فهرست کتاب‌‌ لیست کتاب‌ها
■ KALMAR TARBIYYA CIKIN HARSHEN LARABCI DA YANDA AKA YI 4
■ FASALI NA ( 2 ) 24
■ AUREN DABI'A 24
■ FASALI NA 3
■ FASALI NA 4 73
■ FASALI NA 5 131
■ FASALI NA 6 176
HAQQOQIN DA MA'AURATA SU KAYI TARAYYA CIKI 177
1 – HAQURI 178
2 – KAMEWA DAGA ZALUNCI DA CUATARWA 179
HAQQOQIN MATA 180
CIYARWA DA YALWATAWA 185
TAUSAYAWA DA KAMEWA DAGA ZALUNCI 187
KAMEWA DAGA BARIN DUKA MAI CUTARWA 187
UMARNI DA KYAKKYAWA DA HANI DA MUMMUNA 193
GARKUWA 196
8 – KYAUTATAWA : 196
9 - KYAWUNTA ZAMANTAKEWA 197
3 – TAUSAYAWA MIJI : 208
4 – HIMMATUWA DA KULA DA CIKIN GIDA DA KAYYAKINSA : 209
5 - HIMMATUWA CIKIN SAUKE HAQQOQI 209
6 – JIMA'I 210
7 - ADO 213
8 – KAMEWA CIKIN MAGANA : 219
SHUGABANTAR IYALI 225
DALILAI DA SUKE SANYA DAWWAMAR AURE 227
1 – SON JUNA 228
2 – YAWAITA AIKATA ALHERI: 228
4 – SANYA FARIN CIKI: 229
5 – BIYAYYA DA NEMAN YARDAR MIJI: 230
6 – KIYAYE MUTUNCI DA DUKIYA : 230
7 – TAIMAKO DA TALLAFAWA 230
8 – TARBAR MIJI DA KYAWUNTA BANKWANA DA SALLAMA : 231
9 – KALAMIN AQIDOJI MAI KYAWU DA QARFAFAFFEN FURUCI. 232
10 – KARBAR UZURI DA YIWA JUNA UZURI : 232
11 – BINSU SANNU SANNU CIKIN KOWANNE HALI : 233
12 – KYAWUNTA LAFAZI CIKN KOWANNE YANAYI : 233
13 – RASHIN SAURARON KYAUTATA AIKI DARI BISA DARI 233
14 – RASHIN IKON DAUKAR NAUYI A RAYUWANCE : 234
15 – RASHIN GORI KAN MIJI : 234
16 – RASHIN QAURACEWA AL'AMARIN SHIMFIDA: 235
17 - YIN SHAWARA DA MATA BANDA BIYE MUSU: 235
18 – TAKA TSAN TSAN DA KUMA FARKAWA : 238
19 – HANKALTA 239
20 - MIJI SHI NE MUTUNCIN MATARSA 240
21 – KISHI 240
22 – TAIMAKEKENIYYA 242
23 – DADADAWA IYALI 243
27 – WATSI DA BOAKANCI DA TSAFE TSAFE : 244
28 - HIDIMA MADAWWAMIYA 245
29 – GODIYA 246
29 – QAUNAR JUNA 247
TSINTUWA GUDA BIYU GIDAN ALI DA FATIMA (AS) 248
■ FASALI NA 8 252

2- WASA DA MATA GABANIN JIMA'I : 160

2- WASA DA MATA GABANIN JIMA'I :

 Kafin fara jima'i kusantar juna ya zama dole a danyi barkwanci da wasa ta hanyar fadin wasu kalmomi da za su motsa sha'awa , sannan kuma a dan rurrungumi juna ayi wasa a sumbace juna da dai sauransu, daga qarshe sai shiga kusnatar juna ba a so namiji ya gabaci matarsa fitar da maniyyyi da biyan buqatarsa, idan kuma hakan ya faru to ka da y ace zai tashi ya barta ba tare da ya jira ta biya buqatar ba, idan kuma bai haka za ta iya kamuwa da ciwon jijiyoyi ko dai wani abu da qarshensa bai da kyau.

عن الإمام الصادق (عليه السلام) ، قال  : إنّ أحدكم ليأتي أهله فتخرج من تحته ولو أصابت زنجياً لتشبّثت به ـ  أي لم تشبع في لذّتها فربما في تلك الحالة تفكّر بالحرام والعياذ بالله  ـ فإذا أتى أحدكم أهله فليكن بينهما مداعبة ، فإنّه أطيب للأمر

1-      an karbo daga imam sadiq (as) ya ce: haqiqa dayanku na zuwarwa iyalansa sai ta fita daga qarqashinsa da za ta hadu da baqar fata da ta cudanya da shi – ma'ana ba ta samu biyan buqatarta ba ta sha'awa me yuwawa ta yi tunanin aikata haramun, saboda haka idan dayanku ya je ma iyalansa to kafin zakke musu ayi dan wasanni da juna, haka shi yafi komai dadada ga al'amari.

والنساء بطبعهن أكثر شهوة من الرجال ، حتّى قال الإمام الصادق (عليه السلام)  : فضّلت المرأة على الرجل بتسع وتسعين جزءاً من اللذّة ، ولكنّ الله عزّ وجلّ ألقى عليهن الحياء

2-      a dabi'ance mata sunfi maza sha'awa hatta imam sadiq (as) ya ce : mace ta fifici namiji da kashi 99 daga jin dadi, sai dai cewa Allah ya sanya musu jin kunya.

قال رسول الله (صلى الله عليه وآله)  : من الجفاء مواقعة الرجل أهله قبل المداعبة[1]

3 – manzon Allah ( saw) ya ce: ya na daga cikin jafa'i zakkewa iyali gabanin wasa da su.

عن النبي ص,قال: لا ترتمو على نسائكم كالبهائم, بل اجعلوا بينهن رسولا, قيل: وما الرسول يا رسول الله قال: القبلة

4- an karbo daga annabin rahama (saw) ya ce : kada ku zakkewa iyalinku kamar dabbobi sai dai cewa ku sanya wani dan saqo tsakaninsu, sai aka tamabayi manzon Allah (saw) me ye dan saqo ? sai ya ce: sunbata.

عن الرضا ع, قال للمأمون: لا تجامع امرأة حتى تلاعبها وتكثر ملاعبتها وتغمز ثدييها

5 – an karbo daga imam rida (as) ya cewa mamun abbasi: ka da ka  zakkewa iyalinka sai ka fara wasa da ita kayawaita was an ka tsosi nonanta  ka yi wasa da shi.

عن النبيّ (صلى الله عليه وآله)  : إذا جامع أحدكم أهله فليصدقها ، ثمّ إذا قضى حاجته قبل أن تقضي حاجتها فلا يعجلها حتّى تقضي حاجته[2]ا .

6- daga baban abdullah (as) ya ce : manzon Allah (saw) ya ce : idan dayanku ya zakkewa iyalinsa ka da ya zakke musu kamar yadda tsuntsu ke zakkewa, ya dan jira ya dan zauna har tabiya ta ta buqatar.

عن النبيّ (صلى الله عليه وآله)  : إذا جامع أحدكم أهله فليصدقها ، ثمّ إذا قضى حاجته قبل أن تقضي حاجتها فلا يعجلها حتّى تقضي حاجتها .

7 – daga annabi (saw) ya ce : idan dayanku ya zakkewa iyalinsa to ya gasgata ta, sannan idan ya gama biyan buqatarsa ka da ya yi gaggawa ya tsaya ya jira tabiya ta ta buqatar.

قَالَ: إِذَا أَرَادَ أَحَدُكُمْ أَنْ يَأْتِيَ زَوْجَتَهُ فَلَا يُعَجِّلْهَا فَإِنَّ لِلنِّسَاءِ حَوَائِج

1-        manzon Allah (saw) ya ce : idan dayanku ya yi niyyar zuwamma iyalinsa ka da ya yi gaggawa, haqiqa mata na da buqatu.

2-      عن أبي عبد الله (عليه السلام) ، قال  : ليس شيء تحضره الملائكة إلاّ الرهان وملاعبة الرجل أهله

3-      manzon Allah (saw) yace : bu abin da mala'iku ke halarta face jingina da wasa da iyali.

ـ قال رسول الله (صلى الله عليه وآله)  : ثلاثة من الجفا  : أن يصحب الرجل الرجل فلا يسأله عن اسمه وكنيته ، وأن يُدعى الرجل إلى طعام فلا يجيب وإن يجيب فلا يأكل ، ومواقعة الرجل أهله قبل المداعبة

4-      manzon Allah (saw) ya ce: abubuwa uku na daga cikin jafa'i: mutum ya yi abota da wani ba tare da ya tambayi sunansa ba da alkunyarsa, a gayyaci mutum zuwa cin wani abinci ya qi amsa gayyatar idan ma ya amsa sai ya qi cin abincin, zakkema iyali gabanin wasa da su.

عن إسحاق بن إبراهيم الجعفي ، قال  : سمعت أبا عبد الله (عليه السلام) يقول  : إنّ رسول الله (صلى الله عليه وآله) دخل بيت اُمّ سلمة فشمّ ريحاً طيّبة ، فقال  : أتتكم الحولاء . فقالت  : هو ذا هي تشكو زوجها ، فخرجت عليه الحولاء ، فقالت  : بأبي أنت واُمّي إنّ زوجي عنّي معرض ، فقال  : زيديه يا حولاء ، فقالت  : لا أترك شيئاً طيّباً ممّـا  أتطيّب له به وهو معرض ، فقال  : أما لو يدري ما له بإقباله عليك ، قالت  : وما  له بإقباله عليّ  ؟ فقال  : أما إنّه إذا أقبل اكتنفه ملكان وكان كالشاهر سيفه في سبيل الله ، فإذا هو جامع تحاتّ عنه الذنوب كما يتحاتّ ورق الشجر ، فإذا هو اغتسل انسلخ من الذنوب

11- daga is'haq dan ibrahim alju'ufi, ya ce:  na ji baban abdullah (as) ya na cewa: haqiqa manzon Allah (saw) ya shiga dakin ummu salma sai ya shaqi wata iska daddada, sai ya ce:  shin haula'u ta zo wajenku ne, sai ta ce ga ta nan ta na kokawa da mijinta, sai haula'u ta fito ta ce: babana da babata fansarka ya: haqiqa mijina kwata kwata ba ya kusanta ta, sai manzon Allah ya ce: ki sama masa turare, sai tace na yi amfani da dukkanin turare amma hakan bai sa ya kusanceni ba, sai ya ce: amma da ya son ldan da zai samu idan ya kusance ki, sai ta ce : menene zai samu cikin kusanta ta ? sai ya ce: amma shi idan ya fuskanto ki mala'iku biyu za su lullube shi  sannan zai kasance kamar wanda ya zare takobin cikin tafarkin Allah, sannan zununbansa zasu karkade kamar yanda ganyan bishiya ke zubewa, idan ya yi wanka zai sabule daga cikin zunubai.

fita daga cikin zunubi misalin yanda miciji ke sabewa  daga tsohuwar fatarsa, sai ya zamanto shi an gafarta masa dukkanin zunubansa.

عن أبي عبد الله (عليه السلام) ، في حديث يروى عن النبيّ (صلى الله عليه وآله) أنّ أبا ذر سأله عن هذا ، فقال  : ائتِ أهلك تؤجر ، فقال  : يا رسول الله آتيهم واُؤجر  ؟ فقال رسول  الله  : كما إنّك إذا أتيت الحرام ازرت ـ  أي تعاقب من الوزر  ـ وكذلك إذا أتيت الحلال اُجرت ـ  أي تثاب من الأجر والثواب [3] ـ]) .

5-      daga baban abdullah (as) cikin hadisi da ya rawaito daga annabi (saw) cewa abu zarr ya tambayi shi game da haka, sai ya ce masa: ka jewa iyalinka za ka samu lada, sai ya ce: ya manzon Allah (saw) in zakke musu kuma in samu lada ? sai ya ce: kamar yanda idan ka zakkema haramun ka ke samun zunubi, to haka ma idan ka zakke ma halal ka ke samun lada.

عليّ ، عن أخيه الكاظم (عليه السلام) ، قال  : سألته عن الرجل هل يصلح له أن يقبّل قُبل المرأة  ؟ قال  : لا بأس

6-      aliyu, daga dan'uwansa kazeem (as) ya ce : na tambaye shi game da shin ya halatta mutum ya sumbaci farjin mace, sai ya ce: babu laifi.

عن الصادق (عليه السلام) ، عن آبائه (عليهم السلام) ، قال  : قال رسول الله (صلى الله عليه وآله) لبعض أصحابه يوم جمعة  : هل صمت اليوم  ؟ قال  : لا ، قال له  : فهل تصدّقت اليوم بشيء  ؟ قال  : لا ، قال له  : قم فأصب من أهلك ، فإنّ ذلك صدقة منك إليه[4]ا

7-      daga sadiq (as) daga babanninsa (as) ya ce : manzon Allah ya was ashen sahabbansa ranar juma'a: shin  ka yi azumi yau ? sai ya ce: a' a , ka yi sadaqa wani abu yau ? ya ce : a'a , sai ya ce masa : tashi ka je ma iyalinka haqiqa hakan sadaqa ne daga gareka zuwa gareta.

قال الصادق (عليه السلام)  : ثلاث من سنن المرسلين  : العطر وإحفاء الشعر وكثرة الطروقة

15 – imam sadiq (as) ya ce: abubuwa uku na cikin sunnonin annabawa: sanya turare, taje gashi, yawan kusantar iyali.

yawan kusantar iyali, ma'ana yawan jima'i, sai dai cewa hadisi ya zo kan cewa mumini sha'awa amace ta ke.

وورد عن الإمام الرضا (عليه السلام) ، عن آبائه (عليهم السلام) ، قال  : قال عليّ (عليه السلام)  : من أراد البقاء ولا بقاء فليباكر الغداء ، ويجيّد الحذاء ، ويخفّف الرداء ، وليقلّ غشيان النساء[5]

 16 ya zo daga imam rida (as) daga babanninsa (as) ya ce: ali (as) ya ce: duk mai son wanzuwa cikin wannan duniya babu wanzuwa, to ya gagguta cin abincin safiya, ya jinkirta abincin dare, ya sauqaqwa kansa bashi, ya qaranta zakkewa mata.

zamu iya hada riwayoyin biyu, shi ne cewa shi jima'in mumini  ba ya na yinsa ne dan kansa ba kawai, kadai dai ya na yi don samun da nagari ko kuma don daddawa da farantawa matarsa da dai makamancin haka  daga kyawawan niyyoyi.

عن أمير المؤمنين (عليه السلام) ، قال  : عذاب القبر يكون من النميمة والبول وعزب الرجل عن أهله

16 – an karbo daga sarkin muminai ali (as) ya ce: azabar kabari na kasancewa daga annamimanci da fitsari da tuzurancin mutum daga iyalinsa.

عن سماعة قال  : سألته عن الرجل ينظر في فرج المرأة وهو يجامعها  ؟ قال  : لا بأس به إلاّ أ نّه يورث العمى

17 – an karbo daga samma'atu  ya ce: na tambayi imam kan mutumin da ya ke kallon farjin matarsa  lokacin da yake jima'i da ita ? sai ya ce: babu laifi sai dai ya na haifar da makanta.

قال أبو عبد الله (عليه السلام)  : اتّقوا الكلام عند ملتقى الختانين فإنّه يورث الخرس .

18 – baban Abdullah (as) ya ce : ku ji tsoron yin surutu lokacin da ku ke jima'i, haqiqa ya na haifar da baibanta.

عن عبيد بن زرارة قال  : كان لنا جار شيخ له جارية فارهة قد أعطى بها ثلاثين ألف درهم فكان لا يبلغ منها ما يريد وكانت تقول  : اجعل يدك بين شعري فإنّي أجد لذلك لذّة ـ  وهذا من استمناء النساء الذي يزيد في شهوتهنّ ووصولهن إلى أوج الشهوة وإلى الرعشة المختصّة بهن بعد الدخول والمباشرة  ـ فكان الشيخ الذي لا يبلغ منها ما يريد ـ  أي لا يقدر على وطئها  ـ يكره أن يفعل ذلك فقال لزرارة  : سل لي أبا عبد الله (عليه السلام) عن هذا فسأله فقال  : لا بأس أن يستعين بكلّ شيء من جسده عليها ، ولكن لا يستعين بغير جسده عليه[6]ا

19 – daga ubaid dan zurara ya ce: mu da wani tsoho da ya ke da baiwa, haqiqa an bashi dirhami dubu talatin a kanta, sannan ya kasance bai iya saduwa da ita, ta kasance ta na ce masa: sanya hannunka tsakanin gashina haqiqa ina jin dadi daga haka – wannan na daga cikin hanyar fitar da maniyyin mata wanda ke qara musu sha'awa ya kaisu ga qololuwar sha'awa da girgiza bayan jima'i, tsohon ya kasance ya na kyamar aikata haka sai ya cewa zurara ka tambayar mini baban Abdullah (as) kan wannan al'amari, sai imam ya ce: babu matsala cikin amfani da dukkanin gabar jikinsa amma dai ka da ya yi amfani da wani abu sabanin jikinsa kanta.

Bai halasta mace tayi wasa da jikinta da hujjar cewa ba ta da maniyyi  haka na daga jinkirta zance daga mahallinsa, kadai abin lura shi ne jin dadi ta hanyar da shari'a ba ta aminta saboda sai ya kasance haramun.

عن زرارة قال  : قلت لأبي عبد الله (عليه السلام)  : الرجل تكون عنده جواري فلا يقدر على أن يطأهن يعمل لهن شيئاً يلذّذهن به  ء قال  : أمّا ما كان من جسده فلا بأس به

 20 – daga zurara ya ce: na cewa baban abdullah (as) mutum ya ke da kuyangu amma bai iya takarsu – saduwa da su shin zai iya samar masu wani abu su dandani dadi da shi, sai imam ya ce : idan daga gabar jikinsa ya ke babu matsala.

عن العجلي قال  : قلت لأبي عبد الله (عليه السلام)  : الرجل يأتي جاريته في الماء  ؟ قال  : ليس به بأس

21- daga ijli yace: na tambaya baban Abdullah(as) mutum ne ya ke saduwa da baiwarsa  cikin ruwa , sai imam ya ce: babu matsala.

عن أبي الحسن الرضا (عليه السلام) قال  : سألته عن الرجل يقرأ في الحمّام وينكح فيه  ؟ قال  : لا بأس به

22 – daga baban hassan rida (as) ya ce: na tamabaye shi kan mutum da ya ke yin karatu cikin bandaki ya ke kuma zakkewa matarsa a ciki  sai ya ce : babu laifi.

عن أبي عبد الله (عليه السلام) قال  : لا بأس أن ينام الرجل بين أمتين والحرّتين ، إنّما نساؤكم بمنزلة اللُّعب ـ  جمع لعبة وهي ما يلعب

23 – daga baban Abdullah (as) ya ce: ba laifi mutum ya kwanta tsakanin kuyangu biyu da matansa `yantattu biyu, kadai dai matayenku kamar `yar tsanar wasa ne.

سأل محمّد بن العيص أبا عبد الله (عليه السلام) فقال  : اُجامع وأنا عريان  ؟ فقال  : لا ، ولا تستقبل القبلة ولا تستدبرها .

24 – muhammadu dan isi ya tambayi baban abdullah (as) shin ina iya saduwa da mata alhalin ina tsirara, sai ya ce masa: a'a kada ka aikata haka, kada ka fuskanci alqibla ko ka bata baya halin ka na tsirara.

عن أبي الحسن (عليه السلام) في الرجل يجامع فيقع عنه ثوبه  ؟ قال  : لا بأس

25 – daga baban Hassan (as) : gameda mutumin da ya shagaltu da jima'I sai tufafinsa ya fadi ? sai ya ce : babu laifi

عن إسحاق بن عمّار قال  : قلت لأبي إبراهيم (عليه السلام)  : الرجل يكون معه أهله في السفر ولا يجد الماء أيأتي أهله  ؟ قال  : ما اُحبّ أن يفعل ذلك إلاّ أن يخاف على نفسه ـ  وفي آخر  : إلاّ أن يكون شبقاً أي كثير الشهوة  ـ أو يخاف على نفسه ..

26 – daga is'haq dan ammar ya ce: na tambayi baban abbdullah (as) kan mutumin da ya yi tafiya tare da iyalinsa sai bai samu ruwa ba, shin zai iya jewa iyalinsa, sai ya ce : ba na son shi da aikata haka sai dai idan ya na tsoran fadawa haramun.

قال الإمام الصادق (عليه السلام)  : ثلاث يهدمن البدن وربما قتلن  : دخول الحمّام على البطنة ، والغشيان على الامتلاء ، ونكاح العجائز

27 – imam sadiq (as) ya ce: abubuwa uku na ruguza jiki sannan da yawan lokuta suna iya halaka shi:  shiga bandaki a qoshe, saduwa da iyali a qoshe, jima'I da tsofaffi.

3 – LOKUTAN SADUWA NA MUSTAHABBI DA MAKARUHI.

في حديث عن النبيّ (صلى الله عليه وآله) يقول لعليّ (عليه السلام) ـ  ليعلّم بذلك الناس  ـ  : يا  عليّ ، لا تجامع امرأتك في أوّل الشهر ووسطه وآخره ، فإنّ الجنون والجذام والخَبل يسرع إليها وإلى ولدها

1-cikin hadisi annabi (saw) da ya ke cewa ali (as) da ya koyar da mutane wannan abinda zai zo : ya ali ka da ka jewa matarka a farkon wata ko tsakiyarsa da qarshensa, lalle hauka da kuturta da rauni na gaggawa gareta da danta.

يا عليّ ، لا تتكلّم عند الجماع ، فإنّه إن قضى بينكما ولد لا يؤمن أن يكون أخرس ، ولا ينظرنّ أحدٌ في فرج امرأته ، وليغضّ بصره عند الجماع ، فإنّ النظر إلى الفرج يورث العمى ، يعني في الولد

ya ali ka da ka yi surutu yayin saduwarka da iyali, lalle al'amarin yanda ya ke shi ne idan Allah ya qaddara samun da tsakaninku ba zai aminta daga kasancewa bebe ba, ka da mutum ya dinga kallon farjin matarsa, ya damke idonsa yayin jima'i, lalle kallon farji na gadar da makanta ga yaron da za'a Haifa.

يا عليّ ، لا تتكلّم عند الجماع ، فإنّه إن قضى بينكما ولد لا يؤمن أن يكون أخرس ، ولا ينظرنّ أحدٌ في فرج امرأته ، وليغضّ بصره عند الجماع ، فإنّ النظر إلى الفرج يورث العمى ، يعني في الولد

 ya ali ka da ka je ma matarka da cikin sha'awar matar waninka, lalle ni ina jin tsoron idan ubangiji ya hukunta da tsakininku zai kasance mata maza, mai karkata ya zuwa mata mai matsalar hankali.

يا عليّ ، من كان جنباً في الفراش مع امرأته فلا يقرأ القرآن ، فإنّي أخشى عليهما أن تنزل نار من السماء فتحرقهم يا عليّ

ya ali duk wanda ya kasance cikin janaba a shimfida tare da matarsa ka da ya karanta qur'ani, haqiqa ni ina jiye musu tsoron kada wuta ta sauko daga sama ta konesu.

يا عليّ ، لا تجامع امرأتك إلاّ ومعك خرقة ومع أهلك خرقة ، ولا تمسحا بخرقة واحدة فتقع الشهوة على الشهوة ، فإنّ ذلك يعقب العداوة بينكما ، ثمّ يؤدّيكما إلى الفرقة والطلاق

ya ali ka da jema iyalinka face ka kasance tare da kyalle sannan suma iyalinka da kyalle, ka da ku shafi juna da kyalle guda sai sha'awa ta yi karo da sha'awa, lalle hakan na janyo qiyya tsakaninku, sannan ya kai ku ga saki da rabuwa da juna.

  يا عليّ ، لا تجامع امرأتك من قيام ، فإنّ ذلك من فعل الحمير ، وإن قضي بينكما ولد كان بوّالا في الفراش ، كالحمير البوّالة تبول في كلّ مكان.

ya ali ka da ka jewa iyalinka a tsaye haqiqa hakan na daga dabi'ar jaki  idan an qaddara da tsakaninku zai kasance mai yawan fitsarin kwance kamar jaki mai yawan fitsari a dukkanin wajen da ya samu.

  يا عليّ ، لا تجامع امرأتك في ليلة الفطر ، فإنّه إن قضي بينكما ولد لم يكن ذلك الولد إلاّ كثير الشرّ .

ya ali ka da ka jewa iyalinka daren idil fitri , lalle idan an qaddara da tsaninku zai kasance mai yawan sharri.

يا عليّ ، لا تجامع امرأتك في ليلة الأضحى ، فإنّه إن قضي بينكما ولد يكون ذا ستّة أصابع أو أربعة

ya ali ka da ka jewa iyalinka daren idin babbar sallah, lalle idan an qaddar da tsakaninku zai kasance mai yatsu shida ko hudu.

يا عليّ ، وعليك بالجماع ليلة الاثنين ، فإنّه إن قضي بينكما ولد يكون حافظاً لكتاب الله راضياً بما قسّم الله عزّ وجلّ له

ya ali na umarce ka da jewa iyali daren litinin, lalle idan an qaddara da tsakaninku zai kasance mahaddacin qur'ani, mai yarda da abin da Allah ya hukunta.

   يا عليّ ، إذا جامعت أهلك في ليلة الثلاثاء فقضي بينكما ولد ، فإنّه يرزق الشهادة بعد شهادة أن لا إله إلاّ الله وأنّ محمّداً رسول الله ، ولا يعذّبه الله مع المشركين ، ويكون طيّب النكهة من الفم ، رحيم القلب ، سخيّ اليد ، طاهر اللسان من الغيبة والكذب والبهتان

ya ali idan ka jewa iyalinka daren talat , ubangiji ya qaddara da tsakaninku za a azurta shi da shaidawa bayan shaidawa da la'ilaha illal laha  wa anna muhammadar rasulallah, sannan kuma ya kasance mai qamshin baki, mai zuciya mai jin qai, mai kyautar hannu mai tsarkakakken harshe daga gulma qage da qarya.

يا عليّ ، وإن جامعت أهلك ليلة الخميس فقضي بينكما ولد ، يكون حاكماً من الحكّام أو عالماً من العلماء .

ya ali idan ka je ma iyalinka daren  alhamis  Allah ya qaddra da tsakaninku to zai kasance  shugaba da ga cikin shugabanni ko malami daga  malamai.

يا عليّ ، وإن جامعتها يوم الخميس عند زوال الشمس عن كبد السماء فقضي بينكما ولد ، فإنّ الشيطان لا يلزمه حتّى يشيب ويكون فهماً ، ويرزقه الله عزّ  وجلّ السلامة في الدين والدنيا

Ya ali iadan ka je ma iyalinka ranar alhamis  lokacinna ke zawali daga sama sai kuma Allah ya hukunta da tsakaninku, lalle shaidan bai lazimtar wannan da  Allah kuma zai azurta shi  da lafiya a cikin addininsa da duniyar sa.

   يا عليّ ، وإن جامعتها ليلة الجمعة وكان بينكما ولد ، فإنّه يكون خطيباً قوّالا مفوّهاً ، وإن جامعتها يوم الجمعة بعد العصر فقضي بينكما ولد فإنّه يكون معروفاً مشهوراً عالماً ، وإن جامعتها في ليلة الجمعة بعد العشاء الآخرة فإنّه يرتجى أن يكون لك ولد من الأبدال إن شاء الله تعالى

ya ali idan ka jewa iyalinka daren juma'a da ya kasance tsakininku, zai kasance masanin huduba da zance  mai zaqin kalami, idan kuma ka je masu ranar juma'a bayan la'asar ubangiji ya azurtaka da da  haqiqa zai kasance malami sananne mashahuri, idan kuma daren juma'a bayan isha'i ta qarshe, lalle ana fatan dan zai kasance daga masu zuhudu da gudun duniya da izinin Allah.

يا عليّ ، لا تجامع أهلك في أوّل ساعة من الليل ، فإنّه إن قضي بينكما ولد لا يؤمن أن يكون ساحراً مؤثراً للدنيا على الآخرة

ya ali ka da ka jewa iyalinka farkon dare, haqiqa idan ubangiji ya qaddara da tsakaninku bai aminta daga kasancewa boka ma'abocin sihiri mai fifita duniya kan lahira.

يا عليّ ، احفظ وصيّتي هذه كما حفظتها عن أخي جبرئيل (عليه السلام) .

 ya ali, ka kiyaye wasiyyata  kamar yadda na kiyaye ta daga dan'uwana jibrilu  (as).

يا عليّ ، لا تجامع امرأتك تحت شجرة مثمرة ، فإنّه إن قضي بينكما ولد ، يكون جلاّداً أو قتّالا أو عريفاً ـ  الكاهن 

ya ali, ka da ka jewa iaylinka qarqashin bishiyar mai `ya`ya, lalle idan Allah ya qaddara da tsakaninku zai kasance mai kisa ko boko matsafi.

 يا عليّ ، لا تجامع امرأتك في وجه الشمس وشعاعها إلاّ أن يرخى ستر فيستركما ، فإنّه إن قضي بينكما ولد لا يزال في بؤس وفقر حتّى يموت

ya ali, ka da ka jewa iyalinka cikin fuskar rana da haskenta face kun sanya labule da ya suturceku daga ita, lalle idan Allah ya qaddara da tsakaninku ba zai gushe cikin talauci da quncin rayuwa ba har mutuwarsa.

  يا عليّ ، لا تجامع امرأتك بين الأذان والإقامة ، فإنّه إن قضي بينكما ولد يكون حريصاً على إهراق الدماء

Ya ali ka da ka je wa iyalinka tsakanin kiran sallah da iqama, idan Allah ya qaddara da tsakaninku dan zai kasance mai kwadayin zubar da jinni.

  يا عليّ ، إذا حملت امرأتك فلا تجامعها إلاّ وأنت على وضوء ، فإنّه إن قضي بينكما ولد يكون أعمى القلب ، بخيل اليد

ya ali, idan matarka ta dau ciki  ka da ka je mata face ka na cikin alwala, haqiqa idan Allah ya qaddara da tsakaninku zai kasance mai makauniyar zuciya, marowaci.

يا عليّ ، لا تجامع أهلك في ليلة النصف من شعبان ، فإنّه إن قضي بينكما ولد يكون مشوّهاً ذا شامة في شعره ووجهه

ya ali, ka da ka jewa iyalinka daren nisfu sha'aban, haqiqa idan Allah ya qaddara da tsakaninku zai zama mummuna mai tawadar Allah cikin gashi da fuska.

   يا عليّ ، لا تجامع أهلك في آخر الشهر إذا بقي منه يومان ، فإنّه إن قضي بينكما ولد يكون عشّاراً أو عوناً للظالم ، ويكون هلاك فئام من الناس على يديه .

ya ali, ka da ka jewa iyalinka  cikin kwanaki biyun qarshen wata, haqiqa idan Allah ya qaddara da tsakaninku, zai kasance maha'inci ko mai taimakon azzalumai, sannan mutane masu yawa su halaka ta hannunsa.

يا عليّ ، لا تجامع أهلك على سقوف البنيان ، فإنّه إن قضي بينكما ولد يكون منافقاً مرائياً مبتدعاً .

ya ali, ka da ka zakkewa iyalinka kan rufin gida, haqiqa in Allah ya qaddara da tsakaninku zai kasance munafiqi dan bidi'a ma'abocin riya.

  يا عليّ ، إذا خرجت في سفر فلا تجامع أهلك تلك الليلة ، فإنّه إن قضي بينكما ولد ينفق ماله في غير حقّ . وقرأ رسول الله (صلى الله عليه وآله

ya ali, idan ka fito  tafiya to kada ka jewa iyalinka wannan dare, haqiqa idan Allah ya qaddara da tsakninku zai dinga bayar da dukiyar cikin tafarkin bata.

 sai manzon Allah (saw) ya karanta wannan aya:

إنَّ المُبَذِّرِينَ كَانُوا إخْوَانَ الشَّيَاطِينِ[7] 

lalle masu almubazzaranci sun kasance `yan'uwan shaidanu ne.

يا عليّ ، لا تجامع أهلك إذا خرجت إلى سفر مسيرة ثلاثة أيام ولياليهن ، فإنّه إن قضي بينكما ولد يكون عوناً لكلّ ظالم

ya ali, ka da ka jewa iyalinka idan ka fito tafiyar kwanaki uku da dare uku, haqiqa idan Allah ya qaddara da tsakaninku zai kasance mai taimakon azzalumi.

عن الصادق (عليه السلام) ، قال  : لا تجامع في أوّل الشهر ولا في وسطه ولا في آخره ، فإنّه من فعل ذلك فليستعدّ لسقط الولد ، وإن تمّ أوشك أن يكون مجنوناً ، ألا  ترى أنّ المجنون أكثر ما يتصرّع في أوّل الشهر ووسطه وآخره

2 – an karbo daga sadiq (as) ya ce : ka da ka jewa iyali cikin farkon wata da tsakiyarsa da qarshensa, haqiqa duk wanda ya aikata haka to shiryawa barin cikin, idan kuma ya cika to ya fi komai kusa da ya kasance mahaukaci, ashe baka lura da mahaukaci yawanci ya fi yin farfadiya farkon wata tsakiyar da qarshensa ba.

وعنه (عليه السلام) ، قال  : تكره الجنابة حين تصفرّ الشمس وحين تطلع وهي صفراء

3 – daga sadiq (as) ya ce :  makaruhi ne shiga janaba yayin da rana ta yi ruwan dorawa da lokacin hudowarta ta na ruwan dorawa.

وقال (عليه السلام)  : لا تجامع في السفينة ، ولا مستقبل القلبة ، ولا مستدبرها

4 – sadiq (as) ya ce: ka da ka kusanci iyali cikin jirgin ruwa, haka ma kana halin fuskantar alqibla, ko ba ta baya.

قال رسول الله (صلى الله عليه وآله)  : يكره أن يغشى الرجل المرأة وقد احتلم حتّى يغتسل من احتلامه الذي رأى ، فإن فعل ذلك فخرج الولد مجنوناً فلا يلومنّ إلاّ نفسه

5 – manzon Allah (saw) ya ce: makaruhi ne mutum ya je ma iyalinsa bayan ya yi mafarki ya na cikin janabar mafarkin face ya yi wanka, idan kuma ya qi hakan ya zakke to dansa ya fito mara hankali ka da ya zargi kowa face kansa.

وقال (صلى الله عليه وآله)  : من جامع امرأته وهي حائض فخرج الولد مجذوماً أو أبرص ، فلا يلومنّ إلاّ نفسه .

6 – ya ce: duk wanda ya zakkewa matarsa halin ta na haila sai da ya zo kuturu ko mai ciwon kuturta, ka da ya zargi kowa face kansa.

عن عبد الملك بن عمرو قال  : سألت أبا عبد الله (عليه السلام)  : ما لصاحب المرأة الحائض منها  ؟ فقال  : كلّ شيء ما عدا القبل بعينه . وفي آخر  : ما دون الفرج

7 – daga abdul malik dan amru ya ce:  na tambayi baban abdullah  (as) me mutumin da matarsa ta ke halin haila ya ke da shi daga gareta, sai ya ce: komai in banda farjinta.

من كتاب طبّ الأئمة ، قال رجل لأبي جعفر (عليه السلام)  : أيكره الجماع في وقت من الأوقات وإن كان حلالا  ؟ قال  : نعم ، من طلوع الفجر إلى طلوع الشمس ، ومن مغيب الشمس إلى مغيب الشفق ، وفي اليوم الذي تنكسف فيه الشمس ، وفي الليلة التي ينخسف فيها القمر ، وفى اليوم والليلة التي تكون فيها الريح السوداء ، أو الريح الحمراء أو الريح الصفراء ، واليوم والليلة التي تكون فيها الزلزلة ، وقد بات رسول الله (صلى الله عليه وآله) ليلة الخسف عند بعض نسائه فلم يكن منه فيها ما  كان منه في غيرها ، فقالت له حين أصبح  : يا رسول الله ، أبغضٌ كان منك لي في هذه الليلة  ؟ قال  : لا ، ولكن هذه الآية ظهرت في هذه الليلة فكرهت أن أتلذّذ بالهوى فيها ، وقد عيّر الله أقواماً بما فعلوا في كتابه فقال 

8 – daga littafin dibbul a'imma, wani mutum ya cewa baban jafar (as) shin ana qin yin jima'i cikin wani lokaci daga lokuta duk da cewa ya halasta ? sai ya ce:  na'am daga hudowar alfijir ya zuwa hudowar rana, haka daga faduwar rana ya zuwa buyan shafaqi, da ranar da rana ta ke kisfewa, da daren da wata yake kisfewa, da dare da ranar da baqar iska ke tasowa ko jar iska ko ruwan dorawa, haka lokutan girgizar qasa, haqiqa manzon Allah (saw) ya kwana wajen sashen matansa daren kusufi amma abin da ke afkuwa tare da su a ragowar dararen bai afku ba a wannan dare tsakaninsa da matasa, yayin da gari ya waye, sai ta ce: ya manzon Allah shin kana da wata qiyayya da ni ne cikin daren da ya gabata ? sai ya ce: a'a  sai dai cewa kasantuwar wannan aya da ta bayyana  cikin wannan dare sai na kyamaci jin dadi cikin daren.

Haqiqa Allah ya tozarta wasu mutane cikin littafin sakamakon abin da da suka aikato:

وَإنْ يَرَوْا كِسْفاً مِنَ                                                                          

السَّمَاءِ سَاقِطاً يَـقُولُوا سَحَابٌ مَرْكُومٌ * فَذَرْهُمْ  ) ( يخوضوا ويلعبوا ) (  حَتَّى يُلاقُوا يَوْمَهُمُ الَّذِي فِيهِ يُصْعَـقُونَ[8] 

 idan suka ga babbake daga sama ya na halin fadowa sai su ce wani girgije ne mai hauhawar juna * ka barsu har zuwa lokacin da za su hadu da ranar da za'a sumar da su.

قال أمير المؤمنين (عليه السلام)  : إذا أراد أحدكم أن يأتي زوجته فلا يعجّلها ، فإنّ للنساء حوائج ، إذا رأى أحدكم امرأة تعجبه فليأتِ أهله ، فإنّ عند أهله مثل ما  رأى ، ولا يجعلن للشيطان إلى قلبه سبيلا ، ليصرف بصره عنها ، فإن لم تكن له زوجة فليصلّ ركعتين ويحمد الله كثيراً ويصلّي على النبيّ وآله ، ثمّ ليسأل الله من فضله ، فإنّه يبيح له برأفته ما يغنيه ، إذا أتى أحدكم زوجته فليقلّ الكلام ، فإنّ الكلام عند ذلك يورث الخرس ، لا ينظرن أحدكم إلى باطن فرج امرأته لعلّه يرى ما يكره ويورث العمى .

9 – sarkin muminai ali (as) : idan dayanku ya nufi zakkewa matarsa to ka da yayi mata gaggawa, saboda lalle su ma mata suna da tasu buqatar, idan wani ya ga wata mace na burge shi to ya je ma iyalinsa haqiqa iyalansa na da irin abin da ya gani, ka da ya bawa shaidani mahalli cikin zuciyarsa, ya kauda idonsa daga matar da ba ta sa ba, idan bai da mace to yayi sallah raka'a biyu ya yawaita godiya ga Allah da salati ga annabi da iyalansa (as) sannan ya roqi Allah daga falalarsa, haqiqa Allah zai halasta masa abin da zai wadace shi, idan dayanku ya je ma iyalansa to ya qaranta yin surutu, haqiqa surutu yayin saduwa da iyali na gadar da bebanta, sannan ka da ya dinga kallon cikin farjin matarsa ta yiwu ya ga abin da ba ya so kuma yin hakan ya na gadar da makanta.

وقال (عليه السلام)  : إذا أراد أحدكم أن يأتي أهله فليتوقّ أوّل الأهلّة وأنصاف الشهور ، فإنّ الشيطان يطلب الولد في هذين الوقتين والشياطين يطلبون الشرك فيهما فيجيئون ويحبلون[9]

10 -  wani wajenku kuma ya ce: idan dayanku ya yi nufin jewa iyalansa  to ya guji farkon wata da tsakiyarsa, haqiqa shaidan na neman  wanda zai yi tarayya da shi cikin digon maniyyinsa  dansa a wadannan lokuta,  shaidanu na neman abokin tarayya  cikinsu suna zuwa su dana tarko.

عن الصادق (عليه السلام) ، عن آبائه (عليهم السلام) ، قال  : قال رسول الله (صلى الله عليه وآله)  : إذا تجامع الرجل والمرأة فلا يتعرّيان فعل الحمارين ، فإنّ الملائكة تخرج من بينهما إذا فعلا ذلك

11-daga sadiq (as) daga babanninsa (as) ya ce: manzon Allah (saw) ya ce: idan mata da miji suka sadu da juna ka suyi tsirara kamar jakuna, haqiqa mala'iku suna fita daga qarqashinsu  idan su ka aikata hakan.

ـ في تفسير عليّ بن إبراهيم ، في قوله تعالى  : (  نِسَاؤُكُمْ حَرْثٌ لَكُمْ فَأتُوا حَرْثَكُمْ أ نَّى شِئْتُمْ  ،[10] أي متى شئتم ، وتأوّلت العامّة قوله  : أنّى شئتم ، أي حيث شئتم في القبل أو الدبر ، قال الصادق (عليه السلام)  : أنّى شئتم ، أي حيث شئتم في

الفرج ، والدليل على قوله في الفرج قوله  : (  نِسَاؤُكُمْ حَرْثٌ لَكُمْ  ) فالحرث الزرع ، والزرع في الفرج في موضع الولد

 

12 -  cikin tafsirin ali dan ibarhim qummi  cikin fadin Allah madaukaki

matayenku gunakinku ku jema gonakinku ta inda kuka so ) baqara 223 , ma'ana duk lokacin da kuke so amma amawa sun yi tawili da cewa ku je musu ta farji da dubura, imam sadiq (as) ya ce : ai duk ta yanda ku ka so ammma fa a farji kawai , dalili kan haka fadinsa madaukaki ( matayenku gonakinku ) babu wajen shuka face farji nanne yaro ke samuwa.

قال الصادق (عليه السلام)  : من أتى امرأته في الفرج في أوّل حيضها فعليه أن يتصدّق بدينار ، وعليه ربع حدّ الزنا خمسة وعشرون جلدة ، وإن أتاها في آخر أيام حيضها فعليه أن يتصدّق بنصف دينار ويضرب اثني عشر جلدة ونصفاً

13 – sadiq (as) ya ce: duk wanda ya zakkewa  farjin matarsa cikin farkon  haila to ya zama wajibin kansa ya yi sadakar dinare guda, sannan za'a tsayar masa da daya bisa hudun haddin zina bulala 25 sannan wanda ya zakke cikin qarshen hailarta, to zai yi sadakar rabin dinare sannan ayi masa bulala shabiyu da rabi, abin da ake nufi dinare a yau shine misqalin gwal.

ونهى النبيّ (صلى الله عليه وآله) عن وطي الحبالى حتّى يضعن

14 – manzon Allah (saw) ya yi hani daga zakkema mata masu ciki har sai sun haihu.

قال الصادق (عليه السلام)  : إيّاك والجماع في الليلة التي يهلّ فيها الهلال ، فإنّك إن فعلت ثمّ رزقك ولداً كان مخبوطاً ، قلت  : جعلت فداك ، ولِمَ تكرهون ذلك يا بن رسول الله  ؟ قال  : أما ترى المصروع أكثرهم لا يصرع إلاّ في رأس الهلال

15 – sadiq (as) ya ce: ka guji jima'i daren da jinjirin wata ya ke bayyana, haqiqa kai idan ka aikata haka sannan Allah ya azurtaka da da wannan lokaci dan zai kasance mai fama da ciwon hauka, sannan ya ce: raina fansarka, me ya sa ku ke qin hakan ya dan manzon Allah (saw) ? sai imam ya ce: ashe baka ga yawancin mai farfadiya ba ya yi sai farkon  wata.

كره رسول الله (صلى الله عليه وآله) الجماع في الليلة التي يريد فيها الرجل سفراً ، وقال  : إن رزق ولداً كان حوالة

16 – manzon Allah ya karhanta yin jima'i daren da mutum zai yi tafiya.

Idan Allah ya qaddara da zai kasance me yawan canja fuska.

قال أبو جعفر (عليه السلام)  : إيّاك والجماع حيث يراك صبيّ يحسن أن يصف حالك . قلت  : يا بن رسول الله ، كراهة الشنعة  ؟ قال  : لا ، فإنّك إن رزقت ولداً كان شهرة وعلماً في الفسق والفجور ، وإيّاك أن تجامع أهلك وصبيّ ينظر إليك ، فإنّ رسول الله كان يكره ذلك أشدّ كراهة . قال رسول الله  : إيّاكم وأن يجامع الرجل امرأته والصبيّ في المهد ينظر إليهما

17 – baban jafar (as) ya ce: ka da ka yi jima'i inda yaro qarami zai ganka wanda zai iya bayanin halin da ya ganka ciki, sai na ce: ya dan manzon Allah (saw) shin haka na da karhanci mai tsanani ?  sai ya ce a'a  sai dai cewa idan ka samu da zai zama shahararre cikin fasiqanci da fajirci, na haneka da saduwa da iyalinka halin yaro qarami na kallonka, lalle manzon Allah (saw) ya kasance ya na qin haka tsananin qiyayya, manzon Allah (saw) ya ce: na haneku da zakkewa iyalinku halin yaro qarami na kwance kan shimfida ya na kallonsu.

عن أبي عبد الله (عليه السلام) ، قال  : قال رسول الله (صلى الله عليه وآله)  : والذي نفسي بيده لو  أنّ رجلا غشي امرأته وفي البيت صبيّ مستيقظ يراهما ويسمع كلامهما ونَفَسهما ما أفلح أبداً ، إن كان غلاماً كان زانياً ، أو جارية كانت زانية ، وكان عليّ ابن الحسين (عليهما السلام) إذا أراد أن يغشى أهله أغلق الباب وأرخى الستور وأخرج

الخدم .

18 – daga baban Abdullah (as) ya ce: manzon Allah (saw) ya ce: na rantse da wanda raina ke hannunsa da ace wani mutum  zai zakkewa matarsa halin gidan akwai yaro qarami  idonsa bude ya na ganinsu ya na jin kalamansu  da numfashinsu  to wannan mutum ba zai taba rabauta ba har abada, idan yaron bawa ne to zai kasance mazinaci, idan kuma kuyanga ce zata kasance mazinaciya, aliyu dan husaini (as) ya kasance idan ya nufi jewa iyalinsa sai ya rufe qofa ya saki labule kuma ya fitar da dukkanin hadimansa waje.

قال الصادق (عليه السلام)  : لا بأس أن ينظر الرجل إلى امرأته وهي عريانة . وفي خبر آخر  : وهل اللذّة إلاّ ذلك

19 – sadiq (as) ya ce: babu laifi mutum ya kalli matarsa tsirara, a wata riwayar kuma : shin akwai wani dadi da ya wuce haka.

عن عليّ (عليه السلام) ، قال  : يستحبّ للرجل أن يأتي أهله أوّل ليلة من شهر رمضان ، يقول الله تعالى  : (  اُحِلَّ لَكُمْ لَيْلَةَ الصِّيَامِ الرَّفَثُ إلَى نِسَائِكُم[11]ْ 

20 – daga aliyu (as) ya ce : mustahabbi ne mutum ya jewa iyalansa farkon watan Ramadan , Allah madaukaki na cewa : an halasta muku daren azumi jema iyalanku.

21 – manzon Allah (saw) ya  hana yawan surutu yayin jima'i , ya ce dan zai zamanto bebe.

22 – manzon Allah (saw) ya hana fuskantar alqibala ko bata baya yayin jima'i, duk wanda ya aikata haka to tsinuwar mala'iku ta tabbata kansa gaba dayansu.

23 – daga hannan dan sidir, daga babansa, ya ce: na ji baban abdullah  (as) ya na cewa: ka da mutum ya jema matarsa ko kuyangarsa halin akwai yaro gida, lalle hakan na cikin abin da ke gadar da zina, abin da ake nufi da gida a harshen riwaya shi ne daki, saboda makaruhi ne yin jima'i halain yaro ko yarinya na cikin daki.

24 – daga baban Abdullah (as) ya ce: abubuwa uku suna ruguza jiki kai har ta kai ga kasheshi : cin busashshen nama, shiga bandaki halin ciki na qoshe, da jima'in tsofaffi.

قَالَ أَمِيرُ الْمُؤْمِنِينَ ع إِذَا كَانَ بِأَحَدِكُمْ أَوْجَاعٌ فِي جَسَدِهِ وَ قَدْ غَلَبَتْهُ الْحَرَارَةُ فَعَلَيْهِ بِالْفِرَاشِ قِيلَ لِلْبَاقِرِ ع يَا ابْنَ رَسُولِ اللَّهِ مَا مَعْنَى الْفِرَاشِ قَالَ غِشْيَانُ النِّسَاءِ فَإِنَّهُ يُسَكِّنُهُ وَ يُطْفِئُهُ

 25 – wasu lokuta jima'in kan zama dalilin sauqaqa cututtuka, sarkin muminai ali (as) ya ce: idan dayanku na fama da radadi cikin jikinsa halin zafi ya yi galaba to ya jema shimfida, an tambayi imam baqir (as) ma'anar shimfida  ? sai ya ce : zakkewa mata, lalle ya na sauqaqa radadi da kasheshi.

ـ نهى النبيّ (صلى الله عليه وآله) أن يكثر الكلام عند المجامعة ، قال  : ويكون منه خرس الولد

26-manzon Allah(saw) ya hana  yawaita surutu yayin saduwa da iyali, yace yaro zai zma baibe idan ana aikata hakan.

ونهى أن يجامع الرجل أهله مستقبل القبلة وعلى ظهر طريق عام ، فمن فعل ذلك فعليه لعنة الله والملائكة والناس أجمعين

27- sannan kuma ya hana mutum saduwa da iyali yana mai fuskantar alqila haka kan hanya, yace: duk wanda ya aikata haka Allah ya tsine masa tareda mala'iku gabadayansu.

عن حنان بن سدير ، عن أبيه ، قال  : سمعت أبا عبد الله (عليه السلام) يقول  : لا يجامع الرجل امرأته ولا جاريته وفي البيت صبيّ ، فإنّ ذلك ممّـا يورثه الزنا

28-Daga hannan da sadiru daga babansa, ya ce:. Na ji baban Abdullah(as)ya na cewa: ka da mutum ya sadu fda matarsa  alhalin akwai yaro cikin gida haka kada ya aikata hakan da baiwarsa alhalin akwai yaro cikin gida, lalle aikata hakan na daga cikin abinda o zina.

عن أبي عبد الله (عليه السلام) ، قال  : ثلاث يهدمن البدن وربما قتلن  : أكل القديد القاب ، ودخول الحمّـام على البطنة ، ونكاح العجائز

29- daga baban Abdullah(as) ya ce: abubuwa uku na ruguza jiki kai suna iya halaka shi: cin busashshen nama, shiga bandaki ckina na qoshe, saduwa da tsofaffi.

وربما الجماع ممّـا يوجب تسكين الأوجاع ، قال أمير المؤمنين (عليه السلام): إذا كان بأحدكم أوجاع في جسده وقد غلبته الحرارة فعليه بالفراش ، قيل

للباقر  (عليه السلام)  : يا بن رسول الله ، ما معنى الفراش  ؟ قال  : غشيان النساء ، فإنّه يسكنه ويطفيه

30-Sau da yawa jima'i ya zama sababin samun saukin radadin ciwuka, sarkin muminai{as} yana cewa: idan daya ya kamu da ciwuka cikin jikinsa wanda zafin ciwon yay i galaba to ya lazimci shimfida, an tamabayi imam (as) me ake nufi da shimfida? Sai y ace: zakkewa mata. Lalle hakan nan a kasha radadin ciwo.

وفي حكم ترك المقاربة فيما زاد عن أربعة أشهر ، عن أبي الحسن الرضا (عليه السلام) ، أ نّه سأله عن الرجل يكون عنده المرأة الشابة فيمسك عنها الأشهر والسنة لا يقربها ليس يريد الإضرار بها يكون لهم مصيبة أيكون في ذلك آثماً  ؟ قال  : إذا تركها أربعة أشهر كان آثماً بعد ذلك . وفي خبر آخر زاد فيه  : إلاّ أن يكون بإذنها .

 

31– cikin hukuncin barin jima'i fiye da watanni hudu, daga baban hassan rida (as) wani mutum ya tambaye shi game da mutumin da ke da mata matashiya sai ya daina takarta har tsawon watanni ko ma ya kai shekara, shi kuma bai nufin cutar da ita ko kuma wata musifa ta kasance musu, shin ya aikata sabo ? sai ya ce: idan ya haura wattanni hudu ya aikata sabo, wata riwayar an qara da cewa: sai dai idan ya nemi izininta.

عن أبي عبد الله (عليه السلام) ، قال  : من جمع من النساء ما لا ينكح فزنى منهن شيء فالإثم عليه

32-daga baban Abdullah (as) ya ce: duk wanda ya auri  mata da yawa amma kuma ba ya saduwa da su, sai wani abu ya yi zina da su to laifin na kansa.

وفي نكاح الدبر ، قال رسول الله (صلى الله عليه وآله)  : محاش النساء على اُمّتي حرام[12]

33 – cikin zakkewa dubura, manzon Allah (saw) ya ce : duburar mata ta haramta kan al'umma.

عن أبي عبد الله (عليه السلام) قال  : سألته عن إتيان النساء في أعجازهن فقال  : هي لعبتك لا تؤذها

34 – an karbo daga baban Abdullah (as) ya ce : na tambaye shi kan zakkewa mata ta dubura , sai ya ce : kayan wasanka ka ne ka da ka cutar da ita.

Makaruhi ne yin jima'i sanye da hatimi da ya ke dauke da sunan Allah, ko kuma wani abu daga ayoyin qur'ani.

عن عليّ ، عن أخيه الإمام الكاظم (عليه السلام) ، قال  : سألته عن الرجل يجامع أو يدخل الكنيف وعليه خاتم فيه ذكر الله أو شيء من القرآن أيصلح ذلك  ؟ قال  : لا

35 daga aliyu daga dan'uwansa imam kazeem (as) ya ce: na tambaye shi kan mutumin da ya ke zakkewa ya ke shiga bayan gida  halin ya na sanye da hatimi wanda cikinsa akwai sunan Allah ko kuma wani abu daga ayoyin qur'ani, shin hakan ya inganta ? sai ya ce : a'a [1] Biharul anwar m 100 sh 285

[2] Wasa'ilul shi'a m 20 sh 110 bugum mu'assasar ahlulbaiti

[3] Wasa'ilul shi'a m 20 sh 117

[4] Qurbul  isnad:102

[5] Uyunul akhbar m 2 sh 38

[6] Alwafi m 12 sh 724

[7] Isra'i:27

[8] Durr:44-45

[9] Biharul anwar m 100 sh 223

[10] Baqara:223

[11] Baqara:187

[12][12] Wasa'ilul shi'a m 20 sh 143