فهرست کتاب‌‌ لیست کتاب‌ها
■ KALMAR TARBIYYA CIKIN HARSHEN LARABCI DA YANDA AKA YI 4
■ FASALI NA ( 2 ) 24
■ AUREN DABI'A 24
■ FASALI NA 3
■ FASALI NA 4 73
■ FASALI NA 5 131
■ FASALI NA 6 176
HAQQOQIN DA MA'AURATA SU KAYI TARAYYA CIKI 177
1 – HAQURI 178
2 – KAMEWA DAGA ZALUNCI DA CUATARWA 179
HAQQOQIN MATA 180
CIYARWA DA YALWATAWA 185
TAUSAYAWA DA KAMEWA DAGA ZALUNCI 187
KAMEWA DAGA BARIN DUKA MAI CUTARWA 187
UMARNI DA KYAKKYAWA DA HANI DA MUMMUNA 193
GARKUWA 196
8 – KYAUTATAWA : 196
9 - KYAWUNTA ZAMANTAKEWA 197
3 – TAUSAYAWA MIJI : 208
4 – HIMMATUWA DA KULA DA CIKIN GIDA DA KAYYAKINSA : 209
5 - HIMMATUWA CIKIN SAUKE HAQQOQI 209
6 – JIMA'I 210
7 - ADO 213
8 – KAMEWA CIKIN MAGANA : 219
SHUGABANTAR IYALI 225
DALILAI DA SUKE SANYA DAWWAMAR AURE 227
1 – SON JUNA 228
2 – YAWAITA AIKATA ALHERI: 228
4 – SANYA FARIN CIKI: 229
5 – BIYAYYA DA NEMAN YARDAR MIJI: 230
6 – KIYAYE MUTUNCI DA DUKIYA : 230
7 – TAIMAKO DA TALLAFAWA 230
8 – TARBAR MIJI DA KYAWUNTA BANKWANA DA SALLAMA : 231
9 – KALAMIN AQIDOJI MAI KYAWU DA QARFAFAFFEN FURUCI. 232
10 – KARBAR UZURI DA YIWA JUNA UZURI : 232
11 – BINSU SANNU SANNU CIKIN KOWANNE HALI : 233
12 – KYAWUNTA LAFAZI CIKN KOWANNE YANAYI : 233
13 – RASHIN SAURARON KYAUTATA AIKI DARI BISA DARI 233
14 – RASHIN IKON DAUKAR NAUYI A RAYUWANCE : 234
15 – RASHIN GORI KAN MIJI : 234
16 – RASHIN QAURACEWA AL'AMARIN SHIMFIDA: 235
17 - YIN SHAWARA DA MATA BANDA BIYE MUSU: 235
18 – TAKA TSAN TSAN DA KUMA FARKAWA : 238
19 – HANKALTA 239
20 - MIJI SHI NE MUTUNCIN MATARSA 240
21 – KISHI 240
22 – TAIMAKEKENIYYA 242
23 – DADADAWA IYALI 243
27 – WATSI DA BOAKANCI DA TSAFE TSAFE : 244
28 - HIDIMA MADAWWAMIYA 245
29 – GODIYA 246
29 – QAUNAR JUNA 247
TSINTUWA GUDA BIYU GIDAN ALI DA FATIMA (AS) 248
■ FASALI NA 8 252

HUDUBA 136

HUDUBA                                          

 na daga cikin hukunce hukuncen aure na mustahabbi cikin shari'ar muslunci tsarkakkiya gabanin daura aure, ma'ana karanta sigar aure da karba daga janibi mai aura kamar yadda da sannu zamu kawo haka, huduba na nufin mai daura aure ya ambato wasu faloli da darajojin yin aure daga qur'ani da hadisi, da kwadaitar da yinsa.

haqiqa huduba mai daraja ta zo daga annabi (saw) da a'imma tsarkaka cikin wannan babi:

  وخطب أبو طالب لمّـا تزوّج النبيّ (صلى الله عليه وآله) بخديجة بنت خويلد بعد أن خطبها من أبيها ـ  ومن الناس من يقول إلى عمّها  ـ فأخذ بعضادتي الباب ومن شاهد من قريش حضور ، فقال  : « الحمد لله الذي جعلنا من زرع إبراهيم (عليه السلام)وذرية إسماعيل (عليه السلام) ، وجعل لنا بيتاً محجوباً وحرماً آمناً (  يُجْبَى إلَيْهِ ثَمَرَاتُ كُلِّ شَيْء  )[1] ، وجعلنا الحكّام على الناس في بلدنا الذي نحن فيه ، ثمّ إنّ ابن أخي هذا محمّد بن عبد الله بن عبد المطّلب لا يوزن برجل من قريش إلاّ رجح به ، ولا يقاس به أحد وإن كان في المال قلّ ، فإنّ المال رزق حائل وظلّ زائل ، وله في خديجة رغبة ولها فيه رغبة ، والصداق ما شئتم عاجلة وآجلة من مالي ، وله خطر عظيم وشأن رفيع ولسان شافع جسيم ، فزوّجه ، ودخل بها من الغد

1-      abu dalib ya yi huduba lokacin da annabi (as) ya auri nana khadija (rd) bayan ya nemi aureanta daga mahaifinta, wasu kuma sunce daga wajen baffanta – sai abu dalib ya dafa gefan qofa tareda wanda suka halarta daga quraishawa, ya ce: godiya ta tabbata ga Allah wanda ya sanya mu daga zuriyar Ibrahim (as) da isma'il ya sanya mana gida hijabantacce da harami amintacce:

ana jawowa gareshi `ya`yan itace  kowanne iri.

Ya sanya mu hakimai kan mutane cikin garinmu wanda muke ciki, sannan dan dan'uwana muhammadu dan Abdullah dan abdul-mudallib ba'a auna shi da kowa cikin quraishawa face ya rinjaye shi, ba 'a qiyasta shi da kowa duk da cewa yanada karancin kudi, haqiqa kudi  da arziki masu katangewa inuwa ce mai gushewa, ya na da kwadayi cikin Khadija ita ma tana da kwadayi cikinsa, sannan sadaki duk yadda ku ka so nan take lakadan ba ajalan ba ko kuma bashi to ni zanbiya, shi ya na da muhimmanci da sha'ani madaukaki, da harshe mai warkarwa mai girma, sai ya daura masa aure da ita, washe gari suka tare.

ويستحبّ أن يخطب بخطبة الرضا (عليه السلام) تبرّكاً بها ، لأ نّها جامعة في

معناها ، وهي  : الحمد لله الذي حمد في الكتاب نفسه ، وافتتح بالحمد كتابه ، وجعله أوّل محلّ نعمته وآخر جزاء أهل طاعته ، وصلّى الله على محمّد خير بريّته ، وعلى آله أئمة الرحمة ومعادن الحكمة ، والحمد لله الذي كان في نبئه الصادق وكتابه الناطق ، إنّ من أحقّ الأسباب بالصلة ، وأولى الاُمور بالتقدمة ، سبباً أوجب نسباً ، وأمراً أعقب حسباً ( غنىً ) فقال جلّ ثناؤه 

2- mustahabbi ne ayi huduba da hudubar imam rida (as) don neman albarkarta, saboda ta tattaro ma'ana itace kamar haka: godiya ta tabbata ga Allah wanda ya godewa kansa cikin littafinsa, ya bude littafinsa da godiya, ya sanya shi mahallin farko na ni'imarsa ya sanya shi qarshen sakamakon da'arsa, amincin Allah ya tabbata ga muhammadu mafi alherin halittu da iyalasana jagororin rahama ma'adinan hikima, godiya tabba ga wanda ya kasance mai gaskiya cikin labarinsa, da littafinsa mai magana, haqiqa daga mafi gasgatuwa sabubba da sadar da zumunci, mafi cancantar lamurra da gabata, sababi da ya kawo nasaba, al'amari da ya bar matsayi.

Ubangiji ya na cewa:

وَهُوَ الَّذِي خَلَقَ مِنَ المَاءِ بَشَراً فَجَعَلَهُ نَسَباً وَصِهْراً وَكَانَ رَبُّكَ قَدِيرا[2]ً 

  shi ne wanda ya halicci mutum daga ruwa ya sanya shi nasaba da suruki ubangiji ya kasance mai iko.

 wani wajen kuma ya ce:

وَأنكِحُوا الأيَامَى مِنْكُمْ وَالصَّالِحِينَ مِنْ عِبَادِكُمْ وَإمَائِكُمْ إنْ يَكُونُوا فُقَرَاءَ يُغْنِهِمُ اللهُ مِنْ فَضْلِهِ وَاللهُ وَاسِعٌ عَلِيم[3]ٌ 

 ku aurar da mata marasa mazaje da salihai daga bayinku  da kuyanginku idan sun kasance talakawa Allah zai wadatasu daga falalarsa.

ومن الخطب الشريفة  : لمّـا تزوّج أبو جعفر محمّد بن عليّ الرضا (عليه السلام)ابنة المأمون خطب لنفسه ، فقال  : « الحمد لله متمّم النعم برحمته ، والهادي إلى شكره بمنّه ، وصلّى الله على محمّد خير خلقه الذي جمع فيه من الفضل ما فرّقه في الرسل قبله ، وجعل تراثه إلى من خصّه بخلافته وسلّم تسليماً . وهذا أمير المؤمنين زوّجني ابنته ـ  قال أمير المؤمنين لمخاطبة الناس إيّاه بذلك لا لما هو الواقع ، فإنّ  المأمون أمير الفاسقين كما يشهد بذلك التأريخ الصحيح  ـ على ما فرض الله عزّ وجلّ للمسلمات على المؤمنين من (  فَإمْسَاكٌ بِمَعْرُوف أوْ تَسْرِيحٌ بِإحْسَان  )[4] ، وبذلت لها من الصداق ما بذله رسول الله (صلى الله عليه وآله) لأزواجه وهو اثنتا  عشرة أوقية ونشّ ( الأوقية عندهم أربعون درهماً ، والنش  : النصف من كلّ شيء ) على تمام الخمسمائة ، وقد نحلتها من مالي مئة ألف درهم ، زوّجتني يا  أمير المؤمنين  ؟ قال  : بلى . قال  : قبلت ورضيت

3-daga cikin hudubobi masu daraja yayin da baban jafar muhammadu dan aliyu rida (as) ya auri `yar mamun abbasi ya yiwa kansa huduba ya ce: godiya ta tabbata ga mai cika ni'imomi da rahamarsa, mai shiryarwa ya zuwa gode masa da tautatyinsa  amincin Allah ya tabbata ga mafi alherin halittarsa wanda ya tattara falala cikinsa wacce ya rarraba ta cikin manzanni gabaninsa, ya sanya gadonsa  zuwa ga wanda ya kebance shi da halifancinsa ka sallama sallamawa. wannan sarkin muminai ya aurar mini da `yarsa  imam ya kira shi ne kamar yadda mutane ke kiransa ba bisa cancanta da sarkin muminai saboda shi sarki fasiqaine kamar yadda ingantaccen tarihi ya tabbatar da fasiqancinsa.

Imam ya bata sadaki da dirhami dari hudu da tamanin.

ومن الخطب  : خطبة الإمام محمّد التقي (عليه السلام) عند تزويجه بنت  المأمون  : الحمد لله إقراراً بنعمته ، ولا إله إلاّ الله إخلاصاً بوحدانيّته ، وصلّى الله على محمّد سيّد بريّته ، وعلى الأصفياء من عترته ، أمّا بعد فقد كان من فضل الله على الأنام أن أغناهم بالحلال عن الحرام ، فقال سبحانه  : (  وَأنكِحُوا الأيَامَى مِنْكُمْ وَالصَّالِحِينَ مِنْ عِبَادِكُمْ وَإمَائِكُمْ إنْ يَكُونُوا فُقَرَاءَ يُغْنِهِمُ اللهُ مِنْ فَضْلِهِ وَاللهُ وَاسِعٌ عَلِيمٌ  )[5] ، ثمّ إنّ محمّد بن عليّ بن موسى يخطب اُمّ الفضل ابنة عبد الله المأمون وقد بذل لها من الصداق مهر جدّته فاطمة (عليها السلام) بنت محمّد (صلى الله عليه وآله) وهو خمسمائة درهم جياداً ، فهل زوّجتني يا أمير المؤمنين بها على الصداق المذكور  ؟ قال المأمون  : نعم قد زوّجتك يا أبا جعفر اُمّ الفضل بنتي على الصداق المذكور ، فهل قبلت النكاح  ؟ قال أبو جعفر (عليه السلام)  : نعم قبلت النكاح ورضيت به

4-daga cikin hudubobi hudubar imam mammadu taqiyu (as) locin da ya auri diyar mamun abbasi. Yace: godiyaya ta tabbata ga Allah bisa iqrari da ni'imarsa, babu abin baitawa da gaskiya sai Allah bisa tace ga dayantarsa. Tsira da aminci su taabbata ga muhammadu shugaban dukkanin halittu da zababbu daga tsatsonsa , bayan haka aqiqa fala ta kasance ga gabadayan halittu ta yanda ubangiji ya wadata su da halaliya ga barin haram, ubangiji matsarkaki ya na cewa: ku aura daga marasa auren cikinku da nagargaru daga bayinku idan sun kasance talakawa Allah zai wadata su daga falalrsa. Sannan lalle muhammadu dan Aliyu dan musa ne neman auren ummu fadalu diyar abdullahi mamun kuma haqiqa ya bata sadakinta daga sadakin kakarsa matar sarkin muminai aliyu dan abi dalibi(as) sadakin nata kuwa shine dirhami dari biyar, shin ya sarkin mumini abdullahi mamun ka aura mini diyar taka kan sadakin da na ambata? sai mamun ya ce: na yarda  haqiqa na aura maka ita ya baba jafar. Sai imam yace: na'am ta karba ta kuma yarda.

من أمالي السيّد أبي طالب الهروي ، عن زين العابدين (عليه السلام) ، قال  : خطب النبيّ (صلى الله عليه وآله) حين زوّج فاطمة (عليها السلام) من عليّ (عليه السلام) ، فقال  : الحمد لله المحمود بنعمته ، المعبود بقدرته ، المطاع بسلطانه ، المرهوب من عذابه وسطوته ، المرغوب إليه فيما عنده ، النافذ أمره في سمائه وأرضه ، ثمّ إنّ الله عزّ وجلّ أمرني أن اُزوّج فاطمة من عليّ بن أبي طالب ، فقد زوّجته على أربعمائة مثقال فضّة ، إن رضي بذلك عليّ ، ثمّ دعا (صلى الله عليه وآله) بطبق من بُسر ، ثمّ قال  : انتهبوا ، فبينا ننتهب إذ دخل عليّ  (عليه السلام) فتبسّم النبيّ (صلى الله عليه وآله) في وجهه ، ثمّ قال  : يا عليّ ، أعلمت أنّ الله عزّ وجلّ أمرني أن اُزوّجك فاطمة ، فقد زوّجتكها على أربعمائة مثقال فضّة إن رضيت ، فقال عليّ (عليها السلام)  : رضيت بذلك عن الله وعن رسوله ، فقال النبيّ (صلى الله عليه وآله)  : جمع الله شملكما ، وأسعد جدّكما ، وبارك عليكما ، وأخرج منكما كثيراً طيّباً

  

5- daga amali na sayyid abu dalib harawi, daga zainul-abideen (as) ya ce: manzon Allah (saw) ya karanta huduba lokacinta da ya aurar da fatima (as)  ga ali (as) sai ya ce: godaya ta tabbata ga Allah abin godewa da ni'imarsa, abin bautawa da ikonsa, mai zartar da al'amarinsa cikin sama da qasa, wanda ake yiwa biyayya da mulkinsa,    wanda ake tsoron azabarsa da damqarsa, wanda ake kwadayin abin wajensa, sannan haqiqa Allah mai girma da daukaka ya umarceni da aurar da Fatima ga aliyu (as) lalle na aurar da ita bisa sadaki misqali dari hudu na azurfa, idan aliyu (as) ya yarda da haka, sai manzon Allah (saw) ya sa aka kawo tire din danyan dabino, ya ce: ku diba yayin da mu ke diba sai ga ali (as) ya shigo  sai annabi (saw) ya yi murmushi,  ya ce:  Allah ya umarceni da aura maka Fatima na aura maka ita kan sadaki misqali dari hudu na azurfa amma fa idan ka aminta da hakan, sai aliyu (as) ya ce na aminta na yarda da hakan daga Allah madaukaki da manzonsa, sai annabi (saw) ya ce: Allah ya dinke barakarku ya azurta qoqarinku, ya albarkanceku. Allah ya fitar da tsarkaka masu tarin yawa daga gareku.

عن الرضا ، عن آبائه ، عن أمير المؤمنين (عليهم السلام) ، قال  : ويوم الجمعة يوم خطبة ونكاح

6-dag rida (as) daga babanninsa (as) daga sarkin muminai ali (as) ya ce: ranar juma'a rana ce da ta dace da hudubar da daurin aure.

Kafin daura aura da huduba an halasta me nema ya kalli wanda ya ke neman aurenta ya ji muryarta don sanin gwargwadon hankalinta iliminta da wayewarta, saboda haka ya halasta ya kalli hatta fuskarta ya dubi hannuwanta da  qafafunta yayinda ta ke tattakawa gabansa  haqiqa lokacin da mugira dan shu'uba ya nemi auren wata mata annabi (saw) ya ce masa: ka kalleta haqiqa hakan ya fi dacewa da samun daidaito tsakaninku.

lokacin neman aure lokaci ne muqaddima don su samu fuskantar juna, saboda ya zama wajibi kowanne dayansu ya kiyaye iyakar da muslunci ya iyakance masa kada a sakar musu ragama su ta haduwa da ganin juna yadda ransu ke so, kadai dai an halasta musu hakan ne don gudun kada ya zamanto daren angonci ya zo musu bagatatan ba tare da sun wayi juna ba, saboda haka babu taqaitawa babu wuce dan makadi.

 

 عَنْ مُحَمَّدِ بْنِ مُسْلِمٍ قَالَ: سَأَلْتُ أَبَا جَعْفَرٍ ع عَنِ الرَّجُلِ يُرِيدُ أَنْ يَتَزَوَّجَ الْمَرْأَةَ أَ يَنْظُرُ إِلَيْهَا قَالَ نَعَمْ إِنَّمَا يَشْتَرِيهَا بِأَغْلَى الثَّمَن[6]

7-daga muhammadu dan muslim, ya ce: na tamabayi baban jafar (as) game da mutumin da ya nufi aurar mace shin zai iya kallonta? sai ya ce: na'am haqiqa zai sayeta da mafi tsadar farashi.

عن أبي عبد الله (عليه السلام) ، قال  : لا بأس أن ينظر إلى وجهها ومعاصمها إذا أراد أن يتزوّجها

8-daga baban abdullah (as) ya ce : babu laifi kallon fuskarta da tsintsiyar hannunta idan ya yi nufin aurenta.

عن أبي عبد الله (عليه السلام) ، قال  : قلت  : أينظر الرجل إلى المرأة يريد

تزويجها فينظر إلى شعرها ومحاسنها  ؟ قال  : لا بأس بذلك إذا لم يكن متلذّذ

9- daga bana Abdullah(as)ya ce: na ce: shin ya halasta mutum ya kalli matar da zai aura ya na iya kallon gashinta da surarta? Sai ya e babu matsala ikin hakan matukar bai nufin niyyar jin dadi ba

عَنْ يُونُسَ بْنِ يَعْقُوبَ قَالَ: سَأَلْتُ أَبَا عَبْدِ اللَّهِ ع عَنِ الرَّجُلِ يُرِيدُ أَنْ يَتَزَوَّجَ الْمَرْأَةَ وَ أَحَبَّ أَنْ يَنْظُرَ إِلَيْهَا قَالَ تَحْتَجِزُ «2» ثُمَّ لْتَقْعُدْ وَ لْيَدْخُلْ فَلْيَنْظُرْ قَالَ قُلْتُ: تَقُومُ حَتَّى يَنْظُرَ إِلَيْهَا قَالَ نَعَمْ قُلْتُ فَتَمْشِي بَيْنَ يَدَيْهِ قَالَ مَا أُحِبُّ أَنْ تَفْعَلَ

10-daga yunsu dan yaqub, ya ce: na tambayi baban abdullah (as) game da mutumin da yay i niyyar auren mace sai ya so kallonta ? sai imam ya ce: ta lulluba mayafi  sannan ta tsuguna sai shi kuma ya shiga ya kalleta, sai na ce: tana iya miqewa tsaye ya kalleta ? sai ya ce: na'am,  sai na ce : tana iya tattakawa gabansa ? sai ya ce: bani son ta aikata hakan.

ya zo cikin littafin mahaifin allama majilisi mai suna (jinsani ) qarqashin taken huduba  ya ce:  na daga abin da ka sallamawa shi ne cewa karanta hudubar gabatar daura aure, gwargwadon yanda aka saba, bai dace mutum ya sabawa haka kamar ya kamata ayi a bayyane domin yi a boye ana iya samun afkuwar abinda bai da ce ba .

 

Alqur'ani mai girma ya koya mana yadda za ai nema cikin taqaitattun jumloli:

 وَلا جُنَاحَ عَلَيْكُمْ فِيَما عَرَّضْتُمْ بِهِ مِنْ خِطْبَةِ النِّسَاءِ أوْ أكْنَنتُمْ فِي أنفُسِكُمْ عَلِمَ اللهُ  ) إلى قوله تعالى  : (  وَاعْلَمُوا أنَّ اللهَ غَفُورٌ حَلِيم[7]   

 babu laifi kanku cikin abin da kuka bijiro da shi daga neman aure ko kuma abin da ku boye cikin zukatanku Allah ya san lalle ne zaku gaya musu ) – (ku sani haqiqa Allah mai yawan gafara ne mai haquri.[1] Alqasas:57

[2] Furqan:54

[3] Nurr:32

[4] Baqara:229

[5] Nurr:32

[6] Wasa'ilul shi'a m 20 sh 88

[7] Baqara:235