فهرست کتاب‌‌ لیست کتاب‌ها
■ KALMAR TARBIYYA CIKIN HARSHEN LARABCI DA YANDA AKA YI 4
■ FASALI NA ( 2 ) 24
■ AUREN DABI'A 24
■ FASALI NA 3
■ FASALI NA 4 73
■ FASALI NA 5 131
■ FASALI NA 6 176
HAQQOQIN DA MA'AURATA SU KAYI TARAYYA CIKI 177
1 – HAQURI 178
2 – KAMEWA DAGA ZALUNCI DA CUATARWA 179
HAQQOQIN MATA 180
CIYARWA DA YALWATAWA 185
TAUSAYAWA DA KAMEWA DAGA ZALUNCI 187
KAMEWA DAGA BARIN DUKA MAI CUTARWA 187
UMARNI DA KYAKKYAWA DA HANI DA MUMMUNA 193
GARKUWA 196
8 – KYAUTATAWA : 196
9 - KYAWUNTA ZAMANTAKEWA 197
3 – TAUSAYAWA MIJI : 208
4 – HIMMATUWA DA KULA DA CIKIN GIDA DA KAYYAKINSA : 209
5 - HIMMATUWA CIKIN SAUKE HAQQOQI 209
6 – JIMA'I 210
7 - ADO 213
8 – KAMEWA CIKIN MAGANA : 219
SHUGABANTAR IYALI 225
DALILAI DA SUKE SANYA DAWWAMAR AURE 227
1 – SON JUNA 228
2 – YAWAITA AIKATA ALHERI: 228
4 – SANYA FARIN CIKI: 229
5 – BIYAYYA DA NEMAN YARDAR MIJI: 230
6 – KIYAYE MUTUNCI DA DUKIYA : 230
7 – TAIMAKO DA TALLAFAWA 230
8 – TARBAR MIJI DA KYAWUNTA BANKWANA DA SALLAMA : 231
9 – KALAMIN AQIDOJI MAI KYAWU DA QARFAFAFFEN FURUCI. 232
10 – KARBAR UZURI DA YIWA JUNA UZURI : 232
11 – BINSU SANNU SANNU CIKIN KOWANNE HALI : 233
12 – KYAWUNTA LAFAZI CIKN KOWANNE YANAYI : 233
13 – RASHIN SAURARON KYAUTATA AIKI DARI BISA DARI 233
14 – RASHIN IKON DAUKAR NAUYI A RAYUWANCE : 234
15 – RASHIN GORI KAN MIJI : 234
16 – RASHIN QAURACEWA AL'AMARIN SHIMFIDA: 235
17 - YIN SHAWARA DA MATA BANDA BIYE MUSU: 235
18 – TAKA TSAN TSAN DA KUMA FARKAWA : 238
19 – HANKALTA 239
20 - MIJI SHI NE MUTUNCIN MATARSA 240
21 – KISHI 240
22 – TAIMAKEKENIYYA 242
23 – DADADAWA IYALI 243
27 – WATSI DA BOAKANCI DA TSAFE TSAFE : 244
28 - HIDIMA MADAWWAMIYA 245
29 – GODIYA 246
29 – QAUNAR JUNA 247
TSINTUWA GUDA BIYU GIDAN ALI DA FATIMA (AS) 248
■ FASALI NA 8 252

SAMUN CIKAR KAMALA CIKIN AURE 54

SAMUN CIKAR KAMALA CIKIN AURE                          

Allah madaukakin sarki na cewa : 

يُرِيدُ اللَّهُ أَنْ يُخَفِّفَ عَنْكُمْ وَخُلِقَ الْإِنْسَانُ ضَعِيفً[1]

 Allah na nufin sauqaqa muku an halicci mutum cikin rauni.

خُلِقَ الْإِنْسَانُ مِنْ عَجَل[2]

an halicci mutum daga gaggawa

إِنَّ الْإِنْسَانَ خُلِقَ هَلُوعًا (19) إِذَا مَسَّهُ الشَّرُّ جَزُوعًا (20) وَإِذَا مَسَّهُ الْخَيْرُ مَنُوعً[3]ا

ا  lalle mutum an halicci mai tsananin kwadayi  idan sharri ya sameshi sai ya kasance mai yawan kuka da raki  idan alheri ya same shi sai ya kasance mai yawan rowa.

وَإِذَا مَسَّكُمُ الضُّرُّ فِي الْبَحْرِ ضَلَّ مَنْ تَدْعُونَ إِلَّا إِيَّاهُ فَلَمَّا نَجَّاكُمْ إِلَى الْبَرِّ أَعْرَضْتُمْ وَكَانَ الْإِنْسَانُ كَفُورً[4]ا

idan cutarwa ta sameku ciki teku sai ku manta da abin da ku ke kira face shi sa'ilin da ya tserarta da ku ya zuwa kan qasa  sai kuka bijire mutum ya kasance mai yawan butulci.

فَإِذَا رَكِبُوا فِي الْفُلْكِ دَعَوُا اللَّهَ مُخْلِصِينَ لَهُ الدِّينَ فَلَمَّا نَجَّاهُمْ إِلَى الْبَرِّ إِذَا هُمْ يُشْرِكُون[5]

yayin da suka hau cikin jirgi suka kira suna masu tsarkake addini yayin da ya tseratar da shi ya zuwa kan qasa sai gashi suna shirka.

إِذَا أَذَقْنَا الْإِنْسَانَ مِنَّا رَحْمَةً فَرِحَ بِهَا وَإِنْ تُصِبْهُمْ سَيِّئَةٌ بِمَا قَدَّمَتْ أَيْدِيهِمْ فَإِنَّ الْإِنْسَانَ كَفُور[6] 

 

idan muka dandanawa mutum rahama daga garemu sai yayi farin ciki da ita idan kuma wani mai muni ya samesu bisa abin da hannuwansu suka gabatar haqiqa mutum mai tsananin kafircine. 

قُتِلَ الْإِنْسَانُ مَا أَكْفَرَه[7]

an tsinema mutun kafiri me ya yi kafircinsa.  

إِنَّ الْإِنْسَانَ لِرَبِّهِ لَكَنُود وَإِنَّهُ عَلَى ذَلِكَ لَشَهِيد[8]

lalle  mutum mai tsananin butulci ne ga ubangijinsa  kuma shi mai shaida ne kan haka.

mutum ya kasance mafi jayayya cikin kowanne abubuwa.

إنَّا عَرَضْنَا الأمَانَةَ عَلَى السَّمَوَاتِ وَالأرْضِ وَالجِبَالِ فَأ بَـيْنَ أنْ يَحْمِلْنَهَا وَأشْفَقْنَ مِنْهَا وَحَمَلَهَا الإنْسَانُ إنَّهُ كَانَ ظَلُوماً جَهُولا[9]

Lalle ne mu mun bijiro da amana ga ahalin sama da qasa da duwatsu duka suka qi yarda da su dauka suka tsorata amma sai mutum ya dauka lalle shi mai yawan zaluntar kansa ne mai yawan jahilci.

وَكَانَ الإنسَانُ أكْثَرَ شَيْء جَدَلا[10]

Mutum ya kasance mafi yawan jayayya daga kowanne abu.   

misalin wadannan ayoyi masu karamci na ishara da kan haqiqanin mutum bisa la'akari kansa mai yawan umarni da mummuna, haqiqa shi kamar yadda ya ke dauke da hankali wanda da shi ne zai kai ga ubangijinsa, haqiqa shi mai gogayya ya zuwa gareshi ne kuma tabbas zai gana da ubangijinsa ya zuwa mahallin tsakankanin baka ko mafi kusa daga haka, gareshi ne al'amurra ke komawa, makoma na gareshi haqiqa dukkanin mu ya zuwa gareshi zamu koma, mutum da haskakakken hankalinsa ke tafiya kan hanyar Allah da siradinsa, sai dai cewa cikinsa an halicci rai mai umarni da mummuna don ya zama ya tattaro tsakanin kishiyoyin juna, ko dai yabi son rai sai zuciyarsa ta zama kamar dutsi ko kuma tafi ma dutsi qeqashewa, ya kasance kamar dabbobi ko mafi batan hanya daga dabbobi, ko kuma ya filfila cikin samaniyar darajoji cikin matsugunin gaskiya wuri sarki mai qudura mala'iku suyi masa hidima da matayen aljanna.

kadai hakan na kasancewa da jin qan ubangiji, abin nufa shi ne tsoron Allah me ya sanar da kai gameda tsoron Allah.

يَا أَيُّهَا النَّاسُ اتَّقُوا رَبَّكُمُ الَّذِي خَلَقَكُمْ مِنْ نَفْسٍ وَاحِدَةٍ وَخَلَقَ مِنْهَا زَوْجَهَا وَبَثَّ مِنْهُمَا رِجَالًا كَثِيرًا وَنِسَاء[11]

  ya ku mutane kuji tsoron ubangiji wanda ya halicceku daga rai guda ya halicci daga gareta matarta ya kuma yada mazaje masu yawa da mata.

يَا أَيُّهَا النَّاسُ إِنَّا خَلَقْنَاكُمْ مِنْ ذَكَرٍ وَأُنْثَى وَجَعَلْنَاكُمْ شُعُوبًا وَقَبَائِلَ لِتَعَارَفُوا إِنَّ أَكْرَمَكُمْ عِنْدَ اللَّهِ أَتْقَاكُمْ إِنَّ اللَّهَ عَلِيمٌ خَبِير[12]

ٌya ku mutane haqiqa lalle ne mu mun hallicceku daga mace da namiji muka sanya ku al'ummu da qabilu don kusan juna haqiqa mafi karamcin cikinku wajen Allah shi ne mafi tsoronsa lalle ne Allah masani ne da qididdigawa.

yawancin zunubai daga gwaurantaka suke da galabar sha'awar jinsi, kan haka ne muka samu  nassosi addini da ke kwadaitar da samari kan yin aure da kuma cewa dukkanin wanda ya yi aure to ya tabbatar da rabin addininsa sai ya ji tsoron Allah cikin daya rabin.

 

عن الإمام الصادق (عليه السلام) ، قال  : جاء رجل إلى أبي فقال له  : هل لك زوجة  ؟ قال  : لا ، قال لا اُحبّ أنّ لي الدنيا وما فيها وأ نّي أبيت ليلة ليس لي زوجة ، قال  : ثمّ قال  : إنّ ركعتين يصلّيهما رجل متزوّج أفضل من رجل يقوم ليله ويصوم نهاره أعزباً ، ثمّ أعطاه أبي سبعة دنانير ، قال  : تزوّج بهذه ، وحدّثني بذلك سنة ثمان وتسعين ومائة ، ثمّ قال أبي  : قال رسول الله (صلى الله عليه وآله)  : اتّخذوا الأهل فإنّه أرزق لكم[13]

1-an karbo daga sadiq (as) ya ce : wani mutum ya zo wajen babana sai ya ce masa: shin kana da mata ?  sai ya ce: a'a, sai imam ya ce : ban san ace inada duniya da dukkanin abin da ke cikinta in kwanta dare daya alhalin banda mata, sannan ya qara da cewa: lalle raka'a biyu da mai aure  da ya yi tafi falala daga tsayuwar daren  gwauraye ya kuma kasance sun wayi gari cikin azumi, sannan babana ya bashi dinare 70 ya ce masa kaje kayi aure da wannan. Sannan babana ya a ce: manzon Allah(saw) y ace: kuyi aure lalle shi aure arziqine gareku.  dukkanin wanda bai  samu iko ba kan yin aure to ya zama wajibi kan malamai su samar masa da abin da zai yi aure daga asusun baitul mali  kamar yadda ya kasance shi aure na dada arziqi.

قال أمير المؤمنين (عليه السلام)  : تزوّجوا فإنّ رسول الله (صلى الله عليه وآله) كثيراً ما كان يقول  : من كان يحبّ أن يتّبع سنّتي فليتزوّج ، فإنّ من سنّتي التزويج ، واطلبوا الولد فإنّي اُكاثر بكم الاُمم غداً  

2-sarkin muminai aliyu dan abu dalib (as) na cewa : kuyi aure haqiqa manzon Allah ya kasance yana yawaita fadin cewa : dukkanin wanda ke son bin sunna ta to ya yi aure domin daga cikin sunna ta shi ne aure, ku nemi diya haqiqa zanyi alfahri daku ranar alqiyama.

عن الرضا (عليه السلام) ، قال  : إنّ امرأة سألت أبا جعفر (عليه السلام) فقالت  : أصلحك الله ، إنّي متبتّلة ، فقال لها  : وما التبتّل عندك  ؟ قالت  : لا اُريد التزويج أبداً ، قال  : ولِمَ  ؟ قالت  : ألتمس في ذلك الفضل ، فقال  : انصرفي فلو كان في ذلك فضل لكانت فاطمة (عليها السلام) أحقّ به منكِ ، إنّه ليس أحد يسبقها إلى الفضل[14]

3- an karbo daga imam rida (as) ya ce:wata mace ta tambayi baban jafar (as) tace Allah ye maka gyara lalle ni baiwar Allah ce mai yankewa qauna  daga kowa ya zuwa ga ubangiji, sai baban jafar ya ce mata me ye yankewar ki ? sai tace ni bana son aure har abada, sai ya ce: me yasa ? sai ta ce ina neman daraja da yin hakan, sai ya ce : tafi ki bamu waje da cikin hakan akwai daraja da fatima (as) tafi cancanta da aikata hakan daga gareki lalle babu wani mutum da zai gabaceta cikin daraja.

kamar yadda sarkin mumiani ali (as) ya kasance ma'aunin ayyuka lalle ne fatima (as) tamkace gareshi kuma shugabar matan aljanna, bisa gwauranta da qin yin aure bai sanyawa mutum wata daraja da kamala.

قال رسول الله (صلى الله عليه وآله)  : من تزوّج فقد أحرز نصف دينه ، فليتّقِ الله في النصف الباقي[15]

4- manzon Allah (saw) na cewa dukkanin wanda ya yi aure ya tabbatar da rabin addinisa ya ji tsoron Allah cikin daya rabin.

وقال (صلى الله عليه وآله)  : من أحبّ أن يلقى الله طاهراً مطهّراً فليلقه بزوجة

5- wani fadin kuma ya ce : dukkanin mai son ganawa da Allah ya na tsarkakakke mai tsarkakewa to ya yi qoqarin ganawa da shi alhalin ya na da aure,

وقال  : شرار موتاكم العزّاب

6- a wani hadisin kuma ya ce : mafi qasqancin mamatanku gwagware.

وفي حديث آخر  : رذّال موتاكم العزّاب

7-a wani hadisin kuma yace: wuqantattun mamatanku su ne gwauraye.

وقال (صلى الله عليه وآله)  : النكاح سنّتي فمن رغب عن سنّتي فليس منّي

8-aure sunnata ne dukkanin wanda ke qyamar sunna ta baya daga gareni.

وقال (صلى الله عليه وآله)  : تناكحوا تكثروا فإنّي اُباهي بكم الاُمم يوم القيامة ولو  بالسقط  

9-ku yiyyi aure ku yawaita lalle ni zan yiwa al'ummu alfahari da ku ranar qiyama koda kuwa da dan da akayi barinsa.

wannan hukunci mai gamewa ne har zuwa ranar qiyama yana mai kishiyantar masu cewa a taqaita hayayyafa kamar yadda ya ke cikin wannan zamani da muke ciki, sai dai cewa an riwaito cewa qarancin iyali na daya daga cikin sauki, dukkanin me son rayuwa cikin sauki ba qunci ta fuskanin tattalin arziki, to yalwarsa wani lokaci kan kasancewa cikin kudi da dukiya, wani lokacin kuma cikin qarancin iyali da  `ya`ya, sannan alfaharin manzon Allah (saw) da adadi ne kamar yadda  zahiri  abin da za'a fahimta shi ne cewa alfahari wani lokacin na kasancewa da yawan adadi, wani lokacin kuma da yanayi sau da yawa kana samun mai qarancin iyali amma ka ga ya samu damar tarbiyantar dasu fiye waninsa.

sannan babu  karo da juna cikin hadisan biyu domin cewa rashin yawan iyali daya daga cikin yalwa ne cikin tattalin arziqi, wanda ke da iko da dukiya ya hayayyafa da yawa annabi(saw) zai alfahari da shi  hatta dan da akayi barinsa daga cikin abin da ke ishara ya zuwa cewa aure na kawo kamala shi ne:

عن رسول الله (صلى الله عليه وآله) ، قال  : من تزوّج فقد اُعطي نصف العبادة[16]

10-Abin da aka riwaito daga manzon Allah (saw) dukkanin wanda ya yi aure haqiqa an bashi rabin ibadarsa.

وقال (صلى الله عليه وآله)  : المتزوّج النائم أفضل عند الله من الصائم القائم العزب

11- manzon Allah(saw)yace: mai auri da yake barci ya fi daraja wajen Allah daga tuzuru mai azumi mai tsayuwa dare.

وقال (صلى الله عليه وآله)  : يفتح أبواب السماء بالرحمة في أربع مواضع  : عند نزول المطر ، وعند نظر الولد في وجه الوالدين ، وعند فتح باب الكعبة ، وعند النكاح

12- wani fadin kuma ya ce : ana bude qofofin sama da rahama cikin wurare hudu : yayin zubar ruwan sama, lokacin da da ke kallon fuskar mahaifansa, yayin bude qofar ka'aba, da lokacin daurin aure.

وقال (صلى الله عليه وآله) لرجل اسمه عكّاف  : ألك زوجة  ؟ قال  : لا يا رسول الله ، قال  : ألكَ جارية ، قال  : لا يا رسول الله ، قال  : أفأنت موسر  ؟ قال  : نعم . قال  : تزوّج وإلاّ فأنت من المذنبين

13-Manzon Allah (saw) ya cewa : wani mutu da ake kiransa akkaf shin kana da mata ? sai mutum ya ce banda mata ya manzon Allah, sai ya qara tambayarsa kana da baiwa ? sai ya ce a' a ya manzon Allah, sai ya qara tambayarsa shin kana yalwar hannu ? sai ya ce na'am

sai manzon ya ce masa ka yi aure idan ba haka ba kai mai zunubi ne.

وفي رواية  : تزوّج وإلاّ فأنت من رهبان النصارى

 14- a wata riwayar kuma ka yi aure in ba kayi ba kai baruhubane ne na nasara, ko kuma dan'uwan shaidanu.

قال (عليه السلام)  : شراركم عزّابكم ، والعزّاب إخوان الشياطين

15-manzon Allah (saw) ya ce : mafi sharrin cikinku gwagwarenku, su gwauraye `yan'uwan shaidanu ne.

وقال (عليه السلام)  : خيار اُمّتي المتأهّلون ، وشرار اُمّتي العزّاب

16-ya ce : mafi alherin cikin al'ummatu ma'aurata, mafi sharrinsu gwagware.

وقال (صلى الله عليه وآله)  : من أحبّ أن يكون على فطرتي فليستن بسنّتي ، وإنّ من سنّتي النكاح

17- duk mai son kasancewa kan dabi'a ta to ya raya sunnata, kuma haqiqa daga cikin sunna ta aure.

وقال (صلى الله عليه وآله)  : زوّجوا أياماكم ، فإنّ الله يحسن لهم في أخلاقهم ، ويوسّع لهم في أرزاقهم ، ويزيدهم في مروّاتهم

18-wani gurin ya ce : ku aurar da gwagwarenku, haqiqa Allah zai kyawunta musu  cikin dabi'unsu, ya yalwata musu arziqinsu, ya qara mutunci.

وقال  : ما بني في الإسلام بناء أحبّ إلى الله عزّ وجلّ وأعزّ من التزويج

 ya ce ba ayi wani gini a muslunci mafi soyuwa wajen Allah[1] Nisa'i:28

[2] Anbiya:37

[3] Ma'arij:19-20

[4] Isra'I:67

[5] Isra'i:65

[6] Shura:48

[7]Abasa:17

[8] Adiyat:6-7

[9] Ahzab:72

[10] Kahfu:54

[11] Nisa'i:1

[12] Hujrat:13

[13] Biharun anwar m 100 sh 217

[14] Biharul anwar m 100 sh 219

[15] Masdarin da ya gabata

[16] Biharul anwar m 100 sh 220