فهرست کتاب‌‌ لیست کتاب‌ها
■ KALMAR TARBIYYA CIKIN HARSHEN LARABCI DA YANDA AKA YI 4
■ FASALI NA ( 2 ) 24
■ AUREN DABI'A 24
■ FASALI NA 3
■ FASALI NA 4 73
■ FASALI NA 5 131
■ FASALI NA 6 176
HAQQOQIN DA MA'AURATA SU KAYI TARAYYA CIKI 177
1 – HAQURI 178
2 – KAMEWA DAGA ZALUNCI DA CUATARWA 179
HAQQOQIN MATA 180
CIYARWA DA YALWATAWA 185
TAUSAYAWA DA KAMEWA DAGA ZALUNCI 187
KAMEWA DAGA BARIN DUKA MAI CUTARWA 187
UMARNI DA KYAKKYAWA DA HANI DA MUMMUNA 193
GARKUWA 196
8 – KYAUTATAWA : 196
9 - KYAWUNTA ZAMANTAKEWA 197
3 – TAUSAYAWA MIJI : 208
4 – HIMMATUWA DA KULA DA CIKIN GIDA DA KAYYAKINSA : 209
5 - HIMMATUWA CIKIN SAUKE HAQQOQI 209
6 – JIMA'I 210
7 - ADO 213
8 – KAMEWA CIKIN MAGANA : 219
SHUGABANTAR IYALI 225
DALILAI DA SUKE SANYA DAWWAMAR AURE 227
1 – SON JUNA 228
2 – YAWAITA AIKATA ALHERI: 228
4 – SANYA FARIN CIKI: 229
5 – BIYAYYA DA NEMAN YARDAR MIJI: 230
6 – KIYAYE MUTUNCI DA DUKIYA : 230
7 – TAIMAKO DA TALLAFAWA 230
8 – TARBAR MIJI DA KYAWUNTA BANKWANA DA SALLAMA : 231
9 – KALAMIN AQIDOJI MAI KYAWU DA QARFAFAFFEN FURUCI. 232
10 – KARBAR UZURI DA YIWA JUNA UZURI : 232
11 – BINSU SANNU SANNU CIKIN KOWANNE HALI : 233
12 – KYAWUNTA LAFAZI CIKN KOWANNE YANAYI : 233
13 – RASHIN SAURARON KYAUTATA AIKI DARI BISA DARI 233
14 – RASHIN IKON DAUKAR NAUYI A RAYUWANCE : 234
15 – RASHIN GORI KAN MIJI : 234
16 – RASHIN QAURACEWA AL'AMARIN SHIMFIDA: 235
17 - YIN SHAWARA DA MATA BANDA BIYE MUSU: 235
18 – TAKA TSAN TSAN DA KUMA FARKAWA : 238
19 – HANKALTA 239
20 - MIJI SHI NE MUTUNCIN MATARSA 240
21 – KISHI 240
22 – TAIMAKEKENIYYA 242
23 – DADADAWA IYALI 243
27 – WATSI DA BOAKANCI DA TSAFE TSAFE : 244
28 - HIDIMA MADAWWAMIYA 245
29 – GODIYA 246
29 – QAUNAR JUNA 247
TSINTUWA GUDA BIYU GIDAN ALI DA FATIMA (AS) 248
■ FASALI NA 8 252

KASHE KASHEN AURE: 41

KASHE KASHEN AURE:

 daga mafi muhimmancin wadancan qaidodi kashe kashen da ya halasta cikinsa, da wadanda basu halasta tsakaninsu da adadin mataye da mazaje  da abin da shi aure ke kammala da haqqoqi da wajibai wadanda aka dora kan wuyan ma'aurata cikin wannan alaqar ta aure da shari'a da al'ada.

fagen wannan kashe-kashe ya na sabawa da sabawar jama'a, daga qaidodi akwai abin da ke komawa ya zuwa sabani cikin addini, misali cikin al'ummomi musulmi bai halasta wanda ba musulmi ya auri musulma ba ko da kuwa ya kasance daga ahlul kitabi kamar yadda bai halasta musulmi ya auri wadda ba musulma ba ko da kuwa ahlul kitabi ce, haka bai halasta ya auri mushrika mai bautar gumki kamar yadda ya zo cikin fadin Allah:

وَلا تَنكِحُوا المُشْرِكَاتِ حَتَّى يُؤْمِنَّ وَلأمَةٌ مُؤْمِنَةٌ خَيْرٌ مِنْ مُشْرِكَة وَلَوْ أعْجَبَتْكُمْ وَلا تُنكِحُوا المُشْرِكِينَ حَتَّى يُؤْمِنُوا وَ لَعَبْدٌ مُؤْمِنٌ خَيْرٌ مِنْ مُشْرِك وَلَوْ  أعْجَبَكُمْ [1]

12-kada ku auri mata mushrikai har sai sun yi imani  kuyanga mumina ta fi alheri daga mushrika ko da kuwa wannan mushrika ta qayatar da ku  kada ku auri mazaje mushrikai har sai sun yi imani  lalle bawa mumini shi ne mafi alheri daga bawa mushriki ko da kuwa ya qayatar da ku.

daga qaidodi akwai  wanda ke komawa ga jinsi mutane, misali wajen yahudawa zamanin da ya shude sun kasance suna haramta aure tsakaninsu da kan'aniyawa saboda su yahudawa suna ganin kansu matsayin zababbun Allah, kuma suna la'akari da kan'aniyawa a matsayin qasqantattun halittun Allah don su samu damar mayar da su bayi, kuma dukkanin mutane  al'amarinsu ya kasance haka bai inganta su gurbata banu isra'ila da surutaka ba, kuma sun kasance suna raya cewa wannan qasqanci ya samo asali daga addu'ar da annabi nuhu (as) ya yi kan dansa hamu da tsatsonsa, haqiqa ya zo cikin سفر التكوين cewa nuhu ya sha giyar inibi wanda shi da kansa ya dasa bishiyar wannan inibi bayan ruwan dufana ba tare da ya san cewa wannan inibi yana sanya maye ba, sai ya fita daga hayyacinsa tsiraicinsa ya bayyana fili, yayin da dansa hamu ya ga tsiraicinsa sai ya yi masa isgili ya dauki labarin ya kaiwa ragowar `yan'uwansa samu da yafisu sai dai cewa su sun fishi ladabi da tarbiyya  sai suka dauki kyalle suka dinga tattakawa da baya da baya don kada idonsu ya kai  ga ganin tsaraicin mahaifinsu suka lullube shi da wannan kyalle suka suturce shi, yayin da nuhu ya dawo cikin hayyacinsa ya ji labarin matakin da `ya`yansa suka dauka kansa sai ya tsinewa kan'an dan hamu da `ya`yansa ya yi addu'a da Allah ya sanya su bayi ga samu da yafisu.

kamar yadda aure tsakanin girkawa da ragowar qabilu wanda suke kiransu  da barbar ya ke  cikin wannan zamani, haka al'amarin ya ke cikin rumawa lamarin ya kai ga daya  cikin sarakunansu ya sanya doka wanda ya kai ga uqubar hukuncin kisa  ga dukkanin ba rumen da ya auri wadda ba ba rumiya ba, haka larabawan jahiliya suka kasance basa aurar da balarabiya ga wanda ba balarabe ba, kai lamarin ya kai ga  qabila ba ta aurar wanda ba dan qabilarta ba saboda suna ganin kansu mafi daraja daga waninsu,  cikin ba'arin mazhabobin muslunci kamar mazhabar abu hanifa na ganin wanda ba balarabe bai da ce da auren balarabiya ba haka ma wanda ba baquraishe bai cancanci auren baquraishiya ba.

haka ma cikin amerika da qasashene turai sun kasance suna haramtawa ba'amerike ya auri wadda ba ba'amerikiya ba,  haramatawa baqar fata ya auri farar fata, haka al'amarin ya ke cikin qasar jamus.

daga qaidoji akwai wanda ke komawa ga sabani  matsayi, misali a qasar indiya auratayya bai inganta tsakanin barahima da ragowa mutane musammam ma kason da suke ganinsu qasqantattu, hakan na komawa ga sabanin jinsi, kamar yadda ya kasance cikin rumawa suma sun zama suna haramta auren `ya`yan manya da ragowar mutane, a mazhabar hanafiya wanda danginsa suke qasqantu bai cancanci auren `yar babban dangi ba, haka mai qaramar sana'a kamar wanzami da dan shara bai cancanci `yar wanda suke da babbar sana'a ba kamar manyan `yan kasuwa a qasar masar bai gushe ba dangin dake ganin kansu babban dangi suna ganin abin kunyane su auri `yar qananan dangi duk yadda suka kai da dukiya da matsayi cikin jama'a.

daga qaidoji akwai wanda ke komawa ga kusanci babu wata jama'a da suka kubuta daga gareshi, akwai kashe kashe daga muharramai kamar yadda ya ke a muslunci, kamar uwa da `ya da `yar'uwa da `yar'uwan uba da na uwa, ma'ana ya na haramta ga mutum ya auri asalinsa komai nisansu, kamar uwa, kaka, haka idan sun sauko qasa kamar diya da jika, reshen mahaifinsa can qasa  kamar `yar'uwa da `ya`yan `yar uwa da `ya`yan `yar'uwarsa da dan uwansa, da reshensa da ke kai tsaye ga kakanninsa kamar goggo da goggon babansa da goggon kakansa daga babansa da babarsa duk yadda ya kai da yin nisansu, kamar yadda qur'ani ya yi ishara:

[2] حُرِّمَتْ عَلَيْكُمْ أُمَّهَاتُكُمْ وَبَنَاتُكُمْ وَأَخَوَاتُكُمْ وَعَمَّاتُكُمْ وَخَالَاتُكُمْ وَبَنَاتُ الْأَخِ وَبَنَاتُ الْأُخْتِ

 an haramta muku uwayenku da `ya`yayenku da `yan'uwanku  mata da goggoniku da innoninku da `ya`yan dan'uwa da `yar dan'uwa.

daga qaidodi akwai wanda ke komawa ga surutaka, dukkanin wanda ya aura daga wani dangi zai wayi gari daya daga cikin wannan  dangi sai shari'a ta haramta hada mata `yan'uwan juna daga wannan dangi cikin aure lokaci guda, kamar yadda ya haramta  aurar mahaifiyar matarsa haka ma ya haramta mahaifinsa ya auri matarsa, saboda haka asalin matarsa ya na haramta gareshi duk yadda ya kai ga nisa da reshenta duk yadda ya kai ga saukowa qasa, da matan mahaifinsa da kakanninsa  duk nisansu, ga wannan kashi ne ubangiji ke cewa:

وَلَا تَنْكِحُوا مَا نَكَحَ آبَاؤُكُمْ مِنَ النِّسَاءِ إِلَّا مَا قَدْ سَلَفَ إِنَّهُ كَانَ فَاحِشَةً وَمَقْتا وساء سبيلا[3]

14-kada ku aura daga abin da babanniku suka aura daga mata sai dai abin da ya gabata , haqiqa hakan alfasha ne da qyama tafarki ya munana.

daga qaidodi akwai wanda ke komawa ga shan nono, kamar uwa daga shayarwa da asalinta duk yadda suka kai ga nesa, da matar da ku ka sha nono tare, da `ya`yanta duk yadda suka kai ga saukowa qasa da goggo da inna da kuka hadu ta hanyar shan nono, da uwar wadda ta shayar da nono, wannan hukunci na haramci ya na gudana da zarar an qulla aure da macen  da makamancin haka kamar yadda ya zo cikin littafan fiqihu.

 [1] Baqara:221

[2]Nisa'i:23

[3] Nisa'i:22-23