فهرست کتاب‌‌ لیست کتاب‌ها
■ KALMAR TARBIYYA CIKIN HARSHEN LARABCI DA YANDA AKA YI 4
■ FASALI NA ( 2 ) 24
■ AUREN DABI'A 24
■ FASALI NA 3
■ FASALI NA 4 73
■ FASALI NA 5 131
■ FASALI NA 6 176
HAQQOQIN DA MA'AURATA SU KAYI TARAYYA CIKI 177
1 – HAQURI 178
2 – KAMEWA DAGA ZALUNCI DA CUATARWA 179
HAQQOQIN MATA 180
CIYARWA DA YALWATAWA 185
TAUSAYAWA DA KAMEWA DAGA ZALUNCI 187
KAMEWA DAGA BARIN DUKA MAI CUTARWA 187
UMARNI DA KYAKKYAWA DA HANI DA MUMMUNA 193
GARKUWA 196
8 – KYAUTATAWA : 196
9 - KYAWUNTA ZAMANTAKEWA 197
3 – TAUSAYAWA MIJI : 208
4 – HIMMATUWA DA KULA DA CIKIN GIDA DA KAYYAKINSA : 209
5 - HIMMATUWA CIKIN SAUKE HAQQOQI 209
6 – JIMA'I 210
7 - ADO 213
8 – KAMEWA CIKIN MAGANA : 219
SHUGABANTAR IYALI 225
DALILAI DA SUKE SANYA DAWWAMAR AURE 227
1 – SON JUNA 228
2 – YAWAITA AIKATA ALHERI: 228
4 – SANYA FARIN CIKI: 229
5 – BIYAYYA DA NEMAN YARDAR MIJI: 230
6 – KIYAYE MUTUNCI DA DUKIYA : 230
7 – TAIMAKO DA TALLAFAWA 230
8 – TARBAR MIJI DA KYAWUNTA BANKWANA DA SALLAMA : 231
9 – KALAMIN AQIDOJI MAI KYAWU DA QARFAFAFFEN FURUCI. 232
10 – KARBAR UZURI DA YIWA JUNA UZURI : 232
11 – BINSU SANNU SANNU CIKIN KOWANNE HALI : 233
12 – KYAWUNTA LAFAZI CIKN KOWANNE YANAYI : 233
13 – RASHIN SAURARON KYAUTATA AIKI DARI BISA DARI 233
14 – RASHIN IKON DAUKAR NAUYI A RAYUWANCE : 234
15 – RASHIN GORI KAN MIJI : 234
16 – RASHIN QAURACEWA AL'AMARIN SHIMFIDA: 235
17 - YIN SHAWARA DA MATA BANDA BIYE MUSU: 235
18 – TAKA TSAN TSAN DA KUMA FARKAWA : 238
19 – HANKALTA 239
20 - MIJI SHI NE MUTUNCIN MATARSA 240
21 – KISHI 240
22 – TAIMAKEKENIYYA 242
23 – DADADAWA IYALI 243
27 – WATSI DA BOAKANCI DA TSAFE TSAFE : 244
28 - HIDIMA MADAWWAMIYA 245
29 – GODIYA 246
29 – QAUNAR JUNA 247
TSINTUWA GUDA BIYU GIDAN ALI DA FATIMA (AS) 248
■ FASALI NA 8 252

AUREN WURI 134

                                         AUREN  WURI

ra'ayoyi sun sassaba cikin auren wuri musammama cikin wannan zamani da muke ciki mai cike da duhu, cikinsu akwai wadanda suke maraba da yin hakan da kwadaitar da yinsa, akwai kuma wanda basu madalla da hakan saboda dalilin rashin nunar tunani da matsaltsalin tattalin arziqi , duk da cewa an samu cigaban ilimi cikin fasaha da qere qere da harkokin sadarwa na yanar gizo (internet) duniya ta wayi gari `yar qaramar alqarya ta hanyar komfuta, sa dai cewa dabi'u sun gurbata hanakali ya tabarbara ta rasa dacewarta, matasa sun wayi gari cikin rudewa da firgiciwa basu samma me za su yi ba, ire irensu ba su tafiyar da gida da kiyaye haqqoqin mace da `ya`ya …

a ganina addinin muslunci shi ne addini madawwami dokokinsa da hukunce hukuncensa na har abada ne. ba su taqaita da wani zamani ko wata qasa ba. su tafiya da kowacce al'umma da kowanne irin zamani, amma gigita da firgitar da matasa suka samu kansu ciki ya faru ne sakamakon nisansu daga addini da kyawawan dabi'u, da za mu koma ga addini da alqur'ani mai girma da tsatso mai tsarki  da mun hau jirgin tsira, da munyi birki baqin gabar kogin nutsuwa da razikqi da lafiya.

muslunci ya na ganin kyawun auren wuri ga mace da namiji, yana hakan na daga cikin azurta.

عن النبي ص, قال: من سعادة الرجل أن لا تحيض ابنته في بيته

1- daga manzon Allah (saw) ya ce: na daga cikin azurtar mutum a ce `yarsa ba ta fara jinin al'ada ba a gidansa.

عن الإمام موسى بن جعفر ع, عن آباءه ع, عن النبي ص, قال: ما من شاب تزوج في حداثته سنه الا عج شيطانه: يا ويله, عصم مني ثلثي دينه, فليتقي العبد في الثلث الباقي

2- daga imam musa dan jafar (as) daga babanninsa (as) daga manzon Allah (saw) ya ce : babu wani saurayi da zai aure cikin samartakarsa face shaidan ya daga sautinsa yana cewa : wayyo kaina wayyo ni , ya katange dayan ukun addininsa daga sharrina , bawa ya ji tsoron Allah cikin kason da ya rage.

عن النبي ص, قال: من حق الولد على والده ثلاثة: يحسن اسمه, ويعلمه الكتابة, ويؤوجه اذا بلغ.

3- daga annabi (saw) ya ce: daga haqqin da kan mahaifinsa abubuwa uku : ya kyawunta sunansa, ya koya masa rubutu, ya aurar da shi idan ya balaga.

Auren wuri na da kyawu da amfani, na'am ya zama wajibi kada a bude zuciyar budurwa ga wani mutum face mijinta wanda za ta rayu tare da shi wani yanki na rayuwa ya zama rayuwarta ba cutuwa da tuna baya ba, hakan bai tabbatuwa face ta hanyar yin auren wuri wanda za ta bare kayan marmarin `yan matancinta cikin rayuwar aure qarqashin rufin sheqa azurtacciya.

amma budurwar da take bude rayuwarta da soyayyar samari da kai kawo tsakaninsu, bayan haka ba za ta taba iya jin dadin da amfana da tsarkakakken mutumtacciyar soyayya ba, budurwa nawa ce ta bata rayuwarta kan hannun miyagun samari daga samarin wannan zamani, za su dinga nuna mata suna sonta suyi ta yi mata alqawarin aure amma suqi cika mata wannan alqawarin, wasu cikinsu kan karbar hotonta zamanin da suke tare, bayan tayi aure su fito da wannan hoto wani lokutan sukan aikawa mijinta wannan hoton suyi sanadiyar mutuwar aurenta.

kai kace al'umma sun zaba mace hanyoyi biyu da ba su  da na uku, ko dai jahilci madawwami, ko kuma fadawa halaka, saboda haka nake aika kurarin taimako ya zuwa qasashen muslunci da iyaye maza da mata da matasa maza da mata don kubuta daga fadawa halaka da gina al'umma: a rungumi auren wuri  ayi watsi da tsadar sadaki haqiqa aure wuri shi ne mafi alherin hanyar tsira.[1][1] AZZIWAJ FIL ISLAM:77