lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

Bahasul-Karijul Fikhi 6 ga Shawwal shekara 1441 hijiri

Bahasi kan mustahabban karatun sallah, Fikhu (87)

Wuri: Muntada Jabalul Amil Islami_tareda Ustaz Assayid Adil-Alawi (h)

Lokaci: 8-9 na Safiya

Cigaba na bahasin da ya gabata gabanin bullowar annobar cutar Korona da ta mamaye baki dayan duniya ita cuta ce da ba a iya ganin ta da idanu, cikin jin kan Allah da rahamarsa mai kyawu daga abinda yake cikinta daga darasussuka da ababen fadakuwa da wa’aztuwa, lallai babu abinda muka gani cikinta sai alheri cikin jin kansa, hakika wannan annoba da bata gushe ba tana sauka da fushin ubangijin da azabarsa tana kama milyoyin mutane ta kuma salwantar da rayukan dubban daruruwan mutane a fadin duniya.

A wancan lokaci gabanin wannan annoba mun kasance cikin bayanin jumla daga mustahabban karatun sallah kamar yanda Almuhakkikul Hilli ya gangara cikin bayanin, hakika bayani ya gabata kan guda shida daga cikinsu sune; isti’aza gabanin fara karatun a raka’ar farko.

2- bayyanar da bismilla a muhallin da ake boye karatun salla, haka zalika cikin raka’o’in biyun karshe idan ya zabi karanta Fatiha mayin tasbihi, amma a muhallin bayyana karatu to anan wajibi bayyanar da bismilla kan limami da ma wanda yake sallah shi kadai.

3-Tartili: kyawunta karatu binsa daki-daki sannu-sannu da bayyanar da haruffa da fito da su cikin yanayin da mai sauraro zai iya kidaya su.

4-kyawunta sauti amma ba da yanayin wa`ke ba.

5-wakafu: wakafi ma’ana dagatawa kan gabar kowacce aya.

6-la’akari da ma’anonin da ayoyin suka kunsa da kuma wa’aztuwa da su.

Ya zo cikin littafin Ma’ani Akbar daga Shaik Assaduk (k.s) daga Muhammad Ibn Kasim daga Muhammad Ibn Ali Alkufi daga muhammad Ibn Kalid daga wasu ba’arin Malamai daga Dauda Arrakiyu daga Abu Hamza Assimali daga Abu Jafar amincin Allah ya kara tabbata a gareshi yace:  

قال أمير المؤمنين عليه السلام: ألا أخبركم بالفقيه حقاً؟ ـ والمراد بالفقيه الفاهم في الدين كما في آية النفر في قوله تعالى: ﴿فَلَوْلا نَفَرَ مِنْ كُلِّ فِرْقَةٍ مِنْهُمْ طَائِفَةٌ لِيَتَفَقَّهُوا فِي الدِّينِ وَلِيُنذِرُوا قَوْمَهُمْ إِذَا رَجَعُوا إِلَيْهِمْ لَعَلَّهُمْ يَحْذَرُونَ([1]).

Yanzu bana baku labarin wane ne cikakken Fakihi ba? abinda ake nufi da Fakihi anan shine mai Fahimtar addini kamar yanda ya zo cikin ayatun Nafar cikin fadinsa madaukaki: (saboda me wata jama’a daga kowanne bangare ba zata fita domin neman fahimtar addini da kuma gargadin mutanensu idna sun dawo zuwa garesu tsammaninsu sa gargadu).

Fikihu a cikin isdilahin Kur’ani mai girma yana hadowa Akidu shine ma wanda ake kira da Fikhul Akbar, shi kuma Ilimin Aklak ana kiransa da sunansa Fikhul Ausad, sannan fikihun da ya kunshi bayanin halal da haramun ana kiransa da Fikhul Asgar, Fakihi na hakika bana jeka nayika ba kona wahami da hiyali shine wanda yana tattaro wadannan siffofi halaye da bayaninsu zai zo a kasa.

1-shine wanda baya sanya mutane su debe tsammani da sa rai daga rahamar Allah, babu wanda suke debe tsammani da sa rai daga rahamar Allah sai Kafirai, to kada shi ya zama sila da sababin kafircewar mutane.

2-shine wanda baya lamintar da su daga azabar Allah, lallai babu wanda yake amintuwa da lamintuwa daga makircin Allah da azabarsa face Fasikai da Kafirai.

3-kada ya kasance mai sassauci da sahhale sabon Allah, ya zama yana mayar da abinda yake haramun halal.

4-kada ya zama ya ajiye Kur’ani sakamakon kwadayin waninsa ko da kwadayin littafan sammai da kasa lallai shi Kur’ani shine jigo mai bada kariya ga sauran litattafan sama.

5-lallai babu alheri cikin ilimin da babu fahimta cikinsa, fahimta itace fikhu shine abinda yake bayan ilimi daga tabbatattun abubuwa da ma’arifofi.

6- shin ba zasu dinga yin tadabburin Kur’ani ba ko kuma dai zukatansu a kulle suke.

Ita kalmar tadabburi ta samo asali daga (Adduburi) bayan wani abu, sai ya zama ya ciratu daga zahiri zuwa badini cikin tanjizi da tawili, lallai Kur’ani yana da badinai kumai shi wata mikakkiyar igiya ce geffanta yana hannun Allah daya gefan na hannun mutane, duk wanda yayi riko da Kur’ani Mai girma ya tsira daga fadawa rijiyar zunubai da kaskanci zai kuma daukaka zuwa madaukakin matsayi da mukami tsakanin Baka biyu ko kuma mafi kusanci daga haka.

7-babu alheri cikin ibadar da ba ta tareda fahimta, lallai duk wanda bai samu fahimta cikin ibadarsa da addininsa ya kasance Jakin da ake kodagon nika da shi kamar yanda bayanin hakan ya zo daga Sarkin Muminai Ali amincin Allah ya tabbata a gareshi, wannan Jaki ya kasance ana rufe idanunsa a kada shi ya motsa ya dinga juya na’urar nika dare da rana  sai dai cewa lokacin da aka bude masa idanu sai ya ga cewa yana nan tsaye inda yake kamar bai motsa ko ina ba daga inda yake, ma’ana bai kasance kan hanya mikakka ba, me yafi yawa daga nassoshi da ayoyi cikin bayanin misalin wannan mai ibada babu fahimta, hakika fakaha da tadabburi fahimta suna samar da wayewa cikin addini duniya da lahira.

Ya zo cikin Wasa’il kuma Kulaini ya rawaice shi daga wasu adadi daga Malamanmu daga Ahmad Ibn Muhammad Albaraki daga Isma’il Ibn Mihran daga Abu Sa’id Alkammad daga Halabi daga Abu Abdullah amincin Allah ya tabbata a gareshi yace: Sarkin Muminai Ali (a.s) yace, sai ya kawo hadisin misalinsa.

Ya zo cikin Kabaru Abdur-Rahman Ib Kasir daga Sarkin Muminai  amincin Allah ya tabbata a gareshi cikin siffanta masu takawa cikin hudubar Hammam kamar yanda ya zo cikin Nahjul Balaga: (sune wadanda cikin dare zaka samu kafafunsu sahu-sahu, suna masu karanta juzu’an kur’ani suna kyawunta karatunsa suna jeranta shi jerantawa) har zuwa wajen da yake cewa: idan suka gifta ta gefan wata aya wacce cikinta akwai tsoratarwa sai su gaza kunnen zukatansu gareta da idanuwansu, sai ka ga fatukansu sun kwansare zukatansu suna razana, su ji cewa karajin jahannama da shashshakarta can cikin kunnensu, idan kuma suka gifta gefan wata aya da take kwadaitarwa sai su karkata zuwa gareta sabida sa rai sannan rayukansu su tsinkayu kanta sakamakon shauki zuwa gareta, su yi zaton cewa rabon idanuwansu ce.

Bai buya ba cewa Malamai daga dukkanin bangarrorin biyu Sunna da Shi’a sun yi sharhi da bayani filla-filla kan wannan huduba, kana iya komawa cikin littafin (Azzari’atu).

Almuhakkikul Hilli (k.s) yace: cikin ayoyin ni’ima da azaba ya roki Allah abinda ya dace daga garesu.

Hakika addu’a itace ruhi da `bargon ibada, wanda ya kasance cikin ibadar karatun Kur’ani da da tilawarsa lallai daga abinda yafi dacewa gareshi shine kasancewa Mai addu’a da rokon ubangiji   

﴿قُلْ مَا يَعْبَأُ بِكُمْ رَبِّي لَوْلا دُعَاؤُكُمْ

Kace ubangijina bai damu daku b aba don addu’o’inku ba.

Daga cikin addu’a cikin Kur’ani Mai girma yayin da yake karanta ayoyin niu’ima kamar Ambato Aljanna da ni’imominta to ya roki Allah ya bashi Aljnnar da ni’imominta, haka lokacin da ya zo kan ayar azabar Allah sai ya nemi tsarin Allah daga gareta

 (وإغفر لي الذنوب التي تنزل النقم وتورث السّقم وتغير النّعم)

Ka gafarta mini zunuban da suke saukar da azaba da gadar da cuta da sauya ni’ima.

 ﴿وَاسْأَلُوا اللَّهَ مِنْ فَضْلِهِ﴾.

ku roki Allah falalarsa

ya zo cikin littafin Wasa’il cikin ba babukan Kira’ar Kur’ani Mai girma a babi na uku: (babul istihbabi tafakkuri fil Ma’anil Kur’ani wa amsalihi wa wa’idihi wama yaktadihil I’itibari wal ta’assuri wat itti’azi wa su’ali janna, wal isti’aza minan nari inda ayatiha) cikin wannan babi akwai riwayoyi guda takwas cikin raiwaya ta takwas: daga Fadalu Ibn Hassan Addabarasi cikin littafinsa (Majma’ul Bayan) daga Abu Abdullah yace: idan ka wuce ta gefan wata aya da ta kunshi da ambaton Aljanna, haka idan ka wuce ta gefan aya da ta kunshi ambaton wuta to ka nemi tsarin Allah daga wuta.

Mawallafin littafin Wasa’il (k.s) yace: bayani ya gabata kan abinda yake shiryarwa kansa.

Kamar yanda ya zo cikin riwaya Mursala ta Ibn Abi Umairu daga Abu Abdullah amincin Allah ya kara tabbata a gareshi

 (ينبغي للعبد إذا صلّى أن يرتل في قراءته، فإذا مرّ بآية فيها ذكر الجنة وذكر النار سأل الله الجنة وتعوذ بالله من النّار([4]).

Ya kamata bawa idan yayi sallah ya kyawunta karatunsa, idan ya gifta ta wata aya da cikinta aka ambaci Aljanna da wuta to ya roki Allah Aljanna ya kuma nemi tsari daga wuta.

8-yin shiru kadan tsakanin karatun Fatiha a Sura, haka bayan gama karatun zuwa kunuti ko kabbarar ruku’i.

Ina cewa wannan shine abinda Mashhur suka kai kamar yanda ya zo cikin hadisin Is’hak Ibn Ammar daga Imam Jafar Ibn Muhammad Assadik daga Babansa (a.s)

إسحاق بن عمّار عن الإمام جعفر بن محمد الصادق عليه السلام عن أبيه: أن رجلين من أصحاب رسول الله صلى الله عليه وآله إختلف في صلاة رسول الله صلى الله عليه وآله وسلم فكتبا إلى أبي بن كعب: كم كانت لرسول الله صلى الله عليه وآله وسلم من سكتية؟ قال: كانت له سكتتان إذا فرغ من أم القرآن، وإذا فرغ من السورة([5]).

Wasu mutum biyu daga Sahabban Manzon Allah (s.a.w) sun yi sabani cikin sallar Manzon Allah (s.a.w) sai suka rubuta wasika zuwa ga Ubayyu Ibn Ka’ab suna tambaya: sau nawa Manzon Allah (s.a.w) yake dan yin shiru cikin sallah? Sai yace: sau biyu: lokacin gama karatun Fatiha da kuma bayan gama karatu Sura.


([1]).التوبة: 122.

([2]).

([3]).الوسائل: باب 3 من أبواب قراءة القرآن الحديث السادس.

([4]).الوسائل: باب 18 من أبواب القراءة في القرآن الحديث الأول.

([5]).الوسائل: باب 46 الحديث: 

 

Tura tambaya