فهرست کتاب‌‌ لیست کتاب‌ها
■ KALMAR TARBIYYA CIKIN HARSHEN LARABCI DA YANDA AKA YI 4
■ FASALI NA ( 2 ) 24
■ AUREN DABI'A 24
■ FASALI NA 3
■ FASALI NA 4 73
■ FASALI NA 5 131
■ FASALI NA 6 176
HAQQOQIN DA MA'AURATA SU KAYI TARAYYA CIKI 177
1 – HAQURI 178
2 – KAMEWA DAGA ZALUNCI DA CUATARWA 179
HAQQOQIN MATA 180
CIYARWA DA YALWATAWA 185
TAUSAYAWA DA KAMEWA DAGA ZALUNCI 187
KAMEWA DAGA BARIN DUKA MAI CUTARWA 187
UMARNI DA KYAKKYAWA DA HANI DA MUMMUNA 193
GARKUWA 196
8 – KYAUTATAWA : 196
9 - KYAWUNTA ZAMANTAKEWA 197
3 – TAUSAYAWA MIJI : 208
4 – HIMMATUWA DA KULA DA CIKIN GIDA DA KAYYAKINSA : 209
5 - HIMMATUWA CIKIN SAUKE HAQQOQI 209
6 – JIMA'I 210
7 - ADO 213
8 – KAMEWA CIKIN MAGANA : 219
SHUGABANTAR IYALI 225
DALILAI DA SUKE SANYA DAWWAMAR AURE 227
1 – SON JUNA 228
2 – YAWAITA AIKATA ALHERI: 228
4 – SANYA FARIN CIKI: 229
5 – BIYAYYA DA NEMAN YARDAR MIJI: 230
6 – KIYAYE MUTUNCI DA DUKIYA : 230
7 – TAIMAKO DA TALLAFAWA 230
8 – TARBAR MIJI DA KYAWUNTA BANKWANA DA SALLAMA : 231
9 – KALAMIN AQIDOJI MAI KYAWU DA QARFAFAFFEN FURUCI. 232
10 – KARBAR UZURI DA YIWA JUNA UZURI : 232
11 – BINSU SANNU SANNU CIKIN KOWANNE HALI : 233
12 – KYAWUNTA LAFAZI CIKN KOWANNE YANAYI : 233
13 – RASHIN SAURARON KYAUTATA AIKI DARI BISA DARI 233
14 – RASHIN IKON DAUKAR NAUYI A RAYUWANCE : 234
15 – RASHIN GORI KAN MIJI : 234
16 – RASHIN QAURACEWA AL'AMARIN SHIMFIDA: 235
17 - YIN SHAWARA DA MATA BANDA BIYE MUSU: 235
18 – TAKA TSAN TSAN DA KUMA FARKAWA : 238
19 – HANKALTA 239
20 - MIJI SHI NE MUTUNCIN MATARSA 240
21 – KISHI 240
22 – TAIMAKEKENIYYA 242
23 – DADADAWA IYALI 243
27 – WATSI DA BOAKANCI DA TSAFE TSAFE : 244
28 - HIDIMA MADAWWAMIYA 245
29 – GODIYA 246
29 – QAUNAR JUNA 247
TSINTUWA GUDA BIYU GIDAN ALI DA FATIMA (AS) 248
■ FASALI NA 8 252

SON MATA 84

SON MATA                      

Soyayya na nufin karkatar badini ya zuwa ga abinda ake so, na da tasiri cikin zuciya da gabbai, sannan yakan sassabawa da sasabawar abin da ya ta'allaqa dashi, cikin soyayya akwai son mata haqiqa son mata kan zama abin yabo wani lokaci, wani laokacin kuma abina zargi, daga farko:

قال رسول الله (ص) أحب من دنياكم ثلاث :الطيب,والنساء,وقرة عيني الصلاة.

1-      manzon Allah (saw) ya ce: ina son abubuwa uku daga duniyarku: turare da mata da sanyin idaniyata sallah.

عن الإمام الصادق (عليه السلام) ، قال  : العبد كلّما ازداد في النساء حبّاً ازداد في الإيمان فضلا

2-An karbo daga imam sadiq (as) ya ce : duk sanda bawa ya qaru cikin son mata zai qaru cikin imani falala.

 عن امام الصادق(ع): من أخلاق الأنبياء(ع)حب النساء

3- Daga imam sadiq (saw) yana cewa: daga cikin dabi'un annabawa (as) son mata.

misalin wannan soyayya data kasance muqaddimar sallah, kamar yadda sanya turare shi ma ya kasance haka babu shakka wannan soyayya za ta kasance abun yabawa bari ma dai tana daga abin da ke qara imani da falala, kuma tana cikin dabi'un annabawa.

amma soyayyar mata wadda bata kasance da manufar gabatar da aiki nagari ba, lalle zata zama fitina  da kasancewa abin zargi, kamar yanda zata wayi gari tushen zunubai da jijiyoyinsu kamar yadda ya zo cikin hadisi mai daraja cewa abubuwa shida sun kasance sanadin zunubi, daga cikinsu akawi son mata.

قَالَ أَمِيرُ الْمُؤْمِنِينَ ع الْفِتَنُ ثَلَاثٌ حُبُّ النِّسَاءِ وَ هُوَ سَيْفُ الشَّيْطَانِ وَ شُرْبُ الْخَمْرِ وَ هُوَ فَخُّ الشَّيْطَانِ وَ حُبُّ الدِّينَارِ وَ الدِّرْهَمِ وَ هُوَ سَهْمُ الشَّيْطَانِ فَمَنْ أَحَبَّ النِّسَاءَ لَمْ يَنْتَفِعْ بِعَيْشِهِ وَ مَنْ أَحَبَّ الْأَشْرِبَةَ حُرِّمَتْ عَلَيْهِ الْجَنَّةُ وَ مَنْ أَحَبَّ الدِّينَارَ وَ الدِّرْهَمَ فَهُوَ عَبْدُ الدُّنْيَ[1]ا

4-Sarkin muminai aliyu (as) ya ce : fitina abubuwa uku ne : son mata wanda ya kasance takobin shaidan, na biyu shan giya barasa tarkon shaidan, na uku  son dinare da dirhami kibiyar shaidan, don wanda ke son mata bai zai amfana da rayuwarsa ba, wanda ke son kayan maye aljanna ta haramta gareshi, wanda ke son dinari da darhami ya zama bawan duniya.

Allah ya sanya misalin wannan soyayyar matan cikin zirin son shangiya, da wannan qiyastawa za a fahimci zurfin hatsarin son mata.

قال رسول الله (صلى الله عليه وآله)  : أوّل ما عصي الله تبارك وتعالى بستّة خصال  : حبّ الدنيا ، وحبّ الرئاسة ، وحبّ الطعام ، وحبّ النساء ، وحبّ النوم ، وحبّ الراحة[2]

5-Manzon Allah (saw) ya ce : da abubuwa shida aka fara sabawa Allah madaukaki sune : son duniya, son shugabanci, son abinci, son mata, son barci, son hutu.

Babu karo da juna cikin riwayoyin ko da kuwa soyayyar ta kasance cikin mahanga biyu da la'akari ta fuska biyu, kasantuwar karo da juna da kishinyata akwai sharadin cewa dole ne kafin abubuwa biyu su zamo kishiyoyi juna su kasance ta fuska guda da la'akari ta fuska guda  saboda son mata akwai mai kyawu da mara kyawu.

عَنْ أَبِي عَبْدِ اللَّهِ ع قَالَ: إِنَّ الْمَرْأَةَ خُلِقَتْ مِنَ الرَّجُلِ وَ إِنَّمَا هِمَّتُهَا فِي الرِّجَالِ فَأَحِبُّوا نِسَاءَكُمْ وَ إِنَّ الرَّجُلَ خُلِقَ من الأرض فانما همتهم في الأرض.[3]

6- an karbo daga baban Abdullah (as) ya ce: haqiqa an halicci mace daga maza kuma kadai himmarta daga maza take, ku so matayenku haqiqa an halicci mazaje daga qasa himmarsu daga qasa take.

عن أبي عبد الله(ع)قال كل من اشتد لنا حبا اشتد للنساء حبا ولحواء.[4]

7- an karbo daga baban Abdullah (as) ya ce: duk wanda ya tsananta soyayya gare mu to zai tsananta soyayya ga mata da hauwa'u

قَالَ رَسُولُ اللَّهِ ص أُعْطِينَا أَهْلَ الْبَيْتِ سَبْعَةً لَمْ يُعْطَهُنَّ أَحَدٌ كَانَ قَبْلَنَا وَ لَا يُعْطَاهُنَّ أَحَدٌ بَعْدَنَا الصَّبَاحَةَ وَ الْفَصَاحَةَ وَ السَّمَاحَةَ وَ الشَّجَاعَةَ وَ الْعِلْمَ وَ الْحِلْمَ وَ الْمَحَبَّةَ فِي النِّسَاء[5]ِ

8-Manzon Allah (saw) ya ce: mu ahlul baiti anbamu abubuwa bakwai wanda bawani da aka baiwa gabaninmu, kuma ba za'a baiwa wani ba bayanmu ba : kyawu, fasaha, kyauta, jarumtaka, ilimi, haquri, son mata.

عَنْ أَبِي عَبْدِ اللَّهِ ع قَالَ: مَا أَظُنُّ رَجُلًا يَزْدَادُ فِي هَذَا الْأَمْرِ خَيْراً إِلَّا ازْدَادَ حُبّاً لِلنِّسَاء[6]

9- Alkafi da isnadinsa daga baban Abdullah (as) ya ce : bana tsammanin wani mutum zai qaru cikin wannan al'amari da alheri face ya qaru da son mata.

Abin da ya ke nufi da wannan al'amari shi ne shi'anci da sanin imami da kuma rungumar wilayarsu.

الفقيه([151]) ، بسنده عن أبي العباس ، قال  : سمعت الصادق (عليه السلام) يقول  : العبد كلّما ازداد للنساء حبّاً ازداد في الإيمان فضلا[7]

10- Daga littafin alfaqihu da isnadinsa daga baban abbas ya ce: naji sadiq (as) yana cewa: duk sa'ilin da bawa ya qaru cikin son mata zai qaru cikin imani da falala.

المصدر نفسه ، عن معمر بن خلاّد ، قال  : سمعت عليّ بن موسى الرضا  (عليه السلام) يقول  : ثلاث من سنن المرسلين  : العطر ، وإحفاء الشعر ، وكثرة الطروقة .

11-daga mu'ammar dan kallad naji aliyu dan musa arrida (as) yana cewa : daga sunnonin manzanni : turare  taje kai,  da yawan kusantar mata.

الكافي([152]) ، بسنده عن أبي عبد الله (عليه السلام) ، قال  : قال رسول الله (صلى الله عليه وآله)  : جعل قرّة عيني في الصلاة ، ولذّتي من الدنيا النساء ، وريحانتي الحسن والحسين  (عليهما السلام[8]

12- Alkafi da isnadinsa daga baban Abdullah (as) ya ce: manzon Allah (saw) ya ce: an sanya sallah sanyin idaniyata,haka an sanya mata jin dadina daga duniya,  qamshina Hassan da husaini (as).

بسنده عن بعض أصحابنا ، قال  : سألنا أبو عبد الله (عليه السلام) : أيّ الأشياء ألذّ  ؟ قال  : فقلنا غير شيء ، فقال هو (عليه السلام)  : ألذّ الأشياء مباضعة النساء .

13-Daga ba'arin sahabbanmu yace : mun tambayi baban Abdullah (as) wadanne abubuwa ne sukafi dadada ? sai muka fadi wasu abubuwa, s shi kuma ya ce: mafi dadada cikin abubuwa shi ne kusantar mata.

بسنده عن أبي عبد الله (عليه السلام) ، قال  : ما تلذّذ الناس في الدنيا والآخرة بلذّة أكثر لهم لذّة من النساء ، وهو قول الله عزّ وجلّ  : (  زُيِّنَ لِلنَّاسِ حُبُّ الشَّهَوَاتِ مِنَ النِّسَاءِ وَالبَنِينَ  )([153]) ، إلى آخر الآية ، ثمّ قال  : وإنّ أهل الجنّة ما  يتلذّذون بشيء من الجنّة أشهى عندهم من النكاح لا طعام ولا شراب .

14-An karbo daga baban Abdullah (as) mutane basu danadani dadin wani abu duniya da lahira fiye da dadin mata ba, shi ne fadin Allah madaukaki:

an qayatawata mutane son sha'awa daga mata da `ya`ya 

A wani wajen kuma ya ce : basu jin dadin wani abu a aljanna daga abinci da abin sha mafi ban sha'awa daga kwanciya da mata .

وَ قَالَ رَسُولُ اللَّهِ ص 1 مَا رَأَيْتُ ضَعِيفَاتِ الدِّينِ نَاقِصَاتِ الْعُقُولِ أَسْلَبَ لِذِي لُبٍّ مِنْكُنَّ

Alfaqihu : manzon Allah (saw) ya ce: ban taba ganin masu raunin addini da tawayar hankali mafi zobaitar kwakwale daga gareku ba mata.

ina cewa yana bayyana daga gabadayan riwayoyin masu daraja cewa son mata shi ne son matan aure ba dukkanin mata ba  kamar yadda ya ke a bayyane, sannan tsananin kusanci da daidaita na samuwa daga soyayya, daga nan kuma sai dai-daitar gangar jiki da yawaita kwanciya da juna, haqiqa hakan na daga cikin abin da ke qara soyayya idan ya kasance kewaye da ladubba da muqaddimomi kamar yadda ya gabata cikin riwayoyi masu daraja.[1] Biharul anwar m 100 sh 225

[2] Alkhisal m 1 sh 234

[3] Biharul anwar m 100 sh 227

[4] Biharul anwar m 100 sh 227

[5] Biharu anwar m 100 sh 228

[6] Alkafi m 5 sh 321

[7] Alfakihu m 3 sh 383

[8] Alkafi m 5 sh 321