فهرست کتاب‌‌ لیست کتاب‌ها
■ KALMAR TARBIYYA CIKIN HARSHEN LARABCI DA YANDA AKA YI 4
■ FASALI NA ( 2 ) 24
■ AUREN DABI'A 24
■ FASALI NA 3
■ FASALI NA 4 73
■ FASALI NA 5 131
■ FASALI NA 6 176
HAQQOQIN DA MA'AURATA SU KAYI TARAYYA CIKI 177
1 – HAQURI 178
2 – KAMEWA DAGA ZALUNCI DA CUATARWA 179
HAQQOQIN MATA 180
CIYARWA DA YALWATAWA 185
TAUSAYAWA DA KAMEWA DAGA ZALUNCI 187
KAMEWA DAGA BARIN DUKA MAI CUTARWA 187
UMARNI DA KYAKKYAWA DA HANI DA MUMMUNA 193
GARKUWA 196
8 – KYAUTATAWA : 196
9 - KYAWUNTA ZAMANTAKEWA 197
3 – TAUSAYAWA MIJI : 208
4 – HIMMATUWA DA KULA DA CIKIN GIDA DA KAYYAKINSA : 209
5 - HIMMATUWA CIKIN SAUKE HAQQOQI 209
6 – JIMA'I 210
7 - ADO 213
8 – KAMEWA CIKIN MAGANA : 219
SHUGABANTAR IYALI 225
DALILAI DA SUKE SANYA DAWWAMAR AURE 227
1 – SON JUNA 228
2 – YAWAITA AIKATA ALHERI: 228
4 – SANYA FARIN CIKI: 229
5 – BIYAYYA DA NEMAN YARDAR MIJI: 230
6 – KIYAYE MUTUNCI DA DUKIYA : 230
7 – TAIMAKO DA TALLAFAWA 230
8 – TARBAR MIJI DA KYAWUNTA BANKWANA DA SALLAMA : 231
9 – KALAMIN AQIDOJI MAI KYAWU DA QARFAFAFFEN FURUCI. 232
10 – KARBAR UZURI DA YIWA JUNA UZURI : 232
11 – BINSU SANNU SANNU CIKIN KOWANNE HALI : 233
12 – KYAWUNTA LAFAZI CIKN KOWANNE YANAYI : 233
13 – RASHIN SAURARON KYAUTATA AIKI DARI BISA DARI 233
14 – RASHIN IKON DAUKAR NAUYI A RAYUWANCE : 234
15 – RASHIN GORI KAN MIJI : 234
16 – RASHIN QAURACEWA AL'AMARIN SHIMFIDA: 235
17 - YIN SHAWARA DA MATA BANDA BIYE MUSU: 235
18 – TAKA TSAN TSAN DA KUMA FARKAWA : 238
19 – HANKALTA 239
20 - MIJI SHI NE MUTUNCIN MATARSA 240
21 – KISHI 240
22 – TAIMAKEKENIYYA 242
23 – DADADAWA IYALI 243
27 – WATSI DA BOAKANCI DA TSAFE TSAFE : 244
28 - HIDIMA MADAWWAMIYA 245
29 – GODIYA 246
29 – QAUNAR JUNA 247
TSINTUWA GUDA BIYU GIDAN ALI DA FATIMA (AS) 248
■ FASALI NA 8 252

HAQQOQIN MATA 180

 

                                  HAQQOQIN MACE    

mace abokiyar rayuwa ta na haqqi kan mijinta kamar yanda shi ya ke da haqqi kanta, wajibi kan miji ya kiyaye  haqqoqinta har ya zamanto igiyar alaqarsu ta aure ta samu qarfafa, duk wanda ya ketare iyaka zai koma kishiya sai ya lazimta kishinyanta tsakanin mutane biyu da ke rayuwa qarqashin rufi guda,  nauyi ya hau kan wuyansu na kiyaye tsarinsu da na tarbiyar iyali, kowanne daya daga ckinsu idan ya shallake iyakarsa ya qi aiki da abin da ya hau kansa daga kula da haqqin dan'uwan tarayyarsa a aure, lalle babu shakka zai kai ga lalacewar rayuwarsu ta tarayya, sannan ya zama sunyi asarar `ya`yansu, da afkar da radadi ga kawukansu kai har ma da makusantansu, ta yiwu ya kai ga zubar da jini  da keta alfarma  da rushewar al'umma da lalacewarta,

da farko ya zama wajibi miji ya yi mu'amala da matarsa da iyalinsa cikin qauna  da tausasawa, sannan ya kiyaye haqqoqin matarsa cikin kyautatawa da tausasawa, ya   yi koyi da annabawan Allah da cika makinsu manzon Allah (saw) da zuriyarsa tsarkaka.

قال النبيّ (صلى الله عليه وآله)  : خيركم خيركم لأهله ، وأنا خيركم لأهلي

manzon Allah (saw) ya ce: mafi alheri cikinku shi ne wanda ya kasance alheri ga iyalansa, ni ne mafi alherin cikinku saboda kasantuwa alheri ga iyalina.

haka na nufin  cewa miji  ya kamata ya kasance daga ma'abot alheri,   ayyukan suna da yawn gaske alheri, dukkanin mai hankali bai jahilce su ba, sannan mafi kusa da jibantawa alheri su ne makusantanka, mafi kusa gareka sune mahaifanka sannan matarka.

manzon Allah (saw) ya buga mafi kyawun misali cikin rayuwarsa a wannan babi, haka imamai tsarkaka  (as) haqiqa rayuwarsu fitila ce mai haske  cikin hanyar arziqi  da rayuwa mani'imciya, kalmominsu na haske da ke dauke da ilimi da wayewa ga wanda ke son ya rayu cikin arziqi da mutuwa cikin arziqi, haqiqa sun yi bayanin haqqoqi da iyakoki  cikin kowanne abu, me ya fi kyawu daga abin da imam sajjad (as) ya fadi : cikin risalarsa ta haqqoqi: mutum tare da ubangijinsa, tare da kansa, tare da waninsa.

وفي حقّ الزوجة يقول (عليه السلام) بما هو الجامع والأساس لكلّ الحقوق الزوجية  : وأمّا حقّ الزوجة  : فأن تعلم أنّ الله عزّ وجلّ جعلها لك سكناً واُنساً ، فتعلم أنّ ذلك نعمة من الله عليك ، فتكرمها وترفق بها ، وإن كان حقّك عليها أوجب فإنّ لها عليك أن ترحمها لأ نّها أسيرك وتطعمها وتسقيها وتكسوها ، وإذا جهلت عفوت عنها .

1- imam sajjad (as) ya na cewa: kan haqqin matarka, amma haqqin matarka : shi ne ka san cewa lalle Allah mai girma da daukaka ya sanya ta nutsuwa da debe haso gareka, ka san cewa hakan ni'ima ce kanka, sai ka girmamata ka tausaya mata, duk da cewa haqqinka da ke kanta yafi zama wajabi, lalle ta na haqqi kanka da ka tausaya mata saboda ta zama daurarriyarka wajibi ka ciyar da ita ka shayar da ita  ka kuma tufatar da ita, idan ta zoma da jahilci kayi mata afuwa.

me ya fi kyawu daga wadannan qa'idoji da asalai na farin cikin rayuwar aure: da farko kasancewa Allah madaukaki ya sanya ta nutsuwa gareka, haka na nufin ka samu yaqini kan cewa manufar aure  shi ne samun nutsuwa  da hutu, hakan na tabbatuwa ta hanyar kusantuwa da matarka, kamar yadda mutum ke samun hutu da nutsuwa cikin gidan da ya ka zaune, to wajibi kansa ya yi kai kawo wajen gyara shi  da gina shi da yi masa ado, to haka al'amarin ya ke cikin matar da ka ke aure,  ya zama dole ka lallabata  ka kaucewa dukkanin abin da zai bata mata rai, ka yi kai kawo wajen gyaranta  da abin da ya ke maslaha gareta.

na biyu: debe haso: ta yiwu ka samu wanda ka ke nutsuwa da shi amma ba ka samun debe haso ta hanyarsa, sai imam (as) ya jinginawa nutsuwa debe haso na jiki da ruhi kamar yadda Allah ya jinginawa sanyi da aminci cikin wutar namarudu  ga ibarhim (as) ba da ban lafiya ta kasance ba ta yiwu sanyin ya kasance mai tsanani wanda zai iya kaiwa ga halaka, ubangiji na cewa:

كُونِي بَرْداً وَسَلاما[1] 

 ya ke wuta ki kasance sanyi da aminci ga Ibrahim.

na uku : kasan cewa hakan ni'ima ce daga Allah gareka, macen da ka ke samun nutsuwa ya zuwa gareta da debe haso da ita da samun qaunarta wannan ni'ima ce daga Allah, haka al'amarin ya ke dangane ga mace haqiqa miji nagari na daga cikin ni'imar Allah gareta, haqqin ni'ima shi ne nuna godiya.

na hudu: ka karammata: imam ya bayyana cewa godiya kan wannan ni'imar shi ne  ka karrama matarka da dukkanin abin da ke daukar ma'anar karramawa, daga karramawa shi ne tausasawa da nuna qauna  da kyawunta mu'amala tsakaninka da ita.

na biyar: tausayi: tausaya mata cikin kalami da yafiya da soyayya, ka zama abokinta mai tausaya mata cikin tafiya da  zamanka gida sai ka kiyaye ladubban abokantaka da makwabtaka ka da ka dinga tabo dukkanin abin da zai jawo bacin ranta.

na shida: duk da cewa haqqinka ya fi zama wajibi  kanta yayin da ka ke amfani da wadannan hanyoyi da dabaru da tausasawa ka da kayi tunanin cewa haqqinta ya fi na ka yawa, namiji ya fi mace yawan haqqoqi, sai dai cewa yawan haqqoqi  da ba'arin  fifiko  na cikin al'umma bisa la'akari da kasantuwarsa namiji bai nufi cewa namiji ya takewa mace haqqinta da yin alfahari kanta, abin da zai iya kaiwa ga munanawa da rigima, ya kuma sanya ta neman haqqinta daga gareshi, duk da cewa ka fita yawan haqqoqi bai nufin ka qauracewa tausasa mata, saboda mace na haqqin kan namiji da ya tausaya mata, hujja kan haka shi ne ita daurarriyar gidanka ce tana cikin igiyar aurenka, kuma wanda aka daure ya na buqatar binsa sannu a hankali  da tausasawa  har ya kai ga ka farauci zuciyarsa, amma ta fuskanin tattalin arziqi da batutuwan zahiri, to daga haqqoqinta  kanka:

na bakwai ciyarwa, shayarwa, tufatarwa,  wadannan al'amura  na qarqashin abin da ake kira nafaqa (ciyarwa ) yayin da ciyar da ita ke wajaba kan mijinta da abin da ya da ce da ita  cikin gidan da tabaro na mahaifana, wajibi kan mijinta ya kiyaye wannan al'amari.

na takwas : idan ta zo maka da jahilci ka yi mata afuwa:  babu shakka idan afuwa da kau da kai ta shiga cikin rayuwar aure ba makawa rayuwa za ta kasance cikin farin ciki da kwanciyar hankali, jahilci ya canja zuwa ilimi, qiyayya ta juya zuwa abota da qauna.

abin mamaki duk da kasantuwa qarya ta haramta ta kuma kasance cikin munana siffofi, sai dai cewa saboda kare tsarin iyali wani lokaci mace kan neman abin da mijinta bai da iko kai, to a irin wannan lokaci ya halasta ya yi mata alqawari zai saya mataabin da ta buqata, amma idan ya dawo gida kawai saiya nuna ya manta da wancan alqawari.

الإمام الصادق عن آبائه ، قال  : قال رسول الله (صلى الله عليه وآله)  : ثلاثة يحسن فيهن الكذب  : المكيدة في الحرب ، وعدتك زوجتك ، والإصلاح بين الناس[2]

haqiqa ya zo cikin hadisi daga imam sadiq (as) daga babanninsa, ya ce : manzon Allah (saw) ya ce :  qarya ta kyawunta cikin abubuwa uku : shirya kaidi cikin yaqi , cikin alqawarin da kayiwa matarka  , cikin sulhunta tsakanin mutane.

haqqoqinta cikin abubuwan da za su zo kamar haka:

mijinta ya yafe mata  yayin da ta aikata masa kuskure, ta yiwu saboda qarancin gogewa ko duhun kai da jahilci ya sanya ta ke cutar da mijinta, shi kuma ya kamata ya yi mata afuwa musammam idan ta nemi hakan.

سأل إسحاق بن عمّـار أبا عبد الله (عليه السلام) عن حقّ المرأة على زوجها  ؟ قال  : يشبع بطنها ، ويكسو جثّتها ، وإن جهلت غفر لها ـ  أي عليها أوّلا أن لا تجهل

5 – is'haq dan ammar ya tambayi baban Abdullah (as) kan haqqin mace kan mijinta ? sai ya ce: ya qosar da cikinta, ya tufatar da jikinta idan ta zo masa da jahilci ya gafarta mata, sannan ita kuma ta qauracewa aikata jahilcin.

إنّ إبراهيم خليل الرحمن (عليه السلام) شكا إلى الله عزّ وجلّ خُلق سارة ، فأوحى الله إليه أنّ مثل المرأة مثل الضلع ، إن أقمته انكسر ، وإن تركته استمتعت به ، قلت  : من قال هذا  ؟ فغضب ، ثمّ قال  : هذا والله قول رسول الله (صلى الله عليه وآله) ، وعنه قال  : كان لأبي  عبد الله (عليه السلام) امرأة وكانت تؤذيه فكان يغفر لها

6 haqiqa annabi Ibrahim (as) ya kaiwa Allah kukan halayyar matasra saratu, sai Allah ya yi wahayi zuwa gareshi cewa misalin mace misalin qashin awaga ne, idan ka ce sai ka miqar da shi sai ya karye, idan kuma ka kyaleshi sai ka ji dadinka da shi, sai na ce waye ya fadi haka ? sai imam ya fusata,  ya ce wallahi fadin manzon Allah (saw) haka ma an karbo daga gareshi ya ce: baban abdullah ya kasance ya na da wata kuyanga ta na cutar da shi amma kuma shi ya na gafarta mata.

daga cikin kyawawan siffofi, bari ma ana kidaita shi  cikin jagaba kyawawan dabi'u,  asasin dukkanin dabi'a shi ne haquri , mumini shi ne mai yawan haquri da natsuwa yayin musibu masu girgizarwa, haqurin  mumini nayin tajalli tare da matarsa  ko da kuwa ta kasance ma'abociyar miyagun halayya, lalle shi ya na gafarta mata sakamakon jahilcinta, kai ya na jurewa cutarwarta musammam cikin munanan kalamanta da mu'amalarta mara kyawu, mai ya fi girma daga ladan wanda ya rungumi wannan haquri.

قال (عليه السلام)  : من احتمل من امرأته ولو كلمة واحدة ، أعتق الله رقبته من النار ، وأوجب له الجنّة ، وكتب له مائتي ألف حسنة ، ومحا عنه مئتي ألف سيّئة ، ورفع له مائتي ألف درجة ، وكتب الله عزّ وجلّ له بكلّ شعرة على بدنه عبادة سنة

7 Imam (as) ya ce: duk wanda ya jurewa wani abu mara kyawu daga matarsa ko da kuwa kalma ce guda daya, Allah zai `yanta wuyansa dga wuta, ya bashi aljanna, ya rubuta masa kywawan ayyuka dubu dari biyu , ya goge masa munana ayyuka dubu dari biyu, ya daga masa daraja dubu dari biyu, ya rubuta masa lbadar shekara ga dukkanin silin gashin jikinsa.

da misalin wannan lada mai girma ta qaqa mumini ba zai jurewa cutarwa matarsa ba  , ta qaqa rayuwarsa ba za ta ksance cikin arziqi da farin ciki ba, duk yadda mace takai cikin jahilci ta na da hankali da tausayi  , idan ta fahimci yadda mijinta ke haquri da ita , to wata rana za ta gane cewa abubuwan da ta ke bai da ce kuma kuskure ne , sannan za ta yi qoqarin ganin ba maimaita haka nan gaba , za ta canja da yi masa mu'amala da kyautatawa ta kame daga cutar da shi , za ta fuskanci qimar miji mai haquri da jurewa ba za ta nemi sauyinsa da duniya da abin da ke cikinta ba.[1]anbiya:69

[2]Biharul anwar m 100 sh 242