فهرست کتاب‌‌ لیست کتاب‌ها
■ KALMAR TARBIYYA CIKIN HARSHEN LARABCI DA YANDA AKA YI 4
■ FASALI NA ( 2 ) 24
■ AUREN DABI'A 24
■ FASALI NA 3
■ FASALI NA 4 73
■ FASALI NA 5 131
■ FASALI NA 6 176
HAQQOQIN DA MA'AURATA SU KAYI TARAYYA CIKI 177
1 – HAQURI 178
2 – KAMEWA DAGA ZALUNCI DA CUATARWA 179
HAQQOQIN MATA 180
CIYARWA DA YALWATAWA 185
TAUSAYAWA DA KAMEWA DAGA ZALUNCI 187
KAMEWA DAGA BARIN DUKA MAI CUTARWA 187
UMARNI DA KYAKKYAWA DA HANI DA MUMMUNA 193
GARKUWA 196
8 – KYAUTATAWA : 196
9 - KYAWUNTA ZAMANTAKEWA 197
3 – TAUSAYAWA MIJI : 208
4 – HIMMATUWA DA KULA DA CIKIN GIDA DA KAYYAKINSA : 209
5 - HIMMATUWA CIKIN SAUKE HAQQOQI 209
6 – JIMA'I 210
7 - ADO 213
8 – KAMEWA CIKIN MAGANA : 219
SHUGABANTAR IYALI 225
DALILAI DA SUKE SANYA DAWWAMAR AURE 227
1 – SON JUNA 228
2 – YAWAITA AIKATA ALHERI: 228
4 – SANYA FARIN CIKI: 229
5 – BIYAYYA DA NEMAN YARDAR MIJI: 230
6 – KIYAYE MUTUNCI DA DUKIYA : 230
7 – TAIMAKO DA TALLAFAWA 230
8 – TARBAR MIJI DA KYAWUNTA BANKWANA DA SALLAMA : 231
9 – KALAMIN AQIDOJI MAI KYAWU DA QARFAFAFFEN FURUCI. 232
10 – KARBAR UZURI DA YIWA JUNA UZURI : 232
11 – BINSU SANNU SANNU CIKIN KOWANNE HALI : 233
12 – KYAWUNTA LAFAZI CIKN KOWANNE YANAYI : 233
13 – RASHIN SAURARON KYAUTATA AIKI DARI BISA DARI 233
14 – RASHIN IKON DAUKAR NAUYI A RAYUWANCE : 234
15 – RASHIN GORI KAN MIJI : 234
16 – RASHIN QAURACEWA AL'AMARIN SHIMFIDA: 235
17 - YIN SHAWARA DA MATA BANDA BIYE MUSU: 235
18 – TAKA TSAN TSAN DA KUMA FARKAWA : 238
19 – HANKALTA 239
20 - MIJI SHI NE MUTUNCIN MATARSA 240
21 – KISHI 240
22 – TAIMAKEKENIYYA 242
23 – DADADAWA IYALI 243
27 – WATSI DA BOAKANCI DA TSAFE TSAFE : 244
28 - HIDIMA MADAWWAMIYA 245
29 – GODIYA 246
29 – QAUNAR JUNA 247
TSINTUWA GUDA BIYU GIDAN ALI DA FATIMA (AS) 248
■ FASALI NA 8 252

9 - KYAWUNTA ZAMANTAKEWA 197

9 -  KYAWUNTA ZAMANTAKEWA

Kyawun rayuwa nutsuwa da zaman lafiya da kwanciyar hankali da girmama juna da yalwar hannu na daga cikin burin dukkanin miji da mata tun ranar farko rayuwarsu ta auratayya, kadai ta cewa wakilinta kai wakilina ne ko kuma ta cewa mai neman aurenta, na aura maka kaina kan sadaki bayyananne saboda ta ga rayuwa mani'imciya, ba rayuwar wahala ba da baqin ciki da hasara ba, Kalmar na'am ishara ce ya zuwa ni'ima daga ni'imomin Allah, ma'ana miji wanda ya ke tajalli da rububiyya, kadai dai ta ce na'am ne cikin amsar tambayar da akai mata shin baki yarda da wane matsayin miji da  mai kareki daga bala'i da musibu kuma ki kasance cikin ni'ima qarqashin inuwarsa ba.

 kasantuwar tsarin halittar mace na daga jinsi mai taushi da ni'ima, shi kuma namiji daga jinsi mai kaushi, kasantuwar matantaka na nufin fure wacce ake shaqar qamshinta da kula da ita da dukknin ma'anar kalma kulawa, lalle mace fure ne mai qamshi ba abokiyar kokawa bace da za a sanya zare da ita ana dambacewa, da har wani lokaci zai kai da doke doke kamar dabbar daji, lalle ita mace na buqatar lallabawa da lallashi cikin kowanne hali, idan ya lallasheta shi zai fi kowa girbar sakamakon lallashinta da kyautata zamantakewarsa da ita.

فما أروع ما يقوله أمير المؤمنين عليّ (عليه السلام) ينصح ولده محمّد بن الحنفية ، قائلا  : يا بني ، إذا قَوَيت فأقو على طاعة الله ، وإن ضعفت فاضعف عن معصية الله ، وإن استطعت أن لا تملك المرأة من أمرها ما جاوز نفسها فافعل ـ  أي الشيء الذي يتعلّق بنفسها فهي مختارة ، وأمّا غير ذلك فأمرها بيدك فلا تعطها ما  تشتهي  ـ فإنّه أدم لجمالها ، وأرخى لبالها ، وأحسن لحالها ، فإنّ المرأة ريحانة وليست بقهرمانة ، فدارها على كلّ حال وأحسن الصحبة لها ، فيصفو عيشك .

32 – mai ya fi kyawu daga abinda sarkin muminai ali (as) ke cewa: cikin nasiharsa ga dansa muhammadu dan hanafiyyatu: ya dana idan zaka nuna qarfi ka nuna cikin biyayyar Allah, idan zaka raunana to ka raunana cikn sabonsa, idan kana da iko kan rashin mallakawa mace al'amarin da ya wuce kanta to ka aikata haka, amma abida ya wuce kanta to al'amari na hannunka ka da ka biye mata cikin abin da ta ke sha'awa, lalle hakan shi ya fi dawwama da kyawunta shi yafi saki ga zuciyarta  da kyautata ga halinta, lalle mace fure ne ba itace mai tafiyar da gida sha'anin gida ba, ka bi ta sannu sannu cikin kowanne hali ka kyautata abokantakar da ita, rayuwarka za ta kyawunta.

عن الصادق (عليه السلام) ، قال  : اتّقوا الله في الضعيفين  : يعني المملوك والمرأة

33 – imam sadiq (as) ku ji tsoron Allah cikin raunana biyu, ma'ana basarake da mace

rarrauna  kowanne lokaci ya na buqatar a bishi sannu sannu, shi ba kishiyarka ba ne da har za kayi tsammani abin da ka ke tsammani daga kishiyanka, ita mace duk da cewa abokiyar rayuwa ce, sai dai cewa ta na buqatuwa da kyautatawa da tausasawa  da alheri,da lura da kyautata zamantakewa da ita da binta sannu sannu cikin kowanne yanayi.

عن أبي عبد الله (عليه السلام) ، قال  :  أكثر أهل الجنّة من المستضعفين النساء ، علم الله ضعفهن فرحمهن

34 – daga baban abdullah (as) ya ce: mafi yawan `yan aljanna daga raunanan mata suke, Allah ya san raunin da suke da shi sai ya yi musu rahama.

Ya kamaci namiji ya yi tajalli da siffar Allah da sunansa, ya tausayawa wadanda suke qasa wanda ke sama sai ya tusaya masa, ya tausayawa mace kamar yadda Allah ya tausaya mata, ya kiyaye mazantakarsa  da tsayuwarsa  ka da ya miqa wa mace ragamar gida.

Idan mace ta kasance ta na yiwa mijinta ado musammam daren da zai zo mata, hakama miji ya na daga cikin haqqin matarsa ya cancada  mata ado, mace nasan taga mijinta ya kasance saurayi a kowanne lokaci ko da kuwa ya tsufa ya fara furfura, sai dai cewa cikin ranta  ta na son da kaga mijinta ya kasance kamar saurayi.

Muslunci na kiyaye kowanne bangare a rayuwa, kamar yadda ya kasance ya kiyaye janibin halayya zukatan maza da mata, madalla ace mazaje sun sauya kalar gemukansu sunyi qunshi da bakin kala saboda matansu su samu nutsuwa zuwa garesu.

قال رسول الله (صلى الله عليه وآله)  : اختضبوا بالحنّاء ، فإنّه يجلو البصر وينبت الشعر ويطيّب الريح ويُسكن الزوجة

35– manzon Allah (saw) ya ce: ku tura gemu da lalle, lalle tura gemu da lalle yana yaye gani ya tsiro da gashi  ya na dadada iska ya na sanyawa mace nutsuwa.

قال الصادق (عليه السلام)  : الحنّاء يذهب السهك ـ  ريح كريهة ممّن عرق  ـ ويزيد في ماء الوجه ، ويطيّب النكهة ، ويحسن الولد

36 – imam sadiq (as) ya ce: lalle na tafiyar da iska mai wari, ya qara ruwan fuska, ya dadada qamshi, ya kyawunta danda za'a haifa.

عن ذروان المدائني ، قال  : دخلت على أبي الحسن الثاني ـ  موسى بن جعفر (عليه السلام)  ـ فإذا هو قد اختضب ، فقلت  : جعلت فداك ، قد اختضبت  ؟ فقال  : نعم ، إنّ في الخضاب لأجراً ، أما علمت أن التهيئة تزيد في عفّة النساء  ؟ أيسرّك أ نّك إذا دخلت على أهلك فرأيتها على مثل ما تراك عليه إذا لم تكن على تهيئة  ؟ قال  : قلت  : لا . قال  : هو ذاك . قال  : ولقد كان لسليمان (عليه السلام) ألف امرأة في قصر ، ثلاثمائة مهيرة ـ  أي حرّة ، لأ نّها تنكح بمهر ، فهي فعيلة بمعنى مفعولة  ـ وسبعمائة سريّة ـ  أي مملوكة  ـ وكان يطيف بهنّ في كلّ يوم وليلة .

37-an karbo daga zirwanul mada'ini ya ce: na shiga wajen baban hassan musa alkazim (as) sai na same shi ya yi qunshi, sai na ce: raina fansarka ka tura gemu ? sai ya ce: na'am lalle cikin tura gemu akwai lada, shin baka san cewa kyawunta sura na qara sa mata kamewa ba ?  shin za kayi farin ciki ace kajewa matarka ka sameta kamar yanda kake baka gyara surarka ba ? sai nace : a 'a sai yace: to al'amarin haka yake wurinsu, haqiqa sulaimanu (as) ya na da mata dubu cikin fadarsa, dari uku cikinsu `yantattu da ya aure da sadaki, dari bakwai kuma kuyangu ne bayi, sannan ya kasance ya na dawafi cikinsu cikin kowanne dare.

عن أبي عبد الله (عليه السلام) ، قال  : جاء رجل إلى النبيّ (صلى الله عليه وآله) فنظر في الشيب في لحيته ، فقال النبيّ (صلى الله عليه وآله)  : نورٌ ، من شاب شيبة في الإسلام كانت له نوراً يوم القيامة ، قال  : فخضب الرجل بالحنّا ، ثمّ جاء إلى النبيّ (صلى الله عليه وآله) ، فلمّـا رأى الخضاب قال  : نورٌ وإسلام . قال  : فخضب الرجل بالسواد ، فقال النبيّ (صلى الله عليه وآله)  : نور وإسلام وإيمان ومحبّة إلى نسائكم ورهبة في قلوب عدوّكم

38 daga baban abdullah (as) ya ce: wani mutum ya zo wajen annabi (saw) sai ya kalli furfurar gemansa, sai annabi (saw) ya ce: haske ya tabbata ga wanda ya yi fufura a cikin muslunci, haske zai kasance gareshi ranar qiyama, ya ce : sai mutumin ya tura gemansa da lalle ya zo wajen annabi (saw) yayin da ya ga wannan qunshi da yayiwa gemansa, sai ya qara cewa: haske na tare da muslunci, sai mutumin ya tura gemunsa da baqin launi, sai annabi (saw) ya qara cewa haske da muslunci da imani da soyayya zuwa ga matayenku da kwarjini cikin zukatan maqiyanku.

عن الحسن بن جهم ، قال  : دخلت على أبي الحسن (عليه السلام) وهو مختضب بسواد ، فقلت  : جعلت فداك ، قد اختضبت بالسواد  ؟ قال  : إنّ في الخضاب أجراً ، إنّ الخضاب والتهيئة ممّـا يزيد في عفّة النساء ، ولقد ترك النساء العفّة لترك أزواجهن التهيئة لهن

39– an karbo daga hassan dan jaham, ya ce: na shiga wajen baban hassan (as) halin ya yi tura gemansa da launin baqi, sai na ce: raina fansarka ka tura gemu da launin baqi ?  sai ya ce: a cikin wannan tura gemun akwai lada, lalle tura gemu da ado na daga abin da ke qara sa mata kamewa, lalle mata sunyi watsi da kame kawukansu ne sakamakon kazantar mazajensu.

عن الإمام الصادق (عليه السلام)  : الخضاب بالسواد مهابة للعدوّ واُنس للنساء

40 – imam sadiq (as) ya ce: tura gemu da baqin launi na tsorata maqiyi da sanya mata debe haso.

عن أبي جعفر (عليه السلام) ، قال  : النساء يحببن أن يرين الرجل في مثل ما  يحبّ الرجل أن يرى فيه النساء من الزينة

41– an karbo daga baban jafar (as) ya ce: mata na qaunar ganin mutum a cikin shigar da shima ya ke kaunar ganinsu daga cancada ado.

Na daga cikin take haqqin mace mijinta ya shigo mata gida da kayan aiki da warin wajen aikinsa, mafi muni daga haka shi ne ya nufi shimfidarta da warin karan taba sigari da ya zuka a waje, idan ta so sumbatarsa da kwanciya kusa da shi za ta sha azabar wannan wari na sigari, mai ya fi bushewar zukata daga mazajen da ke zuqar taba sigari sun nufi shimfidar matansu halin bakinsu na warin taba ko barasa, azabar Allah ta tabbata da kunyata duniya da lahaira kansa.

عن أبي الحسن (عليه السلام) ، قال  : في الخضاب ثلاث خصال  : هيبة في الحرب ، ومحبّة إلى النساء ، ويزيد في الباه

42- an karbo daga baban hassan (as) ya ce: cikin tura gemu akwai kyawawan abubuwa uku: kwarjini a filin yaqi, soyuwa zuwa ga mata,  da samu qarfin mazakuta.

عن الحسن بن جهم ، قال  : قلت لعليّ بن موسى (عليه السلام)  : خضبت  ؟ قال  : نعم بالحنّاء والكثم ، أما علمت أنّ في ذلك لأجراً ، إنّها تحبّ أن ترى منك الذي تحبّ أن ترى منها ( يعني المرأة في التهيئة ) ، ولقد خرجن نساء من العفاف إلى الفجور ، ما أخرجهن إلاّ قلّة تهيّؤ أزواجهن  

43 – an karbo daga hassan dan jaham, ya ce : na cewa aliyu dan musa arrida (as) shin kana tura gemunka ? sai ya ce : na'am da lalle da kusum, shin baka san cewa cikin yin haka akwai lada ba, lalle matarka na qaunar ganinka da shigar da kaima ka ke son ganinta ciki, haqiqa mata sun fita daga kamewa ya zuwa fajirci sannan ba komai ya haifar da hakan ba face qaranci tsaftar mazajensu.

وفي الحديث الشريف  : إنّها تشتهي منك الذي تشتهي منها  

44– a wani hadisi kuma: lalle ita na sha'awar abin da kake sha'awa daga gareta.

عن الحسن بن الزيات ، قال  : دخلت على أبي الحسن (عليه السلام) وهو في بيت منجّد ، ثمّ عدت إليه من الغد وهو في بيت ليس فيه إلاّ حصر ، فبرز وعليه قميص غليظ ، فقال  : البيت الذي رأيتم أمس ليس هو بيتي ، إنّما هو بيت المرأة وكان أمس يومها

45 - an karbo daga hassan zayyat, ya ce: na shiga wajen baban hassan (as) halin ya na cikin wani gida qayatacce, sai na dawo wajensa washegari halin ya na cikin wani gida babu komai cikinsa face tabarma, sai ya fito ya na sanye da wata kakkausar riga, sai ya ce: gidan da kuka ganni jiya ba gidana ba ne gidan mata ta ne jiya kuma ranar kwananta ne.

عن أمير المؤمنين (عليه السلام) ، قال  : قال رسول الله (صلى الله عليه وآله)  : اختضبوا بالحنّا ، فإنّه يزيد في شبابكم وجمالكم ونكاحكم وحسن وجوهكم ويباهي الله بكم الملائكة . والدرهم في سبيل الله بسبعمائة ، والدرهم في الخضاب بسبعة آلاف ، فإذا مات أحدكم واُدخل قبره دخل عليه ملكاه ، فإذا نظر إلى خضابه قال أحدهما لصاحبه  : اُخرج عنه ، فما لنا عليه من سبيل

46 – an karbo daga sarkin muminai  ali (as) ya ce: manzon Allah (saw) ya ce: ku yiwa gemunku qunshi da lalle, haqiqa shi ya na qara samartakarku da kyawunku da qarfin mazakuta da kyawun fuska, Allah ya na yiwa mala'iku alfhari da ku. ladan dirhami cikin tafarkin Allah dari bakwai  amma na qunshi dubu bakwai idan dayanku ya mutu a ka shigar da shi qabarinsa mala'iku biyu za su shiga cikin kabarin idan daya daga cikinsu ya ga  qunshinsa sa ya ce: mu fita mu kyaleshi ba yanda za muyi da shi.

da wannan hadisi mai daraja da ire irensa za mu fahimci cewa tura gemu da qunshi na da fa'idoji duniya da lahira, a duniya ya samu qarfafar dangatakarsa da iyali musammam mata.

عن النبيّ (صلى الله عليه وآله) كان ينظر في المرآة ويرجّل جمّته ـ  مجتمع شعر الناصية  ـ ويتمشّط ، وربما نظر في الماء وسوّى جمّته فيه . ولقد كان يتجمّل لأصحابه ، فضلا عن تجمّله لأهله ـ  وهذا يعني أنّ التجمّل للأهل مفروغ عنه  ـ وقال  : إنّ الله يحبّ من عبده إذا خرج إلى إخوانه أن يتهيّأ لهم ويتجمّل[1]

an rawaito cewa annabi (saw) ya kasance ya na yiwa gashin gaban goshinsa ado ya tsefe shi, lalle ya kasance ya na yiwa sahabbansa ado ballantana ma iyalansa  - ya ce: lalle Allah na son bawa wanda idan zai fito wajen `yan'uwansa sai ya shirya ya yi ado.[1] Mukarimul akhlaq:34