TARBIYYAR HALITTA DA MUSLUNCI 9
WANENE MAI TARBIYA ? 10
KASHE KASHEN TARBIYA 12
ABUBUWAN DA SUKA RATAYU DA ITA 13
IYALI CIKIN MA'ANAR LUGGA DA ISDILAHI 13
IYALI A LUGGANCE : 14
■ AUREN DABI'A 24
KASHE KASHEN AURE: 41
ADADIN MAZAJE: 44
HANYOYIN TABBATAR AURE : 46
5 - KASANTUWAR MIJI DAYA RAK MACE DAYA RAK: 46
SAMUN CIKAR KAMALA CIKIN AURE 54
DALILAN YIN AURE CIKIN SUNNA MAI DARAJA 60
1 TAUHIDI: 61
2-TAQAWA : 62
3- MAFI SOYUWAR GINI WAJEN ALLAH: 62
4- SUNNAR ANNABI: 63
5 - QARUWAR ARZIQI : 65
6 – QARUWAR IMANI : 69
7- ALFAHARI : 70
8- QARUWAR IBADA : 71
9- GARKUWA : 71
10 – SADAR DA ZUMUNCI 72
11- ADDINI : 72
12- DEBE HASO: 73
1- ASALI 76
2- WATA CIKIN BURUJIN AQRABU : 76
HUKUNCIN ILIMIN BUGA QASA CIKIN SHARI'A MAI TSARKI 77
MAHALLIN DA MUTUM KE RAYUWA CIKI 84
SON MATA 84
MATA MASU MUTUNCI DA DARAJA 88
1 MATAYE MAFI KYAWUN FUSKOKI MAFI QARANCI SADAKI 90
2- QARANCIN BUQATU DA SAUQAQE HAIHUWA: 91
3- KASHE KASHEN MATA CIKIN KYAWAWAN HALINSU 91
TSARA CIKIN AURE 116
FAFUTIKA CIKIN AURE 133
AUREN WURI 134
HUDUBA 136
SADAKI 142
HADARIN TSADAR SADAKI : 148
AUREN SHARI'A 150
DAREN ANGONCI 150
AYYUKAN DAREN ANGONCI : 154
ZAMA TARE DA AMARYA HAR TSAWON KWANAKI BAKWAI : 155
WALIMA 155
RARRABA ALEWA KO DABINO 157
LADUBBAN SADUWA DA IYALI 158
1- MAFI DADIN DADADA 160
2- WASA DA MATA GABANIN JIMA'I : 160
4 – HUKUNCIN AZALO : 174
5 – ADDU'A YAYIN KUSANTAR IYALI 175
35 – daga abu rabi'i ashshami, ya ce 175
1 – HAQURI 178
2 – KAMEWA DAGA ZALUNCI DA CUATARWA 179
HAQQOQIN MATA 180
CIYARWA DA YALWATAWA 185
TAUSAYAWA DA KAMEWA DAGA ZALUNCI 187
KAMEWA DAGA BARIN DUKA MAI CUTARWA 187
UMARNI DA KYAKKYAWA DA HANI DA MUMMUNA 193
GARKUWA 196
8 – KYAUTATAWA : 196
9 - KYAWUNTA ZAMANTAKEWA 197
3 – TAUSAYAWA MIJI : 208
4 – HIMMATUWA DA KULA DA CIKIN GIDA DA KAYYAKINSA : 209
5 - HIMMATUWA CIKIN SAUKE HAQQOQI 209
6 – JIMA'I 210
7 - ADO 213
8 – KAMEWA CIKIN MAGANA : 219
SHUGABANTAR IYALI 225
DALILAI DA SUKE SANYA DAWWAMAR AURE 227
1 – SON JUNA 228
2 – YAWAITA AIKATA ALHERI: 228
4 – SANYA FARIN CIKI: 229
5 – BIYAYYA DA NEMAN YARDAR MIJI: 230
6 – KIYAYE MUTUNCI DA DUKIYA : 230
7 – TAIMAKO DA TALLAFAWA 230
8 – TARBAR MIJI DA KYAWUNTA BANKWANA DA SALLAMA : 231
9 – KALAMIN AQIDOJI MAI KYAWU DA QARFAFAFFEN FURUCI. 232
10 – KARBAR UZURI DA YIWA JUNA UZURI : 232
11 – BINSU SANNU SANNU CIKIN KOWANNE HALI : 233
12 – KYAWUNTA LAFAZI CIKN KOWANNE YANAYI : 233
13 – RASHIN SAURARON KYAUTATA AIKI DARI BISA DARI 233
14 – RASHIN IKON DAUKAR NAUYI A RAYUWANCE : 234
15 – RASHIN GORI KAN MIJI : 234
16 – RASHIN QAURACEWA AL'AMARIN SHIMFIDA: 235
17 - YIN SHAWARA DA MATA BANDA BIYE MUSU: 235
18 – TAKA TSAN TSAN DA KUMA FARKAWA : 238
19 – HANKALTA 239
20 - MIJI SHI NE MUTUNCIN MATARSA 240
21 – KISHI 240
22 – TAIMAKEKENIYYA 242
23 – DADADAWA IYALI 243
27 – WATSI DA BOAKANCI DA TSAFE TSAFE : 244
28 - HIDIMA MADAWWAMIYA 245
29 – GODIYA 246
29 – QAUNAR JUNA 247
TSINTUWA GUDA BIYU GIDAN ALI DA FATIMA (AS) 248
SON `YA`YA DA QANAN YARA 252
MUQAMI NA 2 254
MUQAMI NA 3 260
NEMAN HAIHUWAR DA NAMIJI 260
MUQAMI NA 4 266
RAINON CIKI DA LADUBBNSA 266
TASIRIN ABINCI KAN MATA MASU CIKI DA YARA DA JIMA'I 267
MUQAMI NA 6 269
HAIHUWA 269
MUQAMI NA 7 270
SHAYARWA 270
MUQAMI NA 8 273
RAINON YARO 273
MUQAMI NA TARA 279
TAYA MURNA DA SAMUN DA 279
MUQAMI NA 10 281
AQIQA 281
WASU AYYUKAN MUSTAHABBAN NA DABAN 286
MUQAMI NA 11 287
KACIYA 287
MUQAMI NA 12 290
KAMANCECENIYAR DA DA MAHAIFINSA 290
MUQAMI NA 13 292
MATAKAN TARBIYYYAR YARA 292
MUQAMI NA 14 298
ADALCI TSAKANIN `YA`YA 298
MUQAMI NA 15 300
SUMBATA NA DAGA ALAMOMIN SO 300
FASALI NA 9 302
FASALI NA 10 317
BATUTUWA DABAN DABAN 317
FASALI NA 11 325
SAKI 325
GABATARWA 327
HAQIQANIN LADABI KAN HASKEN MAZHABAR IYALN GIDAN ANNABI ( AS ) 329
WAYE ME LADABTARWA ? 336
MEYE LADABI ? 338
ASALAN LADUBBA 341
MASADIR CIKIN LADUBBA 347
MASADIR DIN LARABCI 349
TABLE OF CONTENTS 355
- CIKIN HALLARAR ALHERI
- HUJJOJIN HALASCIN YIN TAKIYYA A MUSLUNCI DAGA MAHANGAR MANYAN MALAMAI GUDA BIYU
- FARKAR DA MAI BACCI CIKIN TABBATUWAR GANIN IMAM KA'IM A.S
- ALAMOMIN ANNABI CIIKIN KUR'ANI MAI GIRMA
- HAKURI DA FUSHI
- Bada'u tsakanin hakika da kagen makiya
- FALALAR DAREN LAILATUL KADRI
- WAHABIYANCI A TSAKANIN GUDUMA DA
- HASKEN SASANNI CIKIN SANIN ARZIKI
- AQIDUN MUMINAI
- FATIMA TAGAR HASKAYE
- SIRRIKAN AIKIN HAJJI DA ZIYARA
- TARBIYYAR IYALI A MAHANGAR ALKUR'ANI DA AHLULBAITI
HUKUNCIN ILIMIN BUGA QASA CIKIN SHARI'A MAI TSARKI
Babban malaminmu shehul Ansari ya bijiro da bahasi kan hukuncin ilimin bugun qasa cikin littafinsa mai suna (almakasibul muharrama ) ya yi la'akari da karbar lada kan ilimin da kasantuwar haramcin yin kasuwanci da ilimin.
bugun qasa a kankin kansa aiki ne haramtacce, ya ce sanin bugun qasa haramun ne, kamar yanda al'amarin ya kasance cikin littafin jami'ul maqasida na muhaqqiq karaki shi ilimin sanin taurari shi ne: bada labarin hukunce hukuncen bugun qasa tareda la'akari da jujjuyawar falaki da sadarwar taurari.
bai buya cewa abin da ake nufi da bugun qasa cikin abin da babban malaminmu ya kawo shi ne dai abin da `yan tsubbu keyi tareda da'awar sanin nasibin mutane na rayuwa da makomarsu bisa jujjuyawar tauraro da tafiyarsa bisa la'akari da motsin falaki, shi ne tafiyar taurari bakwai daga wata da rana da mushtari da zuhuli da adarid da zuhra da marriku, bisa yanda masana magabata suka tafi kai, ta yanda suka ce: cibiyar duniya itace qasa, haqiqa halittu da taurari dukkaninsu suna daura da qasa da jujjuyawa geffenta, amma wajen masanan wannan zamani tare da abin da aka kai ga ganowa duniyar guda tara ce sabani abin da magabata suka tafi kai kan cewa bakwai ne, tare da qaruwar tauraron ( uranus da nabtun ) aka kuma qara gano wani abun sabo shine kasantuwar rana matsayin cibiya, cibiyar komai itace rana kuma gefenta komai ke kewayawa, wannan kekkewaya tare da la'akari da naqaltuwa yana haifar da dare da rana da fasali hudu sanyi zafi damuna da kaka, da hijira shamsiya da qamariya.
Ana kiran dukkaninsu da (maj'mu'a shamsiya ) abin da ake nufi da sadarwar tauraro shine kusantar sahsenshi ya zuwa sashe ko nesanatar junansu.
sannan kowanne kusanta da nesanta nada
hukunci kebantacce wajen masana taurari
Sannan babban shehi ya qara bijira zuwa hukuncin bugun qasa da taurari tare da bayani kai dalla-dalla cikin maqamai masu yawa cikin muqamin farko ya yi hukunci da rashin haramcin bada labarin yanayin falaki wanda ya ginu kan tafiyar taurari kamar kisfewar rana da wata da makamancinsu, bari ma dai ya halasta hakan tareda da yin hukunci kai tsaye ko bisa tsammani, sannan mas'alar na daga mas'alar da malamai keda sabani kanta.
muhaqqiq karaki ya tafi kan halascin hakan tare da qarfafarsa da karhancin yin tafiya da yin aure cikin burujin aqrab.
Ina cewa kadai yana halasta cikin wurare kebantattu, idan bugun qasar ya kasance ta fuskanin dalili na biyu ba kasantuwarsa cikakken sababi da illa kan afkuwa wani al'amari ba.
yawancin malamai sun tafi kan haramci wasu cikinsu sun ce gurbatarsa na daga abubuwan da ake sallamawa cikin addini,wasu kuma sun ce ba dukkaninsa ne haramun ba, kamar yadda riwayoyi suka zo da hani mai tsanani kai da yin umarni da a qona dukkanin littafan bugun qasa, sannan kuma akwai riwayoyin da suka zo da yabo kai, da kuma kasancewarsa daya daga cikin iliman annabawa farkon wanda ya fara magana kansa shine annabi idris (as)
duk da kasantuwar cutarwarsa tafi amfanarwarsa yawa.
babban shehi a muqami na biyu ya na cewa: bada labari kan abubuwan da zasu faru gobe ta hanyar bugun qasa da yin hukunci da shi tare da jingina ya zuwa tasirin sadarwar taurari cikinsa kai tsaye ko kuma tare da cudanyashi , zahirin fatawa da nassosi qarfafaffu ana masa hukunci ne da haramci, haqiqa muhaqqiq karaki ya kawo riwaya mursala daga annabi (saw) ya ce:
من صدق منجما أو كاهنا فقد كفر بما أنزل على محمد (ص)
dukkanin wanda ya gasgata mai bugun qasa ko boka to haqiqa ya kafirta da abin da aka aikowa muhammadu (saw) wannan riwaya kai tsaye tana hukunci kan haramcin bugun qasa.
.نصر بن قابوس عن الصادق (ع): ان المنجم ملعون,والكاهن ملعون, والساحر ملعون.
nasru dan qabus daga imam sadiq (as) haqiqa an la'anci mai bugun qasa da boka da matsafi.
Ya zo cikin nahjul balaga : cewa yayin da imam ali (as) ya yi nufin yin tafiya cikin sashen tafiye tafiyensa na daukaka kalmar Allah, wani sashe daga sahabbabnsa wani ya ce masa: idan kayi wannan tafiya cikin wannan lokaci ina jima tsoron karka gaza samun nasarar kan muradanka saboda dogaro da hanyar ilimin taurari.
imam ya ce masa: shin kana raya cewa kai kana shiryarwa zuwa lokaci idan anyi tafiya cikinsa za'a ingijewa mutum sharrinsa, sannan kana tsoratarwa da yin tafiya kan wani lokaci wanda idan mutum ya yi tafiya cikinsa zai fuskanci matsala da cutuwa, duk wanda ya gasgata wannan raye-raye to ya qaryata alqur'ani, ya wadatu gabarin taimakon Allah cikin neman abin da yake so da ingije abin da yake gudarwa da qinsa, ya ku mutane ku sani sanin taurari ba bakin komai yake ba face wanda ake shiriya ya zuwa teku da ban qasa ta hanyarsa, haqiqa bugun qasa da taurari yana kira zuwa bokanci, mai bugun qasa misalin boka yake, boka kuma dai-dai yake da matsafi, matsafi dai-dai yake da kafiri, sannan kafiri kuma na wuta, ku tafi kan sunan Allah.[1]
amma hadisin da ya zo yana hani kan yin tafiya da aure halin burujin aqrab:
عن محمد بن حمران عن أبيه عن أبي عبد الله (ع)قال:من سافر أو تزوج والقمر في العقرب لم ير الحسنى.
ankarbo daga muhammadu dan himran daga babansa daga baban Abdullah (as) ya ce : duk wanda ya yi aure ko tafiya alhalin wata yana burujin aqrab ba zai ga alheri ba.
wannan hadisi yana ishara qarara kan tasirin taurari cikin alheri da sharri.
amma abin da ake nufi da burujin aqrab yana komawa zuwa kalmar tsofaffin masana na qasar babila daga tunaninsu cikin samaniya ga surori da shakalai ga taurari tabbatattu ya zuwa tsari guda. wadannan surori wasunsu kammalallum wasunsu tawayayyu, sannan sun kebancewa dukkanin taurarri shakali wanda adadinsu yakai ga (1025) ko (1022) idan muka kyale guda ukun wanda (badalimus) ya cire saboda tsananin qanqantarsu, shi kuma kawaja Abdurrahman sufi ya shigar dasu da rarrabasu daga wadannan taurari (917) da suka shiga cikin wannan surori, ragowar kuma (105) dake wajenta suna zaune kusa da geffanta, ana kiran kashin farko: cikin sura, kashi na biyu: wajen surori.
Kadai dai sunyi hakan ne saboda ayyana matsugunan wadancan taurari lokacin hisabi, idan suka bada labari sai suce : tauraro mai kewaya rana yana kan sura kaza da kaza ko kan jelarta ko tsakiyarta, don bayyanar da tauraro mai kewaya duniya da matsugunisa a samaniya, hakan idan ya kasance cikin sura, amma idan wajentane sai suce: tauraro kaza yana tsugune kusa da kan sura ko kusa da qafarta …..
Gaba dayan wadannan surori sun kai adadin surori (48) guda 21 suna yankin arewada buruji sannan guda 15 suna kudancin buruji ragowar 15 din kuma suna kan da'irar burujin.
abinda ya ta'allaqantu da maudu'i shi ne (wata cikin burujin aqrab ) itace surar da ke fadawa yankin buruji wadda ita ce ma'auni kekkewayar rana da wata da magudanarsu.
kewayawar rana cikin shekara guda ma'ana kawanaki (365) da rubu'i
Kewayawar wata cikin wata guda kwanaki (27 ) da awanni 7 da minti 42 sai dai kuma kasantuwar rana tana qauracewa mahallinta cikin wannan lokuta saboda cudanyarta da wata a farkonsa sai ta dan qaru kadan ya zama tilas wata ya gudana har ya samu damar haduwa da rana karo na biyu don wata ya kamalla cif cif, da hakanne watan hijira qamariyya ke kaiwa kawanaki (29) da awanni 12 da minti 44.
Sannan( mahallin buruji ) shi ne daga da'irori manya manya guda 10 shi ne da'irorin wahami wanda ya karkace daga da'irar tsakiyar rana
Sun karkasa wannan maguda zuwa kashi 12 kowanne kashi na da buruji guda, sannan suka kasa dukkanin fasalai hudu na shekara ya zuwa buruji uku.
1- burujin hamli cikinsa taurari 13 a wajensa kuma akwai 5.
2- burujin sauru cikinsa taurari 32 waje kuma 11.
3-burujin jauza'i cikinsa taurari 18 waje 8.
4- burujin saradanu cikinsa taurari9 wajensa 4.
5-buruji asadu cikinsa tauraro 27 waje 8.
6-burujin sunbula cikinsa tauraro 26 waje 6.
7- burujin mizani cikinsa taurari 8 waje 9.
8-burujin aqrab cikinsa taurari 21 waje 3.
9- burujin qausu cikinsa taurari 31.
10- burujin jadyu (dan sanuwa) cikinsa taurari 28.
11-burujin dalwu ciknsa taurari 42 waje 3.
12-burujin hutu cikinsa taurari 34 waje 4.
Wadannan sune burujai 12 da wata ke ketasu awanni 13 da miniti 3 da sakonni 54, da wannan kewayawarsa cikin buruji 12 cikin kwanaki 27 da awa 7 da minti 43, sakamakon kasantuwar kowanne burji na da daraja 30 to wata na baqunta cikin kowanne buruji qasa da kwanaki uku, ma'ana kwana biyu da rubu'i .
Masana taurari na cewa : duk wanda aka Haifa cilkin daya daga wadannan buruji 12 to zai kwaikawayi dabi'unsu, misali wanda aka Haifa cikin burujin asadu (zaki) to zai kwaikwayo dabi'unsa. ana kiran wannan da sunan masu tsinkayar abin da zai afku gobe kowanne dayansu yana da mai tsinkaya, sannan kowanne mai tsinkaya yana da fuskoki 3, ya na sanin halayyar rayuwarsa cikin kowanne, mai tsinkaya kamar yadda aka ambaceshi cikin littafin abi masha'aril falak, Allah shi ne mafi sanin dai-dai da ingancin abin da ake fadi. sannan suna da hanyar hisabin tsinkaya bisa dogaro da haruffan abjadiya cikin lissafa suna mutum da sunan mahaifiyarsa sai su karkasa shi zuwa 12 duk abin da ya ragu cikin lissafin zai kasance tsinkayarsa.
tsofaffin masana taurari sun ambaci cewa saukar wata cikin kowanne buruji yanada nasa tasirin na musammam basu gushe ba suna qudurce hakan, ana iya cewa babu inkarin hakan matuqar Allah ya sanya yayewa da alama cikin izininsa, kamar yadda babu wanda ke inkarin tasirin sauyin yanayi cikin dabbobi da tsirrai.
sannan wannan rana mai tsananin haske tanada nata tasirin mai girma cikin wannan qaramar duniyar da muke ciki daga sauyin yanayi halayya da rayuka da kasantuwa da gurbacewa da dai sauran abubuwa da baza mu iya sanin iyakarsu ba.
Kamar yadda cikin hudar wani sashe daga taurari misalin suhailu da haskenshi na da tasiri cikin nunar kayan marmari da kasantar dasu haka al'amarin yake cikin tafiyar wata, kowanne wata nada tasiri cikin dabi'a daga tumbatsa da tawaya da tasirin cikin dandanon mutum cikin al'adar mata ta wata wata wadda ke da dangantaka da hijira qamariya da dukkanin dangantuwa, saboda haka bazai yiwu ayi inkarin tasirin sauye sauye da canji cikin wannan duniyar ba, da kuma cewa akwai dangantaka tsakanin sama da qasa da dangantakar babbar duniyar taurari da qaramar duniyar tsirrai da ma'adanai da mutane da dabbobi.
Sun kawo cewa cirar wata zuwa burujin aqrab na da tasiri daga cikinsu: yawaita damuwa cikin zukatan mutane, afkuwar fitintinu da rigingimu, yawaitar sace sace, rashin daidaitar al'amura, jinkiri cikin ayyuka, yawaitar cututtuka, taurari suna da tasiri cikin alheri da sharri cikin wani bangare, da basu da tasiri da babu abin da zai kawo Magana kan zargin yin aure ko tafiya cikin burujin aqrab.