فهرست کتاب‌‌ لیست کتاب‌ها
■ KALMAR TARBIYYA CIKIN HARSHEN LARABCI DA YANDA AKA YI 4
■ FASALI NA ( 2 ) 24
■ AUREN DABI'A 24
■ FASALI NA 3
■ FASALI NA 4 73
■ FASALI NA 5 131
■ FASALI NA 6 176
HAQQOQIN DA MA'AURATA SU KAYI TARAYYA CIKI 177
1 – HAQURI 178
2 – KAMEWA DAGA ZALUNCI DA CUATARWA 179
HAQQOQIN MATA 180
CIYARWA DA YALWATAWA 185
TAUSAYAWA DA KAMEWA DAGA ZALUNCI 187
KAMEWA DAGA BARIN DUKA MAI CUTARWA 187
UMARNI DA KYAKKYAWA DA HANI DA MUMMUNA 193
GARKUWA 196
8 – KYAUTATAWA : 196
9 - KYAWUNTA ZAMANTAKEWA 197
3 – TAUSAYAWA MIJI : 208
4 – HIMMATUWA DA KULA DA CIKIN GIDA DA KAYYAKINSA : 209
5 - HIMMATUWA CIKIN SAUKE HAQQOQI 209
6 – JIMA'I 210
7 - ADO 213
8 – KAMEWA CIKIN MAGANA : 219
SHUGABANTAR IYALI 225
DALILAI DA SUKE SANYA DAWWAMAR AURE 227
1 – SON JUNA 228
2 – YAWAITA AIKATA ALHERI: 228
4 – SANYA FARIN CIKI: 229
5 – BIYAYYA DA NEMAN YARDAR MIJI: 230
6 – KIYAYE MUTUNCI DA DUKIYA : 230
7 – TAIMAKO DA TALLAFAWA 230
8 – TARBAR MIJI DA KYAWUNTA BANKWANA DA SALLAMA : 231
9 – KALAMIN AQIDOJI MAI KYAWU DA QARFAFAFFEN FURUCI. 232
10 – KARBAR UZURI DA YIWA JUNA UZURI : 232
11 – BINSU SANNU SANNU CIKIN KOWANNE HALI : 233
12 – KYAWUNTA LAFAZI CIKN KOWANNE YANAYI : 233
13 – RASHIN SAURARON KYAUTATA AIKI DARI BISA DARI 233
14 – RASHIN IKON DAUKAR NAUYI A RAYUWANCE : 234
15 – RASHIN GORI KAN MIJI : 234
16 – RASHIN QAURACEWA AL'AMARIN SHIMFIDA: 235
17 - YIN SHAWARA DA MATA BANDA BIYE MUSU: 235
18 – TAKA TSAN TSAN DA KUMA FARKAWA : 238
19 – HANKALTA 239
20 - MIJI SHI NE MUTUNCIN MATARSA 240
21 – KISHI 240
22 – TAIMAKEKENIYYA 242
23 – DADADAWA IYALI 243
27 – WATSI DA BOAKANCI DA TSAFE TSAFE : 244
28 - HIDIMA MADAWWAMIYA 245
29 – GODIYA 246
29 – QAUNAR JUNA 247
TSINTUWA GUDA BIYU GIDAN ALI DA FATIMA (AS) 248
■ FASALI NA 8 252

7 - ADO 213

7 -  ADO

daga cikin haqqin miji kan matarsa, shi ne ta cancada masa ado wani lokaci da yin adon da zai kwana biyu bai tafi ba kamar yin qunshi da lalle, wani lokacin kuma da adon dare, cikin kowannne gari da lokaci ya na da ladubbansa na musammam, abin da aka nufa shi ne cancada ado da dukkanin taken da ke amsa sunan ado, duk da cewa shi ado na biye da al'adun kowacce al'umma  da qabila na da na ta adon.

misali farkon muslunci ado ga mace shi ne ta cancadawa hannayenta ado, mustahabbaccin yin haka na cigaba har ya zuwa ranar qiyama. haqiqa abin da muslunci ya zo da shi na dacewa da halayyar dan adam, matuqar akwai lafiyayyen hankali da dabi'a, to za a samu hukunce hukuncen muslunci da dokokinsa, muslunci na tafiya da dukkanin gari da zamani, shi addini ne na har abada da Allah ya nufi dukkanin al'ummu  har zuwa ranar qiyama.

وَمَنْ يَبْتَغِ غَيْرَ الإسْلامِ دِيناً فَلَنْ يُقْبَلَ مِنْه[1]   

duk wanda ya nemi wani addini sabanin muslunci to ba za'a karba daga gareshi ba.

عن جعفر بن محمّد ، عن آبائه (عليهم السلام) ، قال  : رخّص رسول الله (صلى الله عليه وآله)للمرأة أن تخضب رأسها بالسواد ، قال  : وأمر رسول الله (صلى الله عليه وآله) النساء بالخضاب ـ  ذات البعل وغير ذات البعل  ـ أمّا ذات البعل ـ  أي من لها زوج  ـ فتتزيّن لزوجها ، وأمّا غير ذات البعل فلا تشبه يدها يد الرجال

32 – an karbo daga jafar dan muhammadu (as) ya ce: manzon Allah (saw) ya sauqaqawa mata yiwa gashinsu qunshi da launin baqi, ya ce : manzon Allah (saw) ya umarci mata da yin qunshi,masu aure cikinsu da wadanda basu da aure, wacce ke da aure sai ta cancada ado don mijinta, wadda kuma ba ta da aure ka da ta kamanta hannunta da da na maza.

عن محمّد بن مسلم ، عن أحدهما ـ  الباقر أو الصادق (عليهما السلام)  ـ قال  : لا ينبغي للمرأة أن تدع يدها من الخضاب ، ولو تمسحها بالحناء مسحاً ، ولو كانت مسنّة .

33 – an karbo daga muhammadu dan muslim daga sadiq (as) ya ce: bai kamata mace ta bar hannayenta ba tare da ta yi musu qunshi ba  ko da kuwa ta tsufa.

Wannan na ishara da hatta tsohuwa mustahabbi ne ta yi qunshi.

قال رسول الله (صلى الله عليه وآله)  : الحنّاء سيّد ريحان أهل الجنّة ، النائم في الحنّاء كالمتشحط في سبيل الله

34 – manzon Allah (saw) ya ce: lalle shugaban furen `yan aljanna shi ne wanda ya yi barci cikin lalle, misalin mai jihadi cikin tafarkin Allah.

 قال (عليه السلام)  : إنّي لاُبغض من النساء السلتاء والمرهاء ، فالسلتاء التي لا تختضب ، والمرهاء التي لا تكتحل

35 – manzon Allah (saw) ya ce: lalle ni ina qin macen da bata ado da sanya kwalli da wace ba ta yin qunshi.

عن أبي بصير ، قال  : سألته عن قصّ النواصي ـ  تريد به المرأة الزينة لزوجها  ـ وعن الحفّ ـ  إصلاح الشعر وحفّت المرأة وجهها من الشعر أن زيّنته  ـ والقرامل ـ  جمع قرمل كزبرج  : ما تشدّ المرأة على رأسها من الصوف والخيوط وما شابه  ـ والصوف وما أشبه ذلك  ؟ قال  : لا بأس بذلك كلّه ، قال محمّد  : قال يونس  : يعني لا بأس بالقرامل إذا كانت من صوف ، وأمّا الشعر فلا يوصل الشعر بالشعر لأنّ الشعر ميّت

36 – an karbo daga baban basiru, ya ce: na tambayi baban Abdullah (saw) kan yanke gashin goshi don yiwa miji ado da lullube fuska da gashin kai shi ma don ado, da daure kai da cancada masa ado, sai ya ce: babu laifi kan aikata dukkanin wadannan abubuwa.

daga cikin abubuwan da ke bayyana ado ga `ya mace sanya zinariya da azurfa da cancada ado da awarwaro:

عن محمّد بن مسلم ، عن أحدهما (عليهما السلام) ، وسئل عن حليّ الذهب للنساء  ؟ فقال  : ليس به بأس ولا ينبغي للمرأة أن تعطّل نفسها ولو أن تعلّق في رقبتها قلادة ، ولا ينبغي لها أن تدع يدها من الخضاب ولو أن تمسّحها بالحنّا مسحاً ولو كانت مسنّة

37- an karbo daga muhammadu dan muslim daga jafar sadiq (as)  an tamabaye shin mata zasu iya ado da zinariya  ? sai ya ce : bai kamata mace ta hana ma kanta ado ko do kuwa da sanya sarqar wuya, bai kamaceta ta bar hannayenta haka ba tare da qunshi ba, ko da dai shafa musu lalle ne, ko da kuwa ta tsufa.

daga cikin abubuwan da ke bayyana ado sanya tufafi mai kyawu:

عن أبى عبد الله ، عن أبيه ، عن عليّ (عليهم السلام) ، قال  : الدهن يظهر الغنى ، والثياب تظهر الجمال ، وحسن الملكة يكبت الأعداء

38 – an karbo daga baban Abdullah (as) ya ce:  shafa mai na bayyana wadata, tufafi na bayyana kyawu, kyawunta mu'amala na baqantawa maqiya.

cikin wannan babu banbanci cikin maza da mata .

Allah madaukaki na cewa:

قُلْ مَنْ حَرَّمَ زِينَةَ اللهِ الَّتِي أخْرَجَ لِعِبَادِهِ وَالطَّيِّبَاتِ مِنَ الرِّزْقِ[2] 

  Ka ce waye ya haramta adon Allah wanda ya fitar da shi don bayinsa da kyawawa daga arziqi.

 kayi ado ka sanya tufafi mai kyawu, lalle shi Allah kyakkyawa ne ya na son kyawu, saboda haka ya na da kyau shi kyawun ya kasance daga halaliya, wanda ke da wadata ka da ya yi barna wajen sayen kaya barkatai, lalle Allah madaukaki sarki na cewa:

لِـيُـنفِقْ ذُو سَعَة مِنْ سَعَتِه[3] 

mayalwaci ya ciyar daga yalwarsa.

 ma'ana gwargwadon ikonsa.

daga cikin abin da ke tabbatar da cewa ado na tafiya da zamani da muhalli abin da ya zo daga hadisi mai daraja:

عن سفيان الثوري ، قال  : قلت لأبي عبد الله (عليه السلام)  : أنت تروي أنّ عليّ بن أبي طالب (عليه السلام) كان يلبس الخشن وأنت تلبس القوهي ( ثياب بيض ينسب إلى قوهستان أو قوها كورة بين نيسابور وهرات ) ـ  أي من الألبسة الخارجية آنذاك  ـ والمروي قال  : ويحك إنّ عليّ بن أبي طالب كان في زمان ضيق ، فإذا اتّسع الزمان فأبرار الزمان أولى به

39 – an karbo daga sufyanu assauri, ya ce: na cewa baban Abdullah (as) kai kana rawaito cewa aliyu dan abi dalibi (as) ya kasance ya na sanya kausasan tufafi, amma kai kuma kana sa farare kaya na qasar waje, sai imam ya ce: Allah wadaranka lalle aliyu dan abi dalibi ya sanya wannan tufafi ne zamanin da ya ke cikin quncin rayuwa, idan zamani ya yalwata bayin Allah rabautattu sune suka fi cancanta da shi.

عن أمير المؤمنين (عليه السلام) ، قال  : ليتزيّن أحدكم لأخيه إذا أتاه كما يتزيّن للغريب الذي يحبّ أن يراه في أحسن الهيئة

40 – an karbo daga sarkin muminai ali (as) : dayanku ya yi ado saboda ziyarar dan'uwansa kamar yadda ya ke yin ado saboda ziyarar baqo da ya ke qaunar ya ganshi cikin mafi kyawun shiga.

bisa la'akari sai mu ce mafi cancanta da cancadawa juna ado su ne miji da matarsa.

عن إسحاق بن عمّـار ، قال  : قلت لأبي عبد الله (عليه السلام)  : يكون للمؤمن عشرة أقمصة  ؟ قال  : نعم . قلت  : عشرين  ؟ قال  : نعم ، وليس ذلك من السرف ، إنّما السرف أن يجعل ثوب صونك ثوب بذلتك

41 – an karbo daga is'haq dan ammar, ya ce: na cewa baban abdullah (as) tufafi goma na kasancewa ga mumini ? ya ce: na'am, sai na ce: ishirin fa: ya ce

: na'am hakan ba barna ba ne, barna shi ne sanya tufafi ado da kwalliya a muhallin da bai da ce ba.

عن أبي عبد الله (عليه السلام)  : أدنى الإسراف هراقة فضل الإناء وابتذال ثوب الصون وإلقاء النوى  

42 – an karbo daga baban abdullah (as) mafi qarancin barna zubar da abin da ya rage cikin kwarya da sanya tufafi ado a muhallin qazanta  da

Sannan tufafi da sanya su na da ladubba na musammam wadanda suka zo cikin littafan akhlaq, kamar yadda mace ta ke da kayan da suka kebanta da ita, haka namiji ke da kayan da suka kebance shi, ka da dayansu ya yi ganganci kamanceceniyya da daya.

عن أبي عبد الله ، عن آبائه (عليهم السلام) ، قال  : كان رسول الله (صلى الله عليه وآله) يزجر الرجل يتشبّه بالنساء ، وينهى المرأة أن تتشبّه بالرجال في لباسها .

43 – an karbo daga baban Abdullah (as) daga babanninsa (as) ya ce: manzon Allah (saw) ya kasance ya na hani da tsawatarwa kan namiji ya yi kamanceceniya da mata, haka ya na hana mace yin kamanceceniya da maza cikin sanya tufafinta.

Sannan ya kamata miji ya yalwata iyalinsa , haqiqa hakan na daga azurtar duniya  kamar yadda ya zo cikin hadisai masu yawa.

عن أبي عبد الله (عليه السلام) ، قال  : من السعادة سعة المنزل

44 - an karbo daga baban Abdullah (as) ya ce:ya na daga azurta yalwatar gida.

وقال (عليه السلام)  : للمؤمن راحة في سعة المنزل

45 – imam (as) ya ce: mumini na da hutu cikin yalwatar gida.

وسئل أبو الحسن (عليه السلام) عن أفضل عيش في الدنيا  ؟ قال  : سعة المنزل وكثرة المحبّين

46 – an tambayi baban hassan (as) kan mafificiyar rayuwa cikin duniya ? sai ya ce: yalwar gida  da yawan masoya.

ـ قال النبيّ (صلى الله عليه وآله)  : من سعادة المرء المرأة الصالحة والمسكن الواسع والمركب البهي والولد الصالح

47 – manzon Allah (saw) ya ce: daga cikin azurta shi ne samun mace saliha da gida yalwatacce da abin hawa na alfarma da da nagari.

وقال (صلى الله عليه وآله)  : أربع من السعادة وأربع من الشقاوة ، فالأربع التي من السعادة  : المرأة الصالحة والمسكن الواسع والجار الصالح والمركب البهي ، والأربع التي من الشقاوة  : الجار السوء والمرأة السوء والمسكن الضيّق والمركب السوء

48 – imam (as) ya ce: abubuwa hudu na daga azurta, abubuwa hudu na daga tsiyata, abubuwa hudu da suke daga arziqi shi ne mace saliha,  gida mayalwaci, maqoci nagari, abin hawa na alfarma.  abubuwa hudu da suke daga tsiyata sune: maqoci mugu, quntataccen gida, muguwar mata, abin hawa mara kyawu.

ba boye ya ke kan cewa gida na da iyaka a muslunci, ya zama dole gida ka da ya wuce bakin buqatuwa.

فقد ورد عن أبي عبد الله (عليه السلام)  : كلّ بناء ليس بكفاف فهو وبال على صاحبه

49 - hadisi ya zo daga baban abdullah (as) duk gidan da ya wuce buqata to azaba ne kan ma'abocinsa.

cancada ado cikin kowanne irin hali abune mai kyawu ga mace idan ta kasance ta nayin wannan ado saboda mijinta  dukkanin azaba ta tabbata ga matar da ke yin ado ga wani wanda ba mijinta ba, mai ya fi muni daga mijinta da ke fito da matarsa waje halin ta cancada ado ga kuma qamshin turare na tashi, wannan miji ya tabbata shashasha mara kishi, misalinsa kamar alade da matarsa ke jingina da jikinsa don wani aladen ya samu damar zakke mata, saboda haka nema aka haramta cin naman alade, saboda duk wanda ke cin namansa zai zama mara kishi.

قال رسول الله (صلى الله عليه وآله)  : وأيّما رجل تتزيّن امرأته وتخرج من باب دارها فهو ديّوث ، ولا يأثم من يسمّيه ديوثاً ، والمرأة إذا خرجت من باب دارها متعطّرة والزوج بذلك راض ، يُبنى لزوجها بكلّ قدم بيت في النار .

50 – manzon Allah (saw) ya ce: duk mutumin da matarsa ke cancada ado ta fito ta qofar gidansa halin qamshin turare na tashi, tabbas wannan mutumin bai da kishi,  sannan za 'a gina mata a wuta kan dukkanin taki daya da ta tattaka.

Ado  na halasta da zama abin yabo idan ya kasance anyi shi don miji lalle mutum cikin dabi'arsa ya na son kyawu da tsafta da ado, sau da yawa miji sun rabu da matarsa sakamakon qazantarta, da kuma kasantuwar fuskarta bushe ba tare da ta tsufa ba kamar yadda ya zo cikin hadisi:

عن أمير المؤمنين (عليه السلام) ، أنّ النبيّ (صلى الله عليه وآله) قال  : مرّ أخي عيسى بمدينة وفيها رجل وامرأة يتصايحان ، فقال  : ما شأنكما  ؟ قال  : يا نبيّ الله ، هذه امرأتي وليس بها بأس ، صالحة ، ولكنّي اُحبّ فراقها . قال  : فأخبرني على كلّ حال ما  شأنها  ؟ قال  : هي خلقة الوجه من غير كبر ، قال لها  : يا امرأة ، أتحبّين أن يعود ماء وجهكِ طريّاً  ؟ قالت  : نعم . قال لها  : إذا أكلتِ فإيّاكِ أن تشبعي ، لأنّ الطعام إذا تكاثر على الصدر فزاد في القدر ، ذهب ماء الوجه ، ففعلت ذلك فعاود وجهها طريّا[4]ً

51 – an karbo daga sarkin muminai ali (as) cewa annabi (saw) ya ce: dan'uwana isa (as) ya wuce ta cikin wani gari sai ya hadu da wata mata da mijinta suna cece kuce, sai ya tambaye su ya ce: mai ya faru da ku ? sai mijin ya ce: ya annabin Allah wannan mata ba ta da matsala mace ce saliha, sai dai cewa ni ina son rabuwa da ita, sai isa (as) ya ce masa: ka bani labarin dukkanin abin da ya faru game da ita  sai ya ce : fuskarta ta tsufa ba tare da girma ba ko tsufa, sai isa (as) ya ce mata: shin kina son ruwan fuskarki ya dawo sabo danye ? sai ta ce na'am, sai ya ce: idan kika ci abinci ka da ki qoshi, saboda shi abinci idan ya cika qirji ya wuce gwargwado ya na tafiya da ruwan fuska, sai wannan mata ta aikata haka ruwan fuskarta ya dawo danye.[1] Ali Imran:85

[2] A'araf:32

[3] Addalaq:7

[4] Ilalul shara'I:497