijma'i ne Almadaraki. 
na biyu: wanda shine jigo: littafin Allah da Sunna, abinda ya zo daga littafin Allah shine fadinsa ta'ala

وَرَتِّلْ الْقُرْآنَ تَرْتِيلاً﴾ (المزمل: 4).

Ka kyawunta karanta Kur'ani jerantawa
fuskar kafa dalili :hakika Allah ya umarci Annabinsa da kyawunta karatun Kur'ani, shiko umarni a zahiri yana shiryawa kan wajabci, ta yiwu Annabi ya zama wajabci a kanshi shi kadai kamar umarni da sallar dare amma kan al'umma ya zamana mustahabbi, sai ya zama daga abinda ake kira Isti'imalul majazi cikin ma'anar da ba don ita aka ajiye lafazin ba, sannan dalili ka. kasancewarsa Majazi shine da'awar Ijma'i, ka lura. 
amma daga Sunna: akwai riwaya Mursalatu Ibn Ibn Abi Umairu

 مرسلة ابن أبي عمير عن أبي عبد الله عليه السلام: (ينبغي للعبد إذا صلّى أن يرتل في قراءته، فإذا مرّ بآية فيها ذكر الجنة وذكر النار سأل الله الجنّة وتعوّذ من النّار([1
daga Abu Abdullah Amincin Allah ya tabbata a gare shi: (ya kamaci bawa idan yayi salla ya kyawunta kira'arsa, idan ya gifta ta wata aya da cikinta aka ambaci aljanna da wuta to ya roki Allah aljanna ya nemi tsari daga wuta.
Fuskar kafa dalili : bayan tafiya kan cewa Mursalatu Ibn Abi Umairu tana daga Mursalatu da ake jingina da ita, sabida haka fadin amincin Allah ya kara tabbata a gare shi : (ya kyautata karanta kira'arsa) da shaidar kalmar (ya kamata) na nuni kan mustahabbanci. 
 Akwai Mursalatu Abi Hamzatu

 مرسلة علي بن أبي حمزة.

أنّ القرآن لا يقرأ هذرمةً ولكن يرتّل ترتيلاً.
lallai shi Kur'ani ba a karanta shi a gaggauce babu tsari sai dai cewa ana kyautata karanta shi jerantawa. 
Fuskar kafa dalili : isnadin duk da kasanceqaraa rarrauna sakamkon irsali sai dai cewa kuma yana gyaruwa da aikin Malamai yana kuma nuni cikin koreea da tabbatarwa. ma'ana kada a karanta Kur'ani ci barkatai cikin gaggawa cikin furta lafuzza sakamakon bukatar tabbatar da haruffa don ta iya yiwuwa wani harafi ya shiga cikin wani bari dai akwai bukatar karanta shi a cikin nutsuwa da jerantawa. 

سألت أبا عبد الله عليه السلام عن قول الله عز وجل: ﴿وَرَتِّلْ الْقُرْآنَ تَرْتِيلاً﴾؟ قال عليه السلام: قال أمير المؤمنين عليه السلام: بيّنه تبيناً ولا فهذّه هذا الشعر، ولا 
تنثره نثر الزمل، ولكن إقرعوا به قلوبكم القاسية.
daga ciki akwai hadisin Ibn Sulaiman:
na tambayi Abu Abdullah Amincin Allah ya kara tabbata a gare shi game da fadin Allah Azza wa Jalla: ka kyautata karanta Kur'ani jerantawa? sai ya ce: Sarkin muminai amincin Allah ya kara tabbata a gare shi ya ce ma'ana ka bayyana shi bayyanawa kada ka dinga karanta shi cikin gaggawa kamar wake, kada ka dinga daidaita shi kamar yanda ake daidaita yashi, sai cewa ku kwankwashi kekasassun zukatanku da shi. 
fuskar kafa dalili :a bayyane yake kamar yanda yake daga abin da ya gabata daga korewa da tabbatarwa, da kuma bayanin hikima daga hikimomin kyawunta kira'a da cewa haka yana kwankwasa zukata kekasassu wadanda suka kekashe sakamakon aikata zunubai wanda kyautata karatunsa yana tausasa zuciya da kuma sanya tuba da komawa ga Allah. 
ra'ayinmu kamar yanda malamai ka. Sa suka yi ittifaki shine mustahabbanci kyawunta karatu da karhancin gaggawa da sabu zarce
amma mukami na biyu: Musannif ya bayyana Tartili da rashin gaggautawa cikin kiraa'a wanda yake kishiyar gaggawa da sauri, a cikin, Majma'ul Bahraini {jerarriyar huda, rattil da kasara ta'un da rattala idan ya kasance a bude sashe bai hawan sashe,  natija: jinkirtawa cikin kira'a} 
daga abinda yake ishara zuwa wannan ma'ana lugga kabaru Abdullah Ibn Salaimanu da ya gabata, sabida gaggawa na haifar da yankewa, sai ya zama an ari ma'anar majazan, kamar yadda ruwayar data gabata ta yi ishara kan haka. 
Cikin Kabaru Abu Basir da aka rawaito daga Majma'ul Bayan:

 (هو أن تتمكث فيه، وتحسن به صوتك) ]).
ka dan yi jinkiri cikinsa ka kuma kyawunta sautinka. 
na biyu: bayyana haruffa cikin wani yanayi da mai sauraronka zai iya kidaya su, kada ya zama wani harafi yana shiga wani, daga masana lugga akwai wanda ya fassara tartil da cewa shine jerantawa da bayyanawa ba tareda zalunci ba, ko kuma sakin magana. 
Karfafawa: bayyanar da haruffa da kausasa wasali, na biyu jinkiri da bayyanar da haruffa da wasali, ma'ana kada yayi gavgawa cikin sakin haruffa bari ya tsaya ya nutsu cikinsu da bayyanarwa daki-daki 
bai buya ba dukkanin wadannan bayanai da ta'arifat kadai dai suna daga babin sharhul. Ismi da kuma ishara zuwa abinda yake yafi yaduwa da kafuwa a kwakwalwar mai sauraro da wanda ake magana da shi.
Kamar kalmar Sa'adanatu da zarar an ce mecece ita?  cikin sauri za ace ai wannan wani tsiro ne
haka an fassara tartil cikin littafin Azzikra da waninsa_kamar yanda aka hakaito cikin Almumtamsakjuz 6 sh 274 da cewa shine kiyaye wakafi da sauke haruffa, sannan an danganta wannan ta'arifi zuwa ga Sarkin Muminai amincin Allah ya kara tabbata a gare shi, kamar yanda yazo  cikin Alwafi babi na 12 daga babukan Kur'ani da falalolinsa karshen hadisi na farko, haka cikin Majma'ul Bahraini cikin kalmar (ratala) 

daga wasu ba'ari sun nasabta haka zuwa ga Annabi mafi karamci (s. a. w) Sannan Assayid Hakim {k.s} ya tafi kan cewa shi ne kiyaye wakafi zai iya kasancewa ma'anarsa ta koma zuwa ga abinda ya gabata daga ta'arifat, amma sauke haruffa shi wannan ya a daga wajibi baya daga mustahabbi kamar yadda yake a zahiri, sai dai idan manufa daga gareshi ta kasance bayanin haruffa kada a dinga sururi cikinsa kamar yanda bayani ya gabata, ra'ayinmu shi ne mustahabbanci tartili da dukkanin ma'anarsa a luggance da al'adance
Musannif {k. s} ya ce : na hudu shine kyawunta sauti ba tareda rera wake ba. 

ina cewa : mustahabbi na hudu cikin kira'a shine kyawunta sautinsa da sharadin ka da  ya kai ga zama wake na haramun, amma kyawunta sauti lallai shuhura da ittifakin manyan malamai na shiryarwa zuwa gareshi kamar yanda jumla daga nassoshi ke bada shaida kan hakan, daga cikinsu Kabaru Annaufali
 النوفلي عن أبي الحسن عليه السلام: (ذكرت الصوت عنده، فقال: إن علي بن الحسين عليه السلام كان يقرء فربّما مرّ به المار فصعق من حسن صوته([3]).
daga Abu Hassan amincin Allah ya kara tabbata a gare shi : na ambaci wani sauti a wurinsa sai ya ce : lallai Ali Ibn Husaini Amincin Allah ya kara tabbata a gare shi ya kasance yana kira'a ta yiwu wani mai wuce ya wuce ta gefansa sai ya sume sabida dadin sautinsa. 
وخبر ابن سنان عن أبي عبد الله عليه السلام: قال النبي صلى الله عليه وآله وسلم: لكل شيء حِلية، وحلية القرآن الصوت الحسن.
Kabaru Ibn Sinanu daga Abu Abdullah amincin Allah ya tabbata a gareshi yace:  Annabi (s.a.w) yace: kowanne abu yana da ado shi adon Kur'ani shine kyakkyawan sauti. 
amma maganar cewa kada ya zamana kamar wake shine rinjayar da sauti tareda sassabcewa cikin wasali da dadada shi kamar yanda yake wurin Fasikai. 
cikin riwayar Ibn Sinanu:
عن رسول الله صلى الله عليه وآله: (سيجيء من بعدي أقوام يرجعون القرآن ترجيع الغناء والنوح والرهبانية لا يجوز تراقيهم، وقلوبهم مقلوبة وقلوب من يعجبه شأنهم.

daga Manzon Allah (s. a.w): zamani zai zo bayana za a samu wasu mutane suna rera karatun Kur'ani irin rerawar wake da kuka da Rahbaniyyawa karatun bai ketare makogaronsu, zukatansu juyayyu ne da zukatan da wanda suke birgewa. 
([1]).الوسائل: باب 18 من أبواب القراءة في الصلاة الحديث الأول.

([2]).الوسائل: باب 21 من أبواب قراءة القرآن الحديث الرابع.

([3]).الوسائل: باب 24 من أبواب قراءة القرآن الحديث ا

Tura tambaya