lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

nasiha da nusantar al'umma

Kasantuwar Imam Sajjad ya rayu cikin zamani matsi da tsanani, bai iya samun damar isar da sako a bayyane ba, sai ya zamana yayi amfani da hanyar wa'azi sai ya zamana ya karantar da muatne ta hanyar wa'azi wannan hanyar isar da sako tasa ta dinga tona asirin mahukunta Azzalumai, sakonni da ilimummukan da tuni an rigaya an manta da su ko kuma an jirkitasu, cikin wannan hikima ya dinga tunatar da mutane su ya karantar da sakon muslunci da dukkanin karfin da yake da shi ta wannan hanya.

Bincika wannan hanya ta wa'azi na nuni da cewa Imam (a.s) yayi amfani da hanya ta hikima da basira cikin isar da sako, domin ya kasance yana yiwa mutane nasiha da wa'azi kuma yana isar da sakon da yake son isar zuwa ga mutane ta wannan hanya, wannan yana daga mafi kyawun hanyar isar da sako kuma da haifar da tasiri da samar da natija ta siyasa kan Azzaluman mahukunta, cikin wannan hanya ya tsira daga fushin Azzaluman mahukuntan zamaninsa.

Daya daga cikin samfuri daga irin wadancan bayanai nasa da wa'azuzzuka wanda ya kasance mafi kyawun shaida da tarihi ya dawwana, shine bayaninsa mai fadi dalla dalla kamar yanda malaman hadisi sukayi bayaninsa, cewa Imam ya kasance a kowacce ranar juma'a a masallacin Annabi (s.a.w) yana kwarara wannan bayani ga sahabbansa da sauran mutane.

3 bayyanar ilimin muslunci ta hanyar addu'a da munajati:

daya daga cikin hanyoyinsa a tabligi da yake bayanin iliman muslunci ya kasance cikin zirin addu'a, mun san cewa addu'a tsani da sila ta badini tsakanin bawa da ubangijinsa  d atake dauke da tasirin tarbiya da gina dan Adam, da wannan addu'a a mahangar muslunci ta kasance tana da matsayi da mukami na musammam, idan ta kasance daga cikin addu'arv da naka nakalto daga Annabi (s.a.w) A'imma (a.s) wannan addu'a zata kasance mabubbuga tushen tarbiya mai girma cikin gina `dan Adam sannan tana taka babbar rawa cikin gina rayuwarsa.

Sahifa Sajjadiya

Kasancewa Imam ya rayuwa cikin sa'aidon hukuma da tsanantawarsu ya zamana mafi da yawa daga cikin hadafofi da manufofinsa yana sadar da su da isar da ta hanyar addu'a da munajati, wasu adadi daga addu'o'insa da aka tattare su cikin wasu adadin takardu da aka sanya musu suna Sahifa wannan littafin mai suna a sama baya ga Kur'ani da Nahjul Balaga ya kasance babbar taska da take cike da ilimomi, ya samu kulawa ta musammam daga manya manyan malamai ta kai ga suna masa lakabi da  Linjilar Ahlil baiti (a.s) Zaburar Alu Muhammad.

Sahihfa Sajjadiya bawai kadai  ya tattaro Asararu da munajati da ubangihji da bayyana bukata a hallararsa tsarkakka bari dai wani tafkina d ayake cike daga ilimi da ma'arif din muslunci da ya kunshi ilmin Akida,tarbiyya, zamantakewa, siyasa, wani yanki daga dokokn dabi'a da hukunce hukuncen shari'a cikin dukkansu cikin zirin addu'a.

Sakamakon muhimmancin da wannan littafi yake da shi ya kasance ya rabauta da sharhi kala-kala wasunsu da yaren farisanci wasu larabci, kari kan wadannan sharhohi wasu curi daga masana magabata da na wannan zamani sun tarjama shi zuwa yarurruka daban-daban .

Wannan littafi ya kunshi addu'a guda 54, wannan littafi bayan ga Asararun addu'a da munajati da ubangiji, ya kunshi sasannin siyasa da zamantakewa da tarbiyya da akida, Imam Sajjad cikin addu'o'insa a wurare da daman gaske ya bijiro da bahasosin siyasa musammam mas'alar imamanci da jagoranci al'ummar musulmi ya sanya su cikin samfurin du'a'u mukarimul Aklak cikin jerin addu'a ta 20 da cikin addu'a ranar Arafat jerin addu'a ta 47 da du'a'u Idil Kurban  da ta rabar Juma'a.

4 gwagwarmayarsa da malaman fadar Sarki

Daga yanki mafi daukar hankali da shahara a ranyuwar Imamai shine gwagwarmayarsu da dauki ba dadi da malaman fada ina ma'ana muatne da suke mamaye wurin da basu cancanta da shi ba daga wadanda ake kira, Fakihai malaman hadisi da tafsiri Kari'ai da Alkalai, sune mutanen da suke sarrafa kwakwalen muatne su sanya karkashin ikon Azzaluman shugabanni daga Abbasiya da Umayyawa domin karfafa mulkinsu, sune bada gudummawa da taimakawa don mika su gay i musu biyayya da sallama musu, babban samfuri a wannan gwagwarmaya shine rayuwar siyasa ta  imami na hudu (a.s) hakika ya buga yayi dauki ba dadi da fitacce Malamin hadisin fada muhamnmad Ibn Muslim Zuhuri da aka haifa 58 hijiri ya mutu 124 hijiri.

Wanene Zuhuri?

Zuhuri daya daga tabi'ai Fakihai a wancan zamani kuma yana daga cikin manyan malaman hahdisi a birnin Madina ya kasance cikin jerin Fakihai bakwai a makarantar Ahlus sunna a wancan zamani ya riski mutane goma daga sahabbai, hakika ya kasance daga shahararrun magabata a wurinsu sunansa ya shahara a zauruka da matsugunan ilimi da fikhu a wancan zamani, hakika yayi almajiranta a hannun Imami na hudu aya kuma nakalci hadisai da riwayoyi masu tarin yawa daga hallararsa

Note ..wannan shafin akwai abinda za,a rubuta page ..72

Zazzafar wasikar Imami na hudu zuwa ga Zuhuri

Sakamakon munanar tarihin zuhuri a fada Imam Sajjad (a.s) ya rubuta zazzafar wasika mai nauyi kuma daidai wannan lokaci tana kunshe da fatan alheri da nasiha gareshi, ya zo cikin wasikar:  ubangiji ya karemu tareda da kai daga fitina ya kuma nesanta mu daga shiga wuta baki daya, hakika kana cikin wani hali da matsala duk wanda ya san halin da kake ciki ya kamata ya tausaya maka

Note... akwai rubutu anan shafin  72..

Ya kamata ka janye jikinka daa dukkanin mukamai da matsayi da kake kai domin ka samu damar cudanya da mutane kirki.

Ubangiji ya zabeka ya sanya ka daga cikin mutanen suke dauke da ilimin kur'ani  ya kuma ajiye amanar ilimin addini gurinka sai dai cewa ka tozarta wannan ilimi, ubangiji…….

5 yada hukunce hukunce da tarbiyya da kyawawan halaye

Wani bangare daban daga sasannin gwagwarmayarsa da zalunci da barna zamaninsa, shine yada hukunce hukunce muslunci da bayyanar da bahasosin tarbiyya da kyawawan halaye, a wannan fage Imam ya taka babbar rawa da gudummawa da manya malamai sun yi mamakin wannan gudummawa tasa, alal misali babban Malami a duniyar shi'a Shaik Mufid ya rubuta cewa:  takai ba a san adadin Fakihan Ahlus sunna da suka nakalci ilimi daga gareshi ba, ya shahara an naklaci wa'azozi da addu'a da falaloli da Kur'ani daga gareshi, dan muka ce zamu yi sharhi dalla dalla zai kallafa ma doguwar magana.

Samfuri daga ta'alim da tarbiya da Aklak da aka nakalto daga gareshi suna nan a wanze cikin littafi da ake kira da sunan Risalatul hukuk ya kunshi wazifofi daban daban da suke wuyan mutum daga wazifarsa cikin hallarar ubangijinsa da wazifarsa  kankin kansa da sauaran mutane duka anyi bayninsu a ciki, wadannan wazifofi adadinsu ya kai 50 Imam ya kawo su a dunkule daga baya kuma ya bisu filla filla.

Risalatul hukuk da malaman hadisi suka nakaltota aka rubutata cikin litattafan hadisi an tsamota ita kadai dabba'ata an kuma tarjamata.

6 taimakon mabukata

Daya daga cikin sasannin masu haske daga rayuwarsa shine hidima ga al'umma a zamaninsa a lokutan musibu a garin madina misalin lokacin waki'ar Harra, haka zalika lokacin da hankali yake kwance yak an zuwa wurin Talakawa ya kai musu taimako, hakika ya wanzu kan wannan kyakkyawan hakli har zuwa karehsn rayuwarsa, hakika tarihi ya nakalci fitatattun misalsalai daga wannan hidima da gudummawa.

Hakika Imam Sajjad ya dau nauyin daruwaun Talakawa, wasu mutane daga mutane Madina sun kasance suna rayuwa da abinci da yake zuwar musu tsakar dare daga hannun Imam Sajjad sai dai cewa basu wanene yake kawo musu wannan abinci ba, sai bayan shahadarsa suka gane cewa shine yake kawo musu abinci a kowanne dare.

Ya kasance yana boye fuskarsa da dare ya dauko gurasa da kayan abinci ya dorasu kan kafadarsa yakaiwa kowanne mutum har kofar gidansa , hakika sadaka da ake yinta a boye tana kashe fushin ubangiji.

Mutanen garin Madina sunce: mun dena samun boyayyar sadaka ne bayan mutuwar Aliyu Ibn Husaini (a.s) hakika bayan shahadarsa  a lokacin da ake masa wankan janaza sai aka ga tabo a kafadarsa da akai tambaya kan dalilin samuwar wannan tabo ai aka bada amsa da cewa wannan alama ce data samu sakamakon daukar buhun kayan abinci da yake a kowanne dare yana kaiwa mabukata.

Takaitaccen tarihi Imam Bakir (a.s)

An haifi Imam Bakir a shekara 57 hijiri a garin Madida, mahaifinsa ya rasu ya `dan shekara 9, sunansa Muhammad ana masa Alkumya da Abu Jafar ana masa lakabi da Bakirul ulum.

Mahaifiyarsa ta kasance Ummu Abdullahi `diya ga Imam Hassan Almujtaba (a.s) shine mutum na farko da tsatsonsa daga kowanne bangare ya gangaro daga Fatima Azzahara da Ali (a.s) yayi shahada 114 hijiri a garin Madina an binne shi a makabartar Baki'a kusa da kabarin babansa da kakansa.

Halifofin da suka zamani da shi.

1 Walid Ibn Abdul Malik 86-96

2 Sulaiman Ibn Abdul Malik 96-99

3 Umar Ibn Abdul Aziz 99-101

4 Yazidu Ibn Abdul Malik 101-105

5 Hisham Ibn Abdul Malik 105-125

Assasa babban asasin harkar ilimi

Imam Bakir a lokacin Imamancinsa cikin wannan matsanancin yanayi da ya rayu ya tashi kan yada ilimi da haka'ik da ilimin tauhidi yayi sharhi da warware duk wani dabaibayi na ilimi ya raya ilimi ya zama matsayin wanda ya assasa babbar jami'ar ilimin muslunci wacce takai kololuwar ta da tashen a zamanin `dansa Imama Sadik (a.s)

Hakika Imam Bakir ya shahara da zuhudu da falala ya tattaro dukkanin mukamin ilimi da kyawawan dabi'u da ya kai ga masoya da Makiya kowa na gasgata shi, hakika ya wanzar da hadisai da ilimin tafsiri da sauarn nau'ukan ilimi da babu wasu daga yayan Hassan da Husaini (a.s) daga wadanda suka gabace shi suka wanzar da misalinsu.

Manyan mutane daga Malamai a zamaninsa haka wasu adadi daga sahabbai da suka riski zamaninsa sun amfana daga baiwar da Allah yayi masa, Jabir Ibn Yazid Ju'ufi da Kisanu Sujustani daga Tabi'ai da kuma Fakihai misalin Ibn Mubarak, Zuhuri, Auza'I, Abu Hanifa, Malik Ibn Anas, Shafi'I, Ziyad Ibn Munzir Nahadi dukkanin sun amfana daga iliminsa wani lokacin kai tsaye wani kuma lokaci da wasidar wasu.

Litattafai da talifai manyan malamai da marubuta tarihi misalin Dabari , Balazari,Khadibul Bagdadi, Abu Na'im Isfahani, littafai misalin muwadda Ibn Malik, Sunanu Abi Dauda, Musnadu Abi Hanifa, Musnad Maruzi, Tafsirul Nakkash, Tafsirul Zamakshari, da gomamon litattafai da suka kasance daga mafi muhimmanci littafai aduniyar Ahlus sunna cike suke da ilimummukan Imam Bakir (a.s), kaji ance Muhammad Ibn Ali yace ko kuma Muhammad Albakir.

Suma littafan shi'a cike suke da ilimansa da hadisansa, mafi karanci sani da littafan shi'a zai fahimci wannan magana zai kuma gasgata ta.

Imam Bakir (a.s) a mahangar Malamai

Sautin ilimin Imam Bakir (a.s) ya cika dukkanin garurun musulmi.

Ibn Hajar Haitami daya daga cikin shahararrun Malaman Ahlus sunna ya rubuta: shi Muhammad yana matsayin boyayyar taskar ilimi da ya samar, ya bayyanar da tabbatattun ilimummuka da hikimomi wadanda basu buya ba ga dukkanin mutumi mai basira, ya tsaga ilimi tsagawa, ya daga tutar ilimi, Abdullahi Ibn Ada'u daya daga cikin fitattun Malamai daga a zamanin Imam Bakir yana cewa: ban taba ganin wani masani daga Malaman muslunci da ya kai ilimin Imam Bakir (a.s) ba, misalin Hakam Ibn Atiba da ya kasance daga manyan Malamai to ina ganinsa matsayin dan karamin Almajiri a gaban Muhammad Ibn Ali (a.s) na samehsi ya durskusawa gabansa yana kwasar baiwar da Allah yayi masa.

Imam Bakir (a.s) galibi cikin zantukansa zaka samu yana jingine da ayoyin Kur'ani, yana cewa: duk abinda na fada to ku tambayeni a wacce a ina yake cikin Kur'ani zan gaya muku aya da take da dangantaka da abinda na fada.

Almajiran Imam Bakir (a.s):

Hazrat Bakir (a.s) yana da fitattun dalibai a fannoni daban daban daga fikhu da hadisi tafsiri da sauran ilimin muslunci, kowannensu zaka samesu fitacce shahararre cikin fagen ilimin da ya koya daga gareshi, cikin Almajiransa akwai manyan Malamai misalin Muhammad Ibn Muslim, Zuraratu Ibn A'ayan, Abu Basir, Buraidatu Ibn Mu'awiyatu Al'ijili, Jabir Ibn Yazid, Himranu Ibn A'ayan, Hisham Ibn Salim.

Ya kasance yana cewa: hakika mutane hudu suka raya makarantarmu da hadisan mahaifina, sune: Abu Basir, Muhammad Ibn Muslim, Buraidatu Ibn Mu'awiya Ijili, idan ace basu kasance ba da babu wanda zai amfana daga ilimin addini da hadisan Manzon Allah, wadannan mutane hudu sun kasance masu kare addini, suna daga shi'ar zamaninmu, sune mutane na farko da suka fara sanin makarantarmu, ranar lahira suna na farko da zasu fara riskarmu.

Almajira makarantar Imam Bakir (a.s) a zamaninsu sun kasance shahararru cikin fikhu da hadisi suna idna aka kwatanta su da sauran fakihan Ahlus sunna da Alkalansu zaka same su sune akan gaba sun fifice su.


Tura tambaya