فهرست کتاب‌‌ لیست کتاب‌ها
■ KALMAR TARBIYYA CIKIN HARSHEN LARABCI DA YANDA AKA YI 4
■ FASALI NA ( 2 ) 24
■ AUREN DABI'A 24
■ FASALI NA 3
■ FASALI NA 4 73
■ FASALI NA 5 131
■ FASALI NA 6 176
HAQQOQIN DA MA'AURATA SU KAYI TARAYYA CIKI 177
1 – HAQURI 178
2 – KAMEWA DAGA ZALUNCI DA CUATARWA 179
HAQQOQIN MATA 180
CIYARWA DA YALWATAWA 185
TAUSAYAWA DA KAMEWA DAGA ZALUNCI 187
KAMEWA DAGA BARIN DUKA MAI CUTARWA 187
UMARNI DA KYAKKYAWA DA HANI DA MUMMUNA 193
GARKUWA 196
8 – KYAUTATAWA : 196
9 - KYAWUNTA ZAMANTAKEWA 197
3 – TAUSAYAWA MIJI : 208
4 – HIMMATUWA DA KULA DA CIKIN GIDA DA KAYYAKINSA : 209
5 - HIMMATUWA CIKIN SAUKE HAQQOQI 209
6 – JIMA'I 210
7 - ADO 213
8 – KAMEWA CIKIN MAGANA : 219
SHUGABANTAR IYALI 225
DALILAI DA SUKE SANYA DAWWAMAR AURE 227
1 – SON JUNA 228
2 – YAWAITA AIKATA ALHERI: 228
4 – SANYA FARIN CIKI: 229
5 – BIYAYYA DA NEMAN YARDAR MIJI: 230
6 – KIYAYE MUTUNCI DA DUKIYA : 230
7 – TAIMAKO DA TALLAFAWA 230
8 – TARBAR MIJI DA KYAWUNTA BANKWANA DA SALLAMA : 231
9 – KALAMIN AQIDOJI MAI KYAWU DA QARFAFAFFEN FURUCI. 232
10 – KARBAR UZURI DA YIWA JUNA UZURI : 232
11 – BINSU SANNU SANNU CIKIN KOWANNE HALI : 233
12 – KYAWUNTA LAFAZI CIKN KOWANNE YANAYI : 233
13 – RASHIN SAURARON KYAUTATA AIKI DARI BISA DARI 233
14 – RASHIN IKON DAUKAR NAUYI A RAYUWANCE : 234
15 – RASHIN GORI KAN MIJI : 234
16 – RASHIN QAURACEWA AL'AMARIN SHIMFIDA: 235
17 - YIN SHAWARA DA MATA BANDA BIYE MUSU: 235
18 – TAKA TSAN TSAN DA KUMA FARKAWA : 238
19 – HANKALTA 239
20 - MIJI SHI NE MUTUNCIN MATARSA 240
21 – KISHI 240
22 – TAIMAKEKENIYYA 242
23 – DADADAWA IYALI 243
27 – WATSI DA BOAKANCI DA TSAFE TSAFE : 244
28 - HIDIMA MADAWWAMIYA 245
29 – GODIYA 246
29 – QAUNAR JUNA 247
TSINTUWA GUDA BIYU GIDAN ALI DA FATIMA (AS) 248
■ FASALI NA 8 252

6 – JIMA'I 210

6 – JIMA'I

yayin da mu ke komawa ga ayoyi da riwayoyi masu daraja zamu samu qarfafawa kan batun jima'i da ladubbansa, lalle ne cewa jima'I na daga rukunai na tushe cikin rayuwar aure daga abin da ke garemu daga hikimomi cikin wannan babi, daga wanzuwa nau'in dan adam , da kyawuntar duniyar iyali da qosar da halittar jinsi da dai wasu buqatu daban.

kai ka ce anfi kallon bangaren mazantaka fiye da bangaren mata cikin wannan fage, mai yiwa saboda namiji shi ke dauke da maniyyi da kuma kasantuwar ya fi budewa kan mace kasantuwar tsananin kunyarta, namiji na iya neman kusanta matarsa  cikin kowanne lokaci da kowanne hali face kwanakin jinin haila, kai hatta lokutan haila na iya kusantarta sai dai banda shiga farjinta.

yayin da mu ke duban harshen riwaya mutum zai sha mamaki kan wajabci gaggawar amsawa buqatarsa kan matarsa, ba ta da haqqin qin amsawa buqatarsa ko da kuwa ta na kan raqumi, ko kuma jirgin qasa da mota matuqar wani ba zai gansu ba.

عن الصادق (عليه السلام) ، قال  : إنّ امرأةً أتت رسول الله (صلى الله عليه وآله) لبعض الحاجة ، فقال لها  : لعلّك من المسوّفات ـ  وكأ نّما النبيّ هو يتعرّض بها ليعلّمها ما يجب عليها  ـ فقالت  : يا رسول الله ، وما المسوّفات  ؟ فقال  : المرأة يدعوها زوجها لبعض الحاجة فلا تزال تسوّفه حتّى تنقضي حاجة زوجها فينام ، فتلك لا تزال الملائكة تلعنها حتّى يستيقظ زوجه

21 – an karbo daga imam sadiq (as) ya ce: wata mata ta zo wajen manzon Allah (saw) kan sashen buqatarta, sai ya ce mata: me yiwuwa ke kina cikin mata masu yanga ? sai tace wadanne mata ne masu yanga ? sai ya ce : macen da mijinta ke kiranta kan wata buqatarsa ba zata gushe ba ta na ja masa rai da yanga har sai sha'awarsa ta tafi ya yi barci, to wannan mata mala'iku ba za su gushe ba suna tsine mata har zuwa lokacin da mijinta ya tashi daga barci.

عن رسول الله (صلى الله عليه وآله) في حديث  : من حقّ الزوج ... وإن دعاكِ على قتب ـ  ظهر الجمل  ـ تجيبيه

22 –  manzon Allah (saw) daga cikin haqqin miji kan matarsa idan ya kirata ta amsa masa ko da kuwa ta na kan raqumi

23 – daga cikin nauyi da ya hau kan mace cikin daren da mijinta zai kusanceta shi ne ta aikata abin da manzon Allah (saw) ya sunnata mata cikin fadinsa: bai halasta ga mace ba ta yi barci har sai ta bijiro da kanta ga mijinta, ta kwabe tufafinta ta shiga mayafinsa ta jingina fatarta da fatarsa, idan ta aikata haka to tabbas ta bijiro masa da kanta.

Sananne ala'amari ne cewa jingina fata da fata na kawo dumamar jiki sai ka ga ya haifar da motsawar sha'awa, ma'ana mace ya kamata ta tsokano mijinta don ya kaimata hari ya samu abin da maza ke samu daga mata, kamar yadda tsuntsuwar tattabara ke yiwa mijinta, ya ya kuma idan shi mijinnne da kansa ya nemi hakan, shin ya halasta ta ja masa rai da yanga har ya kai ga ya haqura ya yi barci ?

wannan dangane da mace kenan, amma namiji lalle hadisi mi daraja  ya yi ishara da cewa, yawan jima'i na daga cikin sunnonin annabawa

wannan na nuni kan mustahabbancin yawan kusantar iyali, sai dai cewa wani hadisin ya tabbatr da cewa: shi mumini sha'awarsa a mace ta ke, idan aka hada waccan hadisin da wannan sai mu ce: shi mumini ba ya na yin jima'i ba don buqatar kansa kadai ba sai don ya farantawa matarsa  da kuma kashe zafin sha'awarta, lalle ita tafi shi sha'awa  kamar yadda hadisi ya tabatar da haka.

 an karbo daga manzon Allah (saw) cewa : shi jima'I na daga misdaqin sadaka, har ya kai ga wanda ya ji wannan magana ya yi mamaki daga haka ya ce : ashe ba ka sanya ta farin ciki ba ? .

saboda haka kusantar da mumini zuwa ga matarsa ya na yi ne saboda Allah matsarkaki, saboda in ba don haka ba ita sha'awar mumini a mace ta ke, da shagaltar da zuciyarsa da abin da ya fi ye masa muhimmaci, ya na kasa yininsa da darensa zuwa kashi uku:  kashi daya barci kashi daya rayuwa kashi daya ibada.

a wani hadisi kuma shi mumini kebanta da iyalansa cikin halali.

ثمّ ورد عن الإمام الرضا (عليه السلام)  : لا تجامع إلاّ من شَبَق ( أي مع اشتداد الشهوة وشدّة الميل إلى الجماع

24 – ya zo daga imam rida (as) cewa: ka da ka kusanci iyalinka face kana cikin tsananin sha'awa.

الكافي  : قال أمير المؤمنين (عليه السلام)  : خلق الله الشهوة عشرة أجزاء ، فجعل تسعة أجزاء في النساء وجزءاً واحداً في الرجال ، ولولا ما جعل الله فيهن من الحياء على قدر أجزاء الشهوة لكان لكلّ رجل تسع نسوة متعلّقات به

25 – alkafi : sarkin muminai ali (as) ya ce: Allah ya halicci sha'awa zuwa kashi goma, ya sanya kashi tara ga mata, kashi daya ga maza, ba don Allah ya sanyawa mata kunya gwargwadon sha'awarsu ba, da dukkanin namiji ya kasance da mata tara rataye da shi.

قال أبو عبد الله (عليه السلام)  : إنّ الله جعل للمرأة صبر عشرة رجال ، فإذا هاجت لها كانت لها قوّة شهوة عشرة رجال

26 – baban Abdullah (as) ya ce:  Allah ya sanyawa mace haqurin maza goma, idan kwadayinta ya motsa to sai ya kasance ta na sha'awar mazaje goma.

عن ضريس عن أبي عبد الله (عليه السلام) قال  : سمعته يقول  : إنّ النساء اُعطين بُضع اثنى عشر وصبر اثنى عشر . ( البُضع ) بالضمّ الجماع .

27 – an karbo daga daris daga baban abdullah (as) ya ce: an bawa mata jima'in mazaje shabiyu an kuma basu haqurin mutum shabiyu.

28 – an karbo daga baban basiru ya ce: na ji baban abdullah (as) mace ta fifita cikin dadi kan namiji da kashi casa'in da tara cikin dari, sai dai cewa Allah ya sanya mata kunya.

عن أبي بصير قال  : سمعت أبا عبد الله (عليه السلام) يقول  : فضّلت المرأة على الرجل بتسعة وتسعين من اللذّة ولكنّ الله ألقى عليهنّ الحياء

29 daga baban basir yae: na ji baban Abdullah{as} ya na cewa: an fifita mace da kasha casa'in ckin daga jin dadi sai dai ewa Allah ya sanya mata jin kunya.

عن أبي عبد الله (عليه السلام) قال  : إنّ الله جلّ وعزّ جعل للمرأة أن تصبر صبر عشرة رجال ، فإذا حملت ـ  أي الشهوة  ـ زادها قوّة عشرة رجال .

29 – an karbo daga baban abdullah (as) Allah mai girma da daukaka ya sanyawa mace haqurin mazaje goma, idan sha'awarta ta motsa – sai ya qara mata qarfin mazaje goma.

Kebancewa ya zo kan wannan riwaya mai daraja :

 الفقيه بسنده عن أبي جعفر (عليه السلام) قال  : إنّ الله تعالى خلق الشهوة عشرة أجزاء تسعة في الرجال وواحدة في النساء وذلك لبني هاشم وشيعتهم ، وفي نساء بني اُميّة وشيعتهم الشهوة عشرة أجزاء ، في النساء تسعة وفي الرجال واحدة

30 – alfaqihu da isnadinsa daga baban jafar (as) ya ce: Allah ya halicci sha'awa zuwa kashi goma, kashi tara ga maza, kashi daya ga mata wannan duka cikin banu hashim da shai'arsu, amma cikin matan banu umayya da shi'arsu kashi tara ga mata kashi daya ga mazajensu.

عن أبي عبد الله (عليه السلام) قال  : إنّ الله تعالى نزع الشهوة من رجال بني اُميّة وجعلها في نسائهم وكذلك فعل بشيعتهم ، وإنّ الله تعالى نزع الشهوة من نساء بني  هاشم وجعلها في رجالهم وكذلك فعل بشيعتهم

31- an karbo daga baban Abdullah (as) ya ce: Allah ya cire sha'awar mazajen banu umayya ya sanya ta cikin matayensu, haka ya aikata kan shi'arsu.