فهرست کتاب‌‌ لیست کتاب‌ها
■ KALMAR TARBIYYA CIKIN HARSHEN LARABCI DA YANDA AKA YI 4
■ FASALI NA ( 2 ) 24
■ AUREN DABI'A 24
■ FASALI NA 3
■ FASALI NA 4 73
■ FASALI NA 5 131
■ FASALI NA 6 176
HAQQOQIN DA MA'AURATA SU KAYI TARAYYA CIKI 177
1 – HAQURI 178
2 – KAMEWA DAGA ZALUNCI DA CUATARWA 179
HAQQOQIN MATA 180
CIYARWA DA YALWATAWA 185
TAUSAYAWA DA KAMEWA DAGA ZALUNCI 187
KAMEWA DAGA BARIN DUKA MAI CUTARWA 187
UMARNI DA KYAKKYAWA DA HANI DA MUMMUNA 193
GARKUWA 196
8 – KYAUTATAWA : 196
9 - KYAWUNTA ZAMANTAKEWA 197
3 – TAUSAYAWA MIJI : 208
4 – HIMMATUWA DA KULA DA CIKIN GIDA DA KAYYAKINSA : 209
5 - HIMMATUWA CIKIN SAUKE HAQQOQI 209
6 – JIMA'I 210
7 - ADO 213
8 – KAMEWA CIKIN MAGANA : 219
SHUGABANTAR IYALI 225
DALILAI DA SUKE SANYA DAWWAMAR AURE 227
1 – SON JUNA 228
2 – YAWAITA AIKATA ALHERI: 228
4 – SANYA FARIN CIKI: 229
5 – BIYAYYA DA NEMAN YARDAR MIJI: 230
6 – KIYAYE MUTUNCI DA DUKIYA : 230
7 – TAIMAKO DA TALLAFAWA 230
8 – TARBAR MIJI DA KYAWUNTA BANKWANA DA SALLAMA : 231
9 – KALAMIN AQIDOJI MAI KYAWU DA QARFAFAFFEN FURUCI. 232
10 – KARBAR UZURI DA YIWA JUNA UZURI : 232
11 – BINSU SANNU SANNU CIKIN KOWANNE HALI : 233
12 – KYAWUNTA LAFAZI CIKN KOWANNE YANAYI : 233
13 – RASHIN SAURARON KYAUTATA AIKI DARI BISA DARI 233
14 – RASHIN IKON DAUKAR NAUYI A RAYUWANCE : 234
15 – RASHIN GORI KAN MIJI : 234
16 – RASHIN QAURACEWA AL'AMARIN SHIMFIDA: 235
17 - YIN SHAWARA DA MATA BANDA BIYE MUSU: 235
18 – TAKA TSAN TSAN DA KUMA FARKAWA : 238
19 – HANKALTA 239
20 - MIJI SHI NE MUTUNCIN MATARSA 240
21 – KISHI 240
22 – TAIMAKEKENIYYA 242
23 – DADADAWA IYALI 243
27 – WATSI DA BOAKANCI DA TSAFE TSAFE : 244
28 - HIDIMA MADAWWAMIYA 245
29 – GODIYA 246
29 – QAUNAR JUNA 247
TSINTUWA GUDA BIYU GIDAN ALI DA FATIMA (AS) 248
■ FASALI NA 8 252

17 - YIN SHAWARA DA MATA BANDA BIYE MUSU: 235

17 -  YIN SHAWARA DA MATA BANDA BIYE MUSU:

  dukkanin wanda ya yi shawara da ma'abota hankali zai amfana daga hankalinsu, sai dai cewa mace saboda hikimar ubangiji janibin nuna tausayi ya rinjayi janibin hankali matuqar rinjaya, saboda haka mata ba a shawara da su, ko da ma an nemi shawararsu lalle saboda kasantuwar fifitar tausasawa garesu sai ya zamanto ta ba da shawara zuwa abin da bai da cewa da hankali da lura, sannan riwaya ta zo kan al'amarin yaqi idan aka shawarci mata to tabbas alheri zai koma ga abokan gaba, kasantuwar yanayin yadda ta ke na iya sata ta tsorata, ta kasa zabar janibin jarumtaka da sadaukantaka da gabata a fagen yaqi, haka yawancin mata suke sai `yan kadan daga cikinsu wanda ba'a hukunci da su.

كان رسول الله(صلى الله عليه وآله) إذا أراد الحرب دعا نساءه فاستشارهن ثمّ خالفهن

23 – manzon Allah (saw) ya kasance idan zai fita yaqi sai ya shawarci matansa sannan daga baya ya saba ma ra'ayin da suka zaba.

قال رسول الله (صلى الله عليه وآله)  : طاعة المرأة ندامة .

24 – manzon Allah (saw) ya ce: biyewa mace na tare da nadama.

قال عليّ (عليه السلام)  : كلّ امرئ تدبّره امرأته فهو ملعون ، وقال (عليه السلام)  : في خلافهن البركة

25 – imam ali (as) ya ce : dukkanin namjin da matarsa ke juya shi tsinanne ne, sannan ya ce: cikin sabawa mata akwai albarka.

عن أبي جعفر (عليه السلام)  : لا تشاورهن في النجوى ، ولا تطيعوهنّ في ذي  قرابة

26 – an karbo daga baban jafar (as) ka da ku nemi shawarar mata cikin zaman sirri, ka da ku biye musu cikin al'amarin dan'uwa makusanci.

عن أبي عبد الله (عليه السلام) ، عن آبائه (عليهم السلام) ، قال  : قال رسول الله (صلى الله عليه وآله)  : من أطاع امرأته أكّبه الله على وجهه في النار ، قيل  : وما تلك الطاعة  ؟ قال  : تطلب منه الذهاب إلى الحمّـامات والعرائس والأعياد والنائحات والثياب الرقاق فيجيبها

 27 – an karbo daga baban Abdullah (as) daga babanninsa (as) ya ce: manzon Allah (saw) ya ce: duk wanda ya biyewa matarsa Allah zai kifa fuskarsa a wuta, sai suka ce wacce irin biyewa ? sai ya ce: ta dinga neman izinin ya barta taje gidajen wanka  da tarukan biki da taron bikin idi da wuraren zaman makoki da sanya tufafi shara shara mara kauri shi kuma ya amsa mata.

Wadannan abubuwa duka sun zo nebabin misali da bayani ba'arin masadiq din biyayyar wadda ake zargi da watsi ta b wadda ke janyo shiga wutar jahannama a da yawan lokuta mazaje kan jarrabtuwa da su musammam anwagwaye a lokutan bubkuwa da sukanyi amfani da tufafi na rashin tarbiyya da ake kawo daga qasashen turai wadanda ake yaqartarbiyarmu da su har tsakiya dakunan mu muna halin gafala.

عن أبي جعفر (عليه السلام) ، قال  : لا تخرج المرأة إلى الجنازة ، ولا تؤمّ الخروج إلى الحلية من النساء ، فأمّا الأبكار فلا

28 – an karbo daga baban jafar (as) ya ce: ka da matar aure ta fita zuwa jana'iza, ka da fita zuwa ga ado daga mata, amma idan `yan matane ba matsala.

قال النبيّ (صلى الله عليه وآله)  : لا يفعلنّ أحدكم أمراً حتّى يستشير ، فإنّ لم يجد من يستشير فليستشر امرأته ثمّ يخالفها ، فإنّ في خلافها بركة

29 – manzon Allah (saw) ya ce: ka da dayanku ya sake ya aikata wani aiki ba tare da yin shawara ba, idan ya kasance ya rasa wanda zai shawara da shi to ya yi da matarsa daga baya sai ya saba mata, lalle albarka na cikin sabawa mata.

قال أمير المؤمنين (عليه السلام)  : اتّقوا شرار النساء وكونوا من خيارهن على حذر ، إنّ أمرتكم بالمعروف فخالفوهنّ كيلا يطمعن منكم في المنكر[1]

30 – sarkin muminai ali (as) ya ce: kuji tsoron masharrantan matanku, sannan kuyi taka tsantsan daga mafi alherinsu, idan suka umarce ku da alheri ku saba musu don ka da su yi burin umartarku da munkari.

َ قَالَ رَسُولُ اللَّهِ ص أَرْبَعَةٌ مَفْسَدَةٌ لِلْقُلُوبِ الْخَلْوَةُ بِالنِّسَاءِ وَ الِاسْتِمْتَاعُ مِنْهُنَّ وَ الْأَخْذُ بِرَأْيِهِنَّ وَ مُجَالَسَةُ الْمَوْتَى فَقِيلَ يَا رَسُولَ اللَّهِ وَ مَا مُجَالَسَةُ الْمَوْتَى قَالَ مُجَالَسَةُ كُلِّ ضَالٍّ عَنِ الْإِيمَانِ وَ جَائِرٍ عَنِ الْأَحْكَام

31 – manzon Allah (saw) ya ce: abubuwa hudu barna ne ga zukata: kebanta da mata, jin dadi daga garesu, karbar ra'ayinsu, zama da matattu, sai aka tamabayi manzon Allah (saw) meye zama da matattu ? sai ya ce: shi ne zama da dukkanin batacce daga imani da wanda ya kaucewa hukunce hukunce.2 

وفي وصيّة أمير المؤمنين عليّ (عليه السلام) لولده الحسن (عليه السلام)  : إيّاك ومشاورة النساء ، فإنّ رأيهنّ إلى أفن وعزمهن إلى وهن ، فاكفف عليهم من أبصارهن بحجابك إيّاهن ، فإنّ شدّة الحجاب أبقى عليهن ، وليس خروجهن بأشدّ من إدخالك من لا يوثق به عليهن ، وإن استطعت أن لا يعرفن غيرك فافعل . ولا تملك المرأة من أمرها ما جاوز نفسها ، فإنّ المرأة ريحانة وليست بقهرمانة ، ولا تعد بكرامتها نفسها ، ولا تطمعها أن تشفع لغيره[2]ا

32- cikin wasiyyar sarkin muminai ali (as) ga dansa hassan (as) : na haneka da shawartar mata, lalle ra'ayinsu na kaiwa ga naqasar hankali himmarsu ga rauni, ka kame su daga ganinsu da hijabinka kansu, lalle tsananin hijabi shi ne mafi wanzuwa kansu, fitarsu wajen gida ba ta fi tsanani daga shigar da wanda ba 'a aminta da shi ba garesu, idan ka samu iko kan kasantuwar ka da su san kowa in ba kai ba to ka aikata hakan, ka da ka sake ka malllakawa mace al'amarin da ya wuce kankin kanta, lalle ita mace fure ce mai qamshi ba ta kasance mai gudanar da ala'amarin iyali ba, ka da ta yi sakaci da karamcin kanta, ka da kayi kwadayinta da ceton waninta.[1] Biharul anwar 100 sh 224

[2]Biharul anwar m 100 sh 252