فهرست کتاب‌‌ لیست کتاب‌ها
■ KALMAR TARBIYYA CIKIN HARSHEN LARABCI DA YANDA AKA YI 4
■ FASALI NA ( 2 ) 24
■ AUREN DABI'A 24
■ FASALI NA 3
■ FASALI NA 4 73
■ FASALI NA 5 131
■ FASALI NA 6 176
HAQQOQIN DA MA'AURATA SU KAYI TARAYYA CIKI 177
1 – HAQURI 178
2 – KAMEWA DAGA ZALUNCI DA CUATARWA 179
HAQQOQIN MATA 180
CIYARWA DA YALWATAWA 185
TAUSAYAWA DA KAMEWA DAGA ZALUNCI 187
KAMEWA DAGA BARIN DUKA MAI CUTARWA 187
UMARNI DA KYAKKYAWA DA HANI DA MUMMUNA 193
GARKUWA 196
8 – KYAUTATAWA : 196
9 - KYAWUNTA ZAMANTAKEWA 197
3 – TAUSAYAWA MIJI : 208
4 – HIMMATUWA DA KULA DA CIKIN GIDA DA KAYYAKINSA : 209
5 - HIMMATUWA CIKIN SAUKE HAQQOQI 209
6 – JIMA'I 210
7 - ADO 213
8 – KAMEWA CIKIN MAGANA : 219
SHUGABANTAR IYALI 225
DALILAI DA SUKE SANYA DAWWAMAR AURE 227
1 – SON JUNA 228
2 – YAWAITA AIKATA ALHERI: 228
4 – SANYA FARIN CIKI: 229
5 – BIYAYYA DA NEMAN YARDAR MIJI: 230
6 – KIYAYE MUTUNCI DA DUKIYA : 230
7 – TAIMAKO DA TALLAFAWA 230
8 – TARBAR MIJI DA KYAWUNTA BANKWANA DA SALLAMA : 231
9 – KALAMIN AQIDOJI MAI KYAWU DA QARFAFAFFEN FURUCI. 232
10 – KARBAR UZURI DA YIWA JUNA UZURI : 232
11 – BINSU SANNU SANNU CIKIN KOWANNE HALI : 233
12 – KYAWUNTA LAFAZI CIKN KOWANNE YANAYI : 233
13 – RASHIN SAURARON KYAUTATA AIKI DARI BISA DARI 233
14 – RASHIN IKON DAUKAR NAUYI A RAYUWANCE : 234
15 – RASHIN GORI KAN MIJI : 234
16 – RASHIN QAURACEWA AL'AMARIN SHIMFIDA: 235
17 - YIN SHAWARA DA MATA BANDA BIYE MUSU: 235
18 – TAKA TSAN TSAN DA KUMA FARKAWA : 238
19 – HANKALTA 239
20 - MIJI SHI NE MUTUNCIN MATARSA 240
21 – KISHI 240
22 – TAIMAKEKENIYYA 242
23 – DADADAWA IYALI 243
27 – WATSI DA BOAKANCI DA TSAFE TSAFE : 244
28 - HIDIMA MADAWWAMIYA 245
29 – GODIYA 246
29 – QAUNAR JUNA 247
TSINTUWA GUDA BIYU GIDAN ALI DA FATIMA (AS) 248
■ FASALI NA 8 252

AUREN DABI'A 24

   AUREN  DABI'A

 

 daga cikin dokoki da sunnar dabi'a da ikon kan dukkanin halitta bari ma dai kan dukkanin wani abu koma bayan Allah matsarkaki shi ne dokar nau'i don ya zama dalili kan dayantakar Allah da dabantakarshi  shi ne kasantuwarsa daya rak wanda bai da kishiya babu misalinsa babu wani irinsa bai da nau'i.

dukkanin wani mai da'awa dole ne ya zo da shaida ba a karbar da'awa ba tareda ita ba  kamar yadda ya kasance cikin shari'ar Allah da dokoki dan adam, ana kiranta a shari'ar islama da shaida ta shari'a  tana kasancewa  shaidu biyu adalai, da ita da'awa ke tabbata ta zama gaskiya.

Allah matsarkaki yana da shaida a dabi'ance da ke shaida kan dabantakarsa da dayantakarsa, shi ne dokar kasantuwar komai nau'i haqiqa shi ya halicci kowanni abu tagwai nau'i  bibiyu don ya zama daga cikin ayoyinsa bisa cewa shi dayane rak tal bai da kishiya. domin  nau'i na tilasta cudanya da wani wanda hakan na bayyana buqatuwa da talautuwa, kuma hakan na korewa kasantuwa da wanda samuwarsa take ba wajibi ba a kankin kansa da zatinsa, bari ma dai ita buqatuwa na daga kebantacce abu da ya kebanta cikin wanda samuwarsu bata zama wajibi ba, shi Allah matasarkaki mawadaci ne abin godiya, babu cudanya cikinsa, bai da kishiya, shi samuwa ne tsantsa dayanda bai da na biyu, kwaya daya tal da ba cudanya cikinsa ya na nuni game da dokokin nau'i cikin littafi mai karamci da hikima:

[1] أوَ لَمْ يَرَوْا إلَى الأرْضِ كَمْ أ نْبَـتْنَا فِيهَا مِنْ كُلِّ زَوْج كَرِيم 

shin ba zasu yi duba zuwa ga qasa ba da yawa muqa tsirar cikinta daga dukkan nau'i me kyawu.

اهْتَزَّتْ وَرَبَتْ وَأ نْبَـتَتْ مِنْ كُلِّ زَوْج بَهِيج[2] 

sai ta girgiza kuma ta kumbura ta tsirar daga dukkanin nau'i mai ban sha'awa.

وَمِنْ كُلِّ شَيْء خَلَقْنَا زَوْجَيْنِ لَعَلَّكُمْ تَذَكَّرُونَ[3] 

kuma daga kowanne abu mun halicci nau'i biyu tsammaninku zakuyi tunani.

  [4]وَأ نَّهُ خَلَقَ الزَّوْجَـيْنِ الذَّكَرَ وَالاُ نْثَى 

haqiqa shi ya halicci nau'i biyu sune mace da namiji.

[5] سُبْحَانَ الَّذِي خَلَقَ الأزْوَاجَ كُلَّهَا مِمَّا تُنْبِتُ الأرْضُ   

tsarki ya tabbata ga wanda ya halicci nau'uka dukkaninsu daga abinda qasa ke tsirarwa.

وَاللهُ جَعَلَ لَكُمْ مِنْ أنفُسِكُمْ أزْوَاجا[6] 

Allah ya sanya muku matayen aure daga kawukanku.

وَمِنْ آيَاتِهِ أنْ خَلَقَ لَكُمْ مِنْ أنفُسِكُمْ أزْوَاجاً لِتَسْكُـنُوا إلَيْهَ[7]ا  

yana daga ayarsa ya hilttar muku mataye daga kawukanku do ku samu natsuwa ya zuwa garesu.

وَاللهُ خَلَقَكُمْ مِنْ تُرَاب ثُمَّ مِنْ نُطْفَة ثُمَّ جَعَلَكُمْ أزْوَاجا[8] 

Allah ya halicce ku daga qasa sannan daga digon  maniyi sannan ya sanya ku surkin maza da mata.

وَمِنَ الأ نْعَامِ أزْوَاجا[9]ً 

(daga dabbobi maza da mata ) 

[10] هُوَ الَّذِي خَلَقَكُمْ مِنْ نَفْس وَاحِدَة وَجَعَلَ مِنْهَا زَوْجَهَا    

 shi ne wanda ya halicce ku daga rai guda ya sanya ma'aurata daga gareta.

خَلَقَكُمْ مِنْ نَفْس وَاحِدَة ثُمَّ جَعَلَ مِنْهَا زَوْجَهَ[11]ا 

  ya halicce ku daga rai guda sannan ya sanya ma'uarata daga gareta.

يَا أ يُّهَا النَّاسُ اتَّقُوا رَبَّكُمُ الَّذِي خَلَقَكُمْ مِنْ نَفْس وَاحِدَة وَخَلَقَ مِنْهاَ

زَوْجَهَ[12]ا

ya ku wadanda sukayi imani kuji tsoron Allah  wanda ya halicce daga rai guda ya halicci ma'aurata daga gareta ).

daga cikin ayoyinsa da a ke qafa dalili da dasu kan dayantuwar Allah da kasantuwarsa daya rak tal kuma shi bai da na biyu  shi ne kasantuwar kowanne wanne abu nau'i biyu, haqiqa ubangiji duk da cewa ya halicci mutum daga rai guda sai dai cewa ya halittar masa mace, ya halicci adamu (as) ya halicci hauwa'u daga ragowar yinbun halittar adamu ta kuma kasance mata gareshi.

daga abubuwan ke qara tabbatarda abubuwa nau'i biyu ne mace da miji, kasantuwar qasa da sama nau'i , dare da rana , kasantuwar duk wani tamata  da maza daga tsirrai da dabbobi mutane  kai hatta ruhi wanda ya kasance daga digon maniyyin namiji da jiki wanda ya kasance daga digon maniyyin mace dukkansu daga nau'ine.

dokar kasantuwar kowanne abu  nau'i biyu  mace da namiji ta gudana hatta kan sassan jikin dan adam misali jijiyoyin da suke cikin kwakwalwa sun kasance daga nau'in mace da namiji, barbarar halitta shi ma na gudana kan dokokin nau'i mace da namiji, daga gareshi yake haifar da duniyoyin badini da na ruhi  da zuciya misaliyya da  hisssiya, a duniyar jikkuna dab'ia da sinadarai abubuwa uku ke haifuwa da kasantuwa sune: ma'adanai tsirrai da dabbobi daga cikinsu kwai mutum, daga barbara akwai abin da ke kebanta da kammalallen mutum da duniyar dabi'a, sannnan cikakken mutum babu banbanci cikin kasantuwar mace ko namiji shi `ya`yan bishiyar samuwa ne, shi hadafi ne na harka guda biyu samuwa da samarwa, mace ta na da matsayin wajen halittar ubangiji ita kamar bishiya ce da jijiyarta ta tabbata  reshenta ya daga sama tana ba da kayan marmarinta kowanne lokaci, kammalallen mutum cikakke idan ya kasance daga namiji  matsayin mabayyanar hankalin game gari ne  idan kuma ya kasance mace  mabayyana ce ta surar ruhi game gari ragib isfahani cikin littafin mufradatul qur'ani ya na cewa:  ana amfani da Kalmar زوج kan dukkanin dayan cikin biyun nau'in masu abokantakar juna namiji da mace,  haka cikin dabbobi da wasunsu kamar huffi da takalmi fade da dukkanin abin da ya cudanya da wani da yake kama da shi ko kishiyar nau'in [13]

 ubangiji madaukakin sarki na cewa :

فَجَعَلَ مِنْهُ الزَّوْجَـيْنِ الذَّكَرَ وَالاُنثَى[14] 

sai ya sanya daga gareshi nau'i biyu mace da namiji

 

[15] وَزَوْجُكَ الجَنَّةَ 

 ka zauna aljanna da matarka.

[16] هُمْ وَأزْوَاجُهُمْ 

su da matayensu. 

 [17] احْشُرُوا الَّذِينَ ظَلَمُوا وَأزْوَاجَهُمْ 

ku tara wadanda suka yi zalunci da abokan hadinsu.

إلَى مَا مَتَّعْنَا بِهِ أزْوَاجاً مِنْهُم[18]   

ya zuwa abinda muka jiyar dasu dadi nau'i nau'i daga garesu.

سُبْحَانَ الَّذِي خَلَقَ الأزْوَاجَ[19] 

tsarki ya tabbata ga wanda ya halicci nau'i nau'i.

وَمِنْ كُلِّ شَيْء خَلَقْنَا زَوْجَيْنِ[20]   

daga dukkanin wani abu mun halicci nau'uka biyu.

saboda haka Allah madaukaki shi kadai ne bai da abokin cudanya sannan dukkanin halittun da suke duniya nau'uka ne saboda suna da kishiya ko akwai wanda ke kamanceceniya dasu da cudanya ba zasu gushe da cudanya ta wani fuska ba. Abin da ya sa mu kawo nau'uka don ya zama tunatarwa da cewa dukkanin wani abu ko da kuwa bai da abin da ke kishiyantarsa da kamanceccniya da shi to bai kubuta daga daga jauhari da aradi da wadancan nau'uka biyu cikin fadinsa:

أزْوَاجاً مِنْ نَبَات شَتَّى[21]

nau'i nau'i daga tsirrai daban daban..

ma'ana nau'o'i masu kamanceceniya da juna , haka cikin fadinsa:

مِنْ كُلِّ زَوْج كَرِيم[22]

   daga dukkanin nau'i mai karamci

[23]  ثَمَانِيَةَ أزْوَاج 

nau'o'i guda takwas.

وَكُـنتُمْ أزْوَاجاً ثَلاثَة[24] 

  ( kuma kun kasance nau'i uku )

 ai abokanan cudanya uku sune wanda Allah ya fassara su cikin fadinsa :

وَإذَا النُّفُوسُ زُوِّجَتْ[25] 

 (kuma idan rayuka aka cudanya su da jikkunansu )

Ance an cudanya kowa da tareda wadanda suka yiwa biyayya ko dai wuta ko aljanna, misalin fadinsa madaukaki:

احْشُرُوا الَّذِينَ ظَلَمُوا وَأزْوَاجَهُم[26]

Ku tara wadanda suka yi zalunci da abokanan cudanyansu   

 saboda kwanne irin abu cikin duniyar dabi'a bai gushewa daga nau'i  dokar auratayya ko kuma ace nau'antaka  zartacciya ce kan duniyar dabi'a .[1] Shu'ara:7

[2] Hajji:5

[3] Azzariyat:49

[4] Annajajamu:45

[5] Yasin:36

[6] Annahli:72

[7] Rum:21

[8] Fadir:11

[9] Shura:11

[10] A'araf:189

[11] Zumar:6

[12] Nisa'i:1

 1 mufradat ragib: sh 230

[14] Alqiyamat:39

[15] Baqara:35

[16] Yasin:56

[17] Assafat:22

[18] Alhijir:88

[19] Yasin:36

[20] Azzariyat:8

[21] Azzariyat:49

[22] Shu'ara:7

[23] An'am:8

[24] Waqi'a:7

[25] Takwir:7

[26] Assafat:22