فهرست کتاب‌‌ لیست کتاب‌ها
■ KALMAR TARBIYYA CIKIN HARSHEN LARABCI DA YANDA AKA YI 4
■ FASALI NA ( 2 ) 24
■ AUREN DABI'A 24
■ FASALI NA 3
■ FASALI NA 4 73
■ FASALI NA 5 131
■ FASALI NA 6 176
HAQQOQIN DA MA'AURATA SU KAYI TARAYYA CIKI 177
1 – HAQURI 178
2 – KAMEWA DAGA ZALUNCI DA CUATARWA 179
HAQQOQIN MATA 180
CIYARWA DA YALWATAWA 185
TAUSAYAWA DA KAMEWA DAGA ZALUNCI 187
KAMEWA DAGA BARIN DUKA MAI CUTARWA 187
UMARNI DA KYAKKYAWA DA HANI DA MUMMUNA 193
GARKUWA 196
8 – KYAUTATAWA : 196
9 - KYAWUNTA ZAMANTAKEWA 197
3 – TAUSAYAWA MIJI : 208
4 – HIMMATUWA DA KULA DA CIKIN GIDA DA KAYYAKINSA : 209
5 - HIMMATUWA CIKIN SAUKE HAQQOQI 209
6 – JIMA'I 210
7 - ADO 213
8 – KAMEWA CIKIN MAGANA : 219
SHUGABANTAR IYALI 225
DALILAI DA SUKE SANYA DAWWAMAR AURE 227
1 – SON JUNA 228
2 – YAWAITA AIKATA ALHERI: 228
4 – SANYA FARIN CIKI: 229
5 – BIYAYYA DA NEMAN YARDAR MIJI: 230
6 – KIYAYE MUTUNCI DA DUKIYA : 230
7 – TAIMAKO DA TALLAFAWA 230
8 – TARBAR MIJI DA KYAWUNTA BANKWANA DA SALLAMA : 231
9 – KALAMIN AQIDOJI MAI KYAWU DA QARFAFAFFEN FURUCI. 232
10 – KARBAR UZURI DA YIWA JUNA UZURI : 232
11 – BINSU SANNU SANNU CIKIN KOWANNE HALI : 233
12 – KYAWUNTA LAFAZI CIKN KOWANNE YANAYI : 233
13 – RASHIN SAURARON KYAUTATA AIKI DARI BISA DARI 233
14 – RASHIN IKON DAUKAR NAUYI A RAYUWANCE : 234
15 – RASHIN GORI KAN MIJI : 234
16 – RASHIN QAURACEWA AL'AMARIN SHIMFIDA: 235
17 - YIN SHAWARA DA MATA BANDA BIYE MUSU: 235
18 – TAKA TSAN TSAN DA KUMA FARKAWA : 238
19 – HANKALTA 239
20 - MIJI SHI NE MUTUNCIN MATARSA 240
21 – KISHI 240
22 – TAIMAKEKENIYYA 242
23 – DADADAWA IYALI 243
27 – WATSI DA BOAKANCI DA TSAFE TSAFE : 244
28 - HIDIMA MADAWWAMIYA 245
29 – GODIYA 246
29 – QAUNAR JUNA 247
TSINTUWA GUDA BIYU GIDAN ALI DA FATIMA (AS) 248
■ FASALI NA 8 252

IYALI A LUGGANCE : 14

IYALI A LUGGANCE :

 

kalmar   (iyali) ta samo asali ne daga kalmar الأسر ma'ana daurewa tufkewa kamar fadin larabawa na daura siddi haka ana kiran fursunan yaqi daga wannan ace masa asir sannan akayi amfani da kalmar cikin dukkanin wanda aka qayyade aka tsare shi duk da a zahiri su iyali ba daure suke da igiya ba  a zahiri, domin iyalin mutum sune wanda suka dogara da shi da qarfafa.

wani ba'ari daga mutane na raya cewa iyali ba komai ba ne face sakamako halittar sha'awa ta jinsi da buqatuwar dan adam na dabi'arsa, kuma bai da banbanci da ragowar dabbobi cikinta, ta kasancewa biye da abin da sha'awa ta halitta ke shiftawa ta kaishi  zuwa ga karkata dabi'ar halittarsa sha'aninsa bai da wani banbanci da ire irensa cikin duniya dabbobi.

kamar yadda wasu  daban ke raya cewa iyali daidakun jama'a daga jagorori ke samar da su, saboda samar da iyali na hannun mutum mai kawo gyara, yana da haqqin karawa ko ragewa cikin assasawa ya na iya canjawa  yadda zuciya ta so masa .

wasu ne masa kallon wani tsari mai cin gashi kansa sabanin wasunsa daga tsarin zamantakewa.

gaskiyar ala'amari shi ne shi iyali wani abu ne da yake da dangantaka mai qarfin gaske da aqidun wannan al'umma da wayewar al'adunta da tarihinta da abin da ta ke tafiya kai cikin siyasarta tattalin arziqi tarbiyya da alqalanci, abubuwan da suke kewaye da ita daga yanayi cikin fannoni daban daban na bangaren rayuwa, shi daidai ya ke da kowanne gaba cikin rayayyen jiki, tsarin iyali baya daga qirqirar daidaikun mutane.

fagen iyali tun zamani baya ya kasance ya na nufin dangancewa ya zuwa dangi da sanya mata alama tunawa da wannan dangi.

wajen mutanen qasar girka da rumawa iyali na nufin  wani tsari da dukkanin makusanta ke shiga qarqashinsa  mazaje  sune ke hada kan dangi, haka bayi da iyayayen gijinsu da bayin matayensu wanda shugaban da ke riqarsu matsayin `ya `ya, ko ma ya yi da'awar su matsayin makusanta sai su wayi gari matsayin bangare cikin wannan dangi su dinga amsa sunan wannan dangi a basu damar shiga cikin sha'anin addini da na rayuwar yau da gobe, ma'ana iyali wajen girkawa da rumawa ya tsayu kan da'awa ba kusanci na jini ba, uba wajen mutane girka zamanin da ya shude shi ne mai zabar wanda zai haifa masa da cikin taron danginsa idan dangin suka goyi baya sai wannan da ya shiga danginsu a riskar da shi ciknsu su dinga qidaita shi daga gare su , amma idan suka qi goyon baya to dangantakarsu ta yanke da mahaifinsu da danginsu.

hakaal'amarin ya kasance cikin larabawa gabanin muslunci, hatta dukiyar dangi ta kasance mallakar kowa daga mutanen danginta ma'ana mallaka ce  a ma'anance ba ta mutum guda ba shari'a mai tsarki da ta zo sai ta canja tsarinsu wajen iyakance iyali , tayi wurgi da kufaifayinsa cikin abin da ya rataya da qisasi,  shari'ar muslunci ta iyakance qisasi kisa kadai kan wanda ya aikata kisan a wani wurin kuma ya bar musu wasu dokokinsu na dangi cikin abinda ya ratayu da diyyar laifin da akayi cikin kuskure.

tsarin iyali da dangi a wajen larabawa gabanin muslunci shi ne da'awa sabanin dangantakar jini,  shari'a muslunci ta rushe wannan tsari na da'awa cikin fadinsa madaukaki:

وَمَا جَعَلَ أدْعِيَاءَكُمْ أ بْنَاءَكُمْ ذَلِكُمْ قَوْلُكُمْ بِأ فْوَاهِكُمْ وَاللهُ يَـقُولُ الحَقَّ وَهُوَ يَهْدِي السَّبِيلَ  [1]  

kuma bai sanya hankakarku su zama diyanku ba wannan dai maganar ku ce kawai da bakunanku Allah na fadin gaskiya kuma shi ne mai shiriyarwa ga hanya ta gari.   

 haka kuma ya haramta mutum ya yi da'awar wani mutum matsayin uba koma bayan mahaifinsa:

ادْعُوهُمْ لآ بَائِهِمْ هُوَ أقْسَطُ عِنْدَ اللهِ فَإنْ لَمْ تَعْلَمُوا آبَاءَهُمْ فَإخْوَانُكُمْ فِي الدِّينِ وَمَوَالِيكُم[2]ْ 

ku kiraye su ga mahaifansu shi ne mafi adalci wajen Allah idan kuma baku san mahaifansu ba to `yan'uwanku a addini da dimajojin.

 shari'a ta tabbatar da cewa da na shimfida ne (uba.

daga nan ne iyali suka dinga tsukewa da raguwa akwana a tashi ya zuwa wannan zamani da muke ciki, iyali ya na nufin miji da mata da `ya`yansu su ake kira da iyalin aure.

amma ayyukan iyali suna biye da fadin iyali da tsukewa, iyalin a zamanin da ya shude sun tattaro mafi yawancin al'amurran rayuwar zamantakewa sai dai daga baya ta samu tawaya kadan kadan har a ka wayi gari tarbiyyar iyali da koyar da su ya taqaitu a wuyan iyali kadai

sannan kusanci cikin dangi da cigabansa da tsarinsa al'ummu sun yi saba ni cikinsa , akwai wadanda suke ganin hakan daga uwa mace  ana kiransa tsari na uwantaka, domin wajensu tushen kusanci na dangi shi ne uwa ita kadai, ana riskar da da  ga dangin mahaifiyarsa sannan suna la'akari da dangin uba matsayin bare ga da. wannan shi ne tsarin da ya kasance cikin qabilun qasar astiraliya. daga cikinsu akwai kuma mai ganin hakan na gangarowa ne daga uba mahaifi sun dauki uba shi ne tushe shi kadai ana riskar da da ya zuwa dangin mahaifinsa ana kiran wannan tsari da tsarin iyalin ubantaka sannan cikinsu akwai masu gani tushen dangi daga uba da uwa ya ke tare da fifita bangaren uwa kan na uba, akwai masu ra'ayi fifita bangaren uwa kan na uba, akwai kuma masu ganin duk daya ne babu wani bangare da ya rinjayi daya kamar yadda aka naqalto daga turai amma gaskiyar magana shi ne bangaren uba ya rinjayi bangaren uwa  sannan akwai wadanda ke da ra'ayin cewa tushen dangi ya dori kan wani abu daban sabanin wadannan kamar yadda suka yi riko da al'adarsu cewa yayin da yaro ke jujjuyawa cikin mahaifiyarsa zai ayyana kansa da bangaren da zai kasance, wani lokaci bangaren uba wani lokacin kuma bangaren uwa kamar yadda ya kasance cikin zamani da suka shude. saboda haka ya bayyana cewa tushen dangi cikin wannan mutane bai kasance daga jini ba,  haka bai da banbanci tsakanin uwa da uba kadai dai al'amarin na biye tsarin zamantakewar kowacce al'umma cikinsu .

saboda muhimmacin mas'alar iyali ita ce ke mamayar lamba ta farko cikin mas'alolin zamantakewar al'umma masu muhimmanci domin ita ce sinadarinta na farko, saboda kowacce al'umma na farawa daga adadin wasu iyalai domin da'ira ce guda biyu da baza su taba rabuwa da juna ba, saboda magana kan iyali ba surutu ne kawai mara ma'ana  a'a hakan ya kasance ne saboda tsananin buqatuwar jama'a ya farlanta bahasi kanta, magana game da ita ta fuskanin mahangar muslunci ba baqon abu bane,  haqiqanin muslunci ya dace da ita saboda dabi'ar ta yi daidai da ita daga warware matsaltasalinta gwargawadon yadda ya dace da dabi'arta, hakan ne dalilin da ya sanya magance mas'alar bisa hasken shari'arsa ta  adalci a kebance kuma yayinda  ake kaiwa  tsarkakakkiyar shari'armu hari da  yunkuri kawo sauye sauye da  fakewa da hujjars hada kan dokoki  bisa sallamawa tunanin `yan mulkin mallaka kafirai qarqashin taken (dokokin halayyar dan adam)

da sannu mai karatu idan ya na biye damu zai riski dacewar mahangar muslunci cikin sanin haqiqanin iyali kamar hadin kan zamantakewa, adalci, hikimar shari'a muslunci cikin tsara sha'anin iyali duka cikin bahasin wannan littafi da zai zo nan gaba.

tabbas tsara iyali a muslunce shi ne mafi kammala da gyaruwa daga dukkanin tsarurruka,yana daga cikin babban laifi da kuskuren da ba za'a taba yafewa ba ga dukkanin wanda ke qoqarin da yunqurin kawo wani tsari sabanin muslunci cikin qasashen musulmi da al'ummunsu, duk me neman wani addini koma bayan muslunci ba za a taba karba daga gareshi ba.

muslunci bai gafala ba cikin mafi sauqin al'amurra ta qaqa zai gafala kan batun iyali  wacce ake qirga ta daga mafi muhimmanci tushen al'umma cikin rayuwa bil adama bisa dogaro da abin da ke tattare da ita na daga muhimman dalilai wajen kasancewarta. haqiqa iyali sune tubalin farko wajen kasantar da al'umma, idan iyali suka gyaru suka aminta to al'umma su zasu gyaru da su samu aminci, saboda wanzuwar al'umma da katangatarta ya dogara ne da wanzuwar iyali da katangartuwarsu , rabautar al'umma da cigabansu da wayewarsu ya jingina ga lafiyar iyali da rabautarsu , mafi yawancin matsalolin mu a cikin wannan zamani sakamakon yanayin tabarbarewar iyaline tushen yawancin matsaltsali da rigingimu cikin rayuwar daidaikunmu da jama'a na komawa ga iyali iyali ke shimfida al'umma da  cikata da daidaikunta, lafiyar wadannan daidaiku ta bangaren jiki hankali ruhi da sulukinsu yana jingine ne da kubutar wannan iyali daga ciwo da mummuna gado da tabarbarewa da kaucewa hanya ta gari, qiyayya da rigingimu.  saboda shi ne yanayi na farko da daidaikunta zasu taso ciki, cikin wannan yanayi zai dinga yin mu'amalarsa tunaninsa ruhinsa tausayi da sauransu, cikinsa zai ginu daga gareshi zai karbi dokoki da al'adun al'ummar yasan shari'a da tsare tsare da dokokin zamantakewa wadda ta ke cikin al'umma sannan shi ne zai yanke hukunci mai zurfi da yanayin dangantakarsa da ita, girmamawa da matsayarsa kanta, saboda haka muslunci ya himmatu matuqa kan batun iyali.

shi ya sa ya sanya  tsare tsare wanda iyali za su ginu kai, tare da sanya shari'o'i daban daban wadda a kanta ya  iyakance haqqoqi da wajiban daidaikun wannan iyali ta fuskanin wani sashensu, haka ma muslunci bai qasa gwiwa ba wajen sanya mafita da warwara ga dukkanin matsaltsali da rigingimu da ka iya bijirowa wannan iyali cikin rayuwarsu ta yau da gobe ,

iyali sune matattarar jama'a tubalinta na gina al'umma sune tsanin da al'ummu masu girma ke tsayuwa kanshi. ginshiqin ginuwar iyali kuwa shi ne auren da aka yi nasara cikinsa wanda ke kulla qarfafaffiyar dangantaka da fahimtar  da mutunta juna tsakanin ma'aurata, ya kuma katange su daga rashin mutunta juna, sannan kuma alaqarsu ta qara qarfafa cikin samun azurtuwa da `ya`yaye  da zasu zama fure cikin gidansu su cika zukatansu da farin ciki da bushara da qauna.

mutum an halicce cikin jama'a ma'ane a dabi'ance bai iya rayuwa shi kadaiba tare da da kasantuwa cikin jama'a sai kadan daga cikin wanda suka ratse daga dabi'ar daga aka halicce su kai , saboda haka dole ne mutum ya samar da iyali da zai dinga samun nutsuwa tare da su da qamshim farin ciki .

muslunci ya zo ne shar'anta abinda zai tsare gida ya kiyaye mahalli da tsara al'umma da jama'a , sai ya kewaye iyali da qarfaffa katangar  taqawa, ya yada ruhin tarbiyya da koyarwa cikinta ya qarfafa qafafunta da ilimi da addini, ya qarfafa gininta da kyawawan dabi'u da darajoji, ya sanya mata dokoki don kareta daga rarrabuwa, ya sanya haqqi ga kowanne mutum guda daga wannan iyali da ke kishinyatarsa wanda ya zama wajibi ya sauke shi ya sanya haqqoqi da wajibai tsakanin ma'aurata, wacce qarqashinta jirgin rayuwa ke gudana ya zuwa bakin gabar tsira.

da zamu aikata muslunci haqiqanin aikatawa cikin rayuwarmu  da mun azurta da rabauta. ya zama tilas mu fito da muslunci zuwa matakin aikatawa mu kiyaye koyarwa haqiqanin kiyayewa, da juyar da shi ya zuwa sulukinmu da aiki don tabbatar da amintacciyar rayuwa  yardadda da samar da yanayin fuskantar juna.

maganar gaskiya shi ne da yawa daga rigingimun  iyali da ke kaiwa ya zuwa kotukan shari'a hakan ya faru ne sakamakon jahilcin mutane  ga hukunce hukuncen muslunci  da dokokinsa da abin da ya zo da shi kan tsara iyali nagari, da ace munsan muslunci da ababen da ya zo da su cikin shari'arsa ma'ana qur'ani mai girma da mun rabauta da farin ciki cikin  daidaiku da jama'a, da gida da iyali mai cike da annashuwa sun kasance tareda mu, ya zama dole mu san shari'ar muslunci cikin iyali, domin ta dace da halittar da lafiyayyen hankali. haqiqa hankalin shari'a bai kasance

 qayyadadde  gama gari ko daskararre ba domin tushen shari'ar muslunci shi ne wahayi daga Allah ba dokokin da wani mutum dan adam ba da ya qirqira. kamar yadda shari'ar muslunci ta goge shari'ar da ta gabaceta ta annabawa, sannan ta qara mata wasu abubuwa dadi kan na baya shi ne kasantuwar muslunci addini kammalalle cikin kowanne gari da zamani.

mutum ya na rayuwa cikin kwanciyar hankali da nutsuwa kasantuwarsa cikin inuwar iyalin da muslunci ke jagorantarta, me yafi kyawu daga wannan yanayi da uba musulmi ke dawo gidansa da masaukinsa ta yanda zai ga matarsa da `ya`yansa  ya manta da dukkanin abubuwan da suke damunsa da baqin cikinsa ya nutse cikin yanayi lafiyayye da ya cika da alaqar `yan adamtaka, to hakan bai samuwa sai cikin iyali musulma da  musluncinsu ya ingantasu saboda ingancin aqida da cikakkiyar aikatawa.

idan ba haka ba to haqiqa iyalai zasu wayi gari cikin barazanar tunanin yammacin turai da qirqirarrun dokokinsu, baqaqen musifu suyi ta afkuwa cikin iyalai musulmi daga ranar da suka yaudaru  da zahirin yammacin turai masu fitinarwa.

haqiqa daruruwan miliyoyin musulmin a qasashen najeriya fakistan da indunusiya  ya zuwa ragowar yankuna rayayyu suna fama da dokokin da basu da alaqa da muslunci ta kowacce fuska, haqiqa basu san dandanon muslunci ba basu san tarihin annabi da tsarkin dokokinsa.  dokokin muslunci wajensu basu kai ga takawa bakin qofar dakunan shari'ar aure da saki ba, ba za'a taba samun kubuta ba sai anyi watsi da wayewa da fahimtar yammacin turai, da dawowa ya zuwa mabubbugar wayewa da fahimtar muslunci.

ta bayyana cewa tunanin mutum ya gaza wajen samarwa dan adam farin ciki da rabauta da mutumtakarsa babu abin da ya rage wa mutum face sallamawa tsarin ubangiji  don kubuta, ba zai kasance ya na fagarniya cikinsa da shan wahala ba.

haqiqa fikirar ubangiji wacce ya saukar da ita ta hanyar annabawa wacce ta bayyanu cikin shari'ar da ta zo daga sama wacce ubangiji ya so ta zama mai hukunci kan dokokin da mutum ya qirqira, sannan wannan fikira ta ubangiji ta kasance kammalalliya da manzancin mafi girman annabawa cikamakinsu muhammadu dan abdAllah (saw) don ya zama shi ne tsari na har abada wanda zai samarwa da mutum tsira da rabauta duniya da lahira.ya rabauta tsiran gida biyu:

  اليَوْمَ أكْمَلْتُ لَكُمْ دِينَكُمْ وَأتْمَمْتُ عَلَيْكُمْ نِعْمَتِي وَرَضِيتُ لَكُمُ الإسْلامَ دِينا[3]ً 

اyaune na  kammala muku addininku na cika muku ni'imar da ke gareni na yardar muku muslunci matsayin addini.

fikira da tunanin ubangiji bai zamo iyakantacce da zamani ko wani bigire sabanin hankali da tunani dan adam wanda iyakantacce ne ajizi, fikirar ubangiji na sanar da mutum cewa shi an halicce cikin mafi kyawun tsari da daidaituwa kuma rayuwarsa ba iya kance ta da iya kwanakinsa cikin ban qasa ba, bari ma dai ita miqaqqa ce cikin zamani da bigire, haqiqa ganawarsa da ubangiji ta kasance a duniyar kwayar zarra kuma ya yi imani da ubangijinsa da amsa kiran tauhidinsa, saboda cikin tsarin halittar dan adam akwai aqidar samuwar ubangiji tun yarintarsa ya ke tambayar kansa kan ubangijinsa da neman hujja da dalili, yadda al'amarin ya ke shi ne dukkanin wani sababi ya na da wanda ya yi dalilinsa kuma dukkanin wani abu akwai wanda ya qera shi, dukkanin wani yaro ana haifarsa kan halittar tauhidi sai dai daga baya iyayensa su maishe shi yahudu ko banasare ko bamajuse.

 muslunci ya zo don gyara iyali, haqiqa al'umma ta gari na tasowa kan iyali nagari.

motsin mutum na kasancewa dalilin dayan manhajoji biyu na dan adam da ubangiji, dokokin ban qasa wanda dan adam ya qirqira da dokokin sama na Allah tsarki ya tabbata gareshi  wannan na nuni da cewa fikirar mutum qirqirar tunaninsace amma fikira da tunanin ubangiji daga wahayinsa ke zuwa. saboda haka dole ne mutane su kasance suna da wata manhaja da zata tarbiyantar da su da sanar da su ya ya zasu rayu tare da ubangijinsu da iyalensu da jama'arsu da dabi'ar da suke cikinta, wani lokaci tunanin dan adam kan gazawa ya kai ga inkarin ubangiji to ta qaqa zai iya iyakance alaqarsa da Allah ? kowa ya san irin makircin da turawan yamma ke shirya wajen tarwatsa iyali da rusheta, haqiqa qasar amerika wadda ta gina cigabanta da wayewarta kan tushen zahiri,  ta yadda ya kai ta aike da jirgi zuwa sararin samaniya ya yi yawo cikin samaniya amma duk da haka sun gaza wajen gina iyali guda wanda `ya`yanta za su rayu cikin kwanciyar hankali da farin ciki da tausayin iyaye, wajensu da zarar yarinya ta kai shekaru 12 - 14 cikin iyalin da suke kiransu da sunan jaha  sai su bude mata qofa su ce mata ke kin`yantu fita ki aikata abin da ranki ke so ke yanzu ke cikakkiyar macece doka ta baki ikon yin yadda kike so cikin dukkanin abin da ya kebance ki, me kuke tsammani sakamako zai kasance ? yarinya zata fito tana cikin shekarun `yan matancinta ta kutsa kanta cikin jama'ar da ta gurbata da fasadi, kurayen samari gurbatattu  na nan cikin tsimayinta  basu iya bata gutsiren gurasa sai idan ta sadaukar musu da mutuncinta da karamarta, bayan shudewar shekara 1 ko 2 da barinta gida sai ta wayi gari ana qidaya ta cikin miliyoyin matasa da suka afkawa shaye shayen tabar wiwi hashisha da hodar ibilis da sauran kayan maye masu hatsari da zasu dinga ingiza ta zuwa ga karuwanci, wannan shi ne yadda `ya`ya ke kasancewa ya ka ke tunanin iyaye da suke cikin halin tsufa da gazawa ba tsimi babu dabara da ta rage musu. wannan shi ne bala'in da amerika da ragowar qasashen da suka yi inkari da jayayya da ubangiji da addini da kyawawn dabi'u suka samu kansu. haqiqa sautin masanansu ya daga ya na ta neman dauki wajen dawo da ginin iyali nagari.[1]Ahzab:4

 

[2] Ahzab:5

[3] Ma'ida:3