فهرست کتاب‌‌ لیست کتاب‌ها
■ KALMAR TARBIYYA CIKIN HARSHEN LARABCI DA YANDA AKA YI 4
■ FASALI NA ( 2 ) 24
■ AUREN DABI'A 24
■ FASALI NA 3
■ FASALI NA 4 73
■ FASALI NA 5 131
■ FASALI NA 6 176
HAQQOQIN DA MA'AURATA SU KAYI TARAYYA CIKI 177
1 – HAQURI 178
2 – KAMEWA DAGA ZALUNCI DA CUATARWA 179
HAQQOQIN MATA 180
CIYARWA DA YALWATAWA 185
TAUSAYAWA DA KAMEWA DAGA ZALUNCI 187
KAMEWA DAGA BARIN DUKA MAI CUTARWA 187
UMARNI DA KYAKKYAWA DA HANI DA MUMMUNA 193
GARKUWA 196
8 – KYAUTATAWA : 196
9 - KYAWUNTA ZAMANTAKEWA 197
3 – TAUSAYAWA MIJI : 208
4 – HIMMATUWA DA KULA DA CIKIN GIDA DA KAYYAKINSA : 209
5 - HIMMATUWA CIKIN SAUKE HAQQOQI 209
6 – JIMA'I 210
7 - ADO 213
8 – KAMEWA CIKIN MAGANA : 219
SHUGABANTAR IYALI 225
DALILAI DA SUKE SANYA DAWWAMAR AURE 227
1 – SON JUNA 228
2 – YAWAITA AIKATA ALHERI: 228
4 – SANYA FARIN CIKI: 229
5 – BIYAYYA DA NEMAN YARDAR MIJI: 230
6 – KIYAYE MUTUNCI DA DUKIYA : 230
7 – TAIMAKO DA TALLAFAWA 230
8 – TARBAR MIJI DA KYAWUNTA BANKWANA DA SALLAMA : 231
9 – KALAMIN AQIDOJI MAI KYAWU DA QARFAFAFFEN FURUCI. 232
10 – KARBAR UZURI DA YIWA JUNA UZURI : 232
11 – BINSU SANNU SANNU CIKIN KOWANNE HALI : 233
12 – KYAWUNTA LAFAZI CIKN KOWANNE YANAYI : 233
13 – RASHIN SAURARON KYAUTATA AIKI DARI BISA DARI 233
14 – RASHIN IKON DAUKAR NAUYI A RAYUWANCE : 234
15 – RASHIN GORI KAN MIJI : 234
16 – RASHIN QAURACEWA AL'AMARIN SHIMFIDA: 235
17 - YIN SHAWARA DA MATA BANDA BIYE MUSU: 235
18 – TAKA TSAN TSAN DA KUMA FARKAWA : 238
19 – HANKALTA 239
20 - MIJI SHI NE MUTUNCIN MATARSA 240
21 – KISHI 240
22 – TAIMAKEKENIYYA 242
23 – DADADAWA IYALI 243
27 – WATSI DA BOAKANCI DA TSAFE TSAFE : 244
28 - HIDIMA MADAWWAMIYA 245
29 – GODIYA 246
29 – QAUNAR JUNA 247
TSINTUWA GUDA BIYU GIDAN ALI DA FATIMA (AS) 248
■ FASALI NA 8 252

LADUBBAN SADUWA DA IYALI 158

LADUBBAN  SADUWA DA IYALI

daga cikin girman muslunci shi ne cewa ya sanyawa  komai iyakoki a kebance, kamar yadda ya sanya masu tsari da ladubba  kai hatta kusantar iyali ta jinsi ba a barta a baya ba, ta yiwu mutum ya yi tunanin cewa jima'i na daga bayyanannun siffofin dan adam wadanda mutum ke mantawa da kansa yayin shagaltuwa da da su, ta yiwu ma ya ji kunya bayan kammala abin da ya aikata, sai dai cewa muslunci hatta wannan al'amari sai da sanya masa ladubba da iyakoki, sannan duk wanda ya tsallake wannan iyakoki ba zai taba rabauta ba cikin rayuwarsa ta aure, sannan ya zama tilas mu san asalan kusantar iyali cikin addini, domin ta na zama babban dalilin da ke kawo rabuwa tsakanin ma'aurata, yayin da wannan lokaci za ka ga miji na rowar gayawa matarsa kalma mai dadi da murmushi dalilin gazawarta a kwanciyar aure, haka ma matar za ka same ta ta na munanta mu'amala, daga qarshe `ya`yan da za su haifa su ne za su girbi wannan sakamakon mummunar mu'amalar da ke tsakanin  iyayensu.

 muslunci na kira zuwa ga taqawa  cikin rayuwar aure, manzon Allah (saw) ckin wasiyyar ga zaidu dan harisa: ya na umartarsa da ya riqe matarsa kuma ya ji tsoron Allah

 [1] أمْسِكْ عَلَيْكَ زَوْجَكَ وَا تَّقِ اللهَ

ka riqe matark  ka ji tsoron Allah.

iyali su ne amudi ginshiqin al'umma , tarbiyyar muslunci ita ce asasin iyali, imani da Allah da ranar lahira  da dukkanin abin da ke amsa sunan tsoron Allah  da tsantseni  to shi ne jagoran tarbiyya, sannan babu abin da ke lalata dai daikun mutane da al'umma baki daya sai lokacin da suka nesanta da wadannan qa'idoji ingantattu na asasi, babu nasara da kubuta face komawa ga qur'ani da neman mafaka da Allah da manzonsa da imamai rabautattu (as)  babu gyara babu azurta face tafiya kan shiriyarsu  da tafarkinsu madaidaici.

gaskiya za ta wanzu da dawwama, kamar yadda qarya za ta kauce ta gushe, amma kumfar ruwa sai ya tafi qeqasashshe, amma abin da ke amafanar mutane sai ya zauna bisa qasa, wannan na daga sunnonin ubangiji  wacce ba zaka taba samun canji da sauyi cikinsu ba.

لَقَدْ جَاءَكُمْ رَسُولٌ مِنْ أنفُسِكُمْ عَزِيزٌ عَلَيْهِ مَا عَنِتُّمْ حَرِيصٌ عَلَيْكُمْ بِالمُؤْمِنِينَ رَؤُوفٌ رَحِيم[2] 

haqiqa manzo daga cikinku ya zo muku abin da kuka wahala na nauyaya kansa, mai tsananin kwadayi saboda ku ga muminai mai tausayi mai jin qai.

وَيَضَعُ عَنْهُمْ إصْرَهُمْ وَالأغْلالَ الَّتِي كَانَتْ عَلَيْهِم[3]

فَذَكِّرْ إنَّمَا أ نْتَ مُذَكِّرٌ * لَسْتَ عَلَـيْهِمْ بِمُسَيْطِ[4]ر   

ka tunatar kadai kai dai mai tunatarwa ne  * b aka da iko kansu .

فَأقِمْ وَجْهَكَ لِلدِّينِ حَنِيفاً فِطْرَةَ اللهِ الَّتِي فَطَرَ النَّاسَ عَلَيْهَا لا تَبْدِيلَ لِخَلْقِ اللهِ ذَلِكَ الدِّينُ القَيِّمُ وَلَكِنَّ أكْثَرَ النَّاسِ لا يَعْلَمُونَ[5] 

 ka tsayar da fuskar ga addini kana mai karkata zuwa ga gaskiya, halittar Allah wacce ya  halicci mutane kanta babu sauyi ga halittar Allah  wadancananka addinin Allah sai dai mafi yawan mutane ba su sani.

Wannan shi ne miqaqqen addini da ya kamata mutum ya zabe shi  sai dai cewa jahilci shi ne dalilin na asasi da ke sanyawa kaga mutum ya munanta zabi, ya bar addini wanda cikinsa arziqinsa yake da bautarsa,  ka same shi ya zabi batansa da tsiyatarsa.

Babu laifi idan munyi ishara ga kadan daga asalan kusantar iyali cikin abubuwa da za su zo:[1] Ahzab:37

[2] Tauba:128

[3] A'araf:157

[4] Algashiya:21-22

[5] Rum:30