lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

Kada ku riƙi wannan ƙur'ani abin ƙauracewa


Da sunan Allah Mai rahama Mai jin ƙai

Dukkanin yabo da godiya sun tabbata ga Allah Ubangijin Talikai maɗaukakin Sarki tsira da aminci su ƙara tabbata ga fiyayyen halitta Muhammad da iyalansa tsarkaka waɗanda ya tafiyar da dukkanin kazanta da datti daga barinsu. 

bayan haka:

haƙiƙa ƙarƙashin ludufi da tausayin ubangiji bayan halittar bil Adama tareda haske da yake haskaka masa hanyoyi da banbanta masa abubuwa biyu masu kishiyantar juna ina nufin hankali, ya zo a riwaya cikin littafin Alkafi: farkon Abinda Allah ya fara halitta shine hankali, sai ubangiji yace masa matso fuskanto sai ya matso sannan yace masa juya sai ya juya, ubangiji yace na rantse da buwayata da girmana da kai nake sakawa na bada lada kuma ina uƙuba kan saɓa maka.
Tareda wannan babbar kyauta mai tsada haske mai haskaka hanya ubangiji bai gushe yana cika ni'ima da tautayinsa kan bayinsa ta hanyar aiko da Annabawa da Manzanni da litattafai da saƙonni domin kammala naƙasa da tawayar da suke da ita, sabida akwai abubuwa da hankali kan gaza riskar maslaharsu da mafsadar da take cikinsu, daga wadannan litattafai akwai dawwamammiyar mu'ujiza wato Ƙur'ani Mai girma, shi littafi ne da ya tattaro duk wani amfani da cike gurbi da kammala kamala da maslaha da ta shafi dukkanin shiriyar ɗan Adam. 
ما فرطنا في الكتاب من شئ. 
ma'ana shi wannan littafi ya ƙunshi duk wata shiriya ɗan Adam. 

Cikin misalin wannan zamani da wanda yake halaka yake halaka, wanda kuma Allah ya datar da shi yake tsira musulmi yana bukatar kur'ani mai girma wanda cikinsa akwai waraka ga mutane daga dukkanin  cututtuka da kuma kariya kuma shi mafaka da rahama da dukkanin bala'i da wahala, inda Allah madaukaki yake cewa: 

: وَنُنَزِّلُ مِنَ الْقُرْآنِ مَا هُوَ شِفَاءٌ وَرَحْمَةٌ لِلْمُؤْمِنِينَ وَلَا يَزِيدُ الظَّالِمِينَ إِلَا خَسَاراً (الإسراء: 82).

Kuma muna saukarwa daga Kur'ani abinda yake waraka da rahama ga Muminai kuma babu abinda yake ƙarawa Azzalumai face hasara.

Hakika hadisi ya zo daga manzon Allah (s.a.w) cikin faɗinsa

«فإذا التبست عليكم الفتن كقطع الليل المظلم فعليكم بالقرآن فإنه شافع مشفّع وماحل مصدّق، ومن جعله أمامه قاده إلى الجنة ومن جعله خلفه ساقه إلى النار وهو الدليل يدل على خير سبيل ..» (1).

Idan fitintinu suka rikita ku kamar misalin yankin dare mai tsananin duhu to kuyi riƙo da Ƙur'ani lallai shi Mai ceto ne Mai cetarwa kuma gasgatacce ne, dukkanin wanda ya sanya shi a gabansa zai jagorance shi zuwa Aljanna sannan duk wanda ya yi watsi da shi zai kora shi zuwa wuta shi dalili ne Mai shiryarwa zuwa mafi alherin tafarki.

Muhimmancin tafsirin kur'ani da mahangar tunani da zamantakewa

Mene ne muhimmanci tafsirin kur'ani mai girma a mahangar tunani da zamantakewa?

Hakika mutum ya banbanta da sauran halittu ta fuskanin tunani, amma ta fuskar ci da sha da motsi da barci da girman jiki bai da banbanci da sauran dabbobi daga cikin halittu, amma fifitarsa to wannan ta kasantu ne sakamakon tunani da yake yi, tare da haka hakika hankalin mutum tauyayye ne sakamakon nadama da yake yi a wani lokaci, zaka samu da yawan lokuta mutum yana yin nadama, saboda haka kasantuwarsa ma'abocin tauyayyen tunani yana bukatuwa zuwa ga wahayi, Allah madaukaki ya  saukar mana kur'ani wahayi daga gareshi, shine abin kwaikwayon hankulanmu wanda da shine muka fifitu muka banbantu daga Dabbobi.

Sannan shi kammalallen addini ya zama dole yayi kallo zuwa ga dukkanin mas'aloli, wannan shine abinda muke samu cikin Ƙur'ani Mai girma, alal misali cikin ƙur'ani Allah na magana zuwa ga yaran da basu balaga ba inda yake cewa: 

يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا لِيَسْتَأْذِنْكُمُ الَّذِينَ مَلَكَتْ أَيْمَانُكُمْ وَالَّذِينَ لَمْ يَبْلُغُوا الْحُلُمَ مِنْكُمْ

Tura tambaya