فهرست کتاب‌‌ لیست کتاب‌ها
■ KALMAR TARBIYYA CIKIN HARSHEN LARABCI DA YANDA AKA YI 4
■ FASALI NA ( 2 ) 24
■ AUREN DABI'A 24
■ FASALI NA 3
■ FASALI NA 4 73
■ FASALI NA 5 131
■ FASALI NA 6 176
HAQQOQIN DA MA'AURATA SU KAYI TARAYYA CIKI 177
1 – HAQURI 178
2 – KAMEWA DAGA ZALUNCI DA CUATARWA 179
HAQQOQIN MATA 180
CIYARWA DA YALWATAWA 185
TAUSAYAWA DA KAMEWA DAGA ZALUNCI 187
KAMEWA DAGA BARIN DUKA MAI CUTARWA 187
UMARNI DA KYAKKYAWA DA HANI DA MUMMUNA 193
GARKUWA 196
8 – KYAUTATAWA : 196
9 - KYAWUNTA ZAMANTAKEWA 197
3 – TAUSAYAWA MIJI : 208
4 – HIMMATUWA DA KULA DA CIKIN GIDA DA KAYYAKINSA : 209
5 - HIMMATUWA CIKIN SAUKE HAQQOQI 209
6 – JIMA'I 210
7 - ADO 213
8 – KAMEWA CIKIN MAGANA : 219
SHUGABANTAR IYALI 225
DALILAI DA SUKE SANYA DAWWAMAR AURE 227
1 – SON JUNA 228
2 – YAWAITA AIKATA ALHERI: 228
4 – SANYA FARIN CIKI: 229
5 – BIYAYYA DA NEMAN YARDAR MIJI: 230
6 – KIYAYE MUTUNCI DA DUKIYA : 230
7 – TAIMAKO DA TALLAFAWA 230
8 – TARBAR MIJI DA KYAWUNTA BANKWANA DA SALLAMA : 231
9 – KALAMIN AQIDOJI MAI KYAWU DA QARFAFAFFEN FURUCI. 232
10 – KARBAR UZURI DA YIWA JUNA UZURI : 232
11 – BINSU SANNU SANNU CIKIN KOWANNE HALI : 233
12 – KYAWUNTA LAFAZI CIKN KOWANNE YANAYI : 233
13 – RASHIN SAURARON KYAUTATA AIKI DARI BISA DARI 233
14 – RASHIN IKON DAUKAR NAUYI A RAYUWANCE : 234
15 – RASHIN GORI KAN MIJI : 234
16 – RASHIN QAURACEWA AL'AMARIN SHIMFIDA: 235
17 - YIN SHAWARA DA MATA BANDA BIYE MUSU: 235
18 – TAKA TSAN TSAN DA KUMA FARKAWA : 238
19 – HANKALTA 239
20 - MIJI SHI NE MUTUNCIN MATARSA 240
21 – KISHI 240
22 – TAIMAKEKENIYYA 242
23 – DADADAWA IYALI 243
27 – WATSI DA BOAKANCI DA TSAFE TSAFE : 244
28 - HIDIMA MADAWWAMIYA 245
29 – GODIYA 246
29 – QAUNAR JUNA 247
TSINTUWA GUDA BIYU GIDAN ALI DA FATIMA (AS) 248
■ FASALI NA 8 252

SADAKI 142

SADAKI                                                        

Daga cikin abubuwan da ke wajaba cikin aure akwai sadaki, aure bai tabbatuwa face dashi, ko da kuwa kadanne.

Ubangiji madaukaki na cewa:

وَآ تُوا النِّسَاءَ صَدُقَاتِهِنَّ نِحْلَةً فَإنْ طِبْنَ لَكُمْ عَنْ شَيْء مِنْهُ نَفْساً فَكُلُوهُ هَنِيئاً مَرِيئا[1] 

1 ku baiwa mata sadakokinsu kuna masu saukakawa bayarwa idan suka ya fe muku wani daga gare shi to ku I da dadi.

 

قَالَ إنِّي اُرِيدُ أنْ اُنكِحَكَ إحْدَى ا بْنَتَيَّ هَاتَـيْنِ عَلَى أنْ تَأجُرَنِي ثَمَانِيَةَ حِجَج فَإنْ أتْمَمْتَ عَشْراً فَمِنْ عِنْدِكَ وَمَا اُرِيدُ أنْ أشُقَّ عَلَيْكَ سَتَجِدُنِي إنْ شَاءَ اللهُ مِنَ الصَّالِحِينَ * قَالَ ذَلِكَ بَـيْنِي وَبَـيْنَكَ أيَّمَا الأجَلَيْنِ قَضَيْتُ فَلا عُدْوَانَ عَلَيَّ وَاللهُ عَلَى مَا نَقُولُ وَكِيل[2]

1-      ( sai ya ce haqiqa ni inason in aurar maka daya daga cikin wadannan `ya`yana biyu  bisa sharadin za kayi mini kodago shekaru takwas idan ka ciga goma to wanne daga gareka ne ban a nufin tsananta maka, da sannu da yardarm Allah  za ka sameni daga salihai * sai ya ce wadancananka tsakanina da kai kowanne daya daga ajalin biyu na qare babu zalunci kaina, Allah ne wakili kan abin da mu ke fadi.

وَلِلْمُطَلَّقَاتِ مَتَاعٌ بِالمَعْرُوفِ حَقّاً عَلَى المُتَّقِينَ 

2-      Wanda aka saki suna da dadadawa gwargwadon. Hakan wajibi kan mu taqawa.

لا جُنَاحَ عَلَيْكُمْ إنْ طَلَّقْتُمُ النِّسَاءَ مَا لَمْ تَمَسُّوهُنَّ أوْ تَفْرِضُوا لَهُنَّ فَرِيضَةً وَمَتِّعُوهُنَّ عَلَى المُوسِعِ قَدَرُهُ وَعَلَى المُقْتِرِ قَدَرُهُ مَتَاعاً بِالمَعْرُوفِ حَقّاً عَلَى المُحْسِنِينَ * وَإنْ طَلَّقْتُمُوهُنَّ مِنْ قَبْلِ أنْ تَمَسُّوهُنَّ وَقَدْ فَرَضْتُمْ لَهُنَّ فَرِيضَةً فَنِصْفُ مَا فَرَضْتُمْ إلاَّ أنْ يَعْفُونَ أوْ يَعْفُوَ الَّذِي بِيَدِهِ عُقْدَةُ النِّكَاحِ وَأنْ تَعْفُوا أقْرَبُ لِلتَّقْوَى وَلا تَنسَوْا الفَضْلَ بَيْنَكُمْ إنَّ اللهَ بِمَا تَعْمَلُونَ بَصِير[3]ٌ

3-      ga matayen da aka sake su jiyar da su dadi da alheri wannan haqqin kan masu taqawa.

4-       ( babu laifi kanku idan kuka saki mata gabanion shafasu  kuma baku basu sadaki  ba  , ku jiyar da su dadi kan mai wadata gwargawadon ikonsa , kan mra wadata gwargwadonsa domin dadadawa da alheri haqqi ne kan masi ihsani * idan ku ka sakesu gabanin shafarsu  bayan kuma kun riga kun basu sadaki to kuna rabi daga sadakin , sai dai idan sunyi yafe ko kuma wanda igiyar aure ke hannunsa ya yafe , kuyi afuwa shi ya fi kusa da taqawa , kda ku manta falala tsakaninku haqiqa Allah masani ga abin da ku ke aikatawa.2

mustahabbi ne sadaki ya kasance kadan ya zamanto sadakin bai wuce sadakin sunna ba dirhami dari biyar daga azurfa, ana qaddara kimarsa cikin kowanne  zahirin lamari shi ne dirhami dari biyar a zamanin manzon Allah (saw) sh ine misqali dari hudu na azurfa.

عَنِ الصَّادِقِ عَنْ أَبِيهِ ع قَالَ: مَا زَوَّجَ رَسُولُ اللَّهِ ص شَيْئاً مِنْ بَنَاتِهِ وَ لَا تَزَوَّجَ شَيْئاً مِنْ نِسَائِهِ عَلَى أَكْثَرَ مِنِ اثْنَتَيْ عَشْرَةَ أُوقِيَّةً وَ نَشٍّ يَعْنِي نِصْفَ أُوقِيَّةٍ

.1- daga sadiq (as) daga babansa (as) ya ce: manzon Allah (saw) bai taba aurar da `yarsa kuma bai taba auri wata cikin matansa da sadaki fiye da auqiya shabiyu ba  da nishi, ma'ana dirhami dari biyar.

قال عليّ (عليه السلام)  : إنّي لأكره أن يكون المهر أقلّ من عشرة دراهم لكي لا يشبه مهر البغيّ

2- aliyu (as) ya ce: haqiqa ina qin cewa sadaki ya kasance qasa da dirhami goma, don gudun kada ya yi kama da ladan karuwa.

عن ابن بكير ، قال  : سمعت أبا عبد الله (عليه السلام) يقول  : زوّج رسول الله (صلى الله عليه وآله)علياً (عليه السلام) فاطمة صلوات الله عليها على درع له حطمية تسوي ثلاثين درهماً

3- daga baban bukair, ya ce: na ji baban Abdullah  (as) ya na cewa: manzon Allah (saw) ya aurawa  ali (as) Fatima (as) kan sadakin  sulke na qarfe wanda qimarsa ke daidai da dirhami talatin.

عن الحسين بن خالد ، قال  : سألت أبا الحسن (عليه السلام) عن مهر السنّة ، كيف صار خمسمائة درهم  ؟ فقال  : إنّ الله تبارك وتعالى أوجب على نفسه أن لا يكبره مؤمن مائة تكبيرة ويحمده مائة تحميدة ويسبّحه مائة تسبيحة ويهلّله مائة تهليلة ويصلّي على محمّد وآل محمّد مائة مرّة ثمّ يقول  : اللهمّ زوّجني من الحور العين ، إلاّ زوّجه الله حوراء من الجنّة وجعل ذلك مهرها ، فمن ثمّ أوحى الله عزّ وجلّ إلى نبيّه (صلى الله عليه وآله) أنّ يسنّ مهور المؤمنات خمسمائة درهم ففعل ذلك رسول الله (صلى الله عليه وآله[4]

4 daga husaini dan khalid, ya ce: na tambayi baban hassan (as) kan sadakin sunna, ta yaya ya zama dirhami dari biyar ? sai y ace: Allah  mai girma da daukaka ya wajabtawa kansa kasantuwar mumini yayi masa kabbara 100, tasbishi 100, hailala 100, hamdala 100,  salati 100, sannanan ya ce: Allah ka aura mini daga matan aljanna face Allah ya aura masa yasanya wannan wuridi da yayi matsayin sadakinta. sannan kuma Allah yayi wahayi ga annabinsa (as) da sunnanta sadakin muminai dirhami dari biyar, sai annabi (as) ya aikata hakan.

وفي خبر آخر  : وأيّما مؤمن خطب إلى أخيه حرمة ، وبذل له خمسمائة درهم فلم يزوّجه فقد عقّه واستحقّ من الله عزّ وجلّ ألاّ يزوّجه حوراء

5-      cikin wani hadisin babu wani mumini da zai nemi aure daga dan'uwansa kuma ya bashi dirhami dari biyar sannan ya qi aura masa  haqiqa ya sabawa Allah kuma ya cancanci Allah ya hana shi auren matan aljanna idan ya nema.

6-      عن الرضا (عليه السلام) ، أ نّه كتب إليه  : علّة المهر ووجوبه على الرجاللولا يجب على النساء أن يعطين أزواجهن ، قال  : لأنّ على الرجال مؤونة المرأة بايعة نفسها والرجل مشتر ، ولا يكون البيع بلا ثمن ولا الشراء بغير إعطاء الثمن ، مع أنّ النساء محظورات عن التعامل والمتجر ، مع علل كثيرة

7-daga imam rida (as) ai aiko masa da wasiqa: ana tambaya kan dalilin sadaki da wajabcinsa kan maza amma ba a wajabtwa mata su bawa maza ba, sai ya ce: saboda nauyin ciyarwa da tufatarwa na kan maza su mata masu siyarwa ne shi kuma namiji mai saya, sannan shi cinikayya bai yiwuwa ba tare da kudi ba, tare da cewa an hani yin mu'amala da kasuwanci  ga mata saboda dalilai masu yawa.

وروي في خبر آخر  : أنّ الصادق (عليه السلام) قال  : إنّما صار الصداق على الرجل دون المرأة وإن كان فعلهما واحداً ، فإنّ الرجل إذا قضى حاجته منها قام عنها ولم ينتظر فراغها ، فصار الصداق عليه دونها لذلك

8-an riwaito daga sadiq (as) ya ce: kadai dai dalilin da ya sanya aka dora sadaki kan namiji ba'a dora kan mace ba duk da cewa aikinsu daya ne, haqiqa namiji idan ya biya buqatartsa ta ke zai miqe  ya tafi ba tare da ya jira biyan tata buqatar ba, sai sadaki ya zama kan namiji sabanin mace.

Sannan mustahabbine mace ta yafewa mijinta sadakinta kamar yadda ya zo cikin nassoshinh shari'a.

الكافي بسنده ، عن أبي عبد الله (عليه السلام) قال  : قال النبيّ (صلى الله عليه وآله وسلم)  : أ يّما امرأة تصدّقت على زوجها بمهرها قبل أن يدخل بها إلاّ كتب الله لها بكلّ دينار عتق رقبة ، قيل  : يا رسول الله ، فكيف بالهبة بعد الدخول  ؟ قال  : إنّما ذلك من المودّة والاُلفة[5]

9- alkafi da isnadinsa daga baban Abdullah (as) ya ce: manzon Allah (saw) ya ce: duk macen da ta yafewa mijinta sadakinta gabanin tarawa da ita face Allah ya rubuta mata ladan `yantar da baiwa kan kowanne dinare.

Sadaki bashi ne kan wuyan miji idan bai bayar ba, bai halasata ba ya quduri niyyar ba zai ba ta ba.

عن الإمام الصادق (عليه السلام)  : من تزوّج امرأة ولم ينوِ أن يوفيها صداقها فهو عند الله عزّ وجلّ زان

1-      daga sadiq (as) duk wanda ya auri mace bai yi niyyar ba ta sadakinta ba, to shi a wajen Allah matsayin mazinaci ya ke.

وقال أبو عبد الله (عليه السلام)  : السرّاق ثلاثة  : مانع الزكاة ، ومستحلّ مهور النساء ، وكذلك من استدان ولم ينوِ قضاءه

2-      baban Abdullah(as) y ace  barayi uku suke: mai hana zakka, mai cinye sadaki, da kuma wanda ya ci bashi halin bai dauki niyyar biya ba.

وقال أمير المؤمنين (عليه السلام)  : إنّ أحقّ الشروط أن يوفي بها ما استحللتم به الفروج

13- sarkin muminai ali (as) : mafi cancantar cikawa daga sharudda shi ne wanda kuka halasta farji da shi.

Sunnar annabi muhammadu (saw) cikin sadaki shi ne dirhami dari biyar, dukkanin abinda mace ta sanya shi bashi daga sadakinta to ya na wuyan miji ya wajabta ya bata cikin tsawon rayuwarsa, idan kuma ya mutu to wajibi ne a fara cire mata sadakinta daga abin da ya bari  sannan duk abin da mijin ya bata matsayin sadaki ta yarda ta karba gabanin ya tara da ita to wannan shi ne sadakinta, idan mutum ya aurar da `yarsa ga wani a ka bada sadakinta to bai da haqqin cin sadakin ba da izininta ba.

عن النبيّ (صلى الله عليه وآله) ، قال  : من ظلم امرأة مهرها فهو عند الله زان ، يقول الله عزّ وجل يوم القيامة  : عبدي زوّجتك أمتي على عهدي فلم توفِ بعهدي وظلمت أمتي ، فيؤخذ من حسناته فيدفع إليها بقدر حقّها ، فإذا لم تبقَ له حسنة أمر به إلى النار بنكثه للعهد ، إنّ العهد كان مسؤولا

14 – daga annabi (saw) : duk wanda ya zalunci mace cikin sadakinta to shi mazinaci a wajen Allah, ranar qiyama Allah zai ce bawana na aura ma baiwata bisa alqawalina baka cika alqawalina ba, sai ka zalunci baiwata, sai a diba daga kyawawan ayyukansa gwargawadon haqqinta a miqa mata, idan kuma babu wani aiki kyawawa da ya rage masa, sai a kaishi wuta saboda sabawa alqawali, haqiqa alqwali abin tambya ne.

عن عمر بن يزيد ، قال  : قلت لأبي عبد الله (عليه السلام)  : أخبرني عمّن تزوّج على أكثر من مهر السنّة ، أيجوز له ذلك  ؟ قال  : إذا جاز مهر السنّة فليس هذا مهراً ، إنّما هو نحل ، لأنّ الله يقول  : (  وَآتَيْتُمْ إحْدَاهُنَّ قِنطَاراً فَلا تَأخُذُوا مِنْهُ شَيْئاً )[6] . إنّما عنى النحل ولم يعنِ المهر ، ألا ترى أ نّه إذا أمهرها ثمّ اختلعت كان لها أن تأخذ المهر كاملا ، فما زاد على مهر السنّة فإنّما هو نحل كما أخبرتك ، فمن ثمّ وجب لها مهر نسائها لعلّة من العلل ، قلت  : كيف يعطي وكم مهر نسائها  ؟ قال  : إنّ مهر المؤمنات خمسمائة وهو مهر السنّة ، وقد يكون أقلّ من خمسمائة ولا يكون أكثر من ذلك ، ومن كان مهرها ومهر نسائها أقلّ من خمسمائة اُعطي ذلك الشيء ، ومن فخر وبذخ بالمهر فازداد على خمسمائة ثمّ وجب لها مهر نسائها في علّة من العلل لم يزد على مهر السنّة خمسمائة درهم

15 – daga umar dan yazid, ya ce: na cewa baban Abdullah (as) ka bani labari gameda wanda ya yi aure kan sadaki fiye da na sunnan  shin haka ya halasta gareshi  ? sai imam (as) ya ce idan ya wuce sadakin sunna to wannan ba sadaki bane, kadai dai kyauta ce, saboda Allah na cewa:

  ku ka baiwa daya daga cikinsu dukiya mai tarin yawa to ka da ku ka karbi komai daga ciki.

 kadai dai yay i nufin kyauta ba sadaki ba, ashe bka gani ba idan ya yanka sadakinta ya bayar sannan ta yi kulu'i tana haqiin daukar sadaki baki daya  , duk abin da ya wuce daga sadakin sunna kyautace da ya bayar kamar yadda na fada maka a baya, dag nan kuma ya wajabta mata sadakin mata saboda wasu dalilai, sai na ce qaqa zai bayar, nawa ne sadakin mata ? sai ya ce:  haqiqa sadakin mata muminai shi ne dirhami dari biyar shi ne kuma sadakin sunna, wani lokacin kuma yakan kasance qasa da haka amma dai bai kasancewa sama hakan, duk wacce sadakinta da matan ya kasance qasa da dirhami dari biyar aka bada wannan abu daga alfahari da sadaki sai ya zamanto ya haura dirhami dari biyar, sannan ya wajabta mata sadakin mata saboda wani dalili daga dalilai, to ba zai qara sama da sadakin sunna dirhami dari biyar.

عن زرارة ، قال  : سألت أبا عبد الله (عليه السلام) عن رجل تزوّج امرأة أيحلّ له أن يدخل بها قبل أن يعطيها شيئاً  ؟ قال  : لا ، حتّى يعطيها شيئاً .

16 – daga zurara, na tambayi baban Abdullah  (as) game da mutumin da ya auri mace, shin ya halsta gareshi ya tara da ita kafin ba ta wani abu  ? sai ya ce : bai halasta har sai ya ba ta wani abu.

قال رسول الله (صلى الله عليه وآله)  : إنّ الله لمّـا خلق الدنيا لم يخلق فيها ذهباً ولا فضّة ، فلمّـا أن أهبط آدم وحوّاء أنزل معهما ذهباً وفضّة فسلكهما ينابيع في الأرض منفعة لأولادهما من بعدهما ، وجعل ذلك صداق آدم لحوّاء ، فلا ينبغي لأحد أن يتزوّج إلاّ بصداق  

17 – manzon Allah (saw) ya ce : haqiqa Allah lokacin da ya halicci duniya bai halicci zinariya da azurfa cikinta ba  , yayin da adamu da hauwa'u suka sauko sai suka taho tare da su sai suka sanya su cikn qasa su zama amfani ga `ya`yayensu bayansu  , ya sanya haka sadakin adamu ga hauwa'u, bai kamata wan ya yi aure face da sadaki ba.

عن أبي عبد الله (عليه السلام) ، قال  : إذا طلّق الرجل امرأته قبل أن يدخل بها فلها نصف مهرها ، وإن لم يكن سمّى لها مهراً فمتاع بالمعروف على الموسع قدره وعلى المقتر قدره وليس لها عدّة ، وتتزوّج من شاءت في ساعتها

17 – daga baban abullah (as ) ya ce : idan mutum ya saki matarsa gabanin shafarta  to ta na da rabin sadakinta, idan kuma bai ambata mata sadaki ba to ajiyar da ita dadi da alheri, mai yalwa gwargwadon yalwarsa, talaka gwargwadon ikonsa, sannan ba ta da yin idda, ta na iya auren wanda ta so nan take .

fiqihu rida :  duk wanda ya saki matarsa gabanin tarawa da ita to babu idda kanta , idan ya yanka mata sadaki to ta na da rabinsa, idan kuma bai yanka ba to ya jiyar da ita dadi kadn ko mai yawan gwargwadon ikonsa . idan ya kasanci yana da yalwa to ya jiyar da ita da hadimi ko wata dabba daga cikin dabbobinsa, idan kuma mai dan rufin asiri ne to ya ba ta tufafi, idan kuma talaka ne futik ya ba ta dirhami daya ko zoben qarfe, kamar yadda Allah madaukaki ke cewa: .

  ku jiyar da su dadi mayalwaci gwargwadon ikonsa talaka gwargwadon ikonsa dadi da alheri.

babu laifi cikin kasa sadaki zuwa kashi biyu kamar yadda yake cikin sashen qasashen larabawa, kason da za a bayar nan take da kuma kason da zai zama bashi, wanda aka bayar ta ke za a sayo mata kayayyakin amarci kuma su zama mallakarta, ragowar kuma ya zauna bashi kan wuyan ango har zuwa lokacin da zai biya ta, sannan mustahabbi ne ga mace ta yafewa mijinta sadaki saboda haqan na qara danqon zumunta da qauna.

عن الإمام الصادق (عليه السلام) ، عن آبائه (عليهم السلام) ، قال  : قال النبيّ (صلى الله عليه وآله)  : ما من امرأة تصدّقت على زوجها بمهرها قبل أن يدخل بها إلاّ كتب الله لها بكلّ دينار عتق رقبة ، قيل  : يا رسول الله ، فكيف الهمّة بعد الدخول  ؟ فقال  : إنّما ذلك من المودّة والاُلفة

18 – an karbom daga imam sadiq (as) daga babaninsa (as) ya ce: manzon Allah (saw) ya ce: babu wata mace da za tayi sadakar sadakinta ga mijinta gabanin tarawa da ita face Allah ya rubuta mata ladan `yantar da baiwa ga dukkanin dinare, sai aka tambayi manzon Allah (saw) yay a kuma himmatuwa bayan tarawa da ita, sai ya ce: kadai dai hakan na daga qauna da shaquwa.

Daga cikin abin da tsadar sadaki ke haifarwa shi ne gaba da qiyayya.

عن أمير المؤمنين عليّ (عليه السلام) ، قال  : لا تغالوا في مهور النساء فيكون عداوة

 19 – daga sarkin muminai ali (as) ya ce : ka da ku tsadanta sadakin matayenku  sai qiyayya ta kasance.

daga imam sadiq (as) shu'umanci mace na tare da tsadar sadakinta da sabawa mijinta.

عن الإمام الصادق (عليه السلام) ، قال  : أقذر الذنوب ثلاثة  : قتل البهيمة ، وحبس مهر المرأة ، ومنع الأجير أجره  

20- daga sadiq (as) mafi qazanta cikin zunubai uku ne : kashe dabba , danne sadaki mace, hana dan kwadago ladansa.

قال عليّ (عليه السلام) في قوله تعالى  : (  وَآ تُوا النِّسَاءَ صَدُقَاتِهِنَّ نِحْلَةً  )([216])  : أعطهن الصداق الذي استحللتم به فروجهن ، فمن ظلم المرأة صداقها الذي استحلّ به فرجها فقد استباح فرجها زناً .

21- imam ali (as) ya ce : cikin fadinsa madaukaki:

 

ku bawa mata sadakinsu sauqin bayarwa.

  ku basu sadakinsu da ku ka halasta farjinsu da shi, duk wanda ya zalunci mace cikin sadakinta da ya halasata farjinta da shi to haqiqa ya halasata farjintada zina.[1] Nisa'i:4

[2] Alqasas:27 28

[3] Baqara: 236 237

[4] Biharu anwar 100 sh 348

[5] Alwafi m 12  sh 519

[6] Nisa'i:20