فهرست کتاب‌‌ لیست کتاب‌ها
■ KALMAR TARBIYYA CIKIN HARSHEN LARABCI DA YANDA AKA YI 4
■ FASALI NA ( 2 ) 24
■ AUREN DABI'A 24
■ FASALI NA 3
■ FASALI NA 4 73
■ FASALI NA 5 131
■ FASALI NA 6 176
HAQQOQIN DA MA'AURATA SU KAYI TARAYYA CIKI 177
1 – HAQURI 178
2 – KAMEWA DAGA ZALUNCI DA CUATARWA 179
HAQQOQIN MATA 180
CIYARWA DA YALWATAWA 185
TAUSAYAWA DA KAMEWA DAGA ZALUNCI 187
KAMEWA DAGA BARIN DUKA MAI CUTARWA 187
UMARNI DA KYAKKYAWA DA HANI DA MUMMUNA 193
GARKUWA 196
8 – KYAUTATAWA : 196
9 - KYAWUNTA ZAMANTAKEWA 197
3 – TAUSAYAWA MIJI : 208
4 – HIMMATUWA DA KULA DA CIKIN GIDA DA KAYYAKINSA : 209
5 - HIMMATUWA CIKIN SAUKE HAQQOQI 209
6 – JIMA'I 210
7 - ADO 213
8 – KAMEWA CIKIN MAGANA : 219
SHUGABANTAR IYALI 225
DALILAI DA SUKE SANYA DAWWAMAR AURE 227
1 – SON JUNA 228
2 – YAWAITA AIKATA ALHERI: 228
4 – SANYA FARIN CIKI: 229
5 – BIYAYYA DA NEMAN YARDAR MIJI: 230
6 – KIYAYE MUTUNCI DA DUKIYA : 230
7 – TAIMAKO DA TALLAFAWA 230
8 – TARBAR MIJI DA KYAWUNTA BANKWANA DA SALLAMA : 231
9 – KALAMIN AQIDOJI MAI KYAWU DA QARFAFAFFEN FURUCI. 232
10 – KARBAR UZURI DA YIWA JUNA UZURI : 232
11 – BINSU SANNU SANNU CIKIN KOWANNE HALI : 233
12 – KYAWUNTA LAFAZI CIKN KOWANNE YANAYI : 233
13 – RASHIN SAURARON KYAUTATA AIKI DARI BISA DARI 233
14 – RASHIN IKON DAUKAR NAUYI A RAYUWANCE : 234
15 – RASHIN GORI KAN MIJI : 234
16 – RASHIN QAURACEWA AL'AMARIN SHIMFIDA: 235
17 - YIN SHAWARA DA MATA BANDA BIYE MUSU: 235
18 – TAKA TSAN TSAN DA KUMA FARKAWA : 238
19 – HANKALTA 239
20 - MIJI SHI NE MUTUNCIN MATARSA 240
21 – KISHI 240
22 – TAIMAKEKENIYYA 242
23 – DADADAWA IYALI 243
27 – WATSI DA BOAKANCI DA TSAFE TSAFE : 244
28 - HIDIMA MADAWWAMIYA 245
29 – GODIYA 246
29 – QAUNAR JUNA 247
TSINTUWA GUDA BIYU GIDAN ALI DA FATIMA (AS) 248
■ FASALI NA 8 252

HADARIN TSADAR SADAKI : 148

HADARIN TSADAR SADAKI :

Sannan ku sani manufar daga sunnata shi ne kiyaye da tsare wanzuwar nau'in bil adama, da kubutar al'umma daga karkatar tunani da tafiyarsa a rayuwance, abin takaicin shi ne al'ummu musammam al'umma musulma sun karkace daga tafarki madaidaici saboda qin riqonsu  da dokoki da koyarwar shari'a, sun dauki ma'aunan zahiri sune abin lura cikin al'amarin aure, daga nan ne suka rungumi tsadada sadaki, da sanya banbanci tsakanin mutane kan asasin fifikon abin duniya da makamancin haka, kamar yanda su ka kwaikwayi turawa cikin karkatacciya matafiyarsu ta rayuwa  da yaudaruwa da takensu na qarya da sunan `yancin mata da `yanci saqi ba qaidi da watsi da kyawawan al'adu da dabi'u nagari al'amarin da ya kai ga raguwar aure tsakanin muatne da yaduwar fasadi da barna cikin al'umma.

haqiqa tsadar sadaki da hauhawarsa da yin alfahari da hakan na dga cikin matsalolin al'umma da zamantakewarsu wanda ya kai ga sukan karamar al'umma da ruguje mutumtakar mace kanta  cikin rayuwarta ta aure.

haqiqa iyaye maza da mata ababen tambaya ne  kan `ya`yayensu  sun sani ko basu sani ba daga abin da su ka kai cikin maida `ya`yansu sahun bayi daga abin da su ka aikata cikin tsadanta sadaki, haqiqa dai dai lokacin da su ke tunani nemawa `ya`yansu daraja ta hanyar tsadar sadakin to tabbas sun kaisu kasuwar sayar da bayi, suna masu jahiltar cutuwar da ta riski al'umma daga aikata hakan.

haqiqa fatima zahra (as) ta kasance abin koyi ga dukkanin mata, haqiqa da taso da ta zabi mafi arziqi da dukiyar a yankin hijaz daga wadanda suka nemi aurenta, sai dai ta fifita rayuwa mai ciki da farin ciki tare da talaka mumini, shi ne aliyu dan abi dalibi (as) sadakinta ya kasance wani sulke da mijinta ali (as) ya sayar sannan ya sayo mata kayayyakin gidanta da kudin, hakan ya isar mata abin alfahari ta kasance matar ali (as).