فهرست کتاب‌‌ لیست کتاب‌ها
■ KALMAR TARBIYYA CIKIN HARSHEN LARABCI DA YANDA AKA YI 4
■ FASALI NA ( 2 ) 24
■ AUREN DABI'A 24
■ FASALI NA 3
■ FASALI NA 4 73
■ FASALI NA 5 131
■ FASALI NA 6 176
HAQQOQIN DA MA'AURATA SU KAYI TARAYYA CIKI 177
1 – HAQURI 178
2 – KAMEWA DAGA ZALUNCI DA CUATARWA 179
HAQQOQIN MATA 180
CIYARWA DA YALWATAWA 185
TAUSAYAWA DA KAMEWA DAGA ZALUNCI 187
KAMEWA DAGA BARIN DUKA MAI CUTARWA 187
UMARNI DA KYAKKYAWA DA HANI DA MUMMUNA 193
GARKUWA 196
8 – KYAUTATAWA : 196
9 - KYAWUNTA ZAMANTAKEWA 197
3 – TAUSAYAWA MIJI : 208
4 – HIMMATUWA DA KULA DA CIKIN GIDA DA KAYYAKINSA : 209
5 - HIMMATUWA CIKIN SAUKE HAQQOQI 209
6 – JIMA'I 210
7 - ADO 213
8 – KAMEWA CIKIN MAGANA : 219
SHUGABANTAR IYALI 225
DALILAI DA SUKE SANYA DAWWAMAR AURE 227
1 – SON JUNA 228
2 – YAWAITA AIKATA ALHERI: 228
4 – SANYA FARIN CIKI: 229
5 – BIYAYYA DA NEMAN YARDAR MIJI: 230
6 – KIYAYE MUTUNCI DA DUKIYA : 230
7 – TAIMAKO DA TALLAFAWA 230
8 – TARBAR MIJI DA KYAWUNTA BANKWANA DA SALLAMA : 231
9 – KALAMIN AQIDOJI MAI KYAWU DA QARFAFAFFEN FURUCI. 232
10 – KARBAR UZURI DA YIWA JUNA UZURI : 232
11 – BINSU SANNU SANNU CIKIN KOWANNE HALI : 233
12 – KYAWUNTA LAFAZI CIKN KOWANNE YANAYI : 233
13 – RASHIN SAURARON KYAUTATA AIKI DARI BISA DARI 233
14 – RASHIN IKON DAUKAR NAUYI A RAYUWANCE : 234
15 – RASHIN GORI KAN MIJI : 234
16 – RASHIN QAURACEWA AL'AMARIN SHIMFIDA: 235
17 - YIN SHAWARA DA MATA BANDA BIYE MUSU: 235
18 – TAKA TSAN TSAN DA KUMA FARKAWA : 238
19 – HANKALTA 239
20 - MIJI SHI NE MUTUNCIN MATARSA 240
21 – KISHI 240
22 – TAIMAKEKENIYYA 242
23 – DADADAWA IYALI 243
27 – WATSI DA BOAKANCI DA TSAFE TSAFE : 244
28 - HIDIMA MADAWWAMIYA 245
29 – GODIYA 246
29 – QAUNAR JUNA 247
TSINTUWA GUDA BIYU GIDAN ALI DA FATIMA (AS) 248
■ FASALI NA 8 252

TSARA CIKIN AURE 116

TSARA  CIKIN  AURE

a dabi'ance namiji na bincike neman matar da za ta kasance tsara gareshi, haka al'amarin yake wajen mace, dole ne a kalli tsara wajen samar da iyali da tabbatar da al'amarin aure, sai dai cewa batun tsara ta fuskanin ma'anarta na sassabawa da sabawar wayewa da al'adu da kuma mahallin da ka taso ciki, ta yiwu wasu cikin al'ummu su kalli tsara da cancanta na tare da mai tarin dukiya, wasu kuma su kalli tsara da cancanta cikin takardar shaidar kammala karatun jami'a, wasu kuma su kalli alfarmar danginka daga muqamansu dukiya da dai sauransu.

a daidai lokacin da shi kuma muslunci ke kallonta cikin hankali da riqo da addini da kyawawan dabi'u.

قال الرضا (عليه السلام)  : نزل جبرئيل على النبيّ (صلى الله عليه وآله) ، فقال  : يا محمّد ، ربّك يقرؤك السلام ويقول  : إنّ الأبكار من النساء بمنزلة الثمر على الشجر ، فإذا أينع فلا دواء له إلاّ اجتناؤه وإلاّ أفسدته الشمس وغيّرته الريح ، وإنّ الأبكار إذا أدركن ما تدرك النساء فلا دواء لهن إلاّ البعول ، وإلاّ لم يؤمن عليهن الفتنة ، فصعد رسول  الله (صلى الله عليه وآله) المنبر فخطب الناس ثمّ أعلمهم ما أمرهم الله به ، فقالوا  : ممّن يا  رسول الله  ؟ فقال  : الأكفاء . فقالوا  : ومن الأكفاء  ؟ فقال  : المؤمنون بعضهم أكفاء بعض ، ثمّ لم ينزل حتّى زوّج ضباعة المقداد بن الأسود ، ثمّ قال  : أ يّها الناس إنّما زوّجت ابنة عمّي المقداد ليتّضع النكاح

imam rida (as) ya ce: mala'ika jibrilu ya sauka wajen annabi (as) sai ya ce: ya muhammadu ubangijinka yana gaisheka yana kuma cewa: haqiqa `yan mata daga cikin mata matsayin `ya`yan bishiya ne ga bishiya, idan suka nuna basu da wani magani da wuce ciresu daga jikin bishiyar, idan kuma aka qi yin hakan to rana za ta lalatasu iska kuma ta canja su, haqiqa yan`mata idan suka riski abin da kammalalliya mace ke riska to basu da wani magani da yawuce a sama musu miji, idan kuma ba aikata haka ba to ba za a tsira daga fitinarsu ba, sai manzon Allah (saw) ya hau mimbari ya yiwa mutane huduba da sanar da su abin da Allah ya umarce shi, sai suka ce: su wa zamu aurarwa ? sai ya ce musu: wadanda suke tsara garesu, sai suka ce su waye suke  tsara garesu ? sai ya ce : muminai sashensu tsara ga sashe, sannan bai sauko daga wannan mimbari ba har sai da ya aurawa miqdadu dan aswad dabba'atu, sannan ya ce:  kadai na aurawa miqdad `yar ammina don aure ya sauqaqa.

عن الصادق ، عن آبائه (عليهم السلام) ، قال  : قال النبيّ (صلى الله عليه وآله)  : إنّما النكاح رقّ ، فإذا أنكح أحدكم وليدة فقد أرقّها ، فلينظر أحدكم لمن يرقّ كريمته

2-ankarbo daga sadiq (as) daga babanninsa (as) ya ce: manzon Allah (saw) ya ce: aure dai bauta ne, idan dayanku ya aurar da `ya to haqiqa ya bautar da ita, sai kasan inda zaka kai `yarka bauta

Annabi (as) ya yi bayanin aure matsayin bauta, haqiqa mace ta na kasancewa baiwa fursuna ga mijinta, saboda haka dole mutum ya lura da mahallin da zai sanya `yarsa abin qaunarsa.

عن زرارة ، عن أبي جعفر (عليه السلام) ، قال  : إنّ عليّ بن الحسين (عليه السلام) رأى امرأة في بعض مشاهد مكّة فخطبها إلى نفسها وتزوّجها فكانت عنده ، وكان له صديق من الأنصار فاغتمّ لتزويجه بتلك المرأة ، فسأل عنها فاُخبر أ نّها من آل  ذي  الجدّين من بني شيبان في بيت عليّ من قومها . فأقبل على عليّ بن الحسين فقال  : جعلني الله فداك ، ما زال تزويجك هذه المرأة في نفسي وقلت  : تزوّج عليّ بن الحسين امرأة مجهولة ويقول الناس أيضاً فلم أزل أسأل عنها حتّى عرفتها ووجدتها في بيت قومها شيبانية ، فقال له عليّ بن الحسين (عليه السلام)  : قد كنت أحسبك أحسن رأياً ممّـا أرى ، إنّ الله أتى بالإسلام فرفع به الخسيسة وأتمّ به الناقصة وكرم به اللؤم ، فلا لؤم على المسلم  إنّما اللؤم لؤم الجاهلية

3-Ankarbo daga zurara daga baban jafar (as) ya ce: aliyu dan husaini ya ga wata mace cikin makka sai ya nemi aurenta ya aureta  ta kasance wajensa, ya na da wani abokin daga madina wanda bai ji dadin aurensa da matar ba,sai wannan abokin nasa ya yi tambaya game da wannan mata, aka gaya masa cewa ita daga alu zi jiddin take daga banu shaibani  cikin gidan aliyyin daga mutanenta. sai nan take ya tafi wajen aliyu dan Husain ya ce masa: raina fansarka, aurenka bai gushe ya na cikin zuciyata na kuma ce  yanzu aliyu dan husaini  ne ya auri macen da ba a santa ba mutane na surutu kan hakan ban gushe ba ina tambaya kanta har na gano cewa daga gidan shaibani ta fito, sai aliyu dan husaini(as)  ya ce: da na kasance ina zatonka mafi kyawun ra'ayi daga abin da na ke gani, Allah ya zo da muslunci ya daukaka qasqantacce da shi ya kammala tauyayyiya, ya karrama wulaqantacce, saboda haka babu wata wulaqanta kan musulmi kadi dai wulaqanta wulaqantar jahiliya.

الكافي بسنده  : عن الثمالي قال  : كنت عند أبي جعفر (عليه السلام) إذ استأذن عليه رجل فأذن له فدخل عليه ، فسلّم فرحّب به أبو جعفر (عليه السلام) وأدناه وسأله فقال الرجل  : جُعلت فداك ، إنّي خطبت إلى مولاك فلان بن أبي رافع ابنته فلانة فردّني ورغب عنّي وازدراني لدمامتي وحاجتي وغربتي ، وقد دخلني من ذلك غضاضة هجمة ، عصر لها قلبي تمنّيت عندها الموت

1-      dag alkafi da isnadinsa daga sumali ya ce: na kasance wajen baban jafar (as) sai wani mutum ya nemi izininsa sai ye masa izini, sai mutumin ya shigo ya yi sallama baban jafar (as) ya yi maraba da shi ya matso da shi kusa ya tambaye shi, sai mutumin ya ce: raina fansarka, na nemi auren `yar masoyinka wane dan baban rafi'u sai ya kore ni ya kyamaceni ya wulqantani saboda munina da talauci da baqunta, haqiqa baqin ciki ya cikan zuciya nayi burin ma ace na mutu.

2-      فقال أبو جعفر (عليه السلام)  : اذهب فأنت رسولي إليه وقل له  : يقول لك محمّد بن عليّ بن الحسين بن عليّ بن أبي طالب زوّج منجح بن رماح مولاي بنتك فلانة ولا تردّه

3-      sai baban jafar (as) ya ce: jeka wurinsa kai ne dan aike ne ya zuwa gareshi ka ce masa: na ce ya aurawa munjihu dan rimahu masoyina `yarsa kada ya koreshi.

4-      قال أبو حمزة  : فوثب الرجل فرِحاً برسالة أبي جعفر (عليه السلام) ، فلمّا أن توارى الرجل قال أبو جعفر (عليه السلام)  : « إنّ رجلا كان من أهل اليمامة يُقال له جويبر أتى رسول الله (صلى الله عليه وآله وسلم) منتجعاً للإسلام فأسلم وحسن إسلامه وكان رجلا قصيراً دميماً محتاجاً عارياً ، وكان من قباح السودان فضمّه رسول الله (صلى الله عليه وآله وسلم) لحال غربته وعريه ، وكان يجري عليه طعامه صاعاً من تمر بالصاع الأوّل ، وكساه شملتين وأمره أن يلزم المسجد ويرقد فيه بالليل ، فمكث بذلك ما شاء الله حتّى كثر الغرباء ممّن يدخل في الإسلام من أهل الحاجة بالمدينة وضاق بهم المسجد فأوحى الله تعالى إلى نبيّه أن طهِّر مسجدك وأخرج من المسجد من يرقد فيه بالليل ومذر بسدّ  أبواب كلّ من كان له في مسجدك باب إلاّ باب عليّ ومسكن فاطمة (عليهما السلام)ولا يمرنّ فيه جنب ولا يرقد فيه غريب .

5-     

 

6-                   قال  : فأمر رسول الله (صلى الله عليه وآله وسلم) عند ذلك

7-       baban hamzatu sumali ya ce: sai naga mutumin ya zubura cikin farin ciki da saqon baban jafar (as) yayinda mutum ya tafi sai imam (as) ya ce : akwai wani mutum da ya kasance daga mutanen garin yamamatu ana kiransa da juwaibar ya zo wajen manzon Allah (saw) yana baqo mai neman mafaka sai ya muslunta ya kyawunta musluncinsa sannan shi wannan mutumin ya kasance gajere mummuna talaka wanda ke halin buqatar kayan da zai sanya jikinsa, ya kasance daga munanan sudan sai manzon Allah (saw) ya rungumeshi  saboda halin da ya ke ciki na baqunta da tsiraita ya kasance ana bashi sa'i guda daga dabino, ya tufatar da shi da kayan sawa biyu kuma ya yi umarni da a barshi ya dinga kwana cikin masallaci sai ya zauna nan ila masha'Allah har baqi suka yawaita daga wadanda suke shiga muslunci daga mabuqata daga madina har masallacin ya zama ya yi musu kadan, sai ubangiji ya yi wahayi ga annabi ya umarce shi ya tsarkake masallaci da fitar da masu kwana daga cikinsa waje  da kuma toshe kowacce qofar duk wani wanda ke da qofa a masallaci  face qofar ali da gidan fatima (as) gidanta ya tabbatu a yadda yake. shiko masallaci a ka hana kowa kwanciya cikinshi.

Sai ya  ce : sai manzon Allah ya ba da umarni da.

عند ذلك بسدّ أبوابهم إلاّ باب عليّ (عليه السلام) وأقرّ مسكن فاطمة (عليها السلام) على حاله قال  : ثمّ إنّ رسول الله (صلى الله عليه وآله وسلم) أمر أن يتّخذ للمسلمين سقيفة فعملت لهم وهي الصفّة ثمّ أمر الغرباء والمساكين أن يظلّوا فيها نهارهم وليلهم ، فنزلوها واجتمعوا فيها وكان رسول الله (صلى الله عليه وآله وسلم) يتعاهدهم بالبرّ والتمر والشعير والزبيب إذا كان عنده ، وكان المسلمون يتعاهدونهم ويرقّون عليهم لرقّة رسول الله (صلى الله عليه وآله وسلم) ويصرفون صدقاتهم إليهم .

 a dan rufa musu wani waje da zasu dinga fakewa sai ko akayi hakan aka umarcin dukkanin baqi da komawa wannan sabon wajen , sannan  annabi (as) ya dinga kawo musu dabino da alkama da sha'ir da busasshen inibi wanda ya kasance tare da shi , musulmi sun kasance suna kai musu taimako suna tausaya musu ganin yadda annabi ke tsananin tausayinsu , suna kai musu sadaqarsu da suke fitarwa.

وإنّ رسول الله (صلى الله عليه وآله وسلم) نظر إلى جويبر ذات يوم رحمة منه له ورقّة عليه ، فقال له  : يا جويبر لو تزوّجت امرأة فعففت بها فرجك وأعانتك على دنياك وآخرتك ، فقال له جويبر: يا رسول الله بأبي أنت واُمّي ومن ترغب فيَّ فوَالله ما لي من حسب ولا نسب ولا مال ولا جمال فأيّة امرأة ترغب فيَّ  ؟ فقال له رسول الله (صلى الله عليه وآله وسلم)  : يا  جويبر إنّ الله قد وضع بالإسلام من كان في الجاهلية شريفاً ، وشرّف بالإسلام من كان في الجاهليّة وضيعاً ، وأعزّ بالإسلام من كان في الجاهلية ذليلا ، وأذهب بالإسلام ما كان من نخوة الجاهليّة وتفاخرها بعشائرها وباسق أنسابها ، فإنّ الناس اليوم كلّهم أبيضهم وأسودهم وقرشيّهم وعربيّهم وعجميّهم من آدم وإنّ آدم خلقه الله عزّ وجلّ من طين ، وإنّ أحبّ الناس إلى الله عزّ وجلّ يوم القيامة أطوعهم له وأتقاهم

Wata rana manzon Allah (saw) saboda tausayinsa da rahama ya dubi juwaibar ya ce masa: da za ka aura daga mata ka kiyaye farjinka ita kuma ta taimaka maka duniyarka da lahira, sai juwaibar ya ce: ya manzo Allah (saw) mahaifana fansarka wacece za ta yi kwadayin aurena alhalin banda wani matsayi banda dangi banda kudi banda kyawu wacce mace ce zata soni ? sai manzon Allah ya ce masa ? ya juwaibar haqiqa Allah da muslunci ya qasqantar da wanda ya kasance a jahiliya ma'abocin girma da daukaka, da muslunci ya girmama wulaqntacce  a jahilya, ya  qasqantar da mai daukaka a jahiliya da muslunci ya kuma daukaka qasqantacce da muslunci, ya tafiyar da girma da alfahari qabilun larabawa na jahiliya, a yau dukkanin mutane fararensu da baqaqensu quraishawa da ragowar larabawa da dukkanin ajamawa daga adamu suke haqiqa adamu Allah ya halicce shi daga yunbu, haqiqa mafi soyuwa wajen Allah ranar qiyama daga cikin mutane shi ne wanda ya fi kowa biyayya gareshi da tsoransa.

وما أعلم يا جويبر لأحد من المسلمين عليك اليوم فضلا إلاّ لمن كان أتقى  لله منك وأطوع ، ثمّ قال له  : انطلق يا جويبر إلى زياد بن لبيد فإنّه من أشرف بني بياضة حسباً فيهم فقل له  : إنّي رسول رسول الله (صلى الله عليه وآله وسلم) وهو يقول لك  : زوِّج جويبر ابنتك الذلفاء ، قال  : فانطلق جويبر برسالة رسول الله (صلى الله عليه وآله وسلم) إلى زياد بن لبيد وهو في منزله وجماعة من قومه عنده فاستأذن فأذن له وسلّم ثمّ قال  : يا زياد بن لبيد إنّي رسول رسول الله (صلى الله عليه وآله وسلم) في حاجة لي فأبوح بها أم اُسرّها إليك  ؟ فقال له زياد  : لا بل بح بها فإنّ ذلك شرف لي وفخر

ya juawibar yau ban san wani mutum da ya fika daraja ba face wanda ya fika taqawa da da`a ga Allah, sannan ya ce masa: kaje wajen ziyad dan lubaid wanda yake yana daga cikin mafi girman matsayi daga qabilar bayada ka ce masa: manzon Allah ya ce masa ya aurar da `yarsa zulfa'u ga juwaibar, sai juwaibar ya tafi da saqon manzon alllah (saw) ga ziyad dan lubaid ya sameshi a gida tareda jama'a daga mutanensa sai ya nemi izini akayi masa izini ya yi musu sallama sannan ya ce: ya ziyad dan lubaidi haqiqa nidan aiken manzon Allah (saw) cikin wata buqata tawa in bayyana maka ko kuma in boyeta gareka ? sai ziyad dan lubaid ya ce: a'a bayyana cikin hakan akwai daukaka da alfahari gareni.

فقال له جويبر  : إنّ رسول الله (صلى الله عليه وآله وسلم) يقول لك  : زوِّج جويبراً بنتك الذلفاء ، فقال له زياد  : أرسول الله أرسلك إليَّ بهذا يا جويبر  ؟ فقال له  : نعم ما كنت لأكذب على رسول الله (صلى الله عليه وآله وسلم) ، فقال له زياد  : إنّا لا نزوِّج فتياتنا إلاّ أكفّاءنا من الأنصار فانصرف يا جويبر حتّى ألقى رسول الله (صلى الله عليه وآله وسلم) فاُخبره بعذري ، فانصرف جويبر وهو يقول  : والله ما بهذا نزل القرآن ولا بهذا ظهرت نبوّة محمّد (صلى الله عليه وآله وسلم)

 sai yace: haqiqa manzon Allah (saw) yana umartarka da ka aurar da `yarka zulfa'u ga juwaibar, sai ya ce masa shin manzon Allah (saw) ne ya aiko ka da wannan saqo ya juwaibar ? ya ce: na'am ban kasance ina yin qarya ba kan manzon Allah (saw) sai ziyad ya ce: mu bama aurar da `ya`yanmu sai ga wadanda suke tsara garesu daga mutanen madina, ka tafi ya juwaibar har sai naga manzon Allah (saw) in gaya masa uzurina, sai juwaibar ya juya ya tafi yana cewa wallahi ba da wannan qur'ani ya sauka ba da haka ne annabtar muhammadu (saw) ta bayyana ba.

فسمعت مقالته الذلفاء بنت زياد وهي في خدرها فأرسلت إلى أبيها اُدخل إليّ فدخل إليها فقالت  : يا أباه ما هذا الكلام الذي سمعته منك تحاور به جويبر  ؟ فقال لها  : ذكر لي أنّ رسول الله (صلى الله عليه وآله وسلم) أرسله وقال  : يقول لك رسول الله (صلى الله عليه وآله وسلم)  : زوِّج جويبراً ابنتك الذلفاء ، فقالت له  : والله ما كان جويبر ليكذب على رسول  الله  (صلى الله عليه وآله وسلم) بحضرته فابعث الآن رسولا يردّ عليك جويبراً

ashe zulfa'au ta ji duk tattaunawar da ta kasance tsakanin babanta da juwaibar lokacin tana cikin daki, sai ta aika wajen babanta, da ya zo wajenta sai ta ce masa: ya babana wacce irin magana na ke ji daga gareka kana tattunawa da juawaibar ? sai ya ce mata: ya gaya mini cewa manzon Allah (saw) ya aiko shi gareni  ya na cewa ka aurar da `yarka zulfa'u ga juwaibar, sai ta ce masa: wallahi juwaibar ba zai wa manzon Allah (saw) qarya ba a hallararsa yanzu ka aika dan saqo ya dawo da juwaibar.

فبعث زياد رسولا فلحق جويبراً ، فقال له زياد  : يا جويبر مرحباً بك اطمئن حتّى أعود إليك ، ثمّ انطلق زياد إلى رسول الله (صلى الله عليه وآله وسلم) ، فقال له  : بأبي أنت واُمّي إنّ جويبراً أتاني برسالتك وقال  : إنّ رسول الله (صلى الله عليه وآله وسلم) يقول لك  : زوِّج جويبراً ابنتك الذلفاء ، فلم ألن له في القول ورأيت لقاءك ونحن لا نزوِّج إلاّ أكفّاءنا من الإنصار ، فقال له رسول الله (صلى الله عليه وآله وسلم)  : يا زياد ، جويبر مؤمن والمؤمن كفو المؤمنة والمسلم كفو  المسلمة ، فزوِّجه يا زياد ولا ترغب عنه

sai ziyad ya aika da dan aike ya riski juwaibar, sai ziyad ya cewa juwaibar: zanje in tabbatar da maganarka sannan zan dawo gareka, ziyad ya tafi wajen manzon Allah (saw) ya ce babana da babata fansarka haqiqa juwaibar ya zo wajena da saqonka ya ce mini:  haqiqa manzon Allah ya na ce maka ka aurawa juwaibar `yarka zulfa'u amma ban tausasa harshe cikin magana ba sai naga yafi dacewa inzo in ganka mu bama aurar da `ya`yanmu face da sa'anninsu tsaransu daga mutanen madina, sai manzon Allah (saw) ya ce masa: juwaibar mumuni ne kuma mumuni shi ne tsra ga mumina, musulmi shi ne ya dace da musulma, ka aura masa ya ziyad ka da ka kyamaceshi.

قال  : فرجع زياد إلى منزله ودخل على ابنته فقال لها ما سمعه من رسول  الله  (صلى الله عليه وآله وسلم) ، فقال له  : إنّك إن عصيت رسول الله (صلى الله عليه وآله وسلم) فكرت ، فزوِّج جويبراً ، فخرج زياد فأخذ بيد جويبر ثمّ أخرجه إلى قومه فزوّجه على سنّة الله وسنّة رسول الله (صلى الله عليه وآله وسلم) وضمن صداقه ، قال  : فجهّزها زياد وهيّؤوها ثمّ أرسلوا إلى جويبر ، فقالوا له  : ألك منزل فنسوقها إليك ، فقال  : والله ما لي من منزل ، قال  : فهيّؤوها وهيّؤوا لها منزلا وهيّأوا فيه فراشاً ومتاعاً وكسوا جويبر ثوبين واُدخلت الذلفاء في بيتها واُدخل جويبر عليها مُغتمّاً فلمّا رآها نظر إلى بيت ومتاع وريح طيّبة ، قام إلى زاوية البيت فلم يزل تالياً للقرآن راكعاً وساجداً حتّى طلع الفجر ، فلمّا سمع النداء خرج وخرجت زوجته إلى الصلاة فتوضّأت وصلّت الصبح فسئلت هل مسّكِ 

sai ziyad ya koma gida ya je wajen `yarsa zulfa'u ya gaya mata abin da ya ji daga manzon Allah (saw) sai ya ce masa duk da kasantuwar ka sabawa manzon (saw) to daga baya kayi tunani, sai ya aurawa juawaibar zulfa'u kan sunnar Allah da manzon Allah (saw) ya lamunce  masa biyan sadakinta, ziyad ya shirya mata dukkanin kayan daki  suka aikawa juwaibar suna tambayarsa shin kana da gida mu rako maka ita gidan, sai ya ce: wallahi banda gida, ziyad ya ce: ku shiryata tareda gida da shimfida da kayyyaki , sannan suka tufatar da juwaibar da kaya biyu aka kai zulfa'u dakinta aka kaimata ango juwaibar ya na cikin halin cike da baqin ciki yayinda ya ganta ya kalli kayan alatu da ke gidan da qamshin turare da ya dumame gidan sai yayi wuf ya koma kusurwar gidan bai gusheba yana ta tilawar qur'ani  ya na ruku'u da sujjada har alfijir ya keto, yayin da ya ji kira sai ya fito ita ta fito tareda shi ta yi alwala ta yi sallar asubahi, sai aka tambayeta shin ya kusance ki ya shafeki ?

فقالت  : ما زال تالياً للقرآن وراكعاً وساجداً حتّى سمع النداء ، فخرج فلمّا كان الليلة الثانية فعل مثل ذلك وأخفوا ذلك من زياد ، فلمّا كان اليوم الثالث فعل مثل ذلك فاُخبر بذلك أبوها فانطلق إلى رسول الله (صلى الله عليه وآله وسلم) ، فقال له  : بأبي أنت واُمّي يا رسول الله ، أمرتني بتزويج جويبر ولا والله ما كان من مناكحنا ولكن طاعتك أوجبت عليّ تزويجه ، فقال له النبيّ (صلى الله عليه وآله وسلم)  : فما الذي أنكرتم منه  ؟ فقال  : إنّا هيّئنا له بيتاً ومتاعاً وأدخلت بنتي البيت واُدخل معها مغتمّاً ، فما كلّمها ولا نظر إليها ولا دنا منها ، بل قام إلى زاوية البيت فلم يزل تالياً للقرآن راكعاً وساجداً حتّى سمع النداء ، وخرج وفعل مثل ذلك في الليلة الثانية ومثل ذلك في الليلة الثالثة ، ولم يدن منها ولم يكلّمها إلى أن جئتك وما نراه يريد النساء ، فانظر في أمرنا .

 sai ta ce bai gushe ba ya na ta yin tilawa da ruku'u da sujjada har ketowar alfijir har sai da ya ji kirn sallah, dare na biyu ya qara maimaita haka, sai suka boyewa ziyad labarin abin da ke faruwa, dare na uku sai aka baiwa mahaifinta labari, sai ya tafi wajen manzon Allah (saw) ya ce: babana da babata fansarka ya manzon Allah ka umarce ni da aurawa juwaibar kuma wallahi shi bai cancanci wanda zamuyi auratayya da shi ba amma biyayyarka ta tilastani auratayya da shi, sai annabi (as) ya ce masa: wanne abu kuke inkari daga gareshi ? haqiqa mumun shirya masa gida da kayayyakin alatu da ado aka kaima masa `yata  sai aka shigar da shi dakinta alhalin ransa bace, bai ko yi mata magana ba bai kalleta ba  bai kusanceta ba, sai kawai ya tashi ya koma kusurwar gida ya kama tilawa da ruku'u da sujjada  har sai da ya ji kiran sallah ya fito, ya qara aikata haka dare na biyu haka na dare na uku, bai kusantarta, har Allah ya kawo ni wajenka bama tsammanin ya na son mata.

فانصرف زياد وبعث رسول الله (صلى الله عليه وآله وسلم) إلى جويبر ، فقال له  : أما تقرب النساء  ؟ فقال له جويبر  : أوَ ما أنا بفحل ، بلى يا رسول الله إنّي لشبق نهم إلى النساء ، فقال له رسول الله (صلى الله عليه وآله وسلم)  : قد خُبّرت بخلاف ما وصفت به نفسك ، وقد ذكر لي أ نّهم هيّأوا لك بيتاً وفراشاً ومتاعاً واُدخلت عليك فتاة حسناء عطرة وأتيت مغتمّاً فلم تنظر إليها ولم تكلّمها ولم تدنُ منها فما دهاك إذاً 

 saboda haka kayi duba cikin al'amarinmu, sai mahaifinta ya juya ya tafi, manzon Allah(saw) ya aika aka zo masa juwaibar, ya ce masa: shin kai baka kusantar mata ? sai juwaibar ya ce: sai kace ni ba namiji ne bane, na'am haqiqa ni ina tsananin son mata da sha'awarsu, sai manzon Allah (saw) ya ce: haqiqa an bada labarinka sabanin abin da kake siffanta kanka da shi, haqiqa an gaya min cewa su sun shirya maka gida da shimfida da kayayyakin ado an shigar maka da matarka kyakkyawa ma'abociyar qamshi, amma kuma kai sai ka zo cikin baqin ciki da bacin rai ko kallonta da yi mata Magana ba kai ba ba ka ko kusanceta ba, me ye ya baka mamaki ?

فقال له جويبر  : يا رسول الله اُدخلت بيتاً واسعاً ورأيت فراشاً ومتاعاً وفتاة حسناء عطرة ، وذكرت حالي التي كنت عليها وغربتي وحاجتي ووضيعتي وكينونتي مع الغرباء والمساكين ، فأحببت إذ أولاني الله ذلك أن أشكره على ما  أعطاني وأتقرّب إليه بحقيقة الشكر ، فنهضت إلى جانب البيت فلم أزل في صلاتي تالياً للقرآن راكعاً وساجداً أشكر الله تعالى حتّى سمعت النداء ، فخرجت ، فلمّا أصبحت رأيت أن أصوم ذلك اليوم ففعلت ذلك ثلاثة أيام ولياليها ، ورأيت ذلك في جنب ما أعطاني الله عزّ وجلّ يسيراً ، ولكنّي ساُرضيها واُرضيهم الليلة إن  شاء الله تعالى  

sai ya ce: ya manzon Allah an kaini gida mayalwaci naga shimfidu da kayyayaki da mace kyakkayawa  cikin qamshi, sai na tuna da halin da na kasance cikin da baquntata talaucina da wulaqanata da yanda na kasance tare da sauran baqi da talakawa, sai na qaunaci ace na nuna godiya kan abin da Allah ya bani haqiqa godiya, shi ne na lazimci kusurwar gidan  ina sallah da tilawar qur'ani har sai da naji kiran sallah, yayin da gari ya waye sai na zabi yin azumi, shi ne na maimaita  haka tsawon kwanaki uku, sai na auna godiyata kana bin Allah ya bani ba baki komi ta ke ba, amma da izinin Allah zan yardar da ita da su.

فأرسل رسول الله (صلى الله عليه وآله وسلم) إلى زياد فأتاه فأعلمه بما قال جويبر فطابت أنفسهم ، قال  : ووفى لهم جويبر بما قال ، ثمّ إنّ رسول الله (صلى الله عليه وآله وسلم) خرج في غزوة له ومعه جويبر فاستشهد (رحمه الله) فما كان في الأنصار أيِّم أنفق منها بعد جويبر

sai manzo Allah ya aika aka kira ziyad dan lubaid, ya sanr da shi abin da juwaibar ya gaya masa, sannan manzon Allah (saw) ya fito wani yaqi tare da juwaibar wanda a cikin wannan yaqi ne juwaibar ya yi shahada, ba a samu wata bazawara mafi infaqi daga ita ba bayan juwaibar.

الكافي  : محمّد ، عن أحمد وعلي ، عن أبيه ، عن ابن فضّال ، عن ابن  بكير ، عن زرارة ، عن أبي جعفر (عليه السلام) قال  : « مرّ رجل من أهل البصرة شيبانيّ  يقال له عبد الملك بن حرملة على عليّ بن الحسين (عليهما السلام) فقال له عليّ بن الحسين (عليهما السلام)  : ألك اُخت  ؟ قال  : نعم ، قال  : فتزوِّجنيها  ؟ قال  : نعم ، قال  : فمضى الرجل وتبعه رجل من أصحاب عليّ بن الحسين (عليهما السلام) حتّى انتهى إلى منزله فسأل عنه فقيل له فلان بن فلان وهو سيّد قومه .

5-alkafi : daga ba'arin sahabbanmu daga taimauli  daga naka'i daga muhammad dan sinan daga wani mutum daga baban Abdullah (as) ya ce: wani mutum ya je wajen annabi (as) sai ya ce: haqiqa ni ina da mai tsatstsadan sadaki cikin larabawa ina son ka karbeta kuma ita `ya ta ce , sai annabi (as) ya ce: na karba, sai mutumin ya ce dayarfa, sai annabi s.a.w ya ce wacce kuma ? sai mutumin ya ce: itace wacce ta ke lafiyarta qalau wani ciwo bai taba shafarta ba, sai annabi  ya ce: bani buqatar ta ka aurawa halibu, dajin haka sai yanayin mutumin ya canja, sannan ya juya ya tafi wajen mahaifiyarta ya gaya mata abin da ya faru, sai ita ma yanayinta ya canja, yayin da `yar ta ji abin dabya faru, sai ta cewa mahaifanta: ku yardar mini abin da manzon Allah (saw) ya yardar mini, sai damuwarsu ta yaye, sai mahaifinta ya koma wajen manzon Allah (saw) ya gaya masa abin da `yarsa ta zaba, sai manzon Allah  ya ce: na sanya aljanna sadakinta.

Sufwan ya qara yace : sai halibut ya mutu sadakinta ya zamanto ya kai ga dirhami dubu dari.

الكافي  : محمّد ، عن أحمد وعلي ، عن أبيه ، عن ابن فضّال ، عن ابن  بكير ، عن زرارة ، عن أبي جعفر (عليه السلام) قال  : « مرّ رجل من أهل البصرة شيبانيّ  يقال له عبد الملك بن حرملة على عليّ بن الحسين (عليهما السلام) فقال له عليّ بن الحسين (عليهما السلام)  : ألك اُخت  ؟ قال  : نعم ، قال  : فتزوِّجنيها  ؟ قال  : نعم ، قال  : فمضى الرجل وتبعه رجل من أصحاب عليّ بن الحسين (عليهما السلام) حتّى انتهى إلى منزله فسأل عنه فقيل له فلان بن فلان وهو سيّد قومه

6- alkafi : muhammad daga ahamad da ali daga babansa daga dan faddal wani mutu daga mutanen basara shaibani ya wuce aliyu dan husaini (as) sai aliyu dan husaini (as) ya ce masa: shin kana da `yar'uwa sai ya ce: na'am , sai imam y ace aurar mini da ita , sai mutumin ya ce : na'am  ya tafi, sai wani daga sahabban aliyu dan husaini (as) ya bi bayansa har ya kai ga gidansa, sai ya tambaya game da mutumin sai aka ce masa shi ne wane dan wane kuma shi ne shugaba cikin mutanensa. sai ya dawo wajen imam ya ce: ya baban hassan  na yi tambaya game da wannan sirikin naka shaibani suna riya cewa shi ne shaugaban muatanensa, sai aliyu dan husaini (as) ya ce masa: haqiqa ni zan bayyanar maka abin da nake gani da abin da nake ji, ashe baka san cewa Allah da muslunci ya daukaka wulaqantacce  ya cika masa daga tawaya ya karrama shi daga wulaqanta, babu wulaqanta kan musulmi, wulaqanta na kan jahiliya

الكافي  : عليّ ، عن أبيه ، عن ابن فضّال ، عن ثعلبة بن ميمون ، عمّن يروي ، عن أبي عبد الله (عليه السلام) « أنّ عليّ بن الحسين (عليهما السلام) تزوّج سريّة كانت للحسن بن عليّ (عليهما السلام) ، فبلغ ذلك عبد الملك بن مروان فكتب إليه في ذلك كتاباً  : أ نّك صرت بعلا للإماء ، فكتب إليه عليّ بن الحسين (عليهما السلام)  : إنّ الله رفع بالإسلام الخسيسة وأتمّ به الناقصة وأكرم به اللؤم ، فلا لؤم على مسلم ، إنّما اللؤم لؤم  الجاهلية ، إنّ رسول الله (صلى الله عليه وآله وسلم) أنكح عبده ونكح أمته

7-alkafi: aliyu daga babansa daga dan faddal daga sa'alaba dan maimun daga wajen wanda ya ke riwaita daga baban Abdullah (as) cewa aliyu dan husaini ya auri wata baiwar Hassan dan aliyu (as) sai abdul-malik dan marwan ya ji labari sai ya rubuta wasiqa zuwa ga husaini dan ali (as) ya n ace masa: kai ka zama mijin baiwa, sai aliyu dan husaini (as) ya mayar masa da amsa da cewa: Allah da muslunci ya daukaka qasqantacce ya kammalashi daga naqasa ya karrama shi daga wulaqanta, babu wulaqanta kan musulmi kadai dai wulaqanta itace wulaqantar jahiliya, haqiqa manzon Allah saw) ya aurawa bawansa kuma ya auri baiwarsa, yayin da wasiqar imam ta isa hannun abdul malik  sai ya cewa wanda ke kewaye da shi: ku bani labari  game da mutumin ya aikata abin da mutane ke ganinsa wulaqanci amma kuma babu abin da ya qara masa sai daraja ? sai suka ce ai ba kowa bane face sarkin muminai, sai ya ce musu a'a wallahi ba shi bane, sai suka ce mu dai bamu san kowa face sarkin muminai, yace bashi bane sai dai cewa ba kowa bane face aliyu dan husaini (as).

عن الحسين بن بشار ، قال  : كتبت إلى أبي الحسن (عليه السلام)  : إنّ لي ذا قربة قد خطب إليّ وفي خلقه سوء ، قال  : لا تزوّجه إن كان سيّء الأخلاق .

8 daga husaini dan bashar ya ce: na rubuta wasiqa zuwa ga aliyu dan husaini (as) inace masa ina da wani `dan'uwa makusanci da ya nemi auren `yata sai dai kuma ya na da munin dabi'a, sai imam ya ce masa : ka da ka aura masa matuqar ya na da munin hali.

عن الحسين بن بشار أيضاً ، قال  : كتبت إلى أبي جعفر (عليه السلام) في رجل خطب إليّ ، فكتب (عليه السلام)  : من خطب إليكم فرضيتم دينه وأمانته كائناً من كان فزوّجوه

9 daga husaini dan bashshar ya ce: na rubuta wasiqa zuwa ga baban jafar (as) wani mutum ya nema daga gareni sai imam yace masa: duk wanda ya nema daga gareku ku ka aminta da addininsa da amanarsa kowa ya kasance to ku aura masa:

 [1] إلاَّ تَفْعَلُوهُ تَكُنْ فِتْنَةٌ فِي الأرْضِ وَفَسَادٌ كَبِيرٌ 

 idan baku aikata hakan ba wata fitina za ta kasance cikin qasa da fasadi babba  anfal aya.

Da wannan aya mai daraja imam (as) ya qafa dalili kan cewa dukkanin wanda ya tsananta al'amarin aure kamar tsadar sadaki cikin wannan haqiqa yana daga wadanda suke taimakawa cikin yada fasadia a ban qasa, haqiqa aure garkuwa ne daga yawa yawan tuntube da zunubai da laifuka daidaku da jama'a.

Dukkanin wanda ya bar aure ko kuma ya tsananta al'amarinsa  bai sauqaqa shi ba to haqiqa ya tallafawa yaduwar fitina da barna mai girma cikin qasa.

عن الصادق (عليه السلام) ، قال  : المؤمنون بعضهم أكفاء بعض ، وقال (عليه السلام)  الكفو أن يكون عفيفاً وعنده يسار

10 daga sadiq (as) ya ce: muminai sashensu ne daidai da sashe ya ce: sa'an aure wanda ya cancanta ya kamata ya kasance yana da kamewa da yalwa.

قال رسول الله (صلى الله عليه وآله)  : إنّما أنا بشر مثلكم ، أتزوّج فيكم واُزوّجكم ، إلاّ فاطمة فإنّ تزويجها نزل من السماء ، ونظر رسول الله (صلى الله عليه وآله) إلى أولاد عليّ وجعفر فقال  : بناتنا لبنينا وبنونا لبناتنا

11- manzon Allah (saw) ya ce: kadai dai ni mutum ne irinku, ina aura daga cikinku ina aurar muku, face fatima ita aurenta ya sauko daga sama, ya kalli `ya`yan ali da jafar sai ya ce: `ya`yanmu mata ga `ya`yanmu maza sannan `ya`yanmu maza ga `ya`yanmu mata.

Ta yiwu wannan hukunci kebantacce ne cikin gidan annabta ko kuma cikin bani hashim  ko zuriyar manzon Allah (saw)  da wannan ne zaka samu wasu dangi daga cikin alawiyyawa sharifai basu aurar da `ya`yansu mata ga wanda ba daga alawiyyawa sharifai ya ke ba.

Daga cikin abin lura cikin tsara a aure shi ne taqawa, mai ya sanar da kai game da taqawa, lalle alherin duniya da lahira na cikinta, tana bayyanar da alamunta hatta cikin rayuwar aure.

من كتاب تهذيب الأحكام ، جاء رجل إلى الحسن (عليه السلام) يستشيره في  تزويج ابنته ، فقال  : زوّجها من رجل تقي ، فإنّه إذا أحبّها أكرمها ، وإن أبغضها لم يظلمها .

12 daga littafin tahzibul ahkam: wani mutum ya zo wajen hassan (as) yana neman shawararsa  kan aurar da 'yarsa, sai ya ce masa: ka aurar da ita ga mai tsoron Allah, haqiqa shi mai tsoron Allah idan ya so ta zai karrama ta, idan kuma ya qita ba zai danne haqqinta ba ba zai zalunceta ba, zai yi mata mu'amala da adalci da ihsani da alheri.

هذا لمن يزوّج بنته وكريمته من رجل متّقي ، أمّا من زوّجها من رجل فاسق لا يراعي حقوق الله والناس ، فقد قال رسول الله (صلى الله عليه وآله)  : « من زوّج كريمته من فاسق فقد قطع رحمه » ، ومعلوم قاطع الرحم في النار ، فإنّه يستحبّ صلة الأرحام ، ويحرم قطعها كما هو مذكور في محلّه

13 – wannan ga wanda ya aurar da `yarsa ga mai taqawa amma game da wanda ya aurawa fasiqi haqiqa ba zai kiyaye haqqoqin Allah da mutane ba, manzon Allah (saw) ya ce: duk wanda ya aurawa fasiqi `yarsa to haqiqa ya yanke zumuncinsa, sanann sananne abu ne cewa mai yanke zumunci ya na wuta, haqiqa mustahabbine sadar da zumunci, kuma an haramta yanke shi kamar yadda aka ambaceshi a muhallinsa.

Daga cikin sabo kwai zina da shan barasa, haqiqa hani mai tsanani ya zo kansu.

عن الحلبي ، قال  : قال الصادق (عليه السلام)  : لا تتزوّجوا المرأة المستعلنة بالزنا ، ولا تزوّجوا الرجل المستعلن بالزنا ، إلاّ أن تعرفوا منهما التوبة

14- daga halabi ya ce: sadiq (as) ya ce: kada ku auri macen da ta shahara da zina haka ma namiji da ya shahara da zina face kun san cewa sun tuba.

 وعن زرارة ، قال  : سألت أبا عبد الله (عليه السلام) عن قوله عزّ وجلّ  : (  الزَّانِي لا يَنكِحُ إلاَّ زَانِيَةً أوْ مُشْرِكَةً وَالزَّانِيَةُ لا يَنكِحُهَا إلاَّ زَان أوْ مُشْرِكٌ 

15- daga zurara ya ce: na tambayi baban abdullah (as) kan fadin Allah madaukaki:

mazinaci ba ya aure face da mazinaciya ko mushrika mazinaciya ba ta aure face da mazinaci ko mushriki ?

فقال  : هي نساء مشهورات بالزنا ورجال مشهورون بالزنا ومعروفون به ، والناس اليوم بتلك المنزلة ، من اُقيم عليه حدّ الزنا أو شهر بالزنا لا ينبغي لأحد أن يناكحه حتّى يعرف

 sai ya ce sune matayen da suka shahara da zina da mazajen da suka shahara da zina  aka sansu da ita, mutane  a wanann zamani namu suna kan wannan matsayi, duk wanda aka tsayar masa da haddin zina bai da ce wani ya yi auratayya da shi har sai anga ya tuba.

da wannan ne a'imma (as) suka buga nafi kyawun misali  don kubutar jama'a daga sabo da komawar mutane ga tuba musammam matasa.

قال (صلى الله عليه وآله)  : من شرب الخمر بعدما حرّمها الله فليس بأهل أن يزوّج إذا خطب

16- imam (as) ya ce: duk wanda ya sha giya bayan Allah ya haramta to shi baya cikin wanda za'a aurawa idan ya nema.

قال رسول الله (صلى الله عليه وآله)  : أنكحوا الأكفاء وأنكحوا منهم ، واختاروا لنطفكم[2]

17- manzon Allah(saw) yace: ku aurarwa da tsaraiku sannan kuma ku aura daga gare su, kuma kuyi zabi cikin inda za ku sanya digon maniyyinku.

 Sannan ma'auni cikin ala'amarin shi ne muslunci, ba wadata ba ko dukiya, kamar yadda manzon (saw) ya aikata don cikin tabbatar da hakan, ya ce: na aurawa zaidu dan harisa zainab `yar jahash alhalin shi talaka ne, na kuma aurawa miqdad dabba'atu `yar zubair dan abdul mudallib wacce ta kasance daga gidan manyan quraishawa da shugabanninsu, saboda mutane su sani mafi girma matsayi da daraja na tareda muslunci.

عن أبي جعفر (عليه السلام) ، قال  : قال رسول الله (صلى الله عليه وآله)  : لا تسبّوا قريشاً ولا تبغضوا العرب ، ولا تذلّوا الموالي ، ولا تساكنوا الخوز ، ولا تزوّجوا إليهم ، فإنّ لهم عرقاً يدعوهم إلى غير الوفاء

18-daga baban jafar (as) ya ce: manzon Allah (saw) ka da ku zagi quraishawa  kada kuyi qiyayya da larabawa, kada ku qasqantar da bayi, ka da ku zauna tare da kuzawa, ka da ku aurar musu, haqiqa suna da wata jijiya da ke kiransu da rashin cika alqawari.

عن فقه الرضا ، إن خطب إليكم رجل رضيت دينه وخلقه فزوّجه ، ولا يمنعك فقره وفاقته ، قال الله تعالى  : (  وَإنْ يَتَفَرَّقَا يُغْنِ اللهُ كُلاّ مِنْ سَعَتِهِ  )[3] ، وقال  : (  إنْ يَكُونُوا فُقَرَاءَ يُغْنِهِمُ اللهُ مِنْ فَضْلِهِ وَاللهُ وَاسِعٌ عَلِيمٌ  )[4] ، ولا يتزوّج شارب الخمر ، فإنّ من فعل فكأنّما قادها إلى الزنا

 

19- daga fiqihu rida (as) idan mutumin da kuka nutsu da addininsa  da halayensa ya nemi aura daga cikinku to ku ba shi, kada talauci da rashi ya hanaku ba shi, Allah madaukaki na cewa:

 

idan suka rabu da juna Allah zai azurta kowannensa daga falalarsa. Idan sun kasance talakawa faqiarai Allah zai wadatasu daga falalarsa Allah mayalwacine masani.

 kada da ku aurawa mashayin giya haqiqa duk wanda ya aikata haka to kamar ya tura 'yarsa zuwa ga.

قال بعض الخوارج لهشام بن الحكم  : العجم تتزوّج في العرب  ؟ قال  :  نعم . قال  : فالعرب تتزوّج في قريش  ؟ قال  : نعم . قال  : فقريش تتزوّج في بني هاشم  ؟ قال  : نعم . فجاء الخارجي إلى الصادق (عليه السلام) فقص

ّ عليه ثمّ قال  : أسمعه منك . فقال (عليه السلام)  : نعم ، فقد قلت ذاك . قال الخارجي  : فها أنا ذا قد جئتك خاطباً ، فقال له أبو عبد الله (عليه السلام)  : إنّك لكفو في دينك وحسبك في قومك ، ولكنّ  الله عزّ وجلّ صاننا عن الصدقات وهي أوساخ أيدي الناس فنكره أن نشرك فيما فضّلنا الله به من لم يجعل الله له مثل ما جعل لنا ، فقام الخارجي وهو يقول  : بالله ما رأيت رجلا مثله ردّني والله أقبح ردّ وما خرج من قول صاحبه[5]

20- sashen kawarijawa sun cewa hisham dan hakam: shin wadanda ba larabawa ba zasu iya aurar larabawa ? sai ya ce: na'am, sai suka qara cewa: shin larabawa za su iya auren quraishawa ? ya ce na'am, shin quraishawa za su  iya aurar hashimawa ? yace na'am, sai wannan kawarij ya je wajen imam sadiq (as) ya bashi labari sannan ya ce ina sauraro daga gareka, sai imam (as) ya ce: na'am ina fadin haka sai kawarij ya ce : to gani yanzu nazo ina nema daga gareka, sai imam (as) ya ce masa:  haqiqa kai tsara ne ka cancanta cikin addininka da matsayinka cikin mutanenka, sai dai cewa Allah ya katangemu daga sadaqa wadda ita dattin hannun mutane ce, saboda mu kyamar yin tarayya cikin abin da Allah ya fifita da shi da wanda Allah bai sanya masa abin da ya sanya mana ba, sai kawarij ya ta shi ya na cewa: wAllahi ban taba ganin mutumin yayi martani da mafi munin martani da abin da ya fito daga zancen ma'abocinsa.

عن أبي عبد الله (عليه السلام) ، قال  : لولا أنّ الله تبارك وتعالى خلق أمير  المؤمنين (عليه السلام) لفاطمة ما كان لها كفو على ظهر الأرض

21-daga baban Abdullah (as) ba don Allah ya halicci sarkin muminai ali (as) da babu wanda zai kasance tsara ya cancanta da auren Fatima bisa qasa.

عن أبي عبد الله (عليه السلام) ، قال  : لولا أنّ الله تبارك وتعالى خلق أمير  المؤمنين (عليه السلام) لفاطمة ما كان لها كفو على ظهر الأرض

22- daga baban Abdullah (as) y ace : ku aura daga mai yawan shakka amma ka da ku aura masa, saboda mace na karba daga ladubban miji kuma ya na tilasta ta kan addininsa.

عن ابن سنان ، قال  : سألت أبا عبد الله (عليه السلام)  : بكم يكون الرجل مسلماً يحلّ مناكحته وموارثته وبما يحرم دمه  ؟ فقال  : يحرم دمه بالإسلام إذا أظهره ويحلّ مناكحته وموارثته

23- daga Abdullah dan sinan ya ce: na tamabayi baban Abdullah (as) da abubuwa na wane mutum zai zama musulmi da auratayya da shi za ta halasta, da gadarsa sannan dame jininsa ke haramta ? sai ya ce : jininsa na haramta da muslunci idan ya bayyana shi kuma aure da gado suna halasta.

عن زرارة ، قال  : قلت لأبي جعفر (عليه السلام)  : أتخوّف أن لا تحلّ لي أن أتزوّج صبيّة من لم يكن على مذهبي ، فقال  : ما يمنعك من البله من النساء اللاتي لا يعرفن ما أنتم عليه ولا ينصبن ـ  أي لا تنصب عداوة آل محمّد في قلبها 

24- daga zurara y ace : na cewa babab jafar (as) ina tsoron ka da ka qi halasta mini aure `yar wanda da ba'a mazhaba ya ke ba , sai y ace : me ai hana ka auren wawaye daga mata wadanda ba su san abin da ka ke kai ba  kuma ba sa qiyayya da iyalan annabi (as).

عن ابن سنان ، قال  : سألت أبا عبد الله (عليه السلام) عن الناصب الذي قد عرف نصبه وعداوته ، هل يزوّجه المؤمن وهو قادر على ردّه  ؟ قال  : لا يتزوّج المؤمن ناصبة ولا يتزوّج الناصب مؤمنة ، ولا يتزوّج المستضعف مؤمنة ـ  أي لا يأخذ من أبناء العامة امرأة جعفرية

25- daga dan sinan ya ce: na tambayi baban abdullahi (as) kan nasibi wanda akasan kan nasibanci da adawarsa ga alhul- baiti (as) shin mumini zai iya aurar masa alhalin ya na da ikon korarsa, sai imam (as) ya ce: mumini bai aurar banasibiya , nasibi bai aurar mumina, rarrauna bai aurar mumina –ma'ana ragowar mutane wanda ba shi'a ba su auri mumina bajafariya.

auren bayahudiya da banasariya ya halasta, sai dai cewa a hana su cin namam alade da shangiya, duk wanda ya auresu cikin addininsa akwai nakasa kamar yadda ya zo cikin hadisi ma daraja.

عن زرارة ، قال  : قلت لأبي عبد الله (عليه السلام)  : أتزوّج المرجئة أو الحرورية أو القدرية  ؟ قال  : لا ، عليك بالبله من النساء ، قال زرارة  : فقلت  : ما هي إلاّ مؤمنة أو كافرة  ؟ فقال أبو عبد الله (عليه السلام)  : فأين أهل استثناء الله ، قول الله أصدق من قولك  : (  إلاَّ المُسْتَضْعَفِينَ مِنَ الرِّجَالِ وَالنِّسَاءِ وَالوِلْدَانِ لا يَسْتَطِيعُونَ حِيلَةً وَلا يَهْتَدُونَ سَبِيلا[6]

26- daga zurara ya ce: na cewa baban Abdullah (as) in auri murji'a ko haruriyya ko qadariya ? sai y ace: a'a, na umarce ka da wawiya daga mata, sai ya ce : ba wata mace face mumina ko kafira ? sai baban Abdullah (as) ya ce : ina wanda Allah ya togace, fadin Allah ya fi gasgatuwa daga fadinka:

 

 face raunana daga mazaje da mata da yara wand ba su iya wata dabara , ba su shiriya hanya.[7]

عن العبد الصالح ، قال  : سألناه عن قوله  : (  وَالمُحْصَنَاتُ مِنَ الَّذِينَ اُوتُوا الكِتَابَ مِنْ قَبْلِكُمْ  )[8] ، ما هنّ وما معنى إحصانهن  ؟ قال  : هن العفائف من نسائهم .

27- daga abdul saleh, ya ce mun tambaye shi kan fadinsa madaukaki:

da masu kamun kai daga wadanda aka baiwa littafi gabaninku.

 su waye me ye ma'anar kamewa ? sai ya ce : su ne masu kiyaye farjinsu cikin matansu.

عن أمير المؤمنين (عليه السلام) في قوله تعالى  : (  وَلا تَنكِحُوا المُشْرِكَاتِ حَتَّى يُؤْمِنَّ وَلأمَةٌ مُؤْمِنَةٌ خَيْرٌ مِنْ مُشْرِكَة وَلَوْ أعْجَبَتْكُمْ وَلا تُنكِحُوا المُشْرِكِينَ حَتَّى يُؤْمِنُوا وَ لَعَبْدٌ مُؤْمِنٌ خَيْرٌ مِنْ مُشْرِك وَلَوْ أعْجَبَكُمْ  ) ، وذلك إنّ المسلمين كانوا ينكحون في أهل الكتاب من اليهود والنصارى وينكحونهم حتّى نزلت الآية ، نهى أن ينكح المسلم من المشرك أو ينكحونه ، ثمّ قال تعالى في سورة المائدة ما نسخ هذه الآية ، فقال  : (  وَطَعَامُ الَّذِينَ اُوتُوا الكِتَابَ حِلٌّ لَكُمْ وَطَعَامُكُمْ حِلٌّ لَهُمْ وَالمُحْصَنَاتُ مِنَ المُؤْمِنَاتِ وَالمُحْصَنَاتُ مِنَ الَّذِينَ اُوتُوا الكِتَابَ مِنْ قَبْلِكُمْ  ) ، فأطلق عزّ وجلّ مناكحتهن بعد أن كان نهى وترك قوله  : (  وَلا تُنكِحُوا المُشْرِكِينَ حَتَّى يُؤْمِنُوا ])[9] ، على حاله لم ينسخه .

28-daga sarkin muminai ali (as) cikin fadin Allah madaukaki :

ka da ku auri mata mushrika har sai sun yi imani ko da kuwa sun qayatar da ku , ka da ku auri maza mushriki har saisun yi imani ko da kuwa sun qayatar da ku , bawana mumini shi ne mafi daga mushriki ko kuwa mushrikin ya qayatar da ku.

Wadancananka haqiqa musulmi sun kasance suna aura daga cikin ahlul-kitabi daga yahudu da nasara har zuwa lokacinda aya ta sauka tayi hani da kasantuwar musulmi ya aura daga mushrikai  ko kuma ya aura musu, sannan Allah madaukaki cikin suratul ma'ida abin da ya goge wanann aya sai ya ce

da abincin wadanda aka baiwa littafi halal ne gareku, abincinku halal ne garesu, da kamammu daga mata muminai da kamammu daga daga wadanda aka baiwa  littafi gabaninku.

 sai Allah yayi idlaqin ayar bayan da ya hana ya bar fadinsa ( ka da ku auri maza mushrikai har sai sunyi imani.  a kan halin da yake bai goge shi ba.[1] Anfal:73

[2] Biharul anwar m 100 sh 236

[3] Nisa'i:130

[4] Nurr:32

[5] Almaqib m 3 sh 381

[6] Nisa'i:98

[7] Nisa'i:98

[8] Ma'ida:5

[9] Baqara:221