فهرست کتاب‌‌ لیست کتاب‌ها
■ KALMAR TARBIYYA CIKIN HARSHEN LARABCI DA YANDA AKA YI 4
■ FASALI NA ( 2 ) 24
■ AUREN DABI'A 24
■ FASALI NA 3
■ FASALI NA 4 73
■ FASALI NA 5 131
■ FASALI NA 6 176
HAQQOQIN DA MA'AURATA SU KAYI TARAYYA CIKI 177
1 – HAQURI 178
2 – KAMEWA DAGA ZALUNCI DA CUATARWA 179
HAQQOQIN MATA 180
CIYARWA DA YALWATAWA 185
TAUSAYAWA DA KAMEWA DAGA ZALUNCI 187
KAMEWA DAGA BARIN DUKA MAI CUTARWA 187
UMARNI DA KYAKKYAWA DA HANI DA MUMMUNA 193
GARKUWA 196
8 – KYAUTATAWA : 196
9 - KYAWUNTA ZAMANTAKEWA 197
3 – TAUSAYAWA MIJI : 208
4 – HIMMATUWA DA KULA DA CIKIN GIDA DA KAYYAKINSA : 209
5 - HIMMATUWA CIKIN SAUKE HAQQOQI 209
6 – JIMA'I 210
7 - ADO 213
8 – KAMEWA CIKIN MAGANA : 219
SHUGABANTAR IYALI 225
DALILAI DA SUKE SANYA DAWWAMAR AURE 227
1 – SON JUNA 228
2 – YAWAITA AIKATA ALHERI: 228
4 – SANYA FARIN CIKI: 229
5 – BIYAYYA DA NEMAN YARDAR MIJI: 230
6 – KIYAYE MUTUNCI DA DUKIYA : 230
7 – TAIMAKO DA TALLAFAWA 230
8 – TARBAR MIJI DA KYAWUNTA BANKWANA DA SALLAMA : 231
9 – KALAMIN AQIDOJI MAI KYAWU DA QARFAFAFFEN FURUCI. 232
10 – KARBAR UZURI DA YIWA JUNA UZURI : 232
11 – BINSU SANNU SANNU CIKIN KOWANNE HALI : 233
12 – KYAWUNTA LAFAZI CIKN KOWANNE YANAYI : 233
13 – RASHIN SAURARON KYAUTATA AIKI DARI BISA DARI 233
14 – RASHIN IKON DAUKAR NAUYI A RAYUWANCE : 234
15 – RASHIN GORI KAN MIJI : 234
16 – RASHIN QAURACEWA AL'AMARIN SHIMFIDA: 235
17 - YIN SHAWARA DA MATA BANDA BIYE MUSU: 235
18 – TAKA TSAN TSAN DA KUMA FARKAWA : 238
19 – HANKALTA 239
20 - MIJI SHI NE MUTUNCIN MATARSA 240
21 – KISHI 240
22 – TAIMAKEKENIYYA 242
23 – DADADAWA IYALI 243
27 – WATSI DA BOAKANCI DA TSAFE TSAFE : 244
28 - HIDIMA MADAWWAMIYA 245
29 – GODIYA 246
29 – QAUNAR JUNA 247
TSINTUWA GUDA BIYU GIDAN ALI DA FATIMA (AS) 248
■ FASALI NA 8 252

5 - QARUWAR ARZIQI : 65

5 -  QARUWAR ARZIQI :

وقال (صلى الله عليه وآله)  : « التمسوا الرزق بالنكاح

9-Manzon Allah (saw) ya ce: ku nemi arziqi ta hanyar yin aure.

عَنْ أَبِي عَبْدِ اللَّهِ ع قَالَ: جَاءَ رَجُلٌ إِلَى أَبِي عَبْدِ اللَّهِ ع فَقَالَ لَهُ هَلْ لَكَ مِنْ زَوْجَةٍ فَقَالَ لَا فَقَالَ أَبِي وَ مَا أُحِبُّ أَنَّ لِيَ الدُّنْيَا وَ مَا فِيهَا وَ أَنِّي بِتُّ لَيْلَةً وَ لَيْسَتْ لِي زَوْجَةٌ ثُمَّ قَالَ الرَّكْعَتَانِ يُصَلِّيهِمَا رَجُلٌ مُتَزَوِّجٌ أَفْضَلُ مِنْ رَجُلٍ أَعْزَبَ يَقُومُ لَيْلَهُ وَ يَصُومُ نَهَارَهُ ثُمَّ أَعْطَاهُ أَبِي سَبْعَةَ دَنَانِيرَ ثُمَّ قَالَ لَهُ تَزَوَّجْ بِهَذِهِ ثُمَّ قَالَ أَبِي قَالَ رَسُولُ اللَّهِ ص اتَّخِذُوا الْأَهْلَ فَإِنَّهُ أَرْزَقُ لَكُم[1]

10-Alkafi da isnadinsa daga baban Abdullah (as) wani mutum ya je wajen baban Abdullah (as) sai babana ya ce masa shin kana da aure sai mutum ya ce: a'a, babana ya ce: bana son duniya da dukkanin abin da ke cikinta ya kasance ni na kwana dare daya alhalin banda mata, sannan ya qara cewa raka'a biyu da mai aure zai sallaceta tafi falala daga tsayuwar daren tuzuru da azumce rana, sai ya bashi dinare bakwai ya ce : ka yi aure da wannan,  ya ce: manzon Allah (saw) ya ce ku riqi iyali haqiqa su arziqinku ne.

المصدر بسنده عن جعفر بن محمّد عن أبيه عن آبائه (عليه السلام) قال  : قال رسول الله (صلى الله عليه وآله)  : من ترك التزويج مخافة العيلة فقد أساء ظنّه بالله . إنّ الله عزّ وجلّ يقول  : (  إنْ يَكُونُوا فُقَرَاءَ يُغْنِهِمُ اللهُ مِنْ فَضْلِهِ[2]   

11-daga baban jafar (as) daga babanninsa ya ce : manzon Allah (saw) ya ce : duk mutumim da yaqi yin aure saboda tsoron talauci lalle ya munanta zatonsa ga Allah, haqiqa Allah mai girma da daukaka ya na cewa: idan suka kasance talakawa Allah zai wadatasu daga falalarsa.

ـ الفقيه ، بسنده ، قال النبيّ (صلى الله عليه وآله)  : من سرّه أن يلقى الله طاهراً مطهّراً فليلقه بزوجة ، ومن ترك التزويج مخافة العيلة فقد أساء الظنّ بربّه عزّ وجل[3] .

12-Daga littafin alfaqihu da isnadinsa manzon Allah (saw) na cewa: dukkanin wanda ya ke faranta masa ace ya hadu da ubangiji ya na tsarkakakke mai tsarkakewa  to ya hadu da shi yana mai aure, dukkanin wanda ya bar aure saboda tsoron talauci lalle ya muzanta zatonsa da ubangijinsa mai girma da daukaka.

عَنْ أَبِي عَبْدِ اللَّهِ ع قَالَ: جَاءَ رَجُلٌ إِلَى النَّبِيِّ ص فَشَكَا إِلَيْهِ الْحَاجَةَ فَقَالَ تَزَوَّجْ فَتَزَوَّجَ فَوُسِّعَ عَلَيْه.وقال:اتخذوا الأهل فانه أرزق لكم,وقال:تزوجوا للرزق فان لهن البركة.[4]

13-.Alkafi da isnadinsa daga baban Abdullah (as) ya ce : wani mutum ya zo wajen annabi (saw) sai ya kai kukan buqatarsa ga annabi, sai annabi (saw) ya ce masa kayi aure, sai mutum ya yi aure Allah ya yalwata masa arziqi  a wani fadin manzon  Allah (saw) yace : kuyi aure don neman arziqi haqiqa albarka na tare da mata.

  duk wanda ya kasance talaka  daga cikin tasirin canjin yanayi cikin aure shi ne samun qarin arziqi, kamar yadda ubangiji ke fadi ( idan sun kasance talakawa Allah zai wadatasu daga falalarsa ) yayin da saurayi ya yi aure da farko zai ga cewa an dora nauyi kan wuyansa to anan nefa zaka ga ya daura damara da dagewa wajen yin aiki tukuru, sai kaga arziqinsa na ta qaruwa, Allah na azurta wanda ya so ba tare da lissafi ba ya sanya albarka cikin wanda ke yin aiki da tsarkakakkiyar niyya da dogaro da shi, baya tsoron talauci da yawan iyali  haqiqa arziqin kowa na hannun Allah, kamar yadda ya zo cikin Karin Magana cewa: dukkanin wanda aka azurta shi da haqora to za a azurta da gurasar da zai tauna.

قال رسول الله (صلى الله عليه وآله)  : « من ترك التزويج مخافة العيلة فقد أساء الظنّ بربّه ، لقوله سبحانه وتعالى  :  إنْ يَكُونُوا فُقَرَاءَ يُغْنِهِمُ اللهُ مِنْ فَضْلِه

14-manzon Allah(saw):duk wanda ya qi yin aure saboda tsoron talauci lalle ya munana zato ga Allah, saboda fadin Allah: idan sun kasance talakawa Allah zai wadata su daga falalarsa. 

Lalle mumini ya kyawunta zato ga ubangijinsa, haqiqa Allah matsarkaki na cewa: ni ina wajen zaton bawana mumini, kuma Allah na son masu tawakkali, shi motsi da fita nema suna kan bawa albarka kuma na wajen ubangiji kamar yadda ya zo cikin karin magana.

قال (صلى الله عليه وآله)  : تزوّجوا النساء ، فإنّهنّ يأتين بالمال

15-manzon Allah (saw)ya na cewa : ku auri mataye haqiqa su suna kawo dukiya.

 Allah ma'abocin albarka ya na albarkantakar ma'aurata masu miqa al'marinsu gareshi da tawakkali, matar da ka aura takan zama sanadin samun dukiya da kudade na halaliya da arziqi tsaftatacce mai amfani.

عَنْ إِسْحَاقَ بْنِ عَمَّارٍ قَالَ: قُلْتُ لِأَبِي عَبْدِ اللَّهِ ع الْحَدِيثُ الَّذِي يَرْوِيهِ النَّاسُ حَقٌّ أَنَّ رَجُلًا أَتَى النَّبِيَّ ص فَشَكَا إِلَيْهِ الْحَاجَةَ فَأَمَرَهُ بِالتَّزْوِيجِ فَفَعَلَ ثُمَّ أَتَاهُ فَشَكَا إِلَيْهِ الْحَاجَةَ فَأَمَرَهُ بِالتَّزْوِيجِ حَتَّى أَمَرَهُ ثَلَاثَ مَرَّاتٍ فَقَالَ أَبُو عَبْدِ اللَّهِ ع [نَعَمْ] هُوَ حَقٌّ ثُمَّ قَالَ الرِّزْقُ مَعَ النِّسَاءِ وَ الْعِيَال[5]

16-Alkafi da isnadinsa daga is'haq dan ammar ya ce: na cewa baban Abdullah (as) shin hadisin  da mutane keta rawaitowa gaskiya ne cewa wani mutum ya zo wajen annabi ya kai kukan buqatarsa sai annabi ya umarce shi da yin aure, mutumin ya aikata, ya qara dawowa wajen annabi karo na biyu ya qara kai kukan buqatarsa annabi ya qara umartarsa da yin aure, ya maimaita hakan har karo na uku annabi dai yana qara umartarsa da aure ? sai baban Abdullah (as) ya ce: na'am gaskiya ne, sai ya ce: arziqi na tareda da mata da iyali.

Galibi cikin al'amarin aure shi ne daduwar arziqi, sai dai cewa a wasu  kadan daga cikin lokuta wanda bai fiye afkuwa ba qaruwar arziqi kan kasance cikin rabuwar aure da saki, cikin misalin wannan sai akomar da al'amari ya zuwa annabi ko imami masana ga haqiqanin al'amurra, bai halasata ga wani mutum idan ya riski kunci cikin farkon rayuwarsa ta aure ya fara tunanin yin saki saboda wani nassi da ya ke da shi daga wani hadisi kwaya daya rak, saboda wannan hadisi bai iya jayayya da hadisai masu tarin yawa da suka zo suna ishara kan cewa aure yana qara arziq , saboda haka sai a lura.

عَنِ ابْنِ أَبِي لَيْلَى قَالَ حَدَّثَنِي عَاصِمُ بْنُ حُمَيْدٍ قَالَ: كُنْتُ عِنْدَ أَبِي عَبْدِ اللَّهِ ع فَأَتَاهُ رَجُلٌ فَشَكَا إِلَيْهِ الْحَاجَةَ فَأَمَرَهُ بِالتَّزْوِيجِ قَالَ فَاشْتَدَّتْ بِهِ الْحَاجَةُ فَأَتَى أَبَا عَبْدِ اللَّهِ ع فَسَأَلَهُ عَنْ حَالِهِ فَقَالَ لَهُ اشْتَدَّتْ بِيَ الْحَاجَةُ فَقَالَ فَفَارِق.[6]

17-Alkafi da isnadinsa daga baban laila ya ce : asim dan hamidu ya bani labari ya ce : na kasance wajen baban Abdullah (as) sai wani mutum ya zo wajensa ya gaya masa buqutarsa, sai ya umarce shi da yin aure, yace sai buqatar ta qara tsananta, ya qara zuwa wajen baban Abdullah(as) ya tambaye shi halin da ya ke ciki sai mutumin ya ce : buqatar ta tsananta kaina, sai imam ya ce: ka saketa.

18-daga baya mutumin ya zo wajen imam (as) imam ya tambayeshi halin da ya ke ciki, sai ya ce : nayi kudi halin da na ke ciki ya kyawunta, imam ya ce : haqiqa na umarce ka da al'amura biyu da Allah ya yi umarni da suوَأنكِحُوا الأيَامَى مِنْكُمْ   (ku auri mata marasa miji daga gareku ) ya zuwa[7]وَاللهُ وَاسِعٌ عَلِيمٌ   

 Allah mayalwaci ne masani.

  wata ayar kuma ya ce: وَإنْ يَتَفَرَّقَا يُغْنِ اللهُ كُلاّ مِنْ سَعَتِه[8]ِ   (idan suka rabu Allah zai wadata kowannensu daga yalwarsa.[1] Alkafi m 5 sh 329

[2] Nurr:32

[3]Alfaqihu m 3 sh 385

[4] Alkafi m 5 sh330

[5] Alkafi m 5 sh 330

[6] Alkafi m 5 sh 331

[7] Nurr:32

[8] Nisa'i:130