فهرست کتاب‌‌ لیست کتاب‌ها
■ KALMAR TARBIYYA CIKIN HARSHEN LARABCI DA YANDA AKA YI 4
■ FASALI NA ( 2 ) 24
■ AUREN DABI'A 24
■ FASALI NA 3
■ FASALI NA 4 73
■ FASALI NA 5 131
■ FASALI NA 6 176
HAQQOQIN DA MA'AURATA SU KAYI TARAYYA CIKI 177
1 – HAQURI 178
2 – KAMEWA DAGA ZALUNCI DA CUATARWA 179
HAQQOQIN MATA 180
CIYARWA DA YALWATAWA 185
TAUSAYAWA DA KAMEWA DAGA ZALUNCI 187
KAMEWA DAGA BARIN DUKA MAI CUTARWA 187
UMARNI DA KYAKKYAWA DA HANI DA MUMMUNA 193
GARKUWA 196
8 – KYAUTATAWA : 196
9 - KYAWUNTA ZAMANTAKEWA 197
3 – TAUSAYAWA MIJI : 208
4 – HIMMATUWA DA KULA DA CIKIN GIDA DA KAYYAKINSA : 209
5 - HIMMATUWA CIKIN SAUKE HAQQOQI 209
6 – JIMA'I 210
7 - ADO 213
8 – KAMEWA CIKIN MAGANA : 219
SHUGABANTAR IYALI 225
DALILAI DA SUKE SANYA DAWWAMAR AURE 227
1 – SON JUNA 228
2 – YAWAITA AIKATA ALHERI: 228
4 – SANYA FARIN CIKI: 229
5 – BIYAYYA DA NEMAN YARDAR MIJI: 230
6 – KIYAYE MUTUNCI DA DUKIYA : 230
7 – TAIMAKO DA TALLAFAWA 230
8 – TARBAR MIJI DA KYAWUNTA BANKWANA DA SALLAMA : 231
9 – KALAMIN AQIDOJI MAI KYAWU DA QARFAFAFFEN FURUCI. 232
10 – KARBAR UZURI DA YIWA JUNA UZURI : 232
11 – BINSU SANNU SANNU CIKIN KOWANNE HALI : 233
12 – KYAWUNTA LAFAZI CIKN KOWANNE YANAYI : 233
13 – RASHIN SAURARON KYAUTATA AIKI DARI BISA DARI 233
14 – RASHIN IKON DAUKAR NAUYI A RAYUWANCE : 234
15 – RASHIN GORI KAN MIJI : 234
16 – RASHIN QAURACEWA AL'AMARIN SHIMFIDA: 235
17 - YIN SHAWARA DA MATA BANDA BIYE MUSU: 235
18 – TAKA TSAN TSAN DA KUMA FARKAWA : 238
19 – HANKALTA 239
20 - MIJI SHI NE MUTUNCIN MATARSA 240
21 – KISHI 240
22 – TAIMAKEKENIYYA 242
23 – DADADAWA IYALI 243
27 – WATSI DA BOAKANCI DA TSAFE TSAFE : 244
28 - HIDIMA MADAWWAMIYA 245
29 – GODIYA 246
29 – QAUNAR JUNA 247
TSINTUWA GUDA BIYU GIDAN ALI DA FATIMA (AS) 248
■ FASALI NA 8 252

DALILAN TARBIYA NA GADO DA DABI'A CIKIN AURE 73

DALILAN TARBIYA NA GADO DA DABI'A CIKIN AURE

Allah ya halicci matum cikin halin kasancewarsa mai zabi, ya kuma shiryar da shi hanya, kodai ya yi godiya ko kuma ya kafirce,  bai da wani abu sabanin abin da ya yi fafutika kai, shi ne wanda ke  zabarwa kansa hanyar alheri ko ta sharri, wannan ma'anar na gudana cikin dukkanin bangarorin rayuwarsa da inda ta fuskanta, sai dai cewa da ludufi daga Allah matsarkaki ta hanyar manzanni da annabawa da littafan da suka zo daga sama an sanar da shi abin da bai sani ba, an kuma nuna masa sahihiyar hanya miqaqqa, an sanya masa alamomi da isharori  cikin hanyarsa ta rayuwa, don gudun kada ya bace ya rude cikin duhun kwazazzabon  jahilci.

daga cikin abin da ubangiji ya sanar da shi cikin rayuwar aure da samar da iyali shi ne tunda farko  ya nuna masa cewa akwai wasu dalilai da illoli na ciki da na waje da suke tasiri cikin tarbiyyar iyali da kasantuwarsu ta fuskanin hukuntawa da sababi wadanda dukkaninsu tawayayyu ne  basu zama cikakku ba cikin tasirin, ana kiransu da dokokin al'ada da gado,  kadai an kirasu  hakan don sauqaqawa, domin dokokin sababi da musabbabi da lissafi dokoki ne na haqiqa basu canjawa, amma dokokin jeka nayika kamar dokokin mutum da ya qirqira dokokine da suke karbar canaji, abin da ake kira da dokokin gado, an kira su da hakan ne saboda rashin wadancananka, kamar yadda yake yiwuwa  mukasa dokoki ya zuwa na dabi'a wanda ke karbar canji da na shari'a wanda basa canjawa,

ma'abota imani da jabaru(tilastawa) bisa rayawarsu dake kan bata sun tafi kan dokar gado, sai dai cewa wannan ra'ayi nasu abin wurgine kamar yadda hakan ya tabbata a mahallinsa.[1] haqiqa siffofin gangar jiki da ruhi na iyaye na da tasiri cikin siffar danda aka haifa. 

Haqiqa bayyanannen abune cewa daga cikin tsarin halitta shi ne tasirantuwa da wata siffa daga siffofin mahaifa ya zuwa ga dan da suka haifa bisa tsarin kwayar halitta,

Kamanni da halayyar mahaifa na da tasiri cikin kamannin `ya`ya maza da mata.

Misali uwa ma'abociyar hassada takan gadarda wannan halayya ya zuwa ga `yarta, haka uba marowaci matsolaci yana gadarda wannan dabi'a ya zuwa dansa, haka al'amarin ya ke cikin kyawawan dabi'u kamar jarumataka, karamci, tausayi, qauna, haiqiqa wadannansiffofiyawanci ana gadonsu daga iyaye, kamar yadda ubangiji ke cewa:

 وَالْبَلَدُ الطَّيِّبُ يَخْرُجُ نَبَاتُهُ بِإِذْنِ رَبِّهِ وَالَّذِي خَبُثَ لَا يَخْرُجُ إِلَّا نَكِدً[2]ا

 gari mai kyawu yana fitar da tsirransa da izinin Allah amma wanda ya munana baya fitar da koami face wahala.

Saboda haka ka lura da inda zaka sanya digon maniyyinka domin haqiqa jijiya ta na naso, ta yiwu jijiya anan kamar ishara ne ya zuwa kwayar halitta, halayya da siffar mahaifa haka suke sunada tasiri cikin tarbiyyar yara da halayyarsu, babu wanda ke inkarin haka kamar yadda riwayoyi masu tarin yawa suka nuni kan haka, haqiqa ubangiji ya sanya iyakoki ga aure ga duka bangare biyun bangaren miji da bangaren mata, saboda dalilai na tasirin gangar jiki da  ruhi  cikin iyaye kan `ya`ya, sai dai duk da haka bai kasance tasiri dari bisa dari ba bai kuma kasance cikakken dalili wanda bai yiwuwa a ratse masa ba, sauda yawa munga iyaye munana sun  haifi `ya`ya nagari, hakama mun sami iyaye nagari sun haifi `ya`ya marasa tarbiyya, sai kaga wasu lokutan kyakkyawa ya fito daga mummuna ko mummuna ya fito daga kyakkyawa, ko kuma rayayye ya fito daga matacce, matacce ya fito daga rayayye, da wannan tasirantuwar dari bisa dari ne da bazai taba yiwuwa a tsallake a ratse masa ba,  da tarbiyya da koyarwa sun wayi gari matsayin wargi da wasa.

bari madai sau da yawa mun sami cewa daga ladubba abin da ya iya canja al'umma cikin wani zamani, kamar yadda aka sanya dokokin al'ummu, haka shi ne  mafi bayyanar dalili kan cewa gado bai tilasta mutum kan ayyukansa na'am yana da tasiri a jumalace ta wani sashen  saboda haka ne ma muslunci ya himmatu da mas'alar gado da  irin tasiri da inda aka taso yake da shi, haka tasirin halittarshi  daga mafi muhimmancinsu[1] Masa'alar jabar da iktiyar na da ga cikin masa'alolin ilimin kalam da falsafa masu wahalar gaske, sunada tsohon tarihi. Maganar gaskiaya shi ne abinda ya zo daga daga imamai(as)cikin hadisin iama sadiq (as): babu jabar babu tafwid sai dai cewa al'amari ne da ke tsakaknin al'amura biyu.

Sai dai cewa su asha'ira sun tafi kan jabar(tilastawa) su kuma mu'utazilawa sun tafi kan tafwidi(fawwalawa) haka cikin masana falsafa akwai wadanada suka tafi kan ra'ayin jabar wanda ake kiran ra'yin nasu da jabarul falsafi. Haka madiyun na zamani suna wannan ra'ayi wanda ake kiransa da jabarul madi wanda ke dora ayyukan mutum kan illoli na zahiri na mada da ta ke kasancewa daga kankin kansa  da ruhinsa, iata ce mai gina haqiqanin mutum ta kasantar da shaksiyyarsa ta  tura shi  zuwa ga aiki da ya dace ga wannan shaksiyya ta sa, ita kowacce kwarya na yayyafin abinda ke cikinta ne , mutum duk da kasantuwarsa `yan tacce a zahiri, sai dai cewa iadan akai duba ya zuwa zawiyyarsa uku ta mutum  zamu mu san cewa babu tsira face miqa wuya ya zuwa abin da ransa da ruhinsa ke karta gareshi sabubba uku da ke kasantar da mutumtakarsa a tunanance da suluki da aiki sune:

1 – gado

2 – wayewa

3 – muhalli

Haqiqa cikin kashin farko wato gado `ya`ya na gadon mahaifansu  maza da cikin madaukakan dabi'u ko qasqantattun halaye munana.

Haqiqa halaye na tasowa ta hanyar gado ta hanyar dabbobi masu fitar da maniyyi cikin uba cikin uwa kuma ta hanya kwai ya zuwa ga dansu da suka haifa. Da uwa da ubane mutumtakar da ke kasantuwa da sulukinsa.

Ai na biyu wato saqafa da ta'alim lalle suna da tasiri mai girma cikin mutumtakar mutum haqiqa  shi dasu ne yak e dagawa zuwa tauhidi ko karkacewa da vata, da motsi da jumudi, kwadayi da qana'a,da dai makamantan haka daga ruhoiyat da ke hukunci na musammamn da su mutum ke karkata zuwa suluki ayyananne.

Amma kasha na uku wato muhalli: lalle mutum haifaffen muhallinsa ne cikin sulukinsa da halayyarsa saboda haka ne ma muke ganin savani suluki cikin al'ummu gwargwadon savanin muhallin da suke rayuwa.

Kan wadannan sabubba ne mutum ke harrakawa kuma kowanne irin aiki ke kwarara daga gareshi, kai hatta iradar mutum wadda ake qirga ta alamin zavinsa  iota ta samu sakamakon wancan muhalli da ya taso ciki, yayinda  wadannan sabubba suka kasance sun fita daga zavinsa to haka ma abin da zai tuke garesu.

Amsa ga wadannan abubuwa a bayyane ta ke, babu shakka cikin tasirin wadannan sabubba cikin kasantuwa mutumtaka sai dai ba ta yadda za su raba mutum da zavi ba, idan bah aka ba falsafar aiko annabawa za ta rushe, haka ma dukkanin fafutikar masu tarbiyya da ayyuka bayi salihai masu kwao gyara za su ta fi a iska a wofi. Su dai wadannan sabubba bas u fita da ga kasantuwarsu muqaddima da shimfida da ke bukatar abubuwa bisa dabi'arta sai dai cewa bayan akwai `yancin mutum da zavinsa, kamar yadda laruira ke shaida hakan, mutum nawa yay i galaba kan dabi'un da ya ta so cikin muhallin da aka haife shi da kafiri amma kuma ya canja ya zama musulmi, da ba shi'a ba ne yay i bincike ya koma shi'a, haqiqa ma'abota wancan ra'ayi sun tafka kuskure cikin cudanya abinda ake kira da ijab da ikhtida'I da cikakkiya illa wadda ma'alul dinta ba zai tava yiwuwa ya savawa illarsa ba , dakuma illa tawayayyiya wadda ita na hukunci ne idan abin da zai hukunci ya samu, sai idan wani abu ya shiga tsakani ya kawo cikas.

Su `ya`ya ye nay o gadon siffofi na ruhi da halaye a jumlace daga iyayensu.

 

[2] A'araf:85