فهرست کتاب‌‌ لیست کتاب‌ها
■ KALMAR TARBIYYA CIKIN HARSHEN LARABCI DA YANDA AKA YI 4
■ FASALI NA ( 2 ) 24
■ AUREN DABI'A 24
■ FASALI NA 3
■ FASALI NA 4 73
■ FASALI NA 5 131
■ FASALI NA 6 176
HAQQOQIN DA MA'AURATA SU KAYI TARAYYA CIKI 177
1 – HAQURI 178
2 – KAMEWA DAGA ZALUNCI DA CUATARWA 179
HAQQOQIN MATA 180
CIYARWA DA YALWATAWA 185
TAUSAYAWA DA KAMEWA DAGA ZALUNCI 187
KAMEWA DAGA BARIN DUKA MAI CUTARWA 187
UMARNI DA KYAKKYAWA DA HANI DA MUMMUNA 193
GARKUWA 196
8 – KYAUTATAWA : 196
9 - KYAWUNTA ZAMANTAKEWA 197
3 – TAUSAYAWA MIJI : 208
4 – HIMMATUWA DA KULA DA CIKIN GIDA DA KAYYAKINSA : 209
5 - HIMMATUWA CIKIN SAUKE HAQQOQI 209
6 – JIMA'I 210
7 - ADO 213
8 – KAMEWA CIKIN MAGANA : 219
SHUGABANTAR IYALI 225
DALILAI DA SUKE SANYA DAWWAMAR AURE 227
1 – SON JUNA 228
2 – YAWAITA AIKATA ALHERI: 228
4 – SANYA FARIN CIKI: 229
5 – BIYAYYA DA NEMAN YARDAR MIJI: 230
6 – KIYAYE MUTUNCI DA DUKIYA : 230
7 – TAIMAKO DA TALLAFAWA 230
8 – TARBAR MIJI DA KYAWUNTA BANKWANA DA SALLAMA : 231
9 – KALAMIN AQIDOJI MAI KYAWU DA QARFAFAFFEN FURUCI. 232
10 – KARBAR UZURI DA YIWA JUNA UZURI : 232
11 – BINSU SANNU SANNU CIKIN KOWANNE HALI : 233
12 – KYAWUNTA LAFAZI CIKN KOWANNE YANAYI : 233
13 – RASHIN SAURARON KYAUTATA AIKI DARI BISA DARI 233
14 – RASHIN IKON DAUKAR NAUYI A RAYUWANCE : 234
15 – RASHIN GORI KAN MIJI : 234
16 – RASHIN QAURACEWA AL'AMARIN SHIMFIDA: 235
17 - YIN SHAWARA DA MATA BANDA BIYE MUSU: 235
18 – TAKA TSAN TSAN DA KUMA FARKAWA : 238
19 – HANKALTA 239
20 - MIJI SHI NE MUTUNCIN MATARSA 240
21 – KISHI 240
22 – TAIMAKEKENIYYA 242
23 – DADADAWA IYALI 243
27 – WATSI DA BOAKANCI DA TSAFE TSAFE : 244
28 - HIDIMA MADAWWAMIYA 245
29 – GODIYA 246
29 – QAUNAR JUNA 247
TSINTUWA GUDA BIYU GIDAN ALI DA FATIMA (AS) 248
■ FASALI NA 8 252

DAREN ANGONCI 150

DAREN ANGONCI

 daga abubuwan masu dadi da kyawun tunawa, daga abubuwan da mutum ba zai taba mantawa da su ba shi ne daren angonci, kowacce al'umma ta na da irin na ta ladubban na biki da raka ango dakin amarya, abin mamakin shi ne tare da kasantuwa kowacce al'umma ta kebanta da irin bikinta sai dai cewa kuma dukkaninsu sun yi tarayya kan bayyanar da farin ciki.

yayin da hadafin mu shi ne sanin ladubban muslunci da abin da ya umarce mu da yin tanadi cikin wannan dare mai muhimmacin gaske to yanda za mu san haka qarqashin abin da ya zo daga riwayoyi kan wannan dare mai kyawu.

ayarin raka amarya:

raka amarya na nufin kintsata tsaf da daukota daga gidan mahaifanta ya zuwa gidan mijinta sai ya zamanto an cancada mata ado da kayan amarci  a rakota cikin maukibin mata ya zuwa dakin mijinta  cikin dare.

عن الإمام الصادق ع, قال: زفوا عرائسكم ليلا وأطعموا ضحى

1- an karbo sadiq (as) ya ce : ku kai amarenku dakin miji cikin dare, sannan ku ciyar yayin dagowar rana.

2- addu'a da sallah:

daga cikin ayyuka mustahabbai cikin daren angonci akwai addu'a da yin sallah raka'a biyu, haka na nufin bude darensu na farko kan asasin ginshikin addini ita ce sallah da kuma asasin ibada haqiqa gundarin ibada itace addu'a.

Haqiqa auren muslunci kadai dai tasirinsa na fara bayyana tun farko da farawa da yin addu'a da sallah  duk da cewa abin ban takaici a wannan zamani lamari gaba daya ya canja da sauya ya zuwa aikata zunubai  misalin kade kade da raye raye  wani lokacin abin yakan kaiwa da shaye shayen barasa, Allah kai mana tsari daga aikata haka.

الفقيه بسنده  : قال الصادق (عليه السلام)  : إذا أتى أحدكم أهله فلم يذكر الله عند الجماع وكان منه ولد كان شرك شيطان ، ويعرف ذلك بحبّنا وبغضن[1]ا 

2- alfaqihu da isnadinsa : sadiq (as) ya ce: idan dayanku ya jewa iyalinsa lokacin jima'i ba tare da ya ambaci sunan Allah ba idan ya kasance ya azurtu da to dan zai kasance daga wanda shaidan yayi tarayya cikin digon maniyyin da aka same shi, ana fuskantar hakan cikin soyayyarmu da qiyayyarmu wajen dan.

الكافي ... قال  : أتى رجل أمير المؤمنين (عليه السلام) فقال  : إنّي تزوّجت فادعُ الله لي ، فقال  : قل  : ( اللهمّ بكلماتك استحللتها ، وبأمانتك أخذتها ، اللهمّ اجعلها ولوداً ودوداً لا تفرِك ، تأكل ممّا راح ولا تسأل عمّا سرح ) ـ  كأنّ المراد أ نّها تأكل ممّا جاء وحصل عندها بالعشي كائناً ما كان ولا تسأل عمّا ذهب وغاب عنها  ـ وهذا غريب من معنى رواح الماشية وسراحها كما قال عزّ وجلّ  : (  حِينَ تُرِيحُونَ وَحِينَ تَسْرَحُونَ 

3- alkafi - … y ace : wani mutum ya zo wajen sarkin muminai ali (as) sai ya ce : ni nayi aure ka roqa mini Allah, sai imam ya ce: kace : Allah da kalmarka na halasta ta, da amanarka  na dauketa, Allah ka sanya ta mai haihuwa mai nuna qauna mara nuna qiyayya, wacce ke karba abin da ya sawwaqa ba ta tamabayar abin da babu.

عن أبي عبد الله (عليه السلام) قال أمير المؤمنين (عليه السلام)  : إذا جامع أحدكم فليقل  : بسم الله وبالله ، اللهمّ جنّبني الشيطان وجنّب الشيطان ما رزقتني ، فإن قضى الله بينهما ولداً لا يضرّه الشيطان بشيء أبداً

4- daga baban Abdullah (as) ya ce: idan dayanku ya yi jima'i to ya ce: na fara da sunan Allah da Allah, Allah ka nesanta ni daga shaidani cikin abin da ka azurta ni, to idan Allah ya qaddara da tsakaninsu shaidan bai iya cutar da shi har abada.

عن أبي جعفر (عليه السلام) قال  : إذا أردت الجماع فقل  : ( اللهمّ ارزقني ولداً واجعله تقيّاً زكيّاً ليس في خلقه زيادة ولا نقصان واجعل عاقبته إلى خير

5- daga baban jafar (as) ya ce: idan kayi niyyar yin jima'i to ka ce: Allah ka azurtani da da  mai tsoronka mai kaifin basira ya zamanto cikin halittarsa babu qari babu naqasa ka sanya qarshen rayuwarsa ya zamo alheri.

عن الصادق (عليه السلام) ، أ نّه قال لبعض أصحابه  : إذا أدخلت عليك أهلك فخذ بناصيتها واستقبل بها القبلة وقل  : « اللهمّ بأمانتك أخذتها وبكلماتك استحللتها ، فإن قضيت لي منها ولداً فاجعله مباركاً سوياً تقياً من شيعة آل محمّد ، ولا تجعل للشيطان فيه شركاً ولا نصيباً » ، وفي رواية  : « اللهمّ على كتابك تزوّجتها وبأمانتك أخذتها » إلى آخره

6- daga sadiq (as) ya cewa da sashen sahabbansa: idan aka kaima matarka to ka kama gashin gaban goshinta ka fuskanci alqibla ka ce: Allah da amanarka na dauketa da kalmarka na halasta ta, idan ka qaddara mini da daga gareta to ka sanya shi mai albarka madaidaici  mai tsoronka  daga shai'ar iyalan muhammadu (saw)  ka  da ka sanyawa shaidani tarayya cikinsa  ko wani rabo.

 من كتاب النجاة المروي عن الأئمة (عليهم السلام)  : إذا قرب الزفاف يستحبّ أن تأمرها أن تصلّي ركعتين ( استحباباً ) وتكون على وضوء إذا أدخلت عليك وتصلّي أنت أيضاً مثل ذلك وتحمد الله وتصلّي على النبيّ وآله وتقول  : « اللهمّ ارزقني إلفها وودّها ورضاها بي وأرضني بها ، واجمع بيننا بأحسن اجتماع وأيسر ائتلاف ، فإنّك تحبّ الحلال وتكره الحرام » ، ثمّ قال  : واعلم أنّ الإلف من الله والفرك ـ  أي البغض  ـ من الشيطان ليكره ما أحلّ الله

7-daga littafi najatu  an riwaito dga imamai (as) : idan daren tarewa ya kusanto to ka umarci amarya ta yi sallah raka'a biyu ta mustahabbi sannan ka kasance cikin alwala  yayin da ka a kawo maka amarya to kai ma ka tashi kayi sallah  ka godewa Allah  kayai salati ga annabi da iyalansa  sannan ka ce: Allah ka azurtani soyayyarta da qaunarta da yardarta  ka yardar da ni wajenta, ka hada tsakaninmu  da mafi kyawun hadawa  da sauqi, haqiqa kai ka na son halali ka na qin haramun, sannan y ace: ka sani cewa soyayya daga Allah ta ke qiyayya kuma daga shaidani  haqiqa shi ya na qiyayya da abin da Allah ya halasta.

وقال أمير المؤمنين (عليه السلام)  : إذا زفّت إليه ودخلت عليه فليصلّ ركعتين ، ثمّ ليمسح يده على ناصيتها ، وليقل  : « اللهمّ بارك لي في أهلي وبارك لها فيّ ، وما  جمعت بيننا فاجمع بيننا في خير ويمن وبركة ، وإن جعلتها فرقة فاجعلها فرقة إلى خير

8 – sarkin muminai ali (as) ya ce : idan an kawo masa amarya to ya yi sallah raka'a biyu  sannan ya shafa hannunsa kan gashin goshinta, ya ce: Allah ka sanya mini albarka cikin iyalina  ka albarkanceta ciki na, Allah abin da ka hada tsakakinmu ka hada shi cikin alheri da albarka, idan kuma ka qaddara rabuwa ka sanya ta zama ta rabuwa alheri.[1] Alwafi m 12 sh 711