فهرست کتاب‌‌ لیست کتاب‌ها
■ KALMAR TARBIYYA CIKIN HARSHEN LARABCI DA YANDA AKA YI 4
■ FASALI NA ( 2 ) 24
■ AUREN DABI'A 24
■ FASALI NA 3
■ FASALI NA 4 73
■ FASALI NA 5 131
■ FASALI NA 6 176
HAQQOQIN DA MA'AURATA SU KAYI TARAYYA CIKI 177
1 – HAQURI 178
2 – KAMEWA DAGA ZALUNCI DA CUATARWA 179
HAQQOQIN MATA 180
CIYARWA DA YALWATAWA 185
TAUSAYAWA DA KAMEWA DAGA ZALUNCI 187
KAMEWA DAGA BARIN DUKA MAI CUTARWA 187
UMARNI DA KYAKKYAWA DA HANI DA MUMMUNA 193
GARKUWA 196
8 – KYAUTATAWA : 196
9 - KYAWUNTA ZAMANTAKEWA 197
3 – TAUSAYAWA MIJI : 208
4 – HIMMATUWA DA KULA DA CIKIN GIDA DA KAYYAKINSA : 209
5 - HIMMATUWA CIKIN SAUKE HAQQOQI 209
6 – JIMA'I 210
7 - ADO 213
8 – KAMEWA CIKIN MAGANA : 219
SHUGABANTAR IYALI 225
DALILAI DA SUKE SANYA DAWWAMAR AURE 227
1 – SON JUNA 228
2 – YAWAITA AIKATA ALHERI: 228
4 – SANYA FARIN CIKI: 229
5 – BIYAYYA DA NEMAN YARDAR MIJI: 230
6 – KIYAYE MUTUNCI DA DUKIYA : 230
7 – TAIMAKO DA TALLAFAWA 230
8 – TARBAR MIJI DA KYAWUNTA BANKWANA DA SALLAMA : 231
9 – KALAMIN AQIDOJI MAI KYAWU DA QARFAFAFFEN FURUCI. 232
10 – KARBAR UZURI DA YIWA JUNA UZURI : 232
11 – BINSU SANNU SANNU CIKIN KOWANNE HALI : 233
12 – KYAWUNTA LAFAZI CIKN KOWANNE YANAYI : 233
13 – RASHIN SAURARON KYAUTATA AIKI DARI BISA DARI 233
14 – RASHIN IKON DAUKAR NAUYI A RAYUWANCE : 234
15 – RASHIN GORI KAN MIJI : 234
16 – RASHIN QAURACEWA AL'AMARIN SHIMFIDA: 235
17 - YIN SHAWARA DA MATA BANDA BIYE MUSU: 235
18 – TAKA TSAN TSAN DA KUMA FARKAWA : 238
19 – HANKALTA 239
20 - MIJI SHI NE MUTUNCIN MATARSA 240
21 – KISHI 240
22 – TAIMAKEKENIYYA 242
23 – DADADAWA IYALI 243
27 – WATSI DA BOAKANCI DA TSAFE TSAFE : 244
28 - HIDIMA MADAWWAMIYA 245
29 – GODIYA 246
29 – QAUNAR JUNA 247
TSINTUWA GUDA BIYU GIDAN ALI DA FATIMA (AS) 248
■ FASALI NA 8 252

TARBIYA DA KOYARWA 7

TARBIYA DA KOYARWA

Allah madaukaki  cikin littafinsa mai daraja ya na cewa:

 هو الذي بعث في الأميين رسولا منهم يتلو عليهم آياته ويزكيهم ويعلمهم الكتاب والحكمة[1]

shi ne wanda ya aiko manzo cikin mutanen da basa karatu da rubutu  daga gare su ya na karanta ayoyinsa a kansu yana tsarkakesu  ya na sanar da su littafi da hikima )

dukkanin wani gari da ya ginu da cigaba cikin wannan zamani da muke ciki dole ne ya kasance cikin ma'aikatu akwai ma'aikatar tarbiyya da koyarwa  kuma  ya zamanto ya na da kwalejin tarbiyya da kuma kasancewa ya na da littafin tarbiyya da darasinta cikin makarantun jami'o'i da firamare da ragowar makarantu saboda rabautar dan adam na tattare cikin iliminsa da tarbiyarsa, kamar yadda  cigaban dukkanin wani gari da al'ummarsa na tattare cikinta, addinin muslunci ya qafa wadannan asasi guda biyu tarbiyya da koyarwa cikin rayuwar dan adam cikin rayuwarsa shi kadai da kuma rayuwarsa da ragowar jama'a , haqiqa qur'ani ya yi nuni kan hikimar turo annabi mai daraja da cewa annabtarsa ta tattaru kan abubuwa biyu sune tarbiyantarwa da koyarwa: يزكيهم ويعلمهم ya tsarkakesu ya sanar da su.  tsarkakewa ta na nufin tarbiyya kalmomin biyu na da matsayi guda kamar fuka-fukan tsuntsune  bangaren dama da bangaren hagu haqiqa dan adam idan ya so tashi zuwa sararin samaniyar darajoji da sassan ma'arifa ya samu qololuwar rabauta da kamala hakan kadai na kasancewa ne ta hanyar tarbiyya koyarwa dole ne su kasance bai daya, a na dai kawai gabatar da bayanin tarbiyya kan koyarwa ta fuskacin muhimmancin  tarbiya ba don tarbiyya da har abada dan adam ba zai amfanu da iliminsa ba da iliminsa ya zame masa katanga mafi girma gabarin gaskiya da  qara nesanta daga ita. haqiqa ya fada cikin qasqanci da wulaqanta babu ilimi matukar babu tarbiya, batun tarbiyya ya tattaro  dukkanin muhimmancin shari'a da zamantakewa cikin tarihin bil adama har sai da ta kai ga zama mafi girman batu cikin dukkanin makarantun tunani da na ubangiji .

cikin tarihin wannan zamani da muke ciki  rubuce-rubuce kan tarbiya sun cika maqil albarkacin taka rawar da ta yi wajen fadakarwa da gina iyali da canja al'umma ta yanda ake la'akari da ita tushe wajen gina iyali kuma maudu'i wajen canja zamantakewa wannan wani tushe ne da ya mamaye gurbin da ya dace da shi cikin ginin muslunci  da tarihin musulmi na baya da na yanzu saboda muslunci qari kan gabatarsa kan mazhabobi da aqidoji  na zamani to haqiqa ya tattaro fusaken wayewa cikin hukunce hukuncenshi da ilimansa bari ma dai cikin gabadayan tsarin muslunci ya mai da hankali kan batun tarbiyya kuma ya dayantu da taka rawa kan gina tarbiya cikin rayuwa kowanne mutum da al'umma ballantana ma iyali, muslunci bai qasa a gwiwa ba wajen zurfafar tarbiyya da qoqarin dawo da sigar mutum da  matakinsa na kankin kansa da dangantakarsa cikin al'umma  da jama'a abinda zai sanya dacewa tare da tanadin halittarsa da aka halicce shi kanta da abinda zai  bashi tsari ya motsa shi cikin tsare tsaren tauhidin ubangiji don ya wayi gari halifa na gaskiya .[1] Al'juma'atu : 2