فهرست کتاب‌‌ لیست کتاب‌ها
■ KALMAR TARBIYYA CIKIN HARSHEN LARABCI DA YANDA AKA YI 4
■ FASALI NA ( 2 ) 24
■ AUREN DABI'A 24
■ FASALI NA 3
■ FASALI NA 4 73
■ FASALI NA 5 131
■ FASALI NA 6 176
HAQQOQIN DA MA'AURATA SU KAYI TARAYYA CIKI 177
1 – HAQURI 178
2 – KAMEWA DAGA ZALUNCI DA CUATARWA 179
HAQQOQIN MATA 180
CIYARWA DA YALWATAWA 185
TAUSAYAWA DA KAMEWA DAGA ZALUNCI 187
KAMEWA DAGA BARIN DUKA MAI CUTARWA 187
UMARNI DA KYAKKYAWA DA HANI DA MUMMUNA 193
GARKUWA 196
8 – KYAUTATAWA : 196
9 - KYAWUNTA ZAMANTAKEWA 197
3 – TAUSAYAWA MIJI : 208
4 – HIMMATUWA DA KULA DA CIKIN GIDA DA KAYYAKINSA : 209
5 - HIMMATUWA CIKIN SAUKE HAQQOQI 209
6 – JIMA'I 210
7 - ADO 213
8 – KAMEWA CIKIN MAGANA : 219
SHUGABANTAR IYALI 225
DALILAI DA SUKE SANYA DAWWAMAR AURE 227
1 – SON JUNA 228
2 – YAWAITA AIKATA ALHERI: 228
4 – SANYA FARIN CIKI: 229
5 – BIYAYYA DA NEMAN YARDAR MIJI: 230
6 – KIYAYE MUTUNCI DA DUKIYA : 230
7 – TAIMAKO DA TALLAFAWA 230
8 – TARBAR MIJI DA KYAWUNTA BANKWANA DA SALLAMA : 231
9 – KALAMIN AQIDOJI MAI KYAWU DA QARFAFAFFEN FURUCI. 232
10 – KARBAR UZURI DA YIWA JUNA UZURI : 232
11 – BINSU SANNU SANNU CIKIN KOWANNE HALI : 233
12 – KYAWUNTA LAFAZI CIKN KOWANNE YANAYI : 233
13 – RASHIN SAURARON KYAUTATA AIKI DARI BISA DARI 233
14 – RASHIN IKON DAUKAR NAUYI A RAYUWANCE : 234
15 – RASHIN GORI KAN MIJI : 234
16 – RASHIN QAURACEWA AL'AMARIN SHIMFIDA: 235
17 - YIN SHAWARA DA MATA BANDA BIYE MUSU: 235
18 – TAKA TSAN TSAN DA KUMA FARKAWA : 238
19 – HANKALTA 239
20 - MIJI SHI NE MUTUNCIN MATARSA 240
21 – KISHI 240
22 – TAIMAKEKENIYYA 242
23 – DADADAWA IYALI 243
27 – WATSI DA BOAKANCI DA TSAFE TSAFE : 244
28 - HIDIMA MADAWWAMIYA 245
29 – GODIYA 246
29 – QAUNAR JUNA 247
TSINTUWA GUDA BIYU GIDAN ALI DA FATIMA (AS) 248
■ FASALI NA 8 252

YARDA SHARDI CE CIKIN AURE 131

YARDA SHARDI CE CIKIN AURE                     

dukkanin aiki dan adam sai niyya ta gabace ma'ana neman abin da ka ke son cimma, haka na kasancewa qarqashin wasu muqaddimom : kamar kamar tunano abin da ka ke niyya, gasgata shi da fa'idarsa, shauqi zuwa gareshi, da shauqin da yake cudanye da yunkuri ganin tabbatar da abin a kayi muradi da ganin an samar da shi.

sha'anin aure na buqatar a ce anyi quduri da niyya tun kafin samun damar zaben wacce za'a aura, daga cikin abubuwan da ke lazimtar aure shi ne ya zama akwai yadda tsakanin saurayi da budurwa, kowanne daya daga cikinsu ya zamanto ya na son yin auren da niyyarsa  ba tare da wani ya tilsta shi ba, da zai zamanto an tiasta mace kan yin auren to da aure ya kasance gurbatacce, auren zai kasance alfasha da haramun har zuwa lokacin da ta yarda  sannanne zai zama halastacce, yarda da shi ko rashinsa na komawa ga ita macenne:

عن صفوان ، عن منصور بن حازم ، عن أبي عبد الله (عليه السلام) قال  : تستأمر البكر وغيرها لا تنكح إلاّ بأمرها

1-an karbo daga sufwan , daga mansur dan hazim daga baban abdullah (as) ya ce: ana neman izinin budurwa da wantanta, ba 'a iya aurar da ita sai da izininta.

وقد روي عن أمير المؤمنين عليّ (عليه السلام) أ نّه ذكر حديث تزويجه من فاطمة وأ نّه طلبها من رسول الله (صلى الله عليه وآله) فقال  : يا عليّ ، إنّه قد ذكرها قبلك رجال ، فذكرت ذلك لها فرأيت الكراهة في وجهها ، ولكن على رسلك حتّى أخرج إليك ، فدخل عليها ، فأخبرها وقال  : إنّ عليّاً قد ذكر من أمرك شيئاً فما ترين  ؟ فسكتت ولم تول وجهها ولم ير فيه رسول الله (صلى الله عليه وآله) كراهة ، فقام وهو يقول  : الله أكبر سكوتها إقراره[1]ا

2- an riwaito daga sarkin muminai ali (as) cewa ya ambaci labarin aurensa da Fatima haqiqa shi ne ya nemi aurenta daga manzon Allah (saw)  sai ya ce masa: haqiqa gabaninka wasu sun zo nema aurenta, sai na gaya mata  sai na fuskanci ba ta so daga alamomin fuskarta, amma kadan jira in je in zo maka da bayani, sai manzon Allah (saw) ya shiga wajenta  ya bata labari ya ce: haqiqa ali (as)  ya ambaci wani abu game da al'amarinki amma mai ki ke umarta ? sai ta yi shiru ba ta juya fuska ba kuma bai ga alamun ba ta so ba daga fuskarta ba, sai ya tashi ya na cewa: Allahu akbar shirinta yardarta ne.

وذكر أنّ فتاة جاءت إلى رسول الله (صلى الله عليه وآله) تشكوا أباها فقالت  : يا رسول الله إنّ أبي زوّجني من ابن أخ له ليرفع خسيسته وأنا له كارهة ، فقال (صلى الله عليه وآله)  : أجيزي ما صنع أبوكِ ، فقالت  : لا رغبة لي فيما صنع أبي ، فقال  : إذن فاذهبي وتزوّجي من شئتِ ، فقالت  : لا رغبة لي عمّا صنع أبي

3- an ambaci cewa : wata budurwa ta zo wajen manzon Allah (saw) tana kai kukan babanta ta ce : ya manzon Allah (saw) babana ya aurar da ni daga diyan dan'uwansa saboda kawar da qin jininsa  amma ni ban son mijin, sai manzon Allah (saw) ya ce: ki halasta abin da babanki ya aikat , ta ce ni ban qaunar abin da babana ya aikata, sai ya ce mata: idan haka ne zaki iya tafiya ki auri duk wanda kike so  sai ta ce: ni banda wani kwadayi cikin abin da babana ya aikata.

Abin da za mu fuskanta daga wannan riwaya mai daraja cikin wannan babi shi ne cewa bazawara za ta iya aurar da kanta ba tareda izinin walaiyyita ba, amma budurwa ko dai an aura da ita da izinin waliyyanta sai dai cewa dole ne a nemi izininta domin shi ne asasi cikin asalin aurenta, tana haqqin yarda da qin yarda da auren da ka daura mata, bai inganta a tilasatata kan auren ( ana neman iznin budurwa da waninta ba'a aurar da ita face da izininta ) idan kuwa aka aurar da ita babu izininta auren bai inganta  ba.

shari'ar muslunci itace farkon shari'a da ta daukaka mace ta samarmata da tsari da ta kaita ga qololuwar matsayi  cikin al'umma ta tabbatar mata da dukkanin haqqoqinta da wajibai, haka al'amari ya ke ga namiji , dole ga saurayi ya zamanto ya na da kwadyi ya zuwa ga aure ya zama kwadayinsa kan asalin aure kamar yadda yak e kwadayi kan macen da zai aura, ta yiwu wannan kwadayi da yake ya dace da abin da iyaye ke so, madalla da abin da ake kwadayi kansa  daga nan komai zai kasance kamar yanda ake buqatarsa, sai dai cewa cikin su iyalai akan samu sabani tsakanin zabin iyaye da zabin dansu,  iri wannan waje wanne za'a gabatar ?

عن ابن أبي يعفور ، عن الصادق (عليه السلام) ، قال  : قلت  : إنّي أردت أن أتزوّج امرأة وإنّ أبوي أرادا غيرها ، قال  : تزوّج الذي هويت ودع التي هوى أبواك

 

4-daga dan abi ya'afur daga sadiq (as) ya ce: na ce : haqiqa ni nayi niyyar auren wata mata sai mahaifana suka zaba mini wata daban, sai imam (as) ya ce : ka auri wacce kake so ka kyale wacce mahaifanka ke so,

haka na nufi da da keson rayuwa tare da matarsa zabinsa shi ne abin gabatarwa, sai da cewa ba kowanne lokaci ake gabatar da zabins ba, tayiwu wani lokaci ya rudu da soyayyar qarya ta bata  idonsa ya makance ya gaza ganin haqiqar al'amarin wacce ke son aura, ta yiwu kyawunta na zahiri ya yaudare shi ya ji ya na sonta halin gafala da cewa ita daga tushe mara kyawu take, manzon Allah (saw) na cewa: na haneku da furen juji, aka tambaye shi me ye furen juji ? sai ya ce: kyakkyawar mace daga mummunan tushe.

a iri wannan wuri iyaye na da haqqin sabawa wannan aure saboda kare abin da zai cutar da dansu, saboda sun san jiya sunfi shi ilimi cikin wannan kwazazzabo, saboda  haka ya kamata shi dan a irin wannan wuri ya karbi shawarar iyaye  idan ta kasance ta yi daidai da hankali, ka da ya biye ma son zuciyarsa  haqiqa zai bata kan hanya madaidaiciya cikin rauywarsa ta aure ya kuma rasa babbar garkuwa da jigo cikin zamantakewarsa da manyan al'amudi biyu wanda sune uwa da uba.ya zama wajibi yin shawara ta gaskiya da lura da sanya lafiyayyen hankali.[1] Wasa'ilul shi'a m 7 sh 206