فهرست کتاب‌‌ لیست کتاب‌ها
■ KALMAR TARBIYYA CIKIN HARSHEN LARABCI DA YANDA AKA YI 4
■ FASALI NA ( 2 ) 24
■ AUREN DABI'A 24
■ FASALI NA 3
■ FASALI NA 4 73
■ FASALI NA 5 131
■ FASALI NA 6 176
HAQQOQIN DA MA'AURATA SU KAYI TARAYYA CIKI 177
1 – HAQURI 178
2 – KAMEWA DAGA ZALUNCI DA CUATARWA 179
HAQQOQIN MATA 180
CIYARWA DA YALWATAWA 185
TAUSAYAWA DA KAMEWA DAGA ZALUNCI 187
KAMEWA DAGA BARIN DUKA MAI CUTARWA 187
UMARNI DA KYAKKYAWA DA HANI DA MUMMUNA 193
GARKUWA 196
8 – KYAUTATAWA : 196
9 - KYAWUNTA ZAMANTAKEWA 197
3 – TAUSAYAWA MIJI : 208
4 – HIMMATUWA DA KULA DA CIKIN GIDA DA KAYYAKINSA : 209
5 - HIMMATUWA CIKIN SAUKE HAQQOQI 209
6 – JIMA'I 210
7 - ADO 213
8 – KAMEWA CIKIN MAGANA : 219
SHUGABANTAR IYALI 225
DALILAI DA SUKE SANYA DAWWAMAR AURE 227
1 – SON JUNA 228
2 – YAWAITA AIKATA ALHERI: 228
4 – SANYA FARIN CIKI: 229
5 – BIYAYYA DA NEMAN YARDAR MIJI: 230
6 – KIYAYE MUTUNCI DA DUKIYA : 230
7 – TAIMAKO DA TALLAFAWA 230
8 – TARBAR MIJI DA KYAWUNTA BANKWANA DA SALLAMA : 231
9 – KALAMIN AQIDOJI MAI KYAWU DA QARFAFAFFEN FURUCI. 232
10 – KARBAR UZURI DA YIWA JUNA UZURI : 232
11 – BINSU SANNU SANNU CIKIN KOWANNE HALI : 233
12 – KYAWUNTA LAFAZI CIKN KOWANNE YANAYI : 233
13 – RASHIN SAURARON KYAUTATA AIKI DARI BISA DARI 233
14 – RASHIN IKON DAUKAR NAUYI A RAYUWANCE : 234
15 – RASHIN GORI KAN MIJI : 234
16 – RASHIN QAURACEWA AL'AMARIN SHIMFIDA: 235
17 - YIN SHAWARA DA MATA BANDA BIYE MUSU: 235
18 – TAKA TSAN TSAN DA KUMA FARKAWA : 238
19 – HANKALTA 239
20 - MIJI SHI NE MUTUNCIN MATARSA 240
21 – KISHI 240
22 – TAIMAKEKENIYYA 242
23 – DADADAWA IYALI 243
27 – WATSI DA BOAKANCI DA TSAFE TSAFE : 244
28 - HIDIMA MADAWWAMIYA 245
29 – GODIYA 246
29 – QAUNAR JUNA 247
TSINTUWA GUDA BIYU GIDAN ALI DA FATIMA (AS) 248
■ FASALI NA 8 252

2- WATA CIKIN BURUJIN AQRABU : 76

2- WATA CIKIN BURUJIN AQRABU :

daga cikin abubuwan da ke da tasiri cikin tsiyatar aure da azurtarsa  shi ne kasantuwar mutum ya yi aure dai-dai laokacin da wata ke kan burujin aqrabu, wannan na nuni da cewa halittun sammai na da nasu tasirin cikin jumlar abubuwan da ke afkuwa a bisa qasa, kamar yanda wata ke da tasiri cikin tumbatsar teku da qafewarta, haka taurari bakwai nada nasu hukunci kebantacce cikin ilimin taurari da hai'a  cikinsu akwai tsiyata da arziqi,  kamar yanda muma munada da'irori manya guda goma, qananan da'irori wanda basu iyakantuwa basu qidaituwa, daga manyan da'ira yankin burujin sama wadanda keda buruji 12, suna farawa da burujin hamli  su tiqe da burujin hutu, daga cikin burujai akwai burujin qamaru shi jumlane daga taurarin da ke yankin arewa da sama wajen magabata an siffanta shi da aqrabu  wata cikin tafiyarsa ta wata-wata cikin kwanaki uku yakan kasancewa  cikin wannan buruji, makaruhi ne yin aure cikin wannan lokaci kamar yadda ya zo cikin hadisai masu tarin yawa.

عن الصادق (ع) من تزوج والقمر في العقرب لم ير الحسنى.

1-An karbo daga imam sadiq (as) ya ce: duk wanda yayi aure alhalin wata yana burujin aqrabu bai zai ga alheri ba.

 2-an riwaito karhancin yin aure cikin darare ukun qarshen wata saboda tsananin buyansa ko ganinsa ba a iya yi.

عن الإمام الصادق (عليه السلام)  : من تزوّج والقمر في العقرب لم يرَ خيراً أبداً

3- An karbo daga imam sadiq (as) ya ce : dukkanin wanda yayi aure alhalin wata yana cikin burujin aqrab ba zai ga alheri ba har abada.

Babu laifi muyi qarin bayani cikin wannan maudu'i.