فهرست کتاب‌‌ لیست کتاب‌ها
■ KALMAR TARBIYYA CIKIN HARSHEN LARABCI DA YANDA AKA YI 4
■ FASALI NA ( 2 ) 24
■ AUREN DABI'A 24
■ FASALI NA 3
■ FASALI NA 4 73
■ FASALI NA 5 131
■ FASALI NA 6 176
HAQQOQIN DA MA'AURATA SU KAYI TARAYYA CIKI 177
1 – HAQURI 178
2 – KAMEWA DAGA ZALUNCI DA CUATARWA 179
HAQQOQIN MATA 180
CIYARWA DA YALWATAWA 185
TAUSAYAWA DA KAMEWA DAGA ZALUNCI 187
KAMEWA DAGA BARIN DUKA MAI CUTARWA 187
UMARNI DA KYAKKYAWA DA HANI DA MUMMUNA 193
GARKUWA 196
8 – KYAUTATAWA : 196
9 - KYAWUNTA ZAMANTAKEWA 197
3 – TAUSAYAWA MIJI : 208
4 – HIMMATUWA DA KULA DA CIKIN GIDA DA KAYYAKINSA : 209
5 - HIMMATUWA CIKIN SAUKE HAQQOQI 209
6 – JIMA'I 210
7 - ADO 213
8 – KAMEWA CIKIN MAGANA : 219
SHUGABANTAR IYALI 225
DALILAI DA SUKE SANYA DAWWAMAR AURE 227
1 – SON JUNA 228
2 – YAWAITA AIKATA ALHERI: 228
4 – SANYA FARIN CIKI: 229
5 – BIYAYYA DA NEMAN YARDAR MIJI: 230
6 – KIYAYE MUTUNCI DA DUKIYA : 230
7 – TAIMAKO DA TALLAFAWA 230
8 – TARBAR MIJI DA KYAWUNTA BANKWANA DA SALLAMA : 231
9 – KALAMIN AQIDOJI MAI KYAWU DA QARFAFAFFEN FURUCI. 232
10 – KARBAR UZURI DA YIWA JUNA UZURI : 232
11 – BINSU SANNU SANNU CIKIN KOWANNE HALI : 233
12 – KYAWUNTA LAFAZI CIKN KOWANNE YANAYI : 233
13 – RASHIN SAURARON KYAUTATA AIKI DARI BISA DARI 233
14 – RASHIN IKON DAUKAR NAUYI A RAYUWANCE : 234
15 – RASHIN GORI KAN MIJI : 234
16 – RASHIN QAURACEWA AL'AMARIN SHIMFIDA: 235
17 - YIN SHAWARA DA MATA BANDA BIYE MUSU: 235
18 – TAKA TSAN TSAN DA KUMA FARKAWA : 238
19 – HANKALTA 239
20 - MIJI SHI NE MUTUNCIN MATARSA 240
21 – KISHI 240
22 – TAIMAKEKENIYYA 242
23 – DADADAWA IYALI 243
27 – WATSI DA BOAKANCI DA TSAFE TSAFE : 244
28 - HIDIMA MADAWWAMIYA 245
29 – GODIYA 246
29 – QAUNAR JUNA 247
TSINTUWA GUDA BIYU GIDAN ALI DA FATIMA (AS) 248
■ FASALI NA 8 252

HAQQOQIN MIJI 202

HAQQOQIN MIJI                                 

amma haqqoqin miji kan matarsa:

1- tsantsar biyayya: lalle ya zama tilas mace ta yi biyayya ga mijinta matuqar bai umarceta da aikata haramun ba, kamar barin sallar wajibi  ko shangiya da dai misalin haka, duk da cewar kurewar biyayya shi ne sujjada, saboda haka ne ma bai inganta yin sujjada ga wanin Allah, sai dai cewa ya zo a hadisi cewa:

عن الصادق (عليه السلام) ، قال  : إنّ قوماً أتوا رسول الله (صلى الله عليه وآله) فقالوا  : يا رسول الله ، إنّا رأينا اُناساً يسجد بعضهم لبعض ، فقال رسول الله (صلى الله عليه وآله)  : لو كنت آمر أحداً أن يسجد لأحد لأمرت المرأة أن تسجد لزوجها

1 an karbo daga imam sadiq (as) ya ce: wasu mutane sun zo wajen manzon Allah (saw) sai suka ce masa munga wasu mutane sashensu na yiwa daya sashen sujjada, sai manzon Allah (saw) ya ce: da na kasance ina umarta wani ya yiwa wani sujjada da na umarci mace  ta yiwa mijinta sujjada.

وقال (صلى الله عليه وآله)  : لو أنّ امرأة وضعت إحدى ثدييها طبيخة ـ  كناية عن غاية الفداء والتضحية  ـ والآخر مشوية ، ما أدّت حقّ زوجها ، ولو أ نّها عصت مع ذلك زوجها طرفة عين اُلقيت في الدرك الأسفل من النار ، إلاّ أن تتوب وترجع

2 – a wani wajen kuma ya ce: da ace mace za ta dafa nononta daya ta gasa dayan, don sadukarwa ga mijnta da haryanzu ba ta iya sauken nauyin mijinta ba, da kuma tare da haka za ta sabawa mijinta ko da kuwa gwargwadon qiftawar ido ne  da an wurga ta cikin qasan wuta, har sai idan ta tuba ta qoma gareshi.

وقال (صلى الله عليه وآله)  : حقّ الزوج على الزوجة  : ... أن تطيعه ولا تعصيه  

3 – haqqin miji kan matarsa shi ne ta yi masa biyayya ka da ta saba masa.

وقالت خولة ـ  وخولة جماعة من الصحابيات تسمّى بهذا الاسم ، ولعلّ المراد بها هنا هي خولة بنت عاصم زوجة هلال بن اُميّة التي لاعنها ففرّق النبيّ بينهما  ـ  ، قالت لرسول الله (صلى الله عليه وآله)  : إنّي أتعطّر لزوجي كأ نّي عروس اُزفّ إليه ـ  وهذا يدلّ أنّ على المرأة أن تتعطّر دائماً لزوجها لا سيّما في الليل  ـ فآتيه في لحافه فيولّي عنّي ، ثمّ آتيه من قبل وجهه فيولّي عنّي ، فأراه قد أبغضني يا رسول الله  ؟ فماذا تأمرني  ؟ قال  : اتّقي الله وأطيعي زوجكِ

4 – kaulatu ta cewa manzon Allah (saw) lalle ni ina sanyawa mijina turare kai kace sabuwar amarya da za akai dakin miji, sai inje masa cikin mayafinsa na lulluba sai ya juya mini baya sai inje masa ta barin fuskarsa nan ma ya juya mini baya, sai na ke tsammani ko dai qina ya ke ya manzon Allah ? me kake umarta ta ? sai ya ce mata: kiji tsoron Allah ka da ki sabawa mijinki.

عن عليّ ، عن الإمام الكاظم (عليه السلام) ، قال  : سألته عن المرأة العاصية لزوجها هل لها صلاة وما حالها  ؟ قال  : لا تزال عاصية حتّى يرضى عنها[1]

5- an karbo daga aliyu, daga imam kazim (as) ya ce: na tambaye shi kan matar da ke sabawa mijinta, shin ta na da sallah ya sallarta ta ke ? sai ya ce ba ta gushewa mai sabo har sai mijinta ya yarda da ita.

عن أبي عبد الله (عليه السلام) ، قال  : ملعونة ملعونة امرأة تؤذي زوجها وتغمّه ، وسعيدة سعيدة امرأة تكرم زوجها ولا تؤذيه ، وتطيعه في جميع أحواله[2]

 6 – an karbo daga baba abdullah (as) ya ce: tsinanniya tsinanniya itace matar da ke cutar da mijinta da baqanta masa, mai arziqi mai arziqi itace matar da ta ke karrama mijinta sannan kuma ba ta cutar da shi ta na kuma yi masa biyayya cikin kowanne yanayi.

ـ الكافي بسنده عن أبي جعفر (عليه السلام) قال  : خرج رسول الله (صلى الله عليه وآله وسلم) يوم النحر ـ  أي يوم عيد الأضحى  ـ إلى ظهر المدينة على جمل عاري الجسم فمرّ بالنساء  فوقف عليهن ، ثمّ قال  : يا معاشر النساء تصدّقن وأطعن أزواجكن فإنّ أكثركنّ في النار ، فلمّا سمعن ذلك بكين ، ثمّ قامت إليه امرأة منهنّ ، فقالت  : يا  رسول الله في النار مع الكفّار  ؟  ! والله ما نحن بكفّار فنكون من أهل النار ، فقال لها رسول الله (صلى الله عليه وآله)  : إنّكن كافرات بحقّ أزواجكن[3]

7 – alkafi da isnadinsa daga baba jafar (as) ya ce: manzon Allah (saw) ya fito tsakiyar madina  ranar idin babbar sallah kan raqumi wandajikinsa ya kasance tsirara babu shimfida kansa , sai ya wuce ta gefen wasu mata  sai ya tsaya kansu, sannan ya ce: ya ku taron mata ku yi sadaka ku bi mazajenku, lalle mafi yawancinku `yan wuta ne, yayin da suka ji haka sai suka rushe da kuka, sai daya daga cikinsu ta miqe ta ce: ya manzon Allah shin yanzu mafi yawa daga cikin mu na cikin wuta tare da kafirai ? wallahi mu ba kafirai ba ne da har za mu kasance daga `yan wuta, sai manzon Allah (saw) ya ce mata: lalle ku kun kafircewa haqqin mazajenku.

Kafirci yakan zuwa da ma'ana biyu: wani lokacin kafircin aqida wanda ke kawo najastuwa ma'abocinsa da shiga wuta, wani kuma da ma'anar kafircewa cikin aiki  kamar mai barin sAllah ba ya yinta, ko wanda ya bar zuwa aikin hajji da gangan, matar da ba ta biyayya ga mijinta kafira ce kafircin aiki ba na aqida ba.

الفقيه بسنده عن أبي بصير قال  : سمعت أبا عبد الله (عليه السلام) يقول  : خطب رسول الله (صلى الله عليه وآله) النساء فقال  : يا معاشر النساء تصدّقن ولو من حليتكن ولو بتمرة ولو بشقّ تمرة ، فإنّ أكثركنّ حطب جهنّم ، إنّكن تكثرن اللعن وتكفّرن العشير ـ  أي الزوج  ـ فقالت امرأة من بني سليم لها عقل ـ  أي ذكيّة وفاهمة وتعقل الاُمور جيّداً  ـ يا رسول الله أليس نحن الاُمّهات الحاملات المرضعات ، أليس منّا البنات القيّمات والأخوات المشفقات ، فرقّ لها رسول الله (صلى الله عليه وآله) فقال  : حاملات والدات مرضعات رحيمات ، لولا ما يأتين إلى بعولتهن ما دخلت مصلّية منهنّ النار

8 – alfaqihu da isnadinsa an karbo daga babab basiru, ya ce: na ji baban Abdullah (as)  ya na cewa: manzon Allah (saw) ya yi wata huduba sai ya ce: yaku mata kuyi sadaqa ko da kuwa da kayan adonku ne ko kuma da dabino ko da gutsirin dabino, lalle mafi yawanku makamashin jahannama ne, lalle ku dinnan kuna da yawan tsinuwa da kafircewa miji  - sai wata mata daga qabilar salim mai kaifin basira ta ce: ya manzon Allah (saw) ashe ba mune iyaye masu dauke da ciki da shayarwa ba, ashe cikin mu babu `ya`ya` mata  tsayayyu masu tausayi, sai manzon Allah (saw) ya tausaya mata ya ce: masu dauke da ciki da shayarwa masu nuna jin qai, ba don abin da suke yiwa mazajensu ba da babu wata mai sallah dga cikinsu da za ta shiga wuta.[1] Biharul anwar m 100 sh 244

[2] Biharul anwar m 100 sh 253

[3] Alkafi m 5 sh 514