فهرست کتاب‌‌ لیست کتاب‌ها
■ KALMAR TARBIYYA CIKIN HARSHEN LARABCI DA YANDA AKA YI 4
■ FASALI NA ( 2 ) 24
■ AUREN DABI'A 24
■ FASALI NA 3
■ FASALI NA 4 73
■ FASALI NA 5 131
■ FASALI NA 6 176
HAQQOQIN DA MA'AURATA SU KAYI TARAYYA CIKI 177
1 – HAQURI 178
2 – KAMEWA DAGA ZALUNCI DA CUATARWA 179
HAQQOQIN MATA 180
CIYARWA DA YALWATAWA 185
TAUSAYAWA DA KAMEWA DAGA ZALUNCI 187
KAMEWA DAGA BARIN DUKA MAI CUTARWA 187
UMARNI DA KYAKKYAWA DA HANI DA MUMMUNA 193
GARKUWA 196
8 – KYAUTATAWA : 196
9 - KYAWUNTA ZAMANTAKEWA 197
3 – TAUSAYAWA MIJI : 208
4 – HIMMATUWA DA KULA DA CIKIN GIDA DA KAYYAKINSA : 209
5 - HIMMATUWA CIKIN SAUKE HAQQOQI 209
6 – JIMA'I 210
7 - ADO 213
8 – KAMEWA CIKIN MAGANA : 219
SHUGABANTAR IYALI 225
DALILAI DA SUKE SANYA DAWWAMAR AURE 227
1 – SON JUNA 228
2 – YAWAITA AIKATA ALHERI: 228
4 – SANYA FARIN CIKI: 229
5 – BIYAYYA DA NEMAN YARDAR MIJI: 230
6 – KIYAYE MUTUNCI DA DUKIYA : 230
7 – TAIMAKO DA TALLAFAWA 230
8 – TARBAR MIJI DA KYAWUNTA BANKWANA DA SALLAMA : 231
9 – KALAMIN AQIDOJI MAI KYAWU DA QARFAFAFFEN FURUCI. 232
10 – KARBAR UZURI DA YIWA JUNA UZURI : 232
11 – BINSU SANNU SANNU CIKIN KOWANNE HALI : 233
12 – KYAWUNTA LAFAZI CIKN KOWANNE YANAYI : 233
13 – RASHIN SAURARON KYAUTATA AIKI DARI BISA DARI 233
14 – RASHIN IKON DAUKAR NAUYI A RAYUWANCE : 234
15 – RASHIN GORI KAN MIJI : 234
16 – RASHIN QAURACEWA AL'AMARIN SHIMFIDA: 235
17 - YIN SHAWARA DA MATA BANDA BIYE MUSU: 235
18 – TAKA TSAN TSAN DA KUMA FARKAWA : 238
19 – HANKALTA 239
20 - MIJI SHI NE MUTUNCIN MATARSA 240
21 – KISHI 240
22 – TAIMAKEKENIYYA 242
23 – DADADAWA IYALI 243
27 – WATSI DA BOAKANCI DA TSAFE TSAFE : 244
28 - HIDIMA MADAWWAMIYA 245
29 – GODIYA 246
29 – QAUNAR JUNA 247
TSINTUWA GUDA BIYU GIDAN ALI DA FATIMA (AS) 248
■ FASALI NA 8 252

SHUGABANTAR IYALI 225

SHUGABANTAR IYALI  

Iyali wata `yar qaramar duniya ce da ke buqatar shuga da zai jagoarnce ta da daukar nauyin tafiyar da al'amauran da ke tattare da ita, sannan daukacin wadanda ke qarqashin wannan iyali su yi masa biyayya, idan kuma haka ya gaza samuwa to al'amura za su kasance kara zube babu doka da jagoranci, saboda haka ne ma tsarin  zamatankewa ya larurantu da ayyana shugaban da zai jagoaranci iyali, sannan anyi ittifaqi kan cewa wanda kadai zai dauki wannan nauyi shi ne miji, kamar yanda mafi yawanci dokokin tarrayar turai suka jingina kai, bawai kadai `ya `yane ya wajaba su yi biyayya gare shi ba bari hatta ita kanta matar ya zama tilasa tai masa biyayya da da'a, kamar yanda hakan ya zo cikin shari'ar muslunci, lalle ita shari'a ta sanya maza su zama masu tsayuwa kan mata.

الرِّجَالُ قَوَّامُونَ عَلَى النِّسَاءِ بِمَا فَضَّلَ اللهُ بَعْضَهُمْ عَلَى بَعْض وَبِمَا أنفَقُوا مِنْ أمْوَالِهِمْ 

Dokar qasar faransa mai lamba 13 sakin baka 214 ta kusa zama tarjamar aya ta 34 cikin suratu nisa'i, ta yadda dokar ke cewa:  lalle wajibi kan miji ya kare matarsa, sannan ita kuma matar ya wajabta kanta ta yi masa biyayya, sannan doka ta biyu kuma na cewa (ya lazimta kan mace ta zauna tare da mijinta sannan ta bishi duk inda ya zaba zai zauna, sannan ya zama tilas kan namiji ya yi mu'amala da matarsa,  ya bata dukkanin abin da ta ke buqata wanda ya zama na larura a rayuwance  gwargwadon ikonsa da halinsa)

wannan ma'ana na gudana cikin al'ummar da ke riskar da da ga ubansa, amma cikin tsarin uwantaka, tsarin da ke risker da da ga mahaifiyarsa, lalle jagorantar iyali na hannun mace kamar yadda muka kawo haka baya.

Ya na bayyana gare ni kamar yadda ya zo cikin riwayoyi  da ingantaccen tarihi,  jagorantar gida a jumlace na hannun uba, shi ne ubangijin gida, sai dai cewa cikin batutuwa cikin gida ya na iya fawwala lamari zuwa hannun uwa kasantuwar yara sunfi jin maganarta sakamakon tarbiyyarsu da tafiyar da al'amuransu, kamar yadda aka ambaci misalin wannan ma'ana kan sarkin muminai ali (as) da Fatima (as) ta yanda suka hada kai ya zama dukkanin ayyukan wajen na kansa ita kuma ta jibanci ayyukan cikin gida.

na'am  cikin batutuwa  da akai tarayya ya kamata ya nemi shawarar iyalinsa kamar misalin tafiya nesa, cikin ire iren wadannan wurare ya kamata ya nemi shwararsu, sakamkon yin hakan na taka babbar rawa wajen gina kai, sai ya zama ya shawarci dukkanin gabobin iyali tun daga mata har zuwa yara qanana mazansu da matansu, daga qarshe yanke hukuncin da ya dace na hannun mai gida shugaban dukkanini iyalin, daga nan zaka samu lamuntar arziqi cikin iyali da farin ciki, tabbas ni kaina na jarraba hakan  lokuta da daman gaske, godiya tabbata ga Allah  bisa taufiqi da datarwarsa, lalle ni da iyalina mu na jin kan mu daga mafi farin cikin mutane.