فهرست کتاب‌‌ لیست کتاب‌ها
■ KALMAR TARBIYYA CIKIN HARSHEN LARABCI DA YANDA AKA YI 4
■ FASALI NA ( 2 ) 24
■ AUREN DABI'A 24
■ FASALI NA 3
■ FASALI NA 4 73
■ FASALI NA 5 131
■ FASALI NA 6 176
HAQQOQIN DA MA'AURATA SU KAYI TARAYYA CIKI 177
1 – HAQURI 178
2 – KAMEWA DAGA ZALUNCI DA CUATARWA 179
HAQQOQIN MATA 180
CIYARWA DA YALWATAWA 185
TAUSAYAWA DA KAMEWA DAGA ZALUNCI 187
KAMEWA DAGA BARIN DUKA MAI CUTARWA 187
UMARNI DA KYAKKYAWA DA HANI DA MUMMUNA 193
GARKUWA 196
8 – KYAUTATAWA : 196
9 - KYAWUNTA ZAMANTAKEWA 197
3 – TAUSAYAWA MIJI : 208
4 – HIMMATUWA DA KULA DA CIKIN GIDA DA KAYYAKINSA : 209
5 - HIMMATUWA CIKIN SAUKE HAQQOQI 209
6 – JIMA'I 210
7 - ADO 213
8 – KAMEWA CIKIN MAGANA : 219
SHUGABANTAR IYALI 225
DALILAI DA SUKE SANYA DAWWAMAR AURE 227
1 – SON JUNA 228
2 – YAWAITA AIKATA ALHERI: 228
4 – SANYA FARIN CIKI: 229
5 – BIYAYYA DA NEMAN YARDAR MIJI: 230
6 – KIYAYE MUTUNCI DA DUKIYA : 230
7 – TAIMAKO DA TALLAFAWA 230
8 – TARBAR MIJI DA KYAWUNTA BANKWANA DA SALLAMA : 231
9 – KALAMIN AQIDOJI MAI KYAWU DA QARFAFAFFEN FURUCI. 232
10 – KARBAR UZURI DA YIWA JUNA UZURI : 232
11 – BINSU SANNU SANNU CIKIN KOWANNE HALI : 233
12 – KYAWUNTA LAFAZI CIKN KOWANNE YANAYI : 233
13 – RASHIN SAURARON KYAUTATA AIKI DARI BISA DARI 233
14 – RASHIN IKON DAUKAR NAUYI A RAYUWANCE : 234
15 – RASHIN GORI KAN MIJI : 234
16 – RASHIN QAURACEWA AL'AMARIN SHIMFIDA: 235
17 - YIN SHAWARA DA MATA BANDA BIYE MUSU: 235
18 – TAKA TSAN TSAN DA KUMA FARKAWA : 238
19 – HANKALTA 239
20 - MIJI SHI NE MUTUNCIN MATARSA 240
21 – KISHI 240
22 – TAIMAKEKENIYYA 242
23 – DADADAWA IYALI 243
27 – WATSI DA BOAKANCI DA TSAFE TSAFE : 244
28 - HIDIMA MADAWWAMIYA 245
29 – GODIYA 246
29 – QAUNAR JUNA 247
TSINTUWA GUDA BIYU GIDAN ALI DA FATIMA (AS) 248
■ FASALI NA 8 252

9- GARKUWA : 71

9- GARKUWA :

قال (صلى الله عليه وآله)  : يا معشر الشباب من استطاع منكم الباه فليتزوّج ، فإنّه أغضّ للبصر وأحصن للفرج ، ومن لم يستطع فليدمن من الصوم ، فإنّ له وجاء

24-Manzon Allah (saw)  ya ce: ya ku gayyar samari duk wanda ya samu iko cikinku ya yi aure, haqiqa aure shi ya fi komai kau da kai ga idaniya da garkuwa ga farji, wanda bai da iko to ya lazimci azumi, haqiqa azumi garkuwa ce gareshi.

daga cikin manufofin aure tsarkaka akwai kau da ido gabarin kallon matar da kallonta ya haramata, kamar kallon baquwar mace kallon ribata da sha'awa, da kuma katange farji daga hatsarin zina da sabo  mai halakarwa, wanda bai samu damar auren ba to daga cikin abin da zai karya da rage masa sha'awa shi ne yawan azumi haqiqa azumi garkuwa ne ga tuzuru, da ma'anar cewa azumi yana dandake kwaikwayen da ke cikin maraina da suke haifar da sha'awa .

Idan muka dubi rayuwar imamai (as) zamu ga suna muhimmantar da mas'alar aure, suna yawan tambayar mazaje game da haka, suna bayyana ra'ayinsu cikinsa,wannan ma'anar tana dabbakuwa kan mata, saboda tarayyarsu da kasantuwar ma'auni guda suke da maza a fagen.

عن أبي الحسن (عليه السلام) ، قال  : جاء رجل إلى أبي جعفر (عليه السلام) فقال (عليه السلام)له  : هل لك زوجة  ؟ قال  : لا . فقال أبو جعفر (عليه السلام)  : لا اُحبّ أنّ لي الدنيا وما فيها ، وأن أبيت ليلة وليس لي زوجة ، ثمّ قال  : إنّ ركعتين يصلّيهما متزوّج أفضل من رجل عزب يقوم ليله ويصوم نهار-

25  daga baban hassan(as)yace : wani mutum ya je wajen baban jafar(as) sai baban jafar ya ce : shin kana da mata? Sai mutumin y ace a' a. sai baban jafar y ace: ban qaunar ace na mallaki duniya da dukkanin abinda ke cikinta in kwana dare guda alhalin banda mata, raka'a biyu da mai mata ke sallata ta fi falala daga tasayuwar daren tuzuru da azuminsa da rana.

قال النبيّ (صلى الله عليه وآله)  : من سرّه أن يلقى الله طاهراً مطهّراً فليلقه بزوجة صالحة

26-Manzon Allah(saw) ya ce : duk wanda ya ke farin cikin haduwa da ubangijinsa yana tsarkakakke mai tsarkakewa to ya yi qoqarin haduwa da shi halin yana tare da mace tagari.

me yafi kyawu daga gidan muslunci wanda aka assasashi tun ranar farko kan taqawa da son Allah mai girma da daukaka da dalilai tsarkaka na imani, mumini shi ne mai tsarkake niyya cikin ayyukansa hatta aure, kadai dai yana ayyukansa ne saboda Allah, misalin wannan zai zama mai daraja da girmamawa wajen Allah, asaka mashi da lada gwaggwaba kan ayyukansa, ya kasance tsarkakakke duniya da lahira,