فهرست کتاب‌‌ لیست کتاب‌ها
■ KALMAR TARBIYYA CIKIN HARSHEN LARABCI DA YANDA AKA YI 4
■ FASALI NA ( 2 ) 24
■ AUREN DABI'A 24
■ FASALI NA 3
■ FASALI NA 4 73
■ FASALI NA 5 131
■ FASALI NA 6 176
HAQQOQIN DA MA'AURATA SU KAYI TARAYYA CIKI 177
1 – HAQURI 178
2 – KAMEWA DAGA ZALUNCI DA CUATARWA 179
HAQQOQIN MATA 180
CIYARWA DA YALWATAWA 185
TAUSAYAWA DA KAMEWA DAGA ZALUNCI 187
KAMEWA DAGA BARIN DUKA MAI CUTARWA 187
UMARNI DA KYAKKYAWA DA HANI DA MUMMUNA 193
GARKUWA 196
8 – KYAUTATAWA : 196
9 - KYAWUNTA ZAMANTAKEWA 197
3 – TAUSAYAWA MIJI : 208
4 – HIMMATUWA DA KULA DA CIKIN GIDA DA KAYYAKINSA : 209
5 - HIMMATUWA CIKIN SAUKE HAQQOQI 209
6 – JIMA'I 210
7 - ADO 213
8 – KAMEWA CIKIN MAGANA : 219
SHUGABANTAR IYALI 225
DALILAI DA SUKE SANYA DAWWAMAR AURE 227
1 – SON JUNA 228
2 – YAWAITA AIKATA ALHERI: 228
4 – SANYA FARIN CIKI: 229
5 – BIYAYYA DA NEMAN YARDAR MIJI: 230
6 – KIYAYE MUTUNCI DA DUKIYA : 230
7 – TAIMAKO DA TALLAFAWA 230
8 – TARBAR MIJI DA KYAWUNTA BANKWANA DA SALLAMA : 231
9 – KALAMIN AQIDOJI MAI KYAWU DA QARFAFAFFEN FURUCI. 232
10 – KARBAR UZURI DA YIWA JUNA UZURI : 232
11 – BINSU SANNU SANNU CIKIN KOWANNE HALI : 233
12 – KYAWUNTA LAFAZI CIKN KOWANNE YANAYI : 233
13 – RASHIN SAURARON KYAUTATA AIKI DARI BISA DARI 233
14 – RASHIN IKON DAUKAR NAUYI A RAYUWANCE : 234
15 – RASHIN GORI KAN MIJI : 234
16 – RASHIN QAURACEWA AL'AMARIN SHIMFIDA: 235
17 - YIN SHAWARA DA MATA BANDA BIYE MUSU: 235
18 – TAKA TSAN TSAN DA KUMA FARKAWA : 238
19 – HANKALTA 239
20 - MIJI SHI NE MUTUNCIN MATARSA 240
21 – KISHI 240
22 – TAIMAKEKENIYYA 242
23 – DADADAWA IYALI 243
27 – WATSI DA BOAKANCI DA TSAFE TSAFE : 244
28 - HIDIMA MADAWWAMIYA 245
29 – GODIYA 246
29 – QAUNAR JUNA 247
TSINTUWA GUDA BIYU GIDAN ALI DA FATIMA (AS) 248
■ FASALI NA 8 252

AUREN SHARI'A 30

AUREN SHARI'A

dan adam na da sha'awe sha'awe daban daban daga cikin mafi bayyanarsu shi ne sha'awarsa ta jinsi, haqiqa mutum dauke ya ke da halittar sha'awa abinda ke nuna hakan shi ne sha'awar kusanta da saduwa ta jinsi haqiqa mutum namiji ko mace da dabi'arsa ta sha'awa da Allah ya halicce shi da ita ya na karkata zuwa ga jinsin da ya ke kishiyantakarsa ya yi yunkurin kusantarsa, sai dai ita kusantar

  wani sa'ilin tana kasancewa shar'antacciya wadda Allah ya halasta ya kuma yarda da ita ana kiranta da auren shari'a, akwai kuma kishiyar haka wadda ba halastacciya ba wadda ake kiranta da fajirci Allah ya haramta kamar misalin zina.

aure da ma'ana game gari shi ne tsantsar kusanta da jima'i wanda ke qarqashin auratayya, sannan yana siffantuwa da hukunce hukuncen shari'a guda biyar: wajibi, haramun, mustahabbi, makaruhi,  halal, ko dai ya kasance wajibi idan ana tsoron afkawar fajirci da haramun  ko kuma haramun kamar aurar macen da  aurartaya haramta gareka misalin uwa qanwa da sauransu, ko kuma mustahabbi kamar auren a kankin kansa bisa zamani da yanayi da wurare kebantattu ta yadda za'a rinjayar da yinsa kan barinsa, ko ku

ma makaruhi ta yadda barinsa ya fi yinsa rinjaye da zama alheri, ko kuma daidaitar yinsa da barinsa ta yadda zai zama halal a irin wannan yanayi da lokaci.

aure da ke wajibi mustahabbi da halal shi ne ake kira da halastaccen aure a shari'a, ko dai ya kasance na dindin ko qayyadadde ko mallakar kuyanga, amma aurar muharrama  ana kiransa da haramtaccen aure, haqiqa ubangiji ya haramta ya yi alqawalin narkon azaba da tabewa ga wanda ya yi shi ranar alqiyama, kamar yadda ya wajabta haddi da rajamu jefewa anan duniya idan wanda ya aikata hakan ya kasance ya na da aure, ko kuma bulala dari idan bai da aure kamar yadda hakan ya zo dalla dalla cikin hukunce hukuncen fiqihun muslunci.

auren shari'a na farko da ya fara kasancewa  tsakanin adamu uba ga dukkanin mutane da hauwa'u uwan garesu, kamar yadda ya zo cikin hadisi mai daraja, cikin hakan akwai nuni zuwa ga falsafar aure  a jumlace  zuwa huduba da sadaki.

عن  أبي  عبد الله عليه السلام قال : ان الله  خلق آدم من طین  ثم ابتدع حواء فجعلها في موضع النقرة التي بين وركيه,ذلك لكي تكون المرأة تبعا للرجل,فقال آدم: یا رب ما هذا الحسن الذی آنسنی قربه والنظر الیه؟ فقال الله عز وجل: هذه امتی حواء,افتحبأن تكون معك تؤنسك وتحدثك,وتكون تبعا لأمرك؟فقال نعم يا رب ولك بذلك علي الحمد والشكر ما بقيت, فقال الله عز وجل: فاخلطبها الي,فاءنها أمتي,وقد تصلح لك ايضا زوجة للشهوة,وألقلى الله عليه الشهوة وقد علمه قبل ذلك المعرفة بكل شئ, فقال:یا رب فاءني أخطبها الیك, فما رضاك لذلك؟فقال الله عز وجل رضايا أن تعلمها معالم ديني, فقال: ذلك لك علي يا رب ان شئت ذلك لي, فقال الله قد شئت ذلك,وقد زوجتكها فضمها اليك[1]

an karbo daga baban abdullah (as)  ya na cewa : Allah mai girma da daukaka ya halicci adamu daga yunbu sannan ya qirqirar masa hauwa'u ya sanyata a mahalin tsakankanin matsugunansa domin ta zama biyayya ga da namiji, sai adamu yace: ya ubangiji wacce kyakkyawar halitta ce wannan da kusanatarta da kallonta ke debe mini haso? sai ubangiji ya ce: ya adamu baiwa ta ce hauwa'u, shin ko kana son ta kasance tare da kai ta dinga debe maka haso da dinga hira tare da kai ta  kasance mai biyayya ga umarninka ? sai adamu ya ce na'am ya ubangiji, ka cancanci yabo da godiya kan haka tsawon rayuwata, sai Allah madaukaki ya ce: nemi aurenta daga gareni haqiqa ita baiwa ta ce kuma ta dace da zama matarka don sha'awa, sai Allah ya sanya masa sha'awa kuma gabanin haka ya sanar da shi sanin dukkanin wani abu, sai adamu ya ce: ina neman aurenta daga gareka, meye yardarka kan haka, sai ubangiji ya ce: yarda ta ka sanar da ita ilimin addini na, sai adamu ya ce: idan kana son hakan to zanyi  sai ubangiji ya ce: na yarda  na aurar da ita gareka dauketa ta zama taka 1.

sannan aure na biyu ya kasance ga diyan adamu (as) ba kamar yadda majusawa (la) ke fadi cewa auren `yan'uwan juna uwa daya uba daya , bari dai ga yadda al'amarin ya zo cikin hadisi : cikin littafin manla yahduruhu faqihu:

رَوَى زُرَارَةُ «3» عَنْ أَبِي عَبْدِ اللَّهِ ع أَنَّ آدَمَ ع وُلِدَ لَهُ شَيْثٌ            

 أَنَّ اسْمَهُ هِبَةُ اللَّهِ وَ هُوَ أَوَّلُ وَصِيٍّ أُوصِيَ إِلَيْهِ مِنَ الْآدَمِيِّينَ فِي الْأَرْضِ ثُمَّ وُلِدَ لَهُ بَعْد شَيْثٍ يَافِثُ فَلَمَّا أَدْرَكَا أَرَادَ اللَّهُ عَزَّ وَ جَلَّ أَنْ يُبْلِغَ بِالنَّسْلِ مَا تَرَوْنَ وَ أَنْ يَكُونَ مَا قَدْ جَرَى بِهِ الْقَلَمُ مِنْ تَحْرِيمِ مَا حَرَّمَ اللَّهُ عَزَّ وَ جَلَّ مِنَ الْأَخَوَاتِ عَلَى الْإِخْوَةِ أَنْزَلَ بَعْدَ الْعَصْرِ فِي يَوْمِ خَمِيسٍ حَوْرَاءَ مِنَ الْجَنَّةِ اسْمُهَا نَزْلَةُ فَأَمَرَ اللَّهُ عَزَّ وَ جَلَّ آدَمَ أَنْ يُزَوِّجَهَا مِنْ شَيْثٍ فَزَوَّجَهَا مِنْهُ ثُمَّ أَنْزَلَ بَعْدَ الْعَصْرِ مِنَ الْغَدِ حَوْرَاءَ مِنَ الْجَنَّةِ وَ اسْمُهَا مُنْزَلَةُ فَأَمَرَ اللَّهُ عَزَّ وَ جَلَّ آدَمَ أَنْ يُزَوِّجَهَا مِنْ يَافِثَ فَزَوَّجَهَا مِنْهُ فَوُلِدَ لِشَيْثٍ غُلَامٌ وَ وُلِدَ لِيَافِثَ جَارِيَةٌ فَأَمَرَ اللَّهُ

عَزَّ وَ جَلَّ آدَمَ حِينَ أَدْرَكَا أَنْ يُزَوِّجَ ابْنَةَ يَافِثَ مِنِ ابْنِ شَيْثٍ فَفَعَلَ فَوُلِدَ الصَّفْوَةُ مِنَ النَّبِيِّينَ وَ الْمُرْسَلِينَ مِنْ نَسْلِهِمَا وَ مَعَاذَ اللَّهِ أَنْ يَكُونَ ذَلِكَ عَلَى مَا قَالُوا مِنْ أَمْرِ الْإِخْوَةِ وَ الْأَخَوَاتِ[2]

  daga zuraratu daga baban abdullah (as) haqiqa adamu na da wani diya wanda ake kiransa shissu wanda haqiqanin sunansa hibbatullah,shi ne wasiyyi na farko da aka yi masa wasiyya daga `ya`yan adamu,  bayan shissu an qara haifa ma adamu da mai suna yafis, yayin da ya girma sai ya nufi ya isar abin da zaku gani cikin tsatso, da kuma kasancewa cikin abin da alqalami ya bushe kansa cikin haramcin abin da Allah ya haramta daga auren `yan uwan juna uwa daya uba daya, bayan la'asar ranar alhamis ubangiji ya aiko da mace daga aljanna me suna nuzla ya umarci annabi adamu da ya aurar da ita ga dansa shissu, sannan washegari ya qara aiko da wata me suna manzilla ita ma ya umarci adamu ya aurar da ita ga yafis ya ko aura musu, sannan aka haifawa shissu da namiji shi kuma yafisu aka haifa masa mace, yayin da wadannan `ya`ya suka girma sai ya umarci adamu da ya aurar da `yar yafisu ga dan shissu sai  adamu (as) ya aikata hakan, to daga wannan tsatso ne aka haifi zababbu daga annabawa da manzanni, Allah ya kiyaye ace wai auren `yan uwan juna ne ya kasance kamar yadda majusawa suke fadi.

 daga manla yahadurul faqihu:

 ِّ عَنْ أَبِي جَعْفَرٍ ع قَالَ: إِنَّ اللَّهَ تَبَارَكَ وَ تَعَالَى أَنْزَلَ عَلَى آدَمَ حَوْرَاءَ مِنَ الْجَنَّةِ فَزَوَّجَهَا أَحَدَ ابْنَيْهِ وَ تَزَوَّجَ الْآخَرُ ابْنَةَ الْجَانِّ فَمَا كَانَ فِي النَّاسِ مِنْ جَمَالٍ كَثِيرٍ أَوْ حُسْنِ خُلُقٍ فَهُوَ مِنَ الْحَوْرَاءِ وَ مَا كَانَ فِيهِمْ مِنْ سُوءِ خُلُقٍ فَهُوَ مِنِ ابْنَةِ الْجَانّ

ِ. da isnadinsa daga baban jafar (as) ya ce: Allah mai girma da daukaka ya aiko wa adamu mace daga aljanna sai ya aurar da ita ga daya daga `ya`yansa, dayan kuma ya auri  diyar aljanni, kyawun da ke kasancewa cikin mutane da kyautatar dabi'a to ya kasance daga wannan hurul inin ne da diyan adamu ya aura, sannan idan munanar dabi'a ne to daga `yar wannan aljanni da diyan adamu ya aura  ne.

zamu iya hada hadisan guda biyu sannan hada hadisi da daya hadisin don fitar da sakamako shi ya fi kyawu da cewa mun yi wurgi da su baki daya, Allah matsarkaki ya aurar da `ya`yan adamu karo biyu karon farko da hurul ini matayen aljanna karo na biyu kuma da hurul ini guda daya da aljana daya, ko kuma dai shi auren na farko ya kasance ga `ya`yaye biyu daga adam, sannan na biyun kuma ya kasance ga wasu `ya`yayen daban.

ِ عَنْ أَبِي جَعْفَرٍ ع قَالَ: ذَكَرْتُ لَهُ الْمَجُوسَ وَ أَنَّهُمْ يَقُولُونَ نِكَاحٌ كَنِكَاحِ وُلْدِ آدَمَ وَ إِنَّهُمْ يُحَاجُّونَّا بِذَلِكَ فَقَالَ أَمَّا أَنْتُمْ فَلَا يُحَاجُّونَكُمْ بِهِ لَمَّا أَدْرَكَ هِبَةُ اللَّهِ قَالَ آدَمُ يَا رَبِّ زَوِّجْ هِبَةَ اللَّهِ فَأَهْبَطَ اللَّهُ عَزَّ وَ جَلَّ لَهُ حَوْرَاءَ فَوَلَدَتْ لَهُ أَرْبَعَةَ غِلْمَةٍ ثُمَّ رَفَعَهَا اللَّهُ فَلَمَّا أَدْرَكَ وُلْدُ هِبَةِ اللَّهِ قَالَ يَا رَبِّ زَوِّجْ وُلْدَ هِبَةِ اللَّهِ فَأَوْحَى اللَّهُ عَزَّ وَ جَلَّ إِلَيْهِ أَنْ يَخْطُبَ إِلَى رَجُلٍ مِنَ الْجِنِّ وَ كَانَ مُسْلِماً أَرْبَعَ بَنَاتٍ لَهُ عَلَى وُلْدِ هِبَةِ اللَّهِ فَزَوَّجَهُنَّ فَمَا كَانَ مِنْ جَمَالٍ وَ حِلْمٍ فَمِنْ قِبَلِ الْحَوْرَاءِ وَ النُّبُوَّةِ وَ مَا كَانَ مِنْ سَفَهٍ أَوْ حِدَّةٍ فَمِنَ الْجِنّ

ِyazo cikin littafin alkafi mai daraja da isnadinsa daga baban jafar (as) na ce masa: majusawa na cewa aure kamar auren `ya`yayen adamu ne suna kafa hujja da hakan, sai ya ce: amma ku ba zasu kafa muku hujja da hakan ba, yayin da hibbatul ya girma sai adamu ya ce:ya ubangiji ina roqonka da ka aurarda hibbatullah, sai Allah ya sauko da hurul ini daga aljanna, sai ta haifa masa `ya`ya hudu sai Allah ya mayar da wannan hurul ini, yayin da dan hibbatul ya girma sai adamu ya qara roqon Allah da ya aurar da dan hibbatullah, sai Allah ya yi wahayi ga adamu da ya yi magana da wani mutum daga aljannu wanda ya kasance shi musulmi ne ya na da `ya`ya hudu mata sai ya aurar dasu ga `ya'yan hibbatullah, dukkanin abin da ya kasance daga kyawu da haquri to daga fuskanin hurul ini nan ne da kuma jini annanbta, abin da ya kasance daga wauta da zafi da fusata to daga aljanni ne, domin cewa su aljannu an halicce su daga wuta, رُ cikinsu akwai zafi da fusata.

a abin da ya zo cikin alqur'ani  game da auren shari'a da sashen hukunce hukuncensa kamar haka cikin jumlar wadannan ayoyi :

وَالَّذِينَ هُمْ لِفُرُوجِهِمْ حَافِظُونَ (5) إِلَّا عَلَى أَزْوَاجِهِمْ أَوْ مَا مَلَكَتْ أَيْمَانُهُمْ فَإِنَّهُمْ غَيْرُ مَلُومِينَ (6) فَمَنِ ابْتَغَى وَرَاءَ ذَلِكَ فَأُولَئِكَ هُمُ الْعَادُونَ[3]

1-wadanda ke katange farjinsu face ga matayensu ko abinda damansu tamallaka to su ba ababen zargi bane dukkanin wanda ya nemi koma bayan haka to wadancan sune masu ketare haddi.

masu ketare haddin iyakokin ubangiji da wannan ake kafa hujja kan haramcin fitar da maniyi ta hanyar da ba shari'a ta tanade ba .

wani wajen kuma ya na cewa :

وَجَعَلَ مِنْهَا زَوْجَهَا لِيَسْكُنَ إِلَيَه[4]ا

2-ya sanya matarta daga gareta don samun natsuwa ya zuwa gareta.

وَأَنْكِحُوا الْأَيَامَى مِنْكُمْ وَالصَّالِحِينَ مِنْ عِبَادِكُمْ وَإِمَائِكُمْ إِنْ يَكُونُوا فُقَرَاءَ يُغْنِهِمُ اللَّهُ مِنْ فَضْلِهِ وَاللَّهُ وَاسِعٌ عَلِيمٌ (32) وَلْيَسْتَعْفِفِ الَّذِينَ لَا يَجِدُونَ نِكَاحًا حَتَّى يُغْنِيَهُمُ اللَّهُ مِنْ فَضْلِه[5]

3-ku auri gwauraye daga gareku da salihai daga bayinku da kuyangunku idan sun kasance faqirai talakawa to Allah zai wadata su daga falalarsa* haqiqa Allah ma yalwaci ne masani.

 gwauraye jam'i ne gwauruwa ai gwauruwar da bata da miji daga budurwa da bazawara haka lamarin yake kan namiji, sannan ayar tana magana ne da ga waliyyai da shugabanni (idan sun kasance talakawa ) ma'ana kada ku sanya talauci ya zamanto dallin da zai hana aure, (su kame ) abin da ya shahara cikin tafsirin wannan gaba shi ne danne sha'awa, kamar yadda annabi ya ke cewa: ya ku jam'ar samari dukkanin wanda ya samu dama da iko cikinku ya yi aure, wanda ko bai da iko kan haka to ya lazimci azumi, haqiqa azumi na rage kaifin sha'awa, ayar farko ta zo game da hana yin wurgi da watsi aure saboda haka babu karo da juna tsakaninta da wannan hadisi .

وَمَنْ لَمْ يَسْتَطِعْ مِنْكُمْ طَوْلًا أَنْ يَنْكِحَ الْمُحْصَنَاتِ الْمُؤْمِنَاتِ فَمِنْ مَا مَلَكَتْ أَيْمَانُكُمْ مِنْ فَتَيَاتِكُمُ الْمُؤْمِنَاتِ وَاللَّهُ أَعْلَمُ بِإِيمَانِكُمْ بَعْضُكُمْ مِنْ بَعْضٍ فَانْكِحُوهُنَّ بِإِذْنِ أَهْلِهِنَّ وَآتُوهُنَّ أُجُورَهُنَّ بِالْمَعْرُوفِ مُحْصَنَاتٍ غَيْرَ مُسَافِحَاتٍ وَلَا مُتَّخِذَاتِ أَخْدَانٍ فَإِذَا أُحْصِنَّ فَإِنْ أَتَيْنَ بِفَاحِشَةٍ فَعَلَيْهِنَّ نِصْفُ مَا عَلَى الْمُحْصَنَاتِ مِنَ الْعَذَابِ ذَلِكَ لِمَنْ خَشِيَ الْعَنَتَ مِنْكُمْ وَأَنْ تَصْبِرُوا خَيْرٌ لَكُمْ وَاللَّهُ غَفُورٌ رَحِيم[6]

4-dukkanin wanda bai samu wadata da ikon aurar muminai to ya aura daga abin da hannayen damanku suka mallaka daga kuyangu muminai  Allah ne mafi sani daga imaninku sashenku daga sash, ku auresu da izinin iyayensu ku basu ladayensu bisa sanannen abu kamammu ba masu su zina ba da riqar abokanni,  idan aka aure su suka zo alfasha mabayyaniya  to akwai kansu rabin abinda ke kan `ya`ya daga azaba, wancan daga wanda ya ji tsoron wahala daga gareku, kuyi haquri shi yafi zama alheri gareku , Allah me yawan gafara ne da rahama.

Allah ne mafi sani gameda imaninku )

ma'ana abin da kadai a ka kallafa muku yin  la'akari da shi shi ne zahirin mutum, saboda haka dukkanin mace ko namijin da ya bayyana muku imaninsa to kuyi masa hukunci da shi, aurensu ya halasta ko ba ababen tuhuma ba ne idan sun kasance munafukai (sashenku daga sashe )  dukkkanin bil adam ka da ku qi aurar kuyanga domin jinsi namiji da mace da imani sune ababen dubawa.

حُرِّمَتْ عَلَيْكُمْ أُمَّهَاتُكُمْ وَبَنَاتُكُمْ وَأَخَوَاتُكُمْ وَعَمَّاتُكُمْ وَخَالَاتُكُمْ وَبَنَاتُ الْأَخِ وَبَنَاتُ الْأُخْتِ وَأُمَّهَاتُكُمُ اللَّاتِي أَرْضَعْنَكُمْ وَأَخَوَاتُكُمْ مِنَ الرَّضَاعَةِ وَأُمَّهَاتُ نِسَائِكُمْ وَرَبَائِبُكُمُ اللَّاتِي فِي حُجُورِكُمْ مِنْ نِسَائِكُمُ اللَّاتِي دَخَلْتُمْ بِهِنَّ فَإِنْ لَمْ تَكُونُوا دَخَلْتُمْ بِهِنَّ فَلَا جُنَاحَ عَلَيْكُمْ وَحَلَائِلُ أَبْنَائِكُمُ الَّذِينَ مِنْ أَصْلَابِكُمْ وَأَنْ تَجْمَعُوا بَيْنَ الْأُخْتَيْنِ إِلَّا مَا قَدْ سَلَفَ إِنَّ اللَّهَ كَانَ غَفُورًا رَحِيمً وَالْمُحْصَنَاتُ مِنَ النِّسَاءِ إِلَّا مَا مَلَكَتْ أَيْمَانُكُمْ كِتَابَ اللَّهِ عَلَيْكُمْ وَأُحِلَّ لَكُمْ مَا وَرَاءَ ذَلِكُمْ أَنْ تَبْتَغُوا بِأَمْوَالِكُمْ مُحْصِنِينَ غَيْرَ مُسَافِحِينَ[7]

5- (kada ku aura daga abin da  da iyayenku suka aura daga mata sai da abinda ya gabata haqiqa hakan alfasha ne da kyama ya munana ya zama hanya*an haramta maku uwayenku da `ya`yayenku da `yan'uwanku mata da goggwaninku da innoninku da `ya`yan dan'uwa da `ya`yan `yar'uwa  da uawayenku da suka shayar da ku nono da `yan'uwanku mata na shan nono  da uwayen matanku da agolanku wadanda su ke cikin dakin matayenku da ku ka sadu da su idan kuma ba ku kasance kun sadu da su to babu laifi kanku * da matayen `ya`yanku wadanda suke daga tsatsonku* kada ku hada tsakanin `yan'uwa biyu mata sai abinda ya gabata , haqiqa ubangiji mai yawan gafara da jin-qai da tsararru daga mata face dai abinda hannun damanku ya mallaka* ku kare littafin Allah an halasta  muku koma bayan haka, ku nema da dukiyoyinku kuna masu yin aure ba masu yin zina ba

(sai abinda ya gabata ) ma'ana a jahiliya haqiqa an yi muku uzuri cikin abin da ya rigaya ya faru, (tsararru daga mata ) ai matayen aure matuqar suna cikin igiyar aure da wadanda suke halin idda (face abin da hannun damanku ta mallaka ) ai kuyangu da kuka mallaka ta hanyar saya ko kyauta ko gado ko yaqi, ya na shiga cikinsa idan aure ya lalace tsakaninsu da abin da hannunku ya mallaka ya zama lazimi kowaccensu ta yi idda  (ku tsare littafin Allah ) ai littafin Allah farilla ne kanku.

ubangiji madaukaki na cewa :

وَلَا تُمْسِكُوا بِعِصَمِ الْكَوَافِر[8]

6-ka da ku riqi auren mata kafirai

  وَإِنْ خِفْتُمْ أَلَّا تُقْسِطُوا فِي الْيَتَامَى فَانْكِحُوا مَا طَابَ لَكُمْ مِنَ النِّسَاءِ مَثْنَى وَثُلَاثَ وَرُبَاعَ فَإِنْ خِفْتُمْ أَلَّا تَعْدِلُوا فَوَاحِدَةً أَوْ مَا مَلَكَتْ أَيْمَانُكُمْ ذَلِكَ أَدْنَى أَلَّا تَعُولُو[9]ا

7-idan kun ji tsoron ba za ku iya adalci cikin marayu ba to ku auri abinda ya dadada gareku daga mata biyu biyu ko uku uku ko hudu, idan kun ji tsoron ba ku iya adalci to ku auri guda daya ko kuma abin da hannun damanku ta mallaka, hakan shi ya fi kusa daga da ku tsallake haddi.

:عن محمد بن الحسن، قال: سأل ابن أبي العوجاء هشام بن الحكم، فقال

أليس الله حكيما؟ قال: بلى، هو أحكم الحاكمين.

قال: فأخبرني عن قوله عز و جل: فَانْكِحُوا ما طابَ لَكُمْ مِنَ النِّساءِ مَثْنى‏ وَ ثُلاثَ وَ رُباعَ فَإِنْ خِفْتُمْ أَلَّا تَعْدِلُوا فَواحِدَةً أليس هذا فرض؟ قال: بلى.

قال: فأخبرني عن قوله عز و جل: وَ لَنْ تَسْتَطِيعُوا أَنْ تَعْدِلُوا بَيْنَ النِّساءِ وَ لَوْ حَرَصْتُمْ فَلا تَمِيلُوا كُلَّ الْمَيْلِ «1» أي حكيم يتكلم بهذا؟ فلم يكن عنده جواب، فرحل إلى المدينة، إلى أبي عبد الله (عليه السلام)، فقال: «يا هشام في غير وقت حج و لا عمرة؟» قال: نعم جعلت فداك، لأمر أهمني، إن ابن أبي العوجاء سألني عن مسألة لم يكن عندي فيها شي‏ء قال: «و ما هي»؟ قال: فأخبره بالقصة.

فقال له أبو عبد الله (عليه السلام): «أما قوله عز و جل: فَانْكِحُوا ما طابَ لَكُمْ مِنَ النِّساءِ مَثْنى‏ وَ ثُلاثَ وَ رُباعَ فَإِنْ خِفْتُمْ أَلَّا تَعْدِلُوا فَواحِدَةً يعني في النفقة، و أما قوله: وَ لَنْ تَسْتَطِيعُوا أَنْ تَعْدِلُوا بَيْنَ النِّساءِ وَ لَوْ حَرَصْتُمْ فَلا تَمِيلُوا كُلَّ الْمَيْلِ فَتَذَرُوها كَالْمُعَلَّقَةِ «2» يعني في المودة».

قال: فلما قدم عليه هشام بهذا الجواب و أخبره، قال: و الله، ما هذا من عندك.

8-alkafi da isnadinsa daga muhammad dan hassan ya ce:  dan auja'I ya tambayi hisham dan hakam ya ce masa: shin Allah ba mai hikima ba ne ? sai ya ce: na'am shi ne mafi hikimar masu hikima, sai ya bani labari da fadin Allah ( ku aura daga abin da ya dadada gare ku daga mata bibiyu,uku-uku, hudu-hudu, idan kun ji tsoron rashin iya tsyar da adalci tu ku tsaya ga daya.

baza ku taba iya yin adalci tsakanin mata ba ko da kuwa kunyi kwadayin hakan * kada ku karkata dukkanin karkata kuyi wurgi da ita kamar ratayayya. 

 wanne mai hikima ne zai dinga irin wannan maganar, sai  hikam ya kasa bashi amsa, take ya nufi madina wajen baban abdullah (as) sai imam ya ce masa mai ya kawo madina a wannan lokaci da ba na hajji ba ko umara, sai hisham ya ce: raina fansarka wani al'amari muhimmi ya kawo ni, haqiqa dan abul auja'i ya tambaye ni wata mas'ala wanda na gaza ba da amsa, sai imam  ya ce: mecece mas'ala ? sai ya bashi labari abin da ya faru,  imam (as) ya ce: masa amma fadinsa:

  ku aura daga abin da ya dadada gareku daga mata biyu biyu uku uku  hudu hudu idan kunji tsoron ba zaku iya adalci ba to ku auri guda daya, ayar tana magana ne kan ciyarwa, amma fadinsa ( baza ku taba iya adalci tsakanin mata ba koda kunyi kwadayin hakan kada ku karkata dukkanin karkata ku barta kamar ratayayya.

ma'ana cikin soyayya, sai ya ce: yayin da hisham ya komawa dan abul auja'i da wannan jawabi ya bashi labari sai abul auja'ai ya ce : wallahi wannan jawabin ba daga gareka ya ke ba.[10]

sannan gina iyali na kammala kadai kan tsuhen auren mai asali :

 [11]وَمِنْ آيَاتِهِ أَنْ خَلَقَ لَكُمْ مِنْ أَنْفُسِكُمْ أَزْوَاجًا لِتَسْكُنُوا إِلَيْهَا

9-daga ayoyinsa ya halitta muku mata daga gareku don ku samu natsuwa zuwa garesu )

hadafi na farko da asasi kan aure shi ne samun natsuwa wanda da sannu zai haifar da kyakkyawan sakamako cikin `ya`ya da ma`aurata,  ma fi muhimmanci sinadarin samun gamsuwa  da amfana da wannan natsuwa shi ne zaman lafiyar gida wanda ke samuwa ta dalilin qaunar juna da tausayi wanda Allah ya sanya shi cikin halittar dan adam.

 وَجَعَلَ بَيْنَكُمْ مَوَدَّةً وَرَحْمَة[12]

ya sanya qauna da rahama

 sai dai tare da haka ya umarci mutum da ya motsa don kar ya zama (jabar) tilastawa ya yi kira ya zuwa kayakkayawar mu'amala cikin fadinsa:

وَجَعَلَ بَـيْنَكُمْ مَوَدَّةً وَرَحْمَة[13]   

10-kuyi musu mu'amala da kyautatawa. 

sannan a na ladabtar  dukkanin mara da'a daga cikinsu maza da mata, ba'a yarda da wulankanta mace ba don tana mace , bari madai mace dai-dai take da namiji cikin tarbiyya da koyarwa fagen ladabi daraja da karamci.

وَالْمُؤْمِنُونَ وَالْمُؤْمِنَاتُ بَعْضُهُمْ أَوْلِيَاءُ بَعْضٍ يَأْمُرُونَ بِالْمَعْرُوفِ وَيَنْهَوْنَ عَنِ الْمُنْكَر[14]

11-muminai maza da mata sashensu masoyan sashe suna umarni da kyakkyawa da hani da mummuna.

mace na da saqo cikin muslunci ta hanyar riqonta ga hijabi da muslunci, sannan alaqar namiji da mace ba ta halasta face cikin wasu wurare qayyadaddu iyakantattu da muslunci ya tsara,  wannan alaqa ba ta kasance saki ba kaidi kan nau'in mutum,   ta kasance qayyadaddiya iyakantacciya da wasu qaidodi da shar'ia ta farlanta su   tana sassabawa cikin jumlacewarta da faifaicewa da sassabawar zamani da al'umma.[1] Was'ilul shi'a m 20 sh 24

[2] Manla yahduruhu alfaqihu m 3 sh 381

[3] Almuminun:7

[4] A'araf:189

[5] Nurr:32-33

[6]Nisa'i:25

[7] Nisa'i: 22-24

[8] Mumtahana;10

[9] NISA'I:3

[10]Kitabul alwafi m 12 sh 792

[11] Rum:21

[12] Rum:21

[13] Nisa'i:19

[14] Tauba:71