فهرست کتاب‌‌ لیست کتاب‌ها
■ KALMAR TARBIYYA CIKIN HARSHEN LARABCI DA YANDA AKA YI 4
■ FASALI NA ( 2 ) 24
■ AUREN DABI'A 24
■ FASALI NA 3
■ FASALI NA 4 73
■ FASALI NA 5 131
■ FASALI NA 6 176
HAQQOQIN DA MA'AURATA SU KAYI TARAYYA CIKI 177
1 – HAQURI 178
2 – KAMEWA DAGA ZALUNCI DA CUATARWA 179
HAQQOQIN MATA 180
CIYARWA DA YALWATAWA 185
TAUSAYAWA DA KAMEWA DAGA ZALUNCI 187
KAMEWA DAGA BARIN DUKA MAI CUTARWA 187
UMARNI DA KYAKKYAWA DA HANI DA MUMMUNA 193
GARKUWA 196
8 – KYAUTATAWA : 196
9 - KYAWUNTA ZAMANTAKEWA 197
3 – TAUSAYAWA MIJI : 208
4 – HIMMATUWA DA KULA DA CIKIN GIDA DA KAYYAKINSA : 209
5 - HIMMATUWA CIKIN SAUKE HAQQOQI 209
6 – JIMA'I 210
7 - ADO 213
8 – KAMEWA CIKIN MAGANA : 219
SHUGABANTAR IYALI 225
DALILAI DA SUKE SANYA DAWWAMAR AURE 227
1 – SON JUNA 228
2 – YAWAITA AIKATA ALHERI: 228
4 – SANYA FARIN CIKI: 229
5 – BIYAYYA DA NEMAN YARDAR MIJI: 230
6 – KIYAYE MUTUNCI DA DUKIYA : 230
7 – TAIMAKO DA TALLAFAWA 230
8 – TARBAR MIJI DA KYAWUNTA BANKWANA DA SALLAMA : 231
9 – KALAMIN AQIDOJI MAI KYAWU DA QARFAFAFFEN FURUCI. 232
10 – KARBAR UZURI DA YIWA JUNA UZURI : 232
11 – BINSU SANNU SANNU CIKIN KOWANNE HALI : 233
12 – KYAWUNTA LAFAZI CIKN KOWANNE YANAYI : 233
13 – RASHIN SAURARON KYAUTATA AIKI DARI BISA DARI 233
14 – RASHIN IKON DAUKAR NAUYI A RAYUWANCE : 234
15 – RASHIN GORI KAN MIJI : 234
16 – RASHIN QAURACEWA AL'AMARIN SHIMFIDA: 235
17 - YIN SHAWARA DA MATA BANDA BIYE MUSU: 235
18 – TAKA TSAN TSAN DA KUMA FARKAWA : 238
19 – HANKALTA 239
20 - MIJI SHI NE MUTUNCIN MATARSA 240
21 – KISHI 240
22 – TAIMAKEKENIYYA 242
23 – DADADAWA IYALI 243
27 – WATSI DA BOAKANCI DA TSAFE TSAFE : 244
28 - HIDIMA MADAWWAMIYA 245
29 – GODIYA 246
29 – QAUNAR JUNA 247
TSINTUWA GUDA BIYU GIDAN ALI DA FATIMA (AS) 248
■ FASALI NA 8 252

RARRABA ALEWA KO DABINO 157

RARRABA ALEWA KO DABINO 

Babu laifi a rarraba alewa kudi ga mutane lokacin daurin aure .

ِ عَنِ الصَّادِقِ عَلَيْهِ السَّلَامُ عَنْ آبَائِهِ ع قَالَ قَالَ أَمِيرُ الْمُؤْمِنِينَ صَلَوَاتُ اللَّهِ عَلَيْهِ دَخَلَتْ أُمُّ أَيْمَنَ عَلَى النَّبِيِّ ص وَ فِي مِلْحَفَتِهَا شَيْ‏ءٌ فَقَالَ لَهَا رَسُولُ اللَّهِ ص مَا مَعَكِ يَا أُمَّ أَيْمَنَ فَقَالَتْ إِنَّ فُلَانَةَ أَمْلَكُوهَا فَنَثَرُوا عَلَيْهَا فَأَخَذْتُ مِنْ نُثَارِهِمْ ثُمَّ بَكَتْ أُمُّ أَيْمَنَ وَ قَالَتْ يَا رَسُولَ اللَّهِ فَاطِمَةُ زَوَّجْتَهَا وَ لَمْ تَنْثُرْ عَلَيْهَا شَيْئاً فَقَالَ رَسُولُ اللَّهِ ص يَا أُمَّ أَيْمَنَ لِمَ تَكْذِبِينَ فَإِنَّ اللَّهَ عَزَّ وَ جَلَّ لَمَّا زَوَّجْتُ فَاطِمَةَ عَلِيّاً أَمَرَ أَشْجَارَ الْجَنَّةِ أَنْ تَنْثُرَ عَلَيْهِمْ مِنْ حُلِيِّهَا وَ حُلَلِهَا وَ يَاقُوتِهَا وَ دُرِّهَا وَ زُمُرُّدِهَا وَ إِسْتَبْرَقِهَا فَأَخَذُوا مِنْهَا مَا لَا يَعْلَمُونَ وَ لَقَدْ نَحَلَ اللَّهُ طُوبَى فِي مَهْرِ فَاطِمَةَ صَلَوَاتُ اللَّهِ عَلَيْهَا فَجَعَلَهَا فِي مَنْزِلِ عَلِيٍّ صَلَوَاتُ اللَّهِ عَلَيْه[1]ِ

 24 – daga sadiq (as) daga babanninsa (as) ya ce: sarkin muminai ali (as) y ace :  ummu aimana ta shiga wajen annabi (saw) tare da wani  sai manzon Allah (saw) ya ce : me yake tare da ke ya ummu aimana sai ta ce haqiqa wance da suka daura mata aure  sai da su ka rarraba alewa to shi ne na debo daga abin da su ka rarraba, sai ummu aimana ta fashe da kuka ta ce ya manzon Allah  ka aurar da Fatima  amma ba ka rarraba komai yayin daurin auren, sai manzon Allah ( saw) ya ce: me yasa kike qarya ya ummu aimana ? haqiqa lokacin da na aurar da Fatima Allah ya yi umarni ga bishiyoyin aljanna  da su rarraba kyauta daga adonsu daga yaqutu da zumarad da gwala gwalai da kayan ado sai suka diba suka rarraba abin da ma basu sanshi ba, haqiqa Allah ya yi kyauta, farin ciki cikin sadakin Fatima (as) sai ya sanya ta cikin gidan ali (as).

عن عليّ ، عن أخيه الكاظم (عليه السلام) ، قال  : سألته عن النثار  : السكّر واللوز وغيره ، أيحلّ أكله  ؟ قال  : يكره أكل النهب .

25 an karbo daga ali daga dan'uwansa  kazeem (as) ya ce: na tambaye shi kan alewar daurin aure: sukari da luzu da wasunsu, shin ya halasta aci ? sai ya ce: karahiya ne cin abin da aka qwato.

عن الصادق (عليه السلام) ، أنّ النبيّ (صلى الله عليه وآله) قال  : إذا دعيتم إلى العرسات فأبطئوا ، فإنّها تذكّر الدنيا ، وإذا دعيتم إلى الجنائز فأسرعوا ، فإنّها تذكّر الآخرة

26 – daga sadiq (as) idan an gayya ce ku biki to kuyi jinkiri cikin zuwa  saboda shi biki na tunatar da kai duniya, amma idan an gayya ce ku jana'iza ku yi gaggawa  haqiqa ta na tunatar da kai lahira.[1] Biharul anwar m 100 sh  279