فهرست کتاب‌‌ لیست کتاب‌ها
■ KALMAR TARBIYYA CIKIN HARSHEN LARABCI DA YANDA AKA YI 4
■ FASALI NA ( 2 ) 24
■ AUREN DABI'A 24
■ FASALI NA 3
■ FASALI NA 4 73
■ FASALI NA 5 131
■ FASALI NA 6 176
HAQQOQIN DA MA'AURATA SU KAYI TARAYYA CIKI 177
1 – HAQURI 178
2 – KAMEWA DAGA ZALUNCI DA CUATARWA 179
HAQQOQIN MATA 180
CIYARWA DA YALWATAWA 185
TAUSAYAWA DA KAMEWA DAGA ZALUNCI 187
KAMEWA DAGA BARIN DUKA MAI CUTARWA 187
UMARNI DA KYAKKYAWA DA HANI DA MUMMUNA 193
GARKUWA 196
8 – KYAUTATAWA : 196
9 - KYAWUNTA ZAMANTAKEWA 197
3 – TAUSAYAWA MIJI : 208
4 – HIMMATUWA DA KULA DA CIKIN GIDA DA KAYYAKINSA : 209
5 - HIMMATUWA CIKIN SAUKE HAQQOQI 209
6 – JIMA'I 210
7 - ADO 213
8 – KAMEWA CIKIN MAGANA : 219
SHUGABANTAR IYALI 225
DALILAI DA SUKE SANYA DAWWAMAR AURE 227
1 – SON JUNA 228
2 – YAWAITA AIKATA ALHERI: 228
4 – SANYA FARIN CIKI: 229
5 – BIYAYYA DA NEMAN YARDAR MIJI: 230
6 – KIYAYE MUTUNCI DA DUKIYA : 230
7 – TAIMAKO DA TALLAFAWA 230
8 – TARBAR MIJI DA KYAWUNTA BANKWANA DA SALLAMA : 231
9 – KALAMIN AQIDOJI MAI KYAWU DA QARFAFAFFEN FURUCI. 232
10 – KARBAR UZURI DA YIWA JUNA UZURI : 232
11 – BINSU SANNU SANNU CIKIN KOWANNE HALI : 233
12 – KYAWUNTA LAFAZI CIKN KOWANNE YANAYI : 233
13 – RASHIN SAURARON KYAUTATA AIKI DARI BISA DARI 233
14 – RASHIN IKON DAUKAR NAUYI A RAYUWANCE : 234
15 – RASHIN GORI KAN MIJI : 234
16 – RASHIN QAURACEWA AL'AMARIN SHIMFIDA: 235
17 - YIN SHAWARA DA MATA BANDA BIYE MUSU: 235
18 – TAKA TSAN TSAN DA KUMA FARKAWA : 238
19 – HANKALTA 239
20 - MIJI SHI NE MUTUNCIN MATARSA 240
21 – KISHI 240
22 – TAIMAKEKENIYYA 242
23 – DADADAWA IYALI 243
27 – WATSI DA BOAKANCI DA TSAFE TSAFE : 244
28 - HIDIMA MADAWWAMIYA 245
29 – GODIYA 246
29 – QAUNAR JUNA 247
TSINTUWA GUDA BIYU GIDAN ALI DA FATIMA (AS) 248
■ FASALI NA 8 252

6 – QARUWAR IMANI : 69

6 – QARUWAR IMANI :

قال النبيّ (صلى الله عليه وآله)  : يا شابّ تزوّج ، وإيّاك والزنا ، فإنّه ينزع الإيمان من قلبك .

18-Manzon Allah (saw) ya ce: ya kai saurayi ka yi aure na haneka da yin zina, haqiqa ita zina tana cire imani daga zuciyarka.

Wannan nasiha ce daga annabi da ke tattare da qauna da tausayi, da jima al'umma da daidaikunta tsoron tabarbarewa da fadawa cikin wutar hawiya, ta hanyar ficewar imani daga zuciya haqiqa ita zuciya idan ta kasance mumina ta gari to dukkanin ragowar gabbai zasu gyaru su zama nagari daga nan ne al'umma ta ke gyaruwa, amma idan ta kasance kafira to dukkanin gabbai zasu kafirta al'umma ta kafirta. annabi na kiran saurayi ya zuwa ga yin aure da tsoratar da shi kan hatsarin zina  domin mumini ba ya yin zina yana halin kasancewarsa mumini, haqiqa shi yana cire ruhin imanin yayin da yake zakkewa sabo, kuma dukkanin wanda bai da imani to yana cikin duhu wanda sashensa ke kan sashe, ta yanda babu haske tare da shi, to shi a irin wannan zai wayi gari yana fagarniya cikin duhu ya fada cikin hawiya da mai zame qafafuwa, ya wajabta kan dukkanin musulmi su yi bakin kokarinsu wajen kawar da dukkanin matsala da ke kan hanyar samari matasa, kowanne cikinsu ya yi kokari da dukkanin hikimar da ya ke da ita wajen ganin samari ma'aurata sun samu dacewa.

قال أمير المؤمنين علي (عليه السلام)  : أفضل الشفاعات أن تشفع بين اثنين في نكاح حتّى يجمع الله بينهما

19-Sarkin muminai aliyu dan abi dalibi (as) yana cewa : mafi falalar ceto shi ne ka cetar da tsakanin mutane biyu cikin aure har Allah ya hada tsakaninsu.

Haqiqa hakan aikine me kyawun gaske wanda ke janyo samun yardar Allah da farin cikin manzon Allah da yin alfaharinsa da al'ummarsa ranar qiyama.