فهرست کتاب‌‌ لیست کتاب‌ها
■ KALMAR TARBIYYA CIKIN HARSHEN LARABCI DA YANDA AKA YI 4
■ FASALI NA ( 2 ) 24
■ AUREN DABI'A 24
■ FASALI NA 3
■ FASALI NA 4 73
■ FASALI NA 5 131
■ FASALI NA 6 176
HAQQOQIN DA MA'AURATA SU KAYI TARAYYA CIKI 177
1 – HAQURI 178
2 – KAMEWA DAGA ZALUNCI DA CUATARWA 179
HAQQOQIN MATA 180
CIYARWA DA YALWATAWA 185
TAUSAYAWA DA KAMEWA DAGA ZALUNCI 187
KAMEWA DAGA BARIN DUKA MAI CUTARWA 187
UMARNI DA KYAKKYAWA DA HANI DA MUMMUNA 193
GARKUWA 196
8 – KYAUTATAWA : 196
9 - KYAWUNTA ZAMANTAKEWA 197
3 – TAUSAYAWA MIJI : 208
4 – HIMMATUWA DA KULA DA CIKIN GIDA DA KAYYAKINSA : 209
5 - HIMMATUWA CIKIN SAUKE HAQQOQI 209
6 – JIMA'I 210
7 - ADO 213
8 – KAMEWA CIKIN MAGANA : 219
SHUGABANTAR IYALI 225
DALILAI DA SUKE SANYA DAWWAMAR AURE 227
1 – SON JUNA 228
2 – YAWAITA AIKATA ALHERI: 228
4 – SANYA FARIN CIKI: 229
5 – BIYAYYA DA NEMAN YARDAR MIJI: 230
6 – KIYAYE MUTUNCI DA DUKIYA : 230
7 – TAIMAKO DA TALLAFAWA 230
8 – TARBAR MIJI DA KYAWUNTA BANKWANA DA SALLAMA : 231
9 – KALAMIN AQIDOJI MAI KYAWU DA QARFAFAFFEN FURUCI. 232
10 – KARBAR UZURI DA YIWA JUNA UZURI : 232
11 – BINSU SANNU SANNU CIKIN KOWANNE HALI : 233
12 – KYAWUNTA LAFAZI CIKN KOWANNE YANAYI : 233
13 – RASHIN SAURARON KYAUTATA AIKI DARI BISA DARI 233
14 – RASHIN IKON DAUKAR NAUYI A RAYUWANCE : 234
15 – RASHIN GORI KAN MIJI : 234
16 – RASHIN QAURACEWA AL'AMARIN SHIMFIDA: 235
17 - YIN SHAWARA DA MATA BANDA BIYE MUSU: 235
18 – TAKA TSAN TSAN DA KUMA FARKAWA : 238
19 – HANKALTA 239
20 - MIJI SHI NE MUTUNCIN MATARSA 240
21 – KISHI 240
22 – TAIMAKEKENIYYA 242
23 – DADADAWA IYALI 243
27 – WATSI DA BOAKANCI DA TSAFE TSAFE : 244
28 - HIDIMA MADAWWAMIYA 245
29 – GODIYA 246
29 – QAUNAR JUNA 247
TSINTUWA GUDA BIYU GIDAN ALI DA FATIMA (AS) 248
■ FASALI NA 8 252

UMARNI DA KYAKKYAWA DA HANI DA MUMMUNA 193

UMARNI DA KYAKKYAWA DA HANI DA MUMMUNA

dole ne da farko mai kula da gida ya zamato ya na da tarbiyya ya kasance mumini mai kula da addininsa mai riqo da qarfaffiya igiyar Allah, mai sauki farillansa na ibada da mu'amala, da qauracewa dukkanin abubuwan da suka haramta kai hatta makaruhi, misalin irin wannan uba da ya yi nasara zai iya kasance malami na farko cikin iyali, za a dinka karkata da koyi da kyawawan dabi'unsa a fade da aikace, kamar yadda zai zamanto mai nasiha da wa'azi, kowanne lokaci ya na mai yiwa matars da `ya`yansa nasiha da koyar da su littafi da hikima, da shiryar da su ya zuwa tafarki da hanya miqaqqa, tayiwu yanayi ya hana damar tabbatar da abin da ya ke son tabbatarwa, kamar yanda muhallin da ya ke zaune na da tasiri kan mata da `ya`ya, na daga abin da ke haifar da quncin rayuwa da tsanani har ya kai ga mutum na gudun matarsa da `ya`yansa wani lokacin ya kai ga rasa hayyaci da hankula kaga mutum ya kauce ma hanyar shiriya, sai kaga ya na biyewa matarsa cikin sabon Allah, Allah ka tsaremu daga aikata haka , babbar musifa ma shi ne idan matar ta kasance saliha ko `ya`yanta shi kuma uban ya zama gurbatacce batacce daga hanyar shiriya, misali ya kasance matarsa ta na kula da ibada `ya`yansa na sAllah cikin jama'a da kula da dukkanin ibada  amma kuma shi uban ba ya sallah ya na kuma shan giya  da aikata manya manya zunubai, to a irin wannan lokaci ne matsala babba za ta afku cikin gida, rigima tayi tsanani tsakanin qarya da gaskiya, da yawan lokuta za ka samu anyi asarar haqqoqi al'amari ya rikice, Allah ne kadai wajen kai kuka.

19 an karbo daga baban abdullah (as) ya ce: yayin da wannan aya ta sauko:

يَا أ يُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا قُوا أنفُسَكُمْ وَأهْلِيكُمْ نَار[1]اً 

  ya ku wadanda suka yi imani ku ceci kawukanku da iyalinku daga wuta.

 sai wani daga cikin musulmi ya zauna ya dinga rusa kuka ya na cewa ni yanzu da gaza ceton kaina gashi kuma an kallafa mini ceton iyalina, sai manzon Allah (saw) ya ce: ya isar maka ka umarce su da abin da kake umartar kanka ka hane su da abin da ka ke hana kanka.

عن النبيّ (صلى الله عليه وآله) ، قال  : عظوهن بالمعروف قبل أن يأمرنكم بالمنكر

 annabi (saw) ya ce: ku yi musu wa'azi da alheri gabanin su fara umartarku da munkari

daga cikin alheri shi ne ku hana fajircin da ke gidajenku kamar yadda ya zo cikin hadisi:

‏‏قال رسول الله (صلى الله عليه وآله)  : أيّما رجل رأى في منزله شيئاً من الفجور فلم يغيّر بعث الله تعالى طيراً أبيض يظلّ عليه أربعين صباحاً فيقول كلّما دخل وخرج  : غيّر غيّر ، فإن غيّر وإلاّ مسح رأسه بجناحيه على عينيه ، فإن رأى حسناً لم يستحسنه ، وإن يرى قبيحاً لم ينكره[2] . فيكون بحكم الأنعام بل أضلّ سبيلا .

20 manzon Allah (saw) ya ce: duk mutumin da ya ga wani abu daga fajirci cikin gidansa bai canja shi ba Allah zai aiko da wani tsuntsu fari a kansa ya wanzu har tsawon asubahi arba'in, duk sanda wannan mutumin ya fito daga gida ko ya shiga sai tsuntsun ya dinga cewa ka canja ka canja, idan ya canja idan kuma bai canja ba sai ya dinga shafa fuffukensa kan  idanun mutumin, idan ya ga kyakkyawa bai gani kyawunsa, idan ya ga mummuna ba zai inkarinsa ba.

 sai ya zamanto cikin hukuncin dabbobi ko ma ya fi dabbobi batan hanya.

mahaifi da mahifiya haka suke suna umartar `ya`yayensu da alheri da hana su  mummuna, kamar yadda ubangiji ke fadi:

وَأمُرْ أهْلَكَ بِالصَّلاة[3]   

ka umarci iyalinka da sallah.[1] Tahrim:

[2] Bihar anwar m 100 sh 251

[3] Daha:123