TARBIYYAR HALITTA DA MUSLUNCI 9
WANENE MAI TARBIYA ? 10
KASHE KASHEN TARBIYA 12
ABUBUWAN DA SUKA RATAYU DA ITA 13
IYALI CIKIN MA'ANAR LUGGA DA ISDILAHI 13
IYALI A LUGGANCE : 14
■ AUREN DABI'A 24
KASHE KASHEN AURE: 41
ADADIN MAZAJE: 44
HANYOYIN TABBATAR AURE : 46
5 - KASANTUWAR MIJI DAYA RAK MACE DAYA RAK: 46
SAMUN CIKAR KAMALA CIKIN AURE 54
DALILAN YIN AURE CIKIN SUNNA MAI DARAJA 60
1 TAUHIDI: 61
2-TAQAWA : 62
3- MAFI SOYUWAR GINI WAJEN ALLAH: 62
4- SUNNAR ANNABI: 63
5 - QARUWAR ARZIQI : 65
6 – QARUWAR IMANI : 69
7- ALFAHARI : 70
8- QARUWAR IBADA : 71
9- GARKUWA : 71
10 – SADAR DA ZUMUNCI 72
11- ADDINI : 72
12- DEBE HASO: 73
1- ASALI 76
2- WATA CIKIN BURUJIN AQRABU : 76
HUKUNCIN ILIMIN BUGA QASA CIKIN SHARI'A MAI TSARKI 77
MAHALLIN DA MUTUM KE RAYUWA CIKI 84
SON MATA 84
MATA MASU MUTUNCI DA DARAJA 88
1 MATAYE MAFI KYAWUN FUSKOKI MAFI QARANCI SADAKI 90
2- QARANCIN BUQATU DA SAUQAQE HAIHUWA: 91
3- KASHE KASHEN MATA CIKIN KYAWAWAN HALINSU 91
TSARA CIKIN AURE 116
FAFUTIKA CIKIN AURE 133
AUREN WURI 134
HUDUBA 136
SADAKI 142
HADARIN TSADAR SADAKI : 148
AUREN SHARI'A 150
DAREN ANGONCI 150
AYYUKAN DAREN ANGONCI : 154
ZAMA TARE DA AMARYA HAR TSAWON KWANAKI BAKWAI : 155
WALIMA 155
RARRABA ALEWA KO DABINO 157
LADUBBAN SADUWA DA IYALI 158
1- MAFI DADIN DADADA 160
2- WASA DA MATA GABANIN JIMA'I : 160
4 – HUKUNCIN AZALO : 174
5 – ADDU'A YAYIN KUSANTAR IYALI 175
35 – daga abu rabi'i ashshami, ya ce 175
1 – HAQURI 178
2 – KAMEWA DAGA ZALUNCI DA CUATARWA 179
HAQQOQIN MATA 180
CIYARWA DA YALWATAWA 185
TAUSAYAWA DA KAMEWA DAGA ZALUNCI 187
KAMEWA DAGA BARIN DUKA MAI CUTARWA 187
UMARNI DA KYAKKYAWA DA HANI DA MUMMUNA 193
GARKUWA 196
8 – KYAUTATAWA : 196
9 - KYAWUNTA ZAMANTAKEWA 197
3 – TAUSAYAWA MIJI : 208
4 – HIMMATUWA DA KULA DA CIKIN GIDA DA KAYYAKINSA : 209
5 - HIMMATUWA CIKIN SAUKE HAQQOQI 209
6 – JIMA'I 210
7 - ADO 213
8 – KAMEWA CIKIN MAGANA : 219
SHUGABANTAR IYALI 225
DALILAI DA SUKE SANYA DAWWAMAR AURE 227
1 – SON JUNA 228
2 – YAWAITA AIKATA ALHERI: 228
4 – SANYA FARIN CIKI: 229
5 – BIYAYYA DA NEMAN YARDAR MIJI: 230
6 – KIYAYE MUTUNCI DA DUKIYA : 230
7 – TAIMAKO DA TALLAFAWA 230
8 – TARBAR MIJI DA KYAWUNTA BANKWANA DA SALLAMA : 231
9 – KALAMIN AQIDOJI MAI KYAWU DA QARFAFAFFEN FURUCI. 232
10 – KARBAR UZURI DA YIWA JUNA UZURI : 232
11 – BINSU SANNU SANNU CIKIN KOWANNE HALI : 233
12 – KYAWUNTA LAFAZI CIKN KOWANNE YANAYI : 233
13 – RASHIN SAURARON KYAUTATA AIKI DARI BISA DARI 233
14 – RASHIN IKON DAUKAR NAUYI A RAYUWANCE : 234
15 – RASHIN GORI KAN MIJI : 234
16 – RASHIN QAURACEWA AL'AMARIN SHIMFIDA: 235
17 - YIN SHAWARA DA MATA BANDA BIYE MUSU: 235
18 – TAKA TSAN TSAN DA KUMA FARKAWA : 238
19 – HANKALTA 239
20 - MIJI SHI NE MUTUNCIN MATARSA 240
21 – KISHI 240
22 – TAIMAKEKENIYYA 242
23 – DADADAWA IYALI 243
27 – WATSI DA BOAKANCI DA TSAFE TSAFE : 244
28 - HIDIMA MADAWWAMIYA 245
29 – GODIYA 246
29 – QAUNAR JUNA 247
TSINTUWA GUDA BIYU GIDAN ALI DA FATIMA (AS) 248
SON `YA`YA DA QANAN YARA 252
MUQAMI NA 2 254
MUQAMI NA 3 260
NEMAN HAIHUWAR DA NAMIJI 260
MUQAMI NA 4 266
RAINON CIKI DA LADUBBNSA 266
TASIRIN ABINCI KAN MATA MASU CIKI DA YARA DA JIMA'I 267
MUQAMI NA 6 269
HAIHUWA 269
MUQAMI NA 7 270
SHAYARWA 270
MUQAMI NA 8 273
RAINON YARO 273
MUQAMI NA TARA 279
TAYA MURNA DA SAMUN DA 279
MUQAMI NA 10 281
AQIQA 281
WASU AYYUKAN MUSTAHABBAN NA DABAN 286
MUQAMI NA 11 287
KACIYA 287
MUQAMI NA 12 290
KAMANCECENIYAR DA DA MAHAIFINSA 290
MUQAMI NA 13 292
MATAKAN TARBIYYYAR YARA 292
MUQAMI NA 14 298
ADALCI TSAKANIN `YA`YA 298
MUQAMI NA 15 300
SUMBATA NA DAGA ALAMOMIN SO 300
FASALI NA 9 302
FASALI NA 10 317
BATUTUWA DABAN DABAN 317
FASALI NA 11 325
SAKI 325
GABATARWA 327
HAQIQANIN LADABI KAN HASKEN MAZHABAR IYALN GIDAN ANNABI ( AS ) 329
WAYE ME LADABTARWA ? 336
MEYE LADABI ? 338
ASALAN LADUBBA 341
MASADIR CIKIN LADUBBA 347
MASADIR DIN LARABCI 349
TABLE OF CONTENTS 355
- CIKIN HALLARAR ALHERI
- HUJJOJIN HALASCIN YIN TAKIYYA A MUSLUNCI DAGA MAHANGAR MANYAN MALAMAI GUDA BIYU
- FARKAR DA MAI BACCI CIKIN TABBATUWAR GANIN IMAM KA'IM A.S
- ALAMOMIN ANNABI CIIKIN KUR'ANI MAI GIRMA
- HAKURI DA FUSHI
- Bada'u tsakanin hakika da kagen makiya
- FALALAR DAREN LAILATUL KADRI
- WAHABIYANCI A TSAKANIN GUDUMA DA
- HASKEN SASANNI CIKIN SANIN ARZIKI
- AQIDUN MUMINAI
- FATIMA TAGAR HASKAYE
- SIRRIKAN AIKIN HAJJI DA ZIYARA
- TARBIYYAR IYALI A MAHANGAR ALKUR'ANI DA AHLULBAITI
MAZAJE SUNE MASU TSAYUWA KAN MATA
خَلَقَكُمْ مِنْ نَفْس وَاحِدَة وَجَعَلَ مِنْهَا زَوْجَهَ[1]
Kamar ya da ya kasance babu banbanci tsakanin mace da miji cikin asalin tarbiyya da ta'alim da ilimi da taqawa da suluki zuwa ga Allah matsarkaki, sai daci cewa sakamakon banbancin tsarin ginin halittarsu ta gangar jiki hakada banbantarsu cikin hankali da tausayi, sai ubangiji ya sanyawa kowanne daya cikinsu kebantattun dabi'u ya kuma dora hukunce hukuncen shari'a da al'ada kai, ya sanya limantar sallar jam'I da alqalanci da marja'iyanci ga `ya`ya maza. Ta wanne fuskani namiji shi ne mai tsayuwa kan mata da wannan la'akari ne maza suka fifita kan mata , sai dai hakan bai nufin fifiko na zati cikin kowanne hali, bari dai haka ya taqaitu cikin wani ba'arin mas'uliyar zamantakewar yau da gobe wadda mat aba za su iya yin wannan ayyuka ba sakamakon taushin dabi'arsu [2] amma duk da cewa an rufe diya mace kofar zama annabiya ko imamiya sai dai cewa an bude mata qofofin wilayar mai girma, lalle mace na iya zama waliyiya daga waliyyan Allah ta zamanto ma'abociayr karamomi da darajoji madaukaka, kamar yadda aka bude mata qofofin imani da aiki nagari da ilimi da ma'arifa da taqawa da kyawawan halaye har ta jsance misali cikin kowanne fage, daga nan Allah ke buga misali ga muminai maza cikin littafinsa mai daraja misalign kuwa shin he matar fir'auna asiya diyar mazahim, wannan na nuni kan girman mace da matsayinta madaukaki. Kmara yadda qur'ani ke ambaton maza masu tuba haka ke ambaton mata wadanda suka tuba, cikin kyawawan siffofi daban, maza na yin tarayya da mata cikin wadannan faloli, duk da cewa akwai kyawawan siffofi da mazaje suka kebanta da su koma bayan mata , kamar misalign jarumta da girman da kyauta, amma saboda kiyaye mata daga lalacewa sai aka rinjayar musu da siffofin tsoro da rowa da rashin girma. Kamar yadda ya zo cikin hadisai masu daraja, shi ubangiji shi ne mafi sanin halittarsa da kuma ruhiyar mazaje da mata , dukkanin abin da y ace da dukkanin abin da ya hukunta shi ne gaskiaya, kan haskensa ake fassara abubuwa ake kuma warware matsaloli cikin rayuwa. Idan ubangiji ya fifita mazaje kan mata to yayi hakan ne kan hikima , kamar yadda ya fifita annabawa wasu kan wasu.
Ubangiji matsarkaki na cewa:
الرِّجَالُ قَوَّامُونَ عَلَى النِّسَاءِ بِمَا فَضَّلَ اللهُ بَعْضَهُمْ عَلَى بَعْض وَبِمَا أنفَقُوا مِنْ أمْوَالِهِمْ فَالصَّالِحَاتُ قَانِتَاتٌ حَافِظَاتٌ لِلْغَيْبِ بِمَا حَفِظَ الل[3]ه
mazaje sune masu tsayuwa kan mata da abin da Allah ya fifita sashensu kan sashe da kuma abin da suka ciyar daga kudadensu mataye salihai masu biyayya masu kiyaye gaibu daga abin da Allah ya kiyaye.
kasantuwar an bawa mazaje tsayuwa koma bayan mata, bai kasance al'amari mara hikima da manufa ba daga ubangiji cikin fifita sashe kan sashe, kadai dai hakan ya faru ne sakamakon zurfafawa da hikima cikin tsara al'amuran dan adam wadda suka ginu kan ilimin Allah, larurar miqa tsayuwa ga mazaje koma bayan mata shi ne cewa lalle su maza ne suke daukar nauyi iyali wajen ciyarwa da kai kawo cikin sanyi da zafi don sama musu abin da za su rayu, da sadaukar da dukkanin qoqarinsu don ganin hakan ya tabbata, su ne suka fi kowa sanin ya ya za'a tafiyar da sha'nin gida da warware dukkanin matsalolinsa, saboda haka tsayuwa ta zama haqqin namiji a dabi'ance hakama a hankalce, sannan kuma ita tsayuwar ta fi dacewa da halittar da namiji ta zahiri da badini, dalili kan haka a hankalce bai fita daga da'irar abubuwa hudu:
1-ko dai mace ta zamanto tana cin gashin kanta da kebanta da tsayuwa kan al'amuranta koma bayan maza, sai dai cewa ba'a rinjayar da hakan ba saboda rashin dacewar tsarin halittarta da hakan.
2 – ko kuma suyi tarayya cikin tsayuwa shi da ita, sai ya lazimta rashin tsari da doka da tabarewar rayuwar aure da yawan samun sabani da danne haqqoqi.
3 – ko kuma ya zamanto shi da ita ba wanda zai tsaya kan wani kwata kwata, wannan kuma ya sabawa abin da dabi'a ta hukunta cikin tsara rayuwa zamantakewa da dan adamtaka.
4 – ko kuma dai namiji ya kebanta da tsayuwa kan al'amaurn mace koma bayan ita macen, wannan shi ne abin da dama muke nema, kamar yanda wahayi ya bayyana hakan:
الرِّجَالُ قَوَّامُونَ عَلَى النِّسَاءِ بِمَا فَضَّلَ اللهُ بَعْضَهُمْ عَلَى بَعْض
( maza sune masu tsayuwa kan mata ) lalle ya na dacewa da dabi'ar dukkaninsu, shi ne abin da zai lamunce rayuwa mafi daraja da natsuwa da kwanciyar hankali.
عن الحسن بن عليّ (عليهما السلام) ، قال : جاء نفر من اليهود إلى رسول الله (صلى الله عليه وآله)فسأله عن مسائل فكان فيما سأله : أخبرني ما فضل الرجال على النساء ؟ قال النبيّ (صلى الله عليه وآله) : كفضل السماء على الأرض ، أو كفضل الماء على الأرض ، فبالماء تحيى الأرض ، وبالرجال تحيى النساء ، لولا الرجال ما خلق النساء ، لقول الله عزّ وجلّ : ( الرِّجَالُ قَوَّامُونَ عَلَى النِّسَاءِ بِمَا فَضَّلَ اللهُ بَعْضَهُمْ عَلَى بَعْض ) ، قال اليهودي : لأيّ شيء كان هكذا ؟ قال النبيّ (صلى الله عليه وآله) : خلق الله عزّ وجلّ آدم من طين ، ومن فضلته وبقيّته خلقت حوّاء ، وأوّل من أطاع النساء آدم فأنزله الله من الجنّة ، وقد بيّن فضل الرجال على النساء في الدنيا ، ألا ترى إلى النساء كيف يحضن ولا يمكنهنّ العبادة من القذارة ، والرجال لا يصيبهم شيء من الطمث ، قال اليهودي[4] : صدقت يا محمّد
1-An karbo daga hassan dan ali (as) ya ce: wasu mutune daga yahudawa sun je wajen manzon Allah (saw) sai suka tambayi manzon Allah (saw) cikin abin da dayansu yay i tambaya: ka bani labari game da fifikon maza kan mata ? sai manzon Allah ya ce: fifikon maza kan mata misalin fifikon sama kan qasa, haka ma kamar fifikon ruwa kan qasa, da ruwa ne qasa ke rayuwa, ba da ban maza ba da ba'a halicci mata ba, saboda fadin Allah: ( maza sune masu tsayuwa kan mata da abin da Allah ya fifita sashensu kan sashe ) sai wannan bayahude ya ce: saboda mai ya zama haka ? sai annabi (saw) ya ce: yayin da Allah ya halicci adamu daga tabo daga ragowarsa ne Allah ya halicci hauwa'au, sannan farkon wanda ya biyewa mace shi ne adamu (as) sai Allah ya sauko da shi daga aljanna haqiqa ya bayyana fifikon maza kan mata cikin duniya, ashe ba ka ga cewa mata na yin jinin haila ba da bai basu damar yin ibada saboda qazantar da suke ciki, maza wani abu daga jinin haila bai shafarsu, sai wannan bayahude ya ce: kayi gaskiya ya muhammadu.
ya zo cikin tafsirin aliyu dan Ibrahim qummi:
الرِّجَالُ قَوَّامُونَ عَلَى النِّسَاءِ بِمَا فَضَّلَ اللهُ بَعْضَهُمْ عَلَى بَعْض وَبِمَا أنفَقُوا مِنْ أمْوَالِهِم
فَالصَّالِحَاتُ قَانِتَاتٌ حَافِظَاتٌ لِلْغَيْبِ بِمَا حَفِظَ اللهُ
( maza sune masu tsayuwa kan mata da abin da Allah ya fifita sashensu kan sashe da abin da suka ciyar daga dukiyoyinsu ) ma'ana Allah ya farlantawa maza ciyarda mata, sannan kuma ya yabawa mata cikin fadinsa: (mata salihai masu biyayya masu tsare gaibi bisa abinda Allah ya tsare su ) ma'ana masu tsare kawukansu idan mazajensu sun faku.
وفي رواية أبي الجارود عن أبي جعفر (عليه السلام) في قوله : ( قانتات ) أي مطيعات
2-ya zo cikin riwayar abi jarud daga baban jafar(as) cikin fadin Allah mata masu ibada sai imam(as) yace ma'ana masu biyayya ga mazajensu.
Duk da kasantuwa fifikon namji sai dai cewa haka baya nufin cewa an gabatar da shi kan mace cikin kowanne hali, haqiqa mafi karamcin cikinku sune mafi taqawar cikinku, saboda haka abin lura shi ne taqawa, idan mace ta yi aiki da abin da Allah ya umarce ta, lalle itace mafi daraja daga namjin da bai aiki da nauyin da ka dora kan wuyansa ba, sannan wannan bai kore fifitar mazaje cikin kasantuwarsu masu tsayuwa kan mata.
قال رسول الله (صلى الله عليه وآله) : ما من رجل رديء إلاّ والمرأة الرديّة أردى منه ، ولا من امرأة صالحة إلاّ والرجل ( الصالح ) أفضل منها ، وما ساوى الله قط امرأة برجل إلاّ ما كان من تسوية الله فاطمة بعليّ (عليه السلام) وإلحاقها به وهي امرأة بأفضل رجال العالمين
3 – manzon Allah(saw) ya ce: babu wani lalatacce namiji face ka samu lalatacciyar mace tafi shi lalacewa, sannan babu wata mace saliha face ka samu namiji salihi da ya fificeta, Allah bai taba daidaita mace da namiji ba sai kan fatima da ali (as) da risakar da ita da shi, itace mafi daraja daga mazan dukkanin duniya.
قال رسول الله (صلى الله عليه وآله) : خير رجالكم من اُمّتي الذين لا يتطاولون على أهليهم ويحنون عليهم ولا يظلمونهم ، ثمّ قرأ : ( الرِّجَالُ قَوَّامُونَ عَلَى النِّسَاءِ بِمَا فَضَّلَ اللهُ بَعْضَهُمْ عَلَى بَعْض ) الآية
4-Manzon Allah (saw) ya ce : mafifit mazajenku cikin ala'ummata sune wadanda bas a nuna isa kan iyalansu , sun a tausasa musu bas a zaluntarsu, sannan ya karanta:
maza masu tsayuwa kan mata da abin da Allah ya fifita sashensu kan sashe.
Da tafsirin wannan aya ne zamu fuskanci cewa tsayuwar maza kan mata ba ya nufin nuna fin qarfi da mulki fin qarfi ga mazaje, bari dai ya zo da ma'anar tausayi da nuna qauna da rashin nuna isa da fin qarfi kansu matan, da watsi da zaluntarsu da danne musu haqqoqi, dole namiji ya kiyaye ya guji duk abin da zai kawo bacin ransu, ma'anar tsayuwa kan mata shine namiji ko da yaushe ya kansance b da lura da buqatunsu, haqiqa shi ne ubangijin gida, shi dama ubangijin gida shi ke kare gida, kamar yadda abdul mudallib ya gayawa abrahata yayin ya himmatu da kai hari kan dakin Allah, ya ce masa ni dai ni ne ubangijin raquma na, shi kuma gida na da ubangiji kuma tabbas zai kareshi.
Saboda haka daga cikin abin da ubangidantaka ke hukuntawa shi ne kare gida da ahalinsa, ubangijin gida shi ne mai tsayuwa kan sha'anin gida.
Sannan ina mai kara maimaitawa cewa mai ya fi muni daga mazajen da ke dukan matansu.
Ya zo cikn littafin tahzibul ahkam cewa: yanzu bana baku labari da mafi alherin mazajenku ba ? sai mu ka ce na'am, lalle daga cikin mafi alherin mazajenku shi ne ma taqawa mai tsarkin zuciya mai kyautar hannu, mai lafiyar geffa biyu, mai biyayya ga iyayensa, iyalansa ba sa neman mafaka da waninsa, sannan ya qara cewa: yanzu bana baku labari da sharrin mazajenku ? mu ka ce na'am, lalle daga cikin mafi sharrin mazajenku shi ne maqagi mai yawan alfasha mai ci shi kadai, mai hanawa wanda suka ziyarce shi mai dukan matarsa da bawansa wanda iyalnsa ke fakewa da waninsa, mai sabawa iyayensa
[1] A'araf:189
[2] Haqiqa na tattara hankali na cikin wannan littafi kan wannan ma'ana na tayi maimaita bayani kanta wurare da yawa saboda haka zan kara ma yanzu don ma'anar ta zauna a kwakwaln masu karatu: lalle shi muslunci addeini ne madaidaici bai kuma banbanta mace da namiji ba cikin asalin halittabda mutumtaka ya halicce su daga rai guda kamar yadda qur'ani ya tabbata mana da hakan ya kuma kmsawa wannan rai fajircinta da taqawarta, ya kuma lalle ya rabuata duk wanda ya tsarkake wannan rai daga namiji da mace. Babu banbanci tsakanin mace da miji cikin tushensu saboda dukkaninsu daga adamu da hauwa'u(as) suke kuma babu fifiko cikin nasabobi, babu fifiko face na tsoron Allah(lalle mafi karamcinku wajen Allah shine mafi jin tsoronsa) a wani wajen kuma yace kowanne rai ana jingina mata abin da ta aikata.
[3] Nisa'i:34
[4] Biharul anwar m 100 sh 241