فهرست کتاب‌‌ لیست کتاب‌ها
■ KALMAR TARBIYYA CIKIN HARSHEN LARABCI DA YANDA AKA YI 4
■ FASALI NA ( 2 ) 24
■ AUREN DABI'A 24
■ FASALI NA 3
■ FASALI NA 4 73
■ FASALI NA 5 131
■ FASALI NA 6 176
HAQQOQIN DA MA'AURATA SU KAYI TARAYYA CIKI 177
1 – HAQURI 178
2 – KAMEWA DAGA ZALUNCI DA CUATARWA 179
HAQQOQIN MATA 180
CIYARWA DA YALWATAWA 185
TAUSAYAWA DA KAMEWA DAGA ZALUNCI 187
KAMEWA DAGA BARIN DUKA MAI CUTARWA 187
UMARNI DA KYAKKYAWA DA HANI DA MUMMUNA 193
GARKUWA 196
8 – KYAUTATAWA : 196
9 - KYAWUNTA ZAMANTAKEWA 197
3 – TAUSAYAWA MIJI : 208
4 – HIMMATUWA DA KULA DA CIKIN GIDA DA KAYYAKINSA : 209
5 - HIMMATUWA CIKIN SAUKE HAQQOQI 209
6 – JIMA'I 210
7 - ADO 213
8 – KAMEWA CIKIN MAGANA : 219
SHUGABANTAR IYALI 225
DALILAI DA SUKE SANYA DAWWAMAR AURE 227
1 – SON JUNA 228
2 – YAWAITA AIKATA ALHERI: 228
4 – SANYA FARIN CIKI: 229
5 – BIYAYYA DA NEMAN YARDAR MIJI: 230
6 – KIYAYE MUTUNCI DA DUKIYA : 230
7 – TAIMAKO DA TALLAFAWA 230
8 – TARBAR MIJI DA KYAWUNTA BANKWANA DA SALLAMA : 231
9 – KALAMIN AQIDOJI MAI KYAWU DA QARFAFAFFEN FURUCI. 232
10 – KARBAR UZURI DA YIWA JUNA UZURI : 232
11 – BINSU SANNU SANNU CIKIN KOWANNE HALI : 233
12 – KYAWUNTA LAFAZI CIKN KOWANNE YANAYI : 233
13 – RASHIN SAURARON KYAUTATA AIKI DARI BISA DARI 233
14 – RASHIN IKON DAUKAR NAUYI A RAYUWANCE : 234
15 – RASHIN GORI KAN MIJI : 234
16 – RASHIN QAURACEWA AL'AMARIN SHIMFIDA: 235
17 - YIN SHAWARA DA MATA BANDA BIYE MUSU: 235
18 – TAKA TSAN TSAN DA KUMA FARKAWA : 238
19 – HANKALTA 239
20 - MIJI SHI NE MUTUNCIN MATARSA 240
21 – KISHI 240
22 – TAIMAKEKENIYYA 242
23 – DADADAWA IYALI 243
27 – WATSI DA BOAKANCI DA TSAFE TSAFE : 244
28 - HIDIMA MADAWWAMIYA 245
29 – GODIYA 246
29 – QAUNAR JUNA 247
TSINTUWA GUDA BIYU GIDAN ALI DA FATIMA (AS) 248
■ FASALI NA 8 252

MATA MASU MUTUNCI DA DARAJA 88

MATA MASU MUTUNCI DA DARAJA

mutum a dabi'ance yana karkata ya zuwa kyawu da abu mai kyawu  haqiqa son kyawu da kyakkayawan abu ne wanda yake daga halittar dan adama da bai iya guje masa, shi yasa cikin komai yana koqarin ya ga ya samu mafi darajarsa da kyawu  sau da yawa ya kanyi kuskure cikin fahimta da gane abu mai kyawu, cikin qissar aure yana bincikar mafi darajar mace,  muslunci ya yi ishara da hakan bai gafala da wannan bangaren ba a cikin rayuwar mutum, sai ya yi bayanin mata masu mutunci, hakan na nufi da cewa mata su yi ado da irin wadannan darajoji  don su sami shiga cikin wadannan da aka siffantasu da mata masu daraja su kasance cikin masu albarka,

Cikin wadannan darajoji akwai wanda a zatinsu suke akwai kuma wadanda nemansu su ake da tsiwirwirarsu, dayawan  wadanda ake tsiwirwira sun canja sun koma kamar zati sun cike faraga da naqasar  da take tare da su, hakan yana ishara da cewa mata su zage dantse wajen neman falala da darajojin kyawawan dabi'u da al'amurran badini. 

Muslunci na jebantar bangaren kyakkayawar dabi'a wajen zaben miji tsoron Allah da imani sune tushen ma'auni sabanin kudi da dukiya da kyawu, wanda ya ke kallon abubuwan zahiri cikin aure daga dukiya da alfarma da kyawu kadai,to yana tafka kuskure a mahangar muslunci, saboda dukkanin wadannan abubuwa masu gushewa ne, kadai abun da ke wanzuwa shi ne kyawawan dabi'u da imani mai zurfi da tsoron Allah da kame kai da tsarki da siffofi tsarkaka wadanda suke mazharin sunayen Allah kyawawa da siffofinsa wanda suke wanzazzu da wanzuwarsa madawwami,  sune turaku tabbatu da guguwa bata iya girgizasu, basa girgiza tare da dukkanin jujjuyawar zamani, aure na daga yankin abokantaka da aminintaka, abokai kuma sashensu ga sashen maqiyane face masu tsoron Allah. abokantaka daga ta aure wadda ta ginu kan tushen taqawa tun ranar farko ita tafi cancanta da wanzuwa, sannan ta cigaba duniya da lahira, ta wayi gari mafi kyawu daga matan aljanna cikin dausayin aljanna, gangar jiki na qarewa ruhi kuwa yana wanzuwa har sai jiki ya qara dowowa gareshi ranar alqiyama don ya kammala mutum  karo na biyu. mace da namiji albarkacin abin da suke dauke da shi daga imani da aiki nagari da kyawawan dabi'u , saboda haka mata sai su dage da neman kyawawan dabi'u da darajoji.

Ba zai yiwu a wadatu da barin aure ba domin shi aure hanya ce ta sunnar rayuwar wadda ke kare wanzuwar nau'in mutum da abubuwan da ke biye  da shi na daga tsarin zamantakewa da dabi'ar halittar mutum da sha'awarsa  wadda bai iya gafala daga barinta da watsi da qosar da sha'awarsa ta jinsi wacce bazai taba iya kangeta ba domin yin hakan na iya kawo gurbata da karkacewa ya zuwa munana ayyuka da rushewar al'ummada afkawa fushin ubangiji. kamar yadda a irin wannan lokuta ake jarrabar mutum da cutukan zuciya da kwakwalwa da ganganr jiki haka dangantaka ta halaka  ta qare da dai makamancin wannan.

Saboda haka buqatuwar mutum ya zuwa ga aure buqata ce ta dabi'ar halittarsa da bai iya guje mata, ta hanyar aure ne mutum ke kammala ya hau matakai ya kai ga darajoji  ya filfila cikin sararin samaniyar karamomi ya rabauta da arziqin gida biyu.

Ku taho muje birnin falala da darajoji wadanda muslunci ya shimfida mana, maza da mata ku taho ya zuwa kyawawan dabi'u, ya zama wajibi ga `ya`ya mata su tsiwirwiri falaloli da daraja, su canja da sauya abinda ke tattare da su daga munanan dabi'u zuwa kyawawa, haqiqa mata  sun karkasu kashi kashi kamar yadda maza suka kasance, riwaya na ishara da hakan a bayyane ga kadan daga misalin mataye salihai nagargaru.