فهرست کتاب‌‌ لیست کتاب‌ها
■ KALMAR TARBIYYA CIKIN HARSHEN LARABCI DA YANDA AKA YI 4
■ FASALI NA ( 2 ) 24
■ AUREN DABI'A 24
■ FASALI NA 3
■ FASALI NA 4 73
■ FASALI NA 5 131
■ FASALI NA 6 176
HAQQOQIN DA MA'AURATA SU KAYI TARAYYA CIKI 177
1 – HAQURI 178
2 – KAMEWA DAGA ZALUNCI DA CUATARWA 179
HAQQOQIN MATA 180
CIYARWA DA YALWATAWA 185
TAUSAYAWA DA KAMEWA DAGA ZALUNCI 187
KAMEWA DAGA BARIN DUKA MAI CUTARWA 187
UMARNI DA KYAKKYAWA DA HANI DA MUMMUNA 193
GARKUWA 196
8 – KYAUTATAWA : 196
9 - KYAWUNTA ZAMANTAKEWA 197
3 – TAUSAYAWA MIJI : 208
4 – HIMMATUWA DA KULA DA CIKIN GIDA DA KAYYAKINSA : 209
5 - HIMMATUWA CIKIN SAUKE HAQQOQI 209
6 – JIMA'I 210
7 - ADO 213
8 – KAMEWA CIKIN MAGANA : 219
SHUGABANTAR IYALI 225
DALILAI DA SUKE SANYA DAWWAMAR AURE 227
1 – SON JUNA 228
2 – YAWAITA AIKATA ALHERI: 228
4 – SANYA FARIN CIKI: 229
5 – BIYAYYA DA NEMAN YARDAR MIJI: 230
6 – KIYAYE MUTUNCI DA DUKIYA : 230
7 – TAIMAKO DA TALLAFAWA 230
8 – TARBAR MIJI DA KYAWUNTA BANKWANA DA SALLAMA : 231
9 – KALAMIN AQIDOJI MAI KYAWU DA QARFAFAFFEN FURUCI. 232
10 – KARBAR UZURI DA YIWA JUNA UZURI : 232
11 – BINSU SANNU SANNU CIKIN KOWANNE HALI : 233
12 – KYAWUNTA LAFAZI CIKN KOWANNE YANAYI : 233
13 – RASHIN SAURARON KYAUTATA AIKI DARI BISA DARI 233
14 – RASHIN IKON DAUKAR NAUYI A RAYUWANCE : 234
15 – RASHIN GORI KAN MIJI : 234
16 – RASHIN QAURACEWA AL'AMARIN SHIMFIDA: 235
17 - YIN SHAWARA DA MATA BANDA BIYE MUSU: 235
18 – TAKA TSAN TSAN DA KUMA FARKAWA : 238
19 – HANKALTA 239
20 - MIJI SHI NE MUTUNCIN MATARSA 240
21 – KISHI 240
22 – TAIMAKEKENIYYA 242
23 – DADADAWA IYALI 243
27 – WATSI DA BOAKANCI DA TSAFE TSAFE : 244
28 - HIDIMA MADAWWAMIYA 245
29 – GODIYA 246
29 – QAUNAR JUNA 247
TSINTUWA GUDA BIYU GIDAN ALI DA FATIMA (AS) 248
■ FASALI NA 8 252

HAQQOQIN DA MA'AURATA SU KAYI TARAYYA CIKI 177

HAQQOQIN DA MA'AURATA SU KAYI TARAYYA CIKI

rayuwar aure ta banbanta da waninta  kasantuwar Allah matsarkaki ya sanya qauna da tausayi tsakanin mata da miji, wadannan abubuwa biyu jigo ne da asasi cikin ingantar iyali, da kamalar haduwar kai da fuskantar juna da gudanar al'amura kamar yadda ake buqata, da warwarewar matsaloli da galaba kan wahalhalu  dukkanin haka albarkacin qauna soyayya tare da biyayya da tausasawa.

rayuwar da soyayya da tausasawa ke shugbanta haqiqa wannen rayuwa ba komai bace face rayuwar aljanna, aljanna kuma gidan hutu ne ga muminai wacce rahamar ubangiji ke kewaye da ita  da qauna madawwamiya, cikinta  babu baqin ciki  ba wahala  babu cece kuce, haka kuma gida ne wanda turaren qauna da qamshi rahama ke ta shi cikinsa.

amma tare da haka Allah ya sanya haqqoqi da su ka kebantu da mazaje, kamar yadda ya sanya haqqoqi da su ka kebantu ga mata , saboda kowa ya san iyakarsa, kada ya yi gangan cin ketare wannan iyakoki  saboda dagawa da zalunci  da nuna isa, akwai dokoki da ke lazimtar miji da ya zama wajibi ya kiyaye su, kamar yadda su ke kan mata, sannan akwai wadanda kuma shi da ita su kayi tarayya ciki, zamu kawo kadan daga riwayoyi, gabanin kawo riwayoyi ya kamata muyi dan bayani kan ma'anar haqqi, haqiqa Kalmar: الحق a harshen larabaci  ta na da ma'anar tabbatacen abu, sannan kuma suna daga sunayen Allah kyawawa kamar yadda ya zo cikin fadinsa:

سَنُرِيهِمْ آيَاتِنَا فِي الآ فَاقِ وَفِي أ نْفُسِهِمْ حَتَّى يَـتَبَـيَّنَ لَهُمْ أ نَّهُ الحَقّ[1]ُ 

  da sannu zamu nuna musu ayoyin mu cikin sasanni da kawunansu har ya bayyananr musu lalle cewa shi gaskiya ne.[2]

sannan Kalmar haqqu a ma'anar isdilahi shi ne cewa: abin da ya tabbata ta hanyar hankali da shari'a.

sannan a fiqihu ya na dan banbanta da kasancewa shi haqqi shi ne abin da tabbatuwarsa ke hannun Allah matsarkaki, sai dai cewa watsi da shi wasu lokuta na komawa hannun ma'abocin haqqi, misalign haqqin zabi cikin cinikin da a kayi a mahalllin da mai siya da mai sayarwa suke tare, mai siya yana iya zabar fasa sayen kayan matuqar bai bar mahallin da ya saye kayan ba.

sannan haqqoqin ma'aurata  wani lokaci sukan kasancewa na shari'a, kamar yanda ake cewa bai daga haqqin miji sanya matarsa wankin  tufafi da dafa abinci  kai hatta shayar da dansa in banda shayar farko yayin da ta haifeshi, ya halasta gareta ta karbi ladan shayar masa da da, shi ma kuma namiji na da haqqin auren mata hudu, saboda haka abin da ya fi kamata shi ne yin sulhu da sassautowa kowa ya haqura da wani kaso cikin haqqinsa, mace ta dauki nauyin ayyukan gida ta yi ma mijinta hidima da dukkanin abin da ya ke so, a gefe guda shi kuma ya haqura da qaro aure wannan duka cikin misali.

abin da ake nufi daga bayanin haqqoqin ma'aurata  wadanda suka yi tarayya ciki da wadanda kowanne dayansu ya kebantu da na shi cikin wannan fasali ba haqqoqi na shari'a ne ba kadai har da na kyawawan dabi'u da tarbiyya da mu ka fito da su daga hadisai, amma haqqoqin da suka yi tarayya kai daga cikinsu:[1] Fussilat:53

[2] Fussilat:53