فهرست کتاب‌‌ لیست کتاب‌ها
■ KALMAR TARBIYYA CIKIN HARSHEN LARABCI DA YANDA AKA YI 4
■ FASALI NA ( 2 ) 24
■ AUREN DABI'A 24
■ FASALI NA 3
■ FASALI NA 4 73
■ FASALI NA 5 131
■ FASALI NA 6 176
HAQQOQIN DA MA'AURATA SU KAYI TARAYYA CIKI 177
1 – HAQURI 178
2 – KAMEWA DAGA ZALUNCI DA CUATARWA 179
HAQQOQIN MATA 180
CIYARWA DA YALWATAWA 185
TAUSAYAWA DA KAMEWA DAGA ZALUNCI 187
KAMEWA DAGA BARIN DUKA MAI CUTARWA 187
UMARNI DA KYAKKYAWA DA HANI DA MUMMUNA 193
GARKUWA 196
8 – KYAUTATAWA : 196
9 - KYAWUNTA ZAMANTAKEWA 197
3 – TAUSAYAWA MIJI : 208
4 – HIMMATUWA DA KULA DA CIKIN GIDA DA KAYYAKINSA : 209
5 - HIMMATUWA CIKIN SAUKE HAQQOQI 209
6 – JIMA'I 210
7 - ADO 213
8 – KAMEWA CIKIN MAGANA : 219
SHUGABANTAR IYALI 225
DALILAI DA SUKE SANYA DAWWAMAR AURE 227
1 – SON JUNA 228
2 – YAWAITA AIKATA ALHERI: 228
4 – SANYA FARIN CIKI: 229
5 – BIYAYYA DA NEMAN YARDAR MIJI: 230
6 – KIYAYE MUTUNCI DA DUKIYA : 230
7 – TAIMAKO DA TALLAFAWA 230
8 – TARBAR MIJI DA KYAWUNTA BANKWANA DA SALLAMA : 231
9 – KALAMIN AQIDOJI MAI KYAWU DA QARFAFAFFEN FURUCI. 232
10 – KARBAR UZURI DA YIWA JUNA UZURI : 232
11 – BINSU SANNU SANNU CIKIN KOWANNE HALI : 233
12 – KYAWUNTA LAFAZI CIKN KOWANNE YANAYI : 233
13 – RASHIN SAURARON KYAUTATA AIKI DARI BISA DARI 233
14 – RASHIN IKON DAUKAR NAUYI A RAYUWANCE : 234
15 – RASHIN GORI KAN MIJI : 234
16 – RASHIN QAURACEWA AL'AMARIN SHIMFIDA: 235
17 - YIN SHAWARA DA MATA BANDA BIYE MUSU: 235
18 – TAKA TSAN TSAN DA KUMA FARKAWA : 238
19 – HANKALTA 239
20 - MIJI SHI NE MUTUNCIN MATARSA 240
21 – KISHI 240
22 – TAIMAKEKENIYYA 242
23 – DADADAWA IYALI 243
27 – WATSI DA BOAKANCI DA TSAFE TSAFE : 244
28 - HIDIMA MADAWWAMIYA 245
29 – GODIYA 246
29 – QAUNAR JUNA 247
TSINTUWA GUDA BIYU GIDAN ALI DA FATIMA (AS) 248
■ FASALI NA 8 252

WALIMA 155

WALIMA

Daga mustahabbai cikin angonci shi ne shirya walima kamar yadda sananne abu ne cikin mafi yawan qasashen musulmi da sauran qasashe, kwankin walima basa wuce bakwai, amma abin da ya zo cikin riwaya:

عن النبي (صلى الله عليه وآله) أوصى علياً (عليه السلام)  : يا عليّ ، لا وليمة إلاّ في خمس  : في عرس ، أو خرس ، أو إعذار ، أو وكار ، أو ركاز . فالعرس  : التزويج ، والخُرس  : النفاس بالولد ، والإعذار  : الختان ، والوكار  : في شراء الدار ( الوكر  : عشّ الطائر الذي يأوي إليه ، والوكيرة طعام يعمل عند الفراغ من البناء ، والوكار شراء الدار ) ، والركاز  : الرجل يقدم من مكّة  

16 – daga manzon Allah (saw) cikin wasiyyarsa ga ali (as)  babu walima face cikin abubuwa biyar: aure, haihuwa, kaciya, sayen gida, kammala ginin gida.

عن أنس ، أنّ النبيّ (صلى الله عليه وآله) تزوّج حفصة أو بعض أزواجه ، فأولم عليها بتمر وسويق  

17 – daga anas cewa manzon Allah (saw) yayin da ya  auri hafsa ko dai wata daga cikin matansa, ya shirya mata walima da dabino. 

Duk abin da annabi ( saw ) ya aikata shi ne sunna, tabbas manzon ya zame maku abin koyi.

عن أبي جعفر (عليه السلام) ، قال  : الوليمة يوماً أو يومين مكرمة ، وثلاثة أيام رياء وسمعة

18- daga baban jafar(as) ya ce: ana walima ne yini daya zuwa biyu wanda yin hakan karamci ne, amma idan ya wuce haka ya zama riya da jiji da kai da neman suna.

قال رسول الله (صلى الله عليه وآله)  : أوّل يوم حقّ ، والثاني معروف ، وما زاد رياء وسمعة

19 – manzon Allah (saw) ya ce walimar ranar farko itace walimar gaske, ta rana ta biyu alheri, sannan idan ta wuce haka ta zama riya da neman suna.

عن الإمام الرضا (عليه السلام) ، أنّ النجاشي لمّـا خطب لرسول الله (صلى الله عليه وآله)اُمّ  حبيبة آمنة بنت أبي سفيان فزوّجه دعا بطعام وقال  : إنّ من سنن المرسلين الإطعام عند التزويج .

20- an karbo daga imam rida (as) cewa lokacin da najashi ya nemawa annabi (saw) ummu habib aminatu `yar abu sufyanu ya aura masa ya sa an kawo abinci ya ce: haqiqa cikin sunnar manzanni ciyarwa yayin aure.

عن أبي عبد الله (عليه السلام) ، قال  : إنّ رسول الله (صلى الله عليه وآله) حين تزوّج ميمونة بنت  الحارث أولم عليها وأطعم الناس الحيس

21- daga baban Abdullah (as) ya ce: haqiqa manzon Allah (saw)  ya auri maimunatu ya shirya mata walima ya ciyar da mutanealewar dabino.

عَنْ جَعْفَرٍ الْقَلَانِسِيِّ عَنْ أَبِيهِ قَالَ: قُلْتُ لِأَبِي عَبْدِ اللَّهِ ع إِنَّا نَتَّخِذُ الطَّعَامَ وَ نُجَيِّدُهُ وَ نَتَنَوَّقُ فِيهِ فَلَا يَكُونُ لَهُ رَائِحَةُ طَعَامِ الْعُرْسِ قَالَ ذَلِكَ لِأَنَّ طَعَامَ الْعُرْسِ تَهُبُّ فِيهِ رَائِحَةُ الْجَنَّةِ لِأَنَّهُ طَعَامٌ اتُّخِذَ لِحَلَال[1]

22- daga jafar falansi  daga babansa ya ce: na cewa baban Abdullah (as) haqiqa mu muna shirya abinci mu kyawunta shi amma ba mu jin yana qamshin irin na abincin amarci  ? sai imam ya ce: saboda abincin amarci iskar qamshi daga aljanna na shiga cikinsa, saboda shi abinci ne da aka shirya shi  don halali.[2]

 أَبَا الْحَسَنِ الرِّضَا ع يَقُولُ إِنَّ اللَّهَ جَعَلَ اللَّيْلَ سَكَناً وَ جَعَلَ النِّسَاءَ سَكَناً وَ مِنَ السُّنَّةِ التَّزْوِيجُ بِاللَّيْلِ وَ إِطْعَامُ الطَّعَام2

 23 – imam rida (as) ya ce : Allah ya sanya dare hutu ya sanya mata hutu, daga cikin sunna daura aure da daddare da ciyar da abinci.[1] Biharul anwar m 100  sh 277

[2] Biharul anwar m 100 sh 277